Chapter 1
KAMPALA ESTATE
NA
BILKISU GALADANCHI
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Da sunan Allah me rahama me jinƙai Rabbu samawati ka sanya alkhairi da albarka a cikin wannan rubutun da zanyi, abin da zai cutar da Al'umma ta Allah ka hanani rubutawa Alkhairin da al'umma zasu amfani dashi Allah ka bani ikon rubutawa Ameen.
NASAN WASU ZASUCE MEYASA ANTY BILLY TA KE ƊAUKAR BANGAREN RUBUTU DA KALMOMI MASU WUYAR FAƊA TO KADA KU ƊAUKA NA CANJA NE INA NAN AKAN BAKANA NA ƘI DA KUMA YAƘI DA RUBUTUN BATSA HAR ABADA. WANNAN AL'AMARIN SHINE DAMUWAR MU, SHINE MATSALARMU SHINE GURƁACEWAR TARBIYAR MATA HAR MA DA MAZA, DUK WANI RUBUTU DA ZANYI AKWAI KODA KASO 30 NA ABINDA YA FARU DA GASKE A CIKI KUMA INA YIN RESEARCH SOSAI KAFIN RUBUTU SO KU BIBIYA TUN DAGA MATA HAR MAZA MASU AURE DA MARASU AUREN DUK ZAI AMFANEMU BAKI ƊAYA SON SO.....
01.
Tun a sararin samaniya daya karkato da jirgin zuwa sakkowa wani irin nishaɗi ya mamaye ilahirin zuciyarsa, Nigeria gida ce kuma komai lalacewarta tafiye masa kowace ƙasa zai je, tuƙin jirgi abu ne da yafi so sama da komai a rayuwarsa duk da rashin wadataccen lokacin da baya samu, lokacin da tayar jirgin na gaba suka fita ya saita giyar sauka yin landing sai ya faɗaɗa fara'arsa, zuwa sanda tayar jirgin ta bada wani soft landing a cikin tsananin ƙwarewa sai a hankali ya soma cin burki tare da lumshe ido, tsayawar jirgin cak ya sanya a wannan karon da ya murmusa sai da haƙwaransa suka bayyana cikin lumshe ido da buɗewa ya kalli gabansa tare da furta "Alhamdulillah." Kafin ya fara zare hular kansa da sit belt yana nuna tsananin gajiyawa, co-pilot da suka tuƙo jirgin tare ya kallesa yana murmushi kafin ya ce "Alhamdulillah Captain Leo we are home." Dariya me ɗan sauti ya yi kafin a shagwaɓe da muryarsa me faɗi ya ce
"Alhamdulillah zanga Nannyta." Dariya Captain Munir ya yi sannan ya ce
"Nannyta's Captain ba, kwanan nan zan huta da maganar ta ai." Yana miƙewa ya ce
"Sai na kwana biyu a garin nan ai, idan naje can ma ba wani daɗewa zan yi ba that old lady ban iya fitinar ta zan gaisheta ne kawai in tamun kitso zan dawo Lagos." Captain Munir ma ya miƙe yana dariya ya ce
"Kunfi kusa ai, nima zanje kano fa but bazan daɗe ba zan dawo yaushe zaka tafi mu tafi tare." Yana ragewa tie ɗinsa matsewa ya ce
"Captain I'm going there by road banida lokacin jirgin nan na gaji ya kamata inga garuruwa ai." Captain Munir ya ce
"Ya kamata gaskiya mu je da motar." A gajiye ya ce
"Muyi waya dai yanzu gida kawai nake so lemme change kawai sai mu doshi gida." A haka suka nufi changing room suka yi freshen up sannan kowannensu driver ya ɗaukesu suka nufi gida don dukkansu isowarsu Nigeria sun ɗauki annual leave wasu pilots ne zasuyi piloting jirgin back to Uk.
A matuƙar gajiya yake sanda suka iso wawakeken Estate ɗin a ata gabanshi an rubuta KAMPALA ESTATE da manyan manyan baƙi a jikin wani boad me ruwan zaiba me asalin kyau da faɗi rubutun da zallan ruwan zaiba aka yishi da kuma gold ya haska sosai ya ƙayatar, zallan gate ɗin Estate ɗin kadai abin kallo ne bana wasa ba kana ganin estate ɗin zaka tabbatar mazaunin masu da shi ne, ko dama ba'a gaya maka ba ka san Lekki babbar unguwa ce a birnin Lagos wacce sai wane da wance. Kallo ɗaya securities ɗin suka yiwa motar sa suka wangale musu gate ɗin suka kutsa zuwa ciki. Estate ɗin manya manyan gidane ne a ciki irin gidajen da suke amsa sunansu gidaje na manyan masu kuɗi, Akwai wanda suke biyan haya akwai wanda saya suka yi da kuɗinsu, haya a irin wannan Estate a birnin lagos zai iya kaiwa 30.M a shekara, basa kuma karɓar kuɗin shekara su idan zaka shiga magana ce ta biyan kuɗin shekara biyu haka zuwa sama, wanda kuma suka saya ku daina tunanin hala nawa suka biya kafin suka mallaki gida a cikin Estate ɗin??? Ciki sosai suka shiga har gaban wani gate ƙarami haka zubin na turawa a kaf manya manyan gidajen dake cikin Estate ɗin ba wanda ya kai wannan girma da tsari, suna dosowa gate ɗin ya yi scanning na plate number da kuma motar sannan ya buɗe kansa suka kutsa ciki. Driver ya sakko da sauri tare da guad ɗin guda ɗaya, wanda baya tuƙin shi ya buɗe masa motar ya ɗan matsa baya kaɗan, Idonsa a lumshe ya ɗan ɗago ya kalli wurin face expression ɗin sa yana nuna ohhh har mun ƙaraso? Ƙara lumshe idon sa ya yi ya ƙara kishingida na kusan 7mns kafin a hankali ya ɗago kansa ya miƙe zaune ƙafarsa ɗaya ya sakko da ita sannan ya kuma cillo ɗayar waje ya sakko cike da gajiya, Baƙin wando ne a jikinsa na kampanin Mara choe da shirt blue black round neck da short sleeve ita ma kampanin mara choe, agogonsa na kampanin Rolex me asalin ruwan diamond pcap ce a kansa baƙa amma ya mayar da gabanta baya hannunsa riƙe da battle water, ƙafarsa Sandal ne brown da black kampanin nike, kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar da abubuwa biyu, na farko dai zaka fahimci cewar hutu ya nemawa kansa matsuguni a wurin na biyu kuma shine gajiya don duk ya nuna a yanayinsa. A hankali ya soma takawa sai kuma ya tsaya ya na kallon apartment da ke kallon nasa, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya kalli ɗayan body guad ɗin ya ce da ƙatuwar muryarsa
"Who sold that apartment?" Ya ƙarashe maganar yana nuna apartment da ke dubin nasan da battle water dake hannunsa." Body guad ɗin a cikin ladabi ya ce
"Sir i think rent ne suka biya" Ɗan taɓe baki ya yi sannan ya ce "When?" A hankali Guad ɗin ya ce "Last 2month sir." Kafaɗunsa ya ɗan ɗage sannan ya juya zuwa cikin gidan a bakin ƙofar ya tsaya ya ware hannayensa ƙofar ta gama scaning sannan ta buɗe a hankali ya tura ƙafarsa ciki ɗauke da sallama a bakinsa can ƙasar maƙoshi kamar akwai wani a gidan alhalin ba kowa cleaners ne kuma yasan sun tafi tunda tun safe suka zo. Kai tsaye bedroom ɗinsa ya wuce ya ɗaura gorar ruwan akan makeken mirror na bedroom ɗin, yatsar sa ya kai ya shafi top na mirror ya ƙurawa yatsar ido yana yatsine fuska kwata kwata cleaning ɗin be masa ba wannan wane irin shirme ne? Ɗakin yabi da kallo sai yatsine fuska yake da sauri kuma ya koma yana zagayen katafaren gidan, shifa mutumin tsafta ne irin na ƙwaƙwaf ɗinnan ya zasu zo su masa wannan shirmen da sunan cleaning? Tsaki ya ja sannan ya koma cikin ɗakin da ke Upstairs kai tsaye wurin wani ɗan ƙofa yabi ya shiga ciki ya fito daga shi sai boxers na kampanin Calvin Klein fari ƙal ya wuce zuwa Bathroom. Da lukewarm water ya yi wanka abin sa sannan ya fito daga bathub ɗin ya janyo wani drower sai ga nan wasu mayun collection of designers towel's farare ƙal, miƙa hannunsa ya yi ya ɗauki daya da wani small one daga gefe, ɗaura babban ya yi a murɗaɗɗen kunkurunsa ya soma using ɗayan wurin tsane ruwan jikinsa da na kansa kafin ya juya zuwa cikin bedroom ɗin a saman ottoman na gadon ya zauna ya tsane ruwan tas kafin ya miƙe ya yi shafe shafensa kamar mace ya goge saman farcensa sannan ya duba jallabiya ya zura da zallan boxer da singlet ya shafawa sumar kansa mai ya taje ta sosai sai sheƙi take sannan ya sha turaruka ya miƙe zuwa masallacin da ke cikin Estate ɗin don gabatar da sallar magrib dayaji ana kira.
Da ido yabi apartment da ke kallon nasa yana mamakin abin da ya fito da yarinyar da gudu a firgice haka, kusan 30 seconds yana kallon yanda take shivering sai kuma ya ɗauke kansa ya ci gaba da tafiya kamar me tsoron ƙasa Escort din nan na biya da shi kamar jela, a daidai tsakiyar Estate ɗin akwai wasu gidaje guda takwas da aka zagaye da ƙaramin gate na ƙarfe me kyau guda shida matane zaune akan lallausan carpet suna ihu da shewa, ɗaga ido ya yi ya kallesu so ɗaya ya ɗauke idon sa a ranshi ya ce "Shin wai dama waɗannan matan suna nan basu daina wannan dabar ba? Basa jin ana kiran sallan magrib ne ko me? " Taɓe bakinsa ya yi ya ci gaba da tafiya kawai don bashida lokacin su, daga sallan magrib Azkhar ya hauyi bayan ya idar ya jira isha har sai da aka gama ya yi shafa'i da wutiri sannan ya fito daga masallacin suka doshi gidan.
Ƙarfe 11:30 na daren ranar yana zaune a farfajiyar gidan nasa asamn wasu arnan coffee chairs da aka ƙawata wurin dasu a cikin rumfar hut, gefensa ɗaya ruwan swimming da ya yi amfani da remote control ya buɗe murfinsu don kowane lokaci a rufe suke, lemo ne a hannunsa yana kurɓa a hankali rabin hankalinsa kuma yana online inda yake amsa maganar mutanen dake wurgo masa tambayoyi a inbox ɗinsa na tiktok matsayinsa ma likita ƙwararre a ɓangare gynaecology, Zama likita ra'ayin mahaifiyarsar ne which he cherished so much zama pilot zaɓinsa ne na har abada, don haka a shekarunsa 34 a duniya he achieved both field inda hankalinsa da ra'ayinsa yafi karkata akan tuƙin international flights saboda yafi samun wadataccen lokaci komansa a tsare yake. Duk kuwa da yawa mahaifinsa ya matsa masa lamba akan abubuwa biyu na farkonsa shine daina yin aikin a kowane airline both international and local yazo ya karɓi tayinsa na baje masa jirage iri iri da zai iya piloting kowace ƙasa ko local areas na Nigeria inda wannan musamman tayine me kyau da yakeji hala by new year idan komai ya kammala zeiyi accepting offer na mahaifinsa ya mallakinl kamanin jiragen sama na safara da mutane daga wannan ƙasar zuwa wata lokaci guda kuma yana aiki a ƙatuwar asibitinsa da Nannyta da kanta ta buɗe masa wato mahaifiyar mahaifinsa daga granny yake ce mata Nanny zuwa girmansa ya mayar Nannyta shine favourite jikanta datafi so a duk cikin jikokinta maybe hakan baya rasa nasaba da tsantsar son da take yiwa mahifinsa kasancewarsa autanta kuma ɗa namiji tilo da Allah ya bata, ba shiba duka family har 'ya'yanta sanadin Aliyu Nannyta suke kiranta. Yana tsakiyan duba Dm's ɗinsa hankalinsa ya kai ga wata datake tura masa saƙonni day and night for more than a year yanzu tunda ya buɗe so biyu ya fahimci maganar soyayya take be ƙara buɗe chat nata ba both a Instagram da Tickok cox shi besan ma meye soyayya ba abin is so disgusting, ya kafe sunan da ido da kuma last message nata, ta shafe shekara da wata 6 tana masa saƙon da baya buɗewa sam amma yanzu abin yana nunar masa kusan 4mongh rabon data masa message a ranshi yace ko tana lafiya? Taɓe baki ya yi yaci gaba da scrolling yana amsa masu muhimmanci musamman wanda ya shafi lafiyar mata, bayan ya gama dana Tiktok ya juya IG ya dudduba nan ma ya kai a wurin nata watanni 4 kenan bata aika masa saƙo ba kamar dai yanda tayi a Tiktok, ɗan gajeran tsaki yaja ya ƙara kurɓar juice da ke hannunsa yana shirin gyara zamansa ya tsinkayi mace ta fito daga ƙofar baya ta apartment dake kallon nasa tana sosa jikinta tare da yin ihu mai razanarwa zallan rigar bacci ce a jikinta duk sumar kanta a yamutse, taɓe baki ya yi sabosa ba yau ya saba ganin ana faɗa irin haka ba a tsakanin miji da mata indai yarbawa ne ko iyamurai wannan ba komai ba hala ma gobe sai ka iya ganin su tare sassafe zasu tafi aiki ko kasuwa, tsaki yaja suna so su ɓata masa mood ɗinsa kawai ya miƙe ya nufi cikin gidansa.
Rahima na tsaye a gaban mirror na ɗakinta tana daɗa gyarawa bon straight wig da ke kanta zama sosai majid ya shigo ya kafeta da ido, taci wata arniyar black suit da farar riga shirt me colour a ciki wata arniyar takalmi ce a kafarta black nails ɗinnan sunsha gyara gasunan zara zara sunsha adon stone's masu ƙyalli da kyau, fuskarnan tasha makeup kamar masifa ilahirin ɗakin kuwa banda azabtaccen ƙamshi ba abin sa yake zubawa, a cimin mirror ta kallesa ta sake masa wani malalacin murmushi kafin ta miƙe ta zari handbag dake ajiye akan mirror ɗin black colour itama ta tako wurinsa tana zube masa wannan sassanyar murmushin
"Heeyy kallon fa." Cikin lumshe ido da buɗewa ya ce "Heemah da gaske dai bazaki sauya tsarin shigarki ba? Ke fa hausa fulani ce amma ƙiri ƙiri rayuwar garin nan ya sanja ki kwata kwata kin watsar da al'adunmu na hausa fulani." Ɓata fuska ta yi tana masa wani kallon me haka kafin cikin hasala ta ce
"Look Mj don't you spoil my morning if that's all you got this morning just go please fita kake so ina yi kamar wata me zaman kurkuku and for goodness sake what's wrong with my dressing?" Shiru ya tsaya yana kallonta taja wani arnen tsaki ta juya ta fita a ɗakin da wannan tafiyar tata me ɗaukar hankali ilahirin shape ɗin jikinta a bayyane yake ta zuba kyau kamar ka sace ta ka gudu, Mj da ido ya bita har tazo ta ɓacewa ganinsa, jinjina kansa kawai ya yi ya juya zuwa part ɗinsa ransa a ɗan ɓace koda yake shi kwata kwata dama ba wai damuwar sa bane yanda ta zaɓawa kanta rayuwa.a babban compound ɗin ta haɗu sa Sameerah itama ta ci wani arnen wanka da wata farar riga wacce ta sauka sosai a baya amma ata gabanta ilahirin ƙafarta kafin gwiwa a bayyane yake skin ɗinnan sai wani malalacin sheƙi yake ita kanta Meeran wani hatsabibin ƙamshi take zazzagawa atake ƙamshinsu ya haɗe ya hautsina wurin da wani sassanyan ƙamshi, Heemah na kallonta tana murmushi ta ce "Meerah harkin fito ohh wow what a surprise kece ta biyu." Dariga duka sukayi kafin suyi wata maganar matan duk compound ɗin huɗu sun bayyana ko wacce da shiga irinta matan da duniya tasan da zamansu duk suka gaisa, Meenah na yiwa Meerah wani kallo ta ce "Babe jiya kin tashi kaina wallahi ni da Zuby muna jiyoku fa gaskiya ke bala'ee ce."
"Bana wasa da harkar nan nafison in baka once in a month yanda in ka zo kanamun kamar zaka yi sujjada." Duk wurin suka kwashe da dariya, Suhaima ta ce
"Thanks to my gumbar kaca kaca and tsumin Tsakeni in sarara." Dariyar aka sake kwashewa dashi kafin Amra ta ce
"You guys idan mun dawo we talk about that tsumin sakeni in sarara yanzu zamuyi kate cox damn that thing is a secret killer!" Duk suka kwashe da dariya suka wuce kowacce ta shiga motar da take ji da ita akanta wanda manya manyan motocine na alfarma suka nufi various places of work's nasu wasu suka wuce shagunansu.
KAMPALA ESTATE
BILLY GALADANCHI
NEW BOOK 2025
FREE PAGES