28
by @maidambu41
*❤️🩹SO da CIWO❤️🩹*
®©Ramlat A Manga
Mai_Dambu
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
***
Or
***
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
Dakata hajia💃💃💃💃💃 kin Dade kina Neman inda Zaki sai amintattun jaka, da takalma, sarkoki,masu kyau da quality cikin farashi Mai sauki❓
Ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,wannan gidan na RUMIEE UNIQUE BAG'S GALLARY na budeshi ne saboda na Baku damar siyan jaka,da takalma na Yara Dana manya masu kyau da quality da Kuma saukin kudi cikin aminci daga wajena.masu siyan daya da masu sari duk Muna mataba daku
Muna Kano Muna Tura kaya kowanne state da makotan Nigeria cikin yardar Allah,
Uhmm rigi-rigi ko kun san kayanmu sun iso like bags irin wanda Maamah take amfani da shi, Veils, Shoe's, more and more suna nan dasu...... Let go ❤️🩹💃🏻🐾
*28*
"Innar Ayuba!" " Na'am!" Ta kalli Bintu da fuskartar dauke da Mamaki, "innar Ayuba yarinyar da Ayuba yake so kabila ce." Ta fada tana karantar yanayin Innar Ayuba din, murmushi tayi tana faɗin. "Ina musluma ce?" "Eh musluma ce yar kabilar Ibra na jahar kogi!" "Allah ya tabbatar da alkhairi." "Alhamdulillahi na zata zaki ce a'a ne shima ya damu bai san yadda zai miki magana ba, amma sai gashi kome ya zo cikin sauki da sassauci, Allah ya bar mana ke Innar Ayuba. Allah ya ja kwananki." "Au dama hada baki kuka yi don na yarda." Ta balla mata harara, dariya tayi tana faɗin. "Ai Innarmu ai magana ya kare tunda kin amince." "Allah ya muku albarka."
Ta fada tana murmushi irin na jin dadi, bata taɓa tsintar kanta a ciki ba kamar yau,.domin a duk lokacin da daya daga cikinsu ya bukaci abu, sai sun goyi bayanshi saboda zumunci da kaunar juna da suke ta yarda da Allah kuma tayi imani da shi babu wanda ya isa raba mata kan Yaranta domin Allah ya hade kansu, bata yi zina ba, sannan bata lalata tarbiyyar Yaran wasu ba, bata lalata zumuntar wasu ba, bata ji wani zai samu damar lalata mata nata yakinin haka yasa duk lokacin da suka tsayawa juna domin dayansu sai ta ji kamar tafi kowa sa'a. Kwananta uku a Kano ta dawo Rano, abin mamaki shine yadda aka gyara mata gidanta, Bintu da ta rakota sai dariya take tana faɗin. "Innar ayuba, danki dai ya zama ɗan kwallon gaske domin ya san yadda zai sayi zuciyar Innarshi." "Bintu ni kakarki ce?" "Innarmu tunda bani da kakar kece kakar tawa." Dake ta kofar baya suka shiga gidan cikin gida baa san tazo ba, sai da ta gama ta nufi cikin gidan Bintu tana dafa mata abinci tunda zo da miya, cikin gidan ta nufa suna zaune a filin tsakar gida, masu surfe nayi masu hira nayi, can Inna Lantana ce tana wankan Ma'aruf sai Labibah da ta kurawa kofar gidan idanun kamar tana jiran wani, domin tayi nisa cikin tunani. "Labibah!" Innar ayuba ta kira sunanta. Da sauri ta juya tana kallon Innar Ayuba, wani ihu ta saka tare da rantawa a guje ta rungume Innar, tana faɗin.."Nayi kewarki." "Ina haka Labibah ta." "Innarmu sannu da dawowa, ina Aunty Bintu!" "Tana cikin gida!" Sake Innar Ayuba tayi ta wuce ɓangaren, har cikin zuciyar Innar ayuba tana jin ba dad'i, a hankali suka shiga gaisawa cikin girmamawa da mutuntawa. "Lantana yanxu a waje kike wanke bawan Allah nan, so kike sanyi ya shige shi." Murmushi tayi tana faɗin. "Yau ce kawai Innar Ma'aruf, ba zan sake ba tunda kika tafi yake mitan Innarmu taki dawowa ta bani abin dad'i!" Shima yaron sai dariya yaƙe yana tsalle, Innarsu ta dawo Haƙa yaran gidan. Ta shiga kofa kofa aka gaisa da juna, sannan ta wuce bangarenta, tsarabar da tazo da shi, jaka jaka ta rabawa kowa na shi, tsakanin Bintu da Labibah magana suke amma Labibah sai kuka take bata tanka su ba, ta kuma fita ta kira kowani Yaro sannan ta basu na kofarsu. "Aunty na farko na san anyi kuskure, kuma anyi laifi mai girma ki lura da dalilin da zai saka nayi magana. Da ina da ikon dawowa da hannun agogo da na yi haka domin gyara wancan barakar, amma duk abin da Allah yayi mai kyau ne ba ni da rabon hada alaka da ku ne,.na gode sosai Aunty Bintu." Daga haka ta mike zata fita Innar ayuba ta mika mata wata jaka, "wannan naki ne wannan nasu Laraba da Kafifah, Allah ya miki albarka." Hawaye ne ya zubo mata tana faɗin. "Innar Ayuba, duk wannan kyautatawar zuciyata bashi take bukata ba, kin san abin da nake so." Ta fada hawaye na zuba a idanunta. "Ban damu idan duniya zata juya min baya ba, ban damu idan kowa zai guje ni ba. Amma na damu da abinda zuciyata take so. Innar Ayuba tun daga lokacin da na fahimci girma da zunubin da aka aikata muku, duk dare zuciyata sai tayi barazanar tsayawa aiki. Dakyar nake kokuwa da rayuwata domin na rayu koda zan samu amincewar Ayuba da Ya Ibrahim." Kanta ne ya sara ta dafe goshinta kayan hannunta suka zubo. Lumshe idanunta tayi tana murmushi ta ce mata. "Innar Ayuba, idan aka wayi gari babu ni ki gayawa Yaya Ibrahim naso shi a boye na so shi a fili na kuma mutu ina sonshi." Ta durkusa ta kwashe kayan tana ganin duhu-duhu a idanunta, dakyar ta isa bakin kofar tana jin kamar ba zata iya bangarensu ba. Kome na rabe mata bibiyu.
Har ta isa bakin kofarsu ta saka kafa amma bakiɗaya ta tafi bata kara sanin me ya faru ba, ihun Laraba da Jamilah ya ja hankalin Mutanen gidan aka firfito tare da budar asibiti da ita idan ka ga Yadda Dalhat dan Mama Yaron wurin Sahura ya dauke ta zaka ɗauka Baby ce, jin haka Bintu ta ce mishi ya zo ta kai su a mota, kuka Laraba take tana karawa. Shi sharri dan aike ne, duk yadda ka tura shi zai dawo maka abun da ya faru kenan, sun aika amma ta dawo musu ta yadda basu zata ba, lokacin da suka isa babban asibitin Rano, ganin case din suka ce dama tana fama da barazanar bugun zuciya so su wace da ita asibitin Malam Aminu Kano ko Asibitin Murtala. Wanann tashin hankalin yasa Bintu ta bar Rano babu shiri aka wuce da ita asibitin Malam Aminu Kano, inda tayi ta kiran nurse da ta sani da likitocin da tayi aiki da su, su hudu ne, Inna Laraba, Dalhatu, sai ita Bintu da Labibah. Sun isa asibitin akan lokaci abin ka da mutane masu hadin kai suna ganinta da Labibah suka karbeta, Yaran Innar ayuba akwai halin girmama da dattako duk inda suka zauna sai sun bayyana halin Innarsu haka yasa mutane dayawa kafin auren Bintu suka yi sha'awar aurenta domin halinta da tarbiyyarta, wannan yasa koda ta tashi aure ta samu kara da gudunmawa me yawa gashi mota guda suka cika aka je daurin auren, suka kuma mata karamar walima a nan asibitin, kishi irin na mijinta yasa ta bar Malam Aminu Kano,.ta koma wata karamar asibiti kuma private da yake akwai kudi me kyau da suke bata.
Tunda aka shige da ita sai kuka Inna Laraba take tana jin kamar ta bada rayuwarta domin ta Labibah din, kasancewar ita uwa ce bata ga laifin Innar Ayuba ba, duk wanda aka mishi abin da aka yi dole ya fusata. Ya kuma ko hada iri da su. Duk abinda ake bukata duk Bintu ta saya sannan ta cewa Dalhatu. "Dan Mama kana nan ko muje gida a ka kawo muku kayan amfani?" "Eh muje Aunty B!" "Innah bari muje gida na hada mishi kaya ya kawo kafin gobe, sannan idan ya kawo zaki biyo drive ki kwana gobe sai mu dawo tare." Shiru tayi kafin ta ce mata. "Bintu ku je Allah ya muku albarka, amma ni zan zauna a jikinta ko naje ba zan iya barci ba!" "Tow shi kenan yanzu dai dawo." Suka bar asibitin duk wani abin bukata sai da Bintu ta haɗa musu, sannan da abinci Dalhatu ya kawo musu yana ta godiya, wannan abin da suka yi ba kowa bane zai iya musu. Haka ya kawo asibitin shi ya tafi bangaren da maza suke kwana, yayi salolin kanshi, sannan ya koma wurin Innar ko zaa bukaci wani abu, har wurin karfe tara kafin likitocin suka fito suna masu wuce su, Kallon Innah Dalhatu yayi ya ce. "Bari ka tambaye su." "Doctor wani hali take ciki Yarinyar?" "Zamu yiwa Nurse Bintu bayani amma yanzu ma an samu kanta zuwa gobe za a mata ward." "Shi kenan!" Ya fada yana koma ya gayawa Inna Laraba, itama cewa tayi . "Alhamdulillahi Ubangiji ya bata lafiya." Ta zauna tana share kwalla da yake zuba mata, "ka tafi ka kwnata ni zan tsaya anan" "A'a Inna Laraba Labibah yar uwata ce, zan taya ki kwana." Haka suka kwana a wurin ita Inna Laraba ganin zata yi asarar daren ta shimfida abin sallah, a karon farko a rayuwata da ta mika lamarinta da na Yarta ga Allah, ta kuma bawa Ubangiji zabi akan Yarta. Haka ta kasance har wurin asuba Dalhatu da yake barci bata tashe shi ba, ta bar shi yayi barcin domin ta haka zai wuta daga gajiyar da ya kwaso daga makaranta zuwa asibiti. Tana zaune har aka kira Allah farko a kunnenta aka yi shi, haka kawai take jin ai innar Ayuba bata samu yadda take so ba, sai da ta hana idanunta barci haka yasa itama ta daura dammaran zama irin Innar Ayuba. Ko zata samu rayuwa me kyau tunda aka kai wannan matakin Innar ayuba bata yi approved din bukatar Labibah ba tabbas babu hanyar da zata amsa gara ta nimawa yarta sassauci.
Wurin karfe takwas Bintu ta zo, ta biya abin bukata. Sannan ya jira har likitan yazo suka yi magana, kasa gayawa Inna Laraba tayi zuciyar Labibah ya tabu ainun, sai ta ji bakiɗaya basu yiwa Inna Laraba adalci ba, soyayyar Ibrahim ce silar haka, don ma ana tunanin za ayi mata aiki a zuciyar domin akwai wani jijiya da yayi rauni. Zama tayi a kusa da Inna Laraba, cikin wani irin yanayi mara dadi, muryanta a sanyayye kamar ta innar Ayuba, ta ce. "Innarmu!" Kallonta Inna Laraba tayi idanunta cike da kwallar nadama. Ta cigaba da cewa. "Labibah za mata aiki a zuciyarta." "Aiki a zuciyarta!" Ta fada tana dafe kirjinta da taji yayi wani irin bugawa. "Innalillahi wainnalihir rajouna! Fadimah hakki ce ko? Alhakkin Bello ce ko? Sakamakon ukubar yan uba ko? Yau Labibah take girba?" Rike hannunta Bintu tayi gam, girgiza kai tayi tana faɗin. "Ciwo ce daga Allah, ciwo ce Allah ya daura mata shima kuma ciwo ne Allah ya daura mishi. Wanann tdakaninta ce da zuciyarta. Amma tsakanin bawa da mahaliccinsa wani bawan bai isa ya shiga ba. " Wani irin kuka Inna Laraba ta fashe da shi tana faɗin. "Yau naga illar sharri na tura shi ya dawo min cikin inda ban zata ba, ciwon zuciya ga Labibah me yasa bai daura mana ba, mune muka muku laifi ba ita ba ce. Wani idanun zan kalli Boɗɗo." Ta fada tana kuka, "itama tana zuwa an jima kadan, zasu zo da Baba Bashir idan yazo zai saka hannu mun hada kudin aikin da za a mata zan koma gida yau ina hutun aikin wata shida da nayi ne, xan yi abinci kafin su iso, tunda gidan babu nisa da asibitin nan."
"Fadimah zata tashi kuwa." Murmushi tayi tana faɗin. "Zata tashi Innarmu zata warke tai aure ta haifa mana Yaranta masu kyau da sanyin halinta." Kara rike Bintu tayi tana zubda hawaye ta ce mata. "Kin san labibah ita daban ce a cikin Yarana, sanyinta da halinta daban yake don Allah ki yafe min." Girgiza kai Bintu tayi tana murmushi ya ce mata. "Innarmu ni baki min kome ba, domin Innar ayuba ta gaya mana kada mu dauki maslahar wasu mu saka a ransu zai iya jagorantarmu da kiyayya da gaba me tsanani, wanda haka zai iya haifar da damuwa ga al'ummar da zamu haifa gaba. Idan har Al'ummar mu suka taso da tsana da kiyayar juna Allah zai kama mu da laifin raba zumunci." Taya suka yi barci Innar Ayuba ta musu wayo har haka? Suna ina Innar Ayuba ta gina yafiya da afwa akan Yaranta, suna can suna bakin ciki da cigaban Yaranta. Dubi Bintu kamar bata haifi dan shekara takwas da yar shekara biyar ba, yarinya ce karama me cike da kuruciya zuciyarta fal da farin ciki da taimakon nata, hakuri da juriya. "Bintu mun gode;" "ba kome Innarmu! Laa" ta fada tana murmushi, a hankali take tafiya kamar wata cartoon, tana wani blush tare da murmushi me haɗe da wani dan karen kunya. Tun kafin ta isa gare shi, ya bude mata hannu. Isa gare shi tayi cike da kunya ta shige tana wani irin ihu me cike da murna, bata zaci zai zo ba sai gashi domin daren jiya ta gaya mishi case din Labibah tana kuka a waya sai ga shi yayi sammako. "Shi ne baka gaya min ba!" Rungume ta yayi yana faɗin. "Lady Fadi ai ba zan iya gaya miki ba, ki kasa barci." Murmushi tayi tana faɗin. "Ai kuwa dai gashi nan kazo ba zata." Murmushi Inna Laraba tayi tana share kwalla da yake zubo mata. Ina ma ace Yaranta daya ya samu irin wannan rayuwar babu arabi babu boko Yaran da ko ayi aurensu matsalar gidansu kara gaba yake. Sake ta yayi ya isa wurin Inna Laraba ya gaida ta da mai jikin,sannan a lokacin ya samu likitan aka canza mata dakin da za a kaita bayan aikin. Gida suka dawo Bintu kamar ta raba kanta biyu, tunda suka tarbi juna da Barka da zuwa sannan aka shiga kitchen suka sheka girki ya kalleta yana rungume da ita hannunshi yana kugunta ya ce mata. "My lady;" "na'am My Man!" "Ina son na gyara can bangaren." "Zaka yi aure ne?" "Waye ni?" "Kai Mana Mustapha!" "A'a Innata xan dawo da ita nan, tana bukatar." "Da gaske fa?" Ta tambaye shi cike da farin ciki. Dukar kirjinshi tayi cike da fara'a ta ce mishi. "Innarka Innata ce, don haka kada ka kara tambayata zaka dawo da ita, Yaranma zasu yi farin ciki sannan zasu taso da kaunarta a ransu idan baka manta ba six months ago kasan Arif har sign language ya fara koya a wurinta, Inna zata rike mu ni da Yaran bakiɗaya." Sumbatar wuyarta yayi yana me faɗin. "Na sani shi yasa nace bari na tambaye ki!" Yana mata abin da dole ta biye shi a zauna lafiya. "Hmm! Yaya tafi ka bar ni nayi aiki!" Jinginata yayi da firjin din kitchen din, ita kanta tasan tayi missing dinsa, anan suka shagala sai da tuwon ya fara kauri ya sake yana tari, suka fashe da dariya, sannan suka kwashe abincin suka gyara kitchen din wurin karfe daya, tare suka yi wanka, bayan sun yi shagalinsu sannan suka nufi asibiti bayan sun yi sallah azahar. A motar Innar Ayuba aka tawo,, Baba Bashir bai zaci lamarin ya kai haka ba.