ZIYAAN

1

by @kdeey

🦋🦋🦋🦋🦋🦋🦋

*ZIYAAN*

🦋🦋🦋🦋🦋🦋🦋

DijahAM (Oum Amani)

Daga Marubuciyar..

-NOOR

-TASWIRAR KADDARA

-ELHAJJ

-AASMAA

-JUYIN RAYUWA

-ALKALAMIN SO

-NOURAH

Day 1

THE PROPHET (S A W) SAID

"If they knew the reward of offering the Zuhr prayer early (in its stated time), they would race for it."

SAHIH AL-BUKHARI 652 (SAHIH)

Page 1

TRUE LIFE STORY

بسم الله الرحمن الرحيم

Suna na Ziyaan, haifaffiyar garin Kano. Mu hudu ne a wajen iyayen mu, ni ce babba sai Sa’a, Anas da auta Abdullah. Shekara biyu da suka wuce Allah yyi wa mahaifiyar mu rasuwa, ta rasu da tsowon ciki. Har ynxu kuma tsawon shekarun nan babanmu bai Kara aure ba, mu kadai muke zama a gidan m, sai dai ni da Sa’a muna yawan zuwa gidan kakar mu kwana wacce ta haifi mamanmu, mazan ne dai basu çıka son zuwa ba.

Shekaruna goma sha shida, amma a sura ta zaka dauka na wuce haka, Ubangiji ya min wani irin diri mai daukar hankali ko da yake kusan ta haka ake gane dangin mahaifiya ta ko waccen mu ka gani duk sirantar ta tana da diri mai kyau. Ni ma din ba wata mai kiba bace amma sbd manyan halittun da nake da su front and back yasa ake min kallon mai kibar. A fatar jiki chocolate color ce, Ina da kyau na dai dai gwargwado Maa sha Allah, ga kuma tsayi shiyasa da yawa kawaye na suke cewa ni Allah ya gama min komai, Ina da sura mai kyau Ina da kyau da kuma fatar jiki mai kyau. Mahaifina b wani mai kudi bane muna da rufin asiri dai Alhamdulillah tun da mun fi karfin ci da sha da kuma sutura.

Numfashi na sake Ina kallon Maman Amir da ke karasa girkin rana, tun da safe na ke gidan ta, tsakanin gidan ta da namu gidaje biyu ne, ita nake wa kallon uwa don nima lokacin da tawa mahaifiyar tana raye Maman Amir ta dauki Ummana kamar tata mahaifiyar.

Zaman gidan na ta naji ya gundure ni, mike wa tsaye nayi Ina jawo mayafi na na yafa a kafada ta, fito wa daga falon nayi na ce “Maman Amir bara na tafi”

Dagowa tayi daga tsugunnen da take ta kalle ni “in kika fita ynxu gida zaki koma?”

“A’a gidan su Surayya zan je”

Tuni fara’ar dake fuskar Maman Amir ta chanja, cikin damuwa ta ce “ni dai ZIYAAN bana son mu’amalar ki da yarinyar nan Wallahi, Kai daga gani kasan ba ta kwarai ba ce”

“Ki kyautata mata zato dai Maman Amir, ni ban taba kama ta tana aikata wani abu ba, kawai dai kin san ba girman kasar nan ba ce, don haka wasu abubuwan in tana yi kar ai saurin fassara ta”

“Don tana girman Saudiya shine zaki ce ba tashin Nigeria ba ce, ai ita data tashi a kasa mai tsarki ce ma ya kamata tazo tana shiga ta mutunci, nidai bana son mu’amalar ki da ita daga gani ba alkhairi. Ynxu kallon shigar ki don Allah, ke abubuwa ba kadan ba kina tafiya jiki na rangaji kamar bishiyar da iska ke kadawa, da hijab din ki kike saka wa amma haduwar ki da Surayya ta koya miki sa mayafi”

Ajiyar zuciya na sauke na ce “ni dai na tafi, anjima da daddare zan zo ki min kari In sha Allah”

Cikin takaici Maman Amir ta ce “ba dole kizo na miki kari ba tun da ynxu islamiyyar ma kin dai na zuwa, lokacin islamiyya shine lokacin zuwa wajen Surayya, ita kan ta bokon ba kullum kike zuwa ba, ki mai da hankali don Allah ki karasa karatun ki, duka duka saura miki wata nawa kiyi WAEC din na”

Sanin in har akan Surayya ce Maman Amir baza ta taba iya daina mita ba yasa ni fice wa kawai. Ni Ina mamakin mai Maman Amir ta gani a tattare da Surayya da yasa ta tsane ta haka. Wata shida kenan da haduwar mu da Surayya, a lokacin kuma shekarar ta biyu ta dawowa Nigeria, mahaifiyar ta ce takaru a Makka, babanta daya je ya nemi duka su dawo gida Nigeria da zama amma maman taki dole ya bata takardar saki ya taho kuma da Surayya.

Ni a farko ma ba wani shige mata nake sosai ba, sai dai yadda ta kwantar da Kai tana min kyauta da nuna min banbancin shekaru biyar dake tsakanin mu ba komai ba ne yasa ni sakin jiki da ita.

Maman Amir kam sai biyu ta taba ganin Surayya amma ta dauki karan tsana ta dora mata, ni dai bata min komai da zan ce, abu daya ne kawai take min da bana so shine kokarin kai hannu jikina duk lokacin data samu dama, bama in nasa rigar data matse min kirji. Dana mata magana sai ta ce ita kawai burge ta nake yi, tana ji dama ita take da irin sura ta Allah ne kadai yaşan iskancin da zata yi a Nigeria. Ban bawa maganar ya muhimmancin ba tun da ba ita ba ce ta fara cemin sura ta na burge ta ba.

Ina ta tunani na har na isa gidan su, da sallama na shiga gidan kamar ko yaushe compound din ba kowa, kofar dake tsakar gidan a can gefe na nufa, nan ne dakin Surayya, da farko ta ce min a cikin gidan take zaune, ganin ba privacy yasa ta ce wa babanta dakin samarin gidan take so ta koma tun da har bandaki akwai, da yaki kuma ta tattara kayan ta ta gudu, da kyar ya samo ta ya bata dakin, ita kuwa ta gyare sa tsaf in ka shiga baza ka dauka a gidan su daki da bandakin yke ba.

Tura kofar nayi na shiga da sallama, dagowa tayi ta kalle ni tana murmushi, tana sanye da bra da bom short, ban ji komai ba tun da ta saba, matar dake tsirara a gaba na ma in zata sa kaya.

Ajiye wayar ta tayi cikin muryar ta da kana ji kasan idon ta a bude yake ta ce “ynxu nake cewa in baki zo ba zan biki gidan, an kawo mana dinkin mu Ina so ki gwada in akwai abinda bai ba sai a gyara tun wuri”

Mayafin jikina na cire na ajiye akan kujera daya dake dakin na nufu gado na zauna na ce “ni fa da don kin takura ba Wallahi baxan je ba, ba wanda na sani kawai sai na je”

Hade rai tayi ta ce “ni baki sanni ba kenan?”

Hannu kawai na mika mata ban ce komai ba, dariya tai tana janyo ledar kayan ta dora min akan hannu na, Ina jin yadda da zata cire sai da ta shafa yatsuna amma na share ba wai yau aka saba haka ba.

Kofar toilet na nufa ai kuwa tayi saurin riko hannu na tana murzawa ta ce “kar ki ce min a toilet zaki saka kayan sbd Ina zaune”

Hannu na na zare a cikin nata na ce “to kawai sai na chanja Kaya a gaban ki?”

“Eh mana ni so nake nake chanja Kaya kina zaune, wai tsaya ma ba tambaye ki, in na chanja kaya kina zaune bakya Jin komai?”

Cikin rashin fahimta na ce “wani abu ya kamata naji neh?”

Da alamar takaici Surayya ta ce “ko dai baki da lafiya ne, don in ba mara lafiya ba wanda bashi da sha’awa in cire kaya kina zaune amma ki ce baki jin komai, ni in kika shigo dakin nan har ki tafi tsiya ya na ke”

Tsaka ni da Allah bana gane mai take cewa don haka kawai na nufi toilet din na ce “bana gane wa”

Shige wa ta toilet din nayi na murza key a halayyar Surayya zata iya bude kofar. Kayan jikina na cire na saka doguwar rigar, wata iriyar fitted gown ce wacce ta shige ni da kyar, diri na a ciki kamar zasu yi magana, ga boobs din tamkar an hura balloons, numfashi na sauke Ina kallon tsagar da aka wa rigar ta a kasa ta gaba, zuciya ta rawa take Ina tunanin anya kuwa zan iya saka kayan nan.

Jin Surayya na kwankwasa wa ysa ni bude kofar kawai na fito, tun da na fito take bina da mayataccen kallon nan nata da wasu lokutan suke takura ni.

Numfashi na sauke na ce “ni dai gaskiya kamar baxan iya saka wa ba, kalli fa yadda suka matse ni”

“Ke dai ZIYAAN wasu lokutan kamar baki waye ba, sai ka ce girman kauye, ai ynxu ko yan kauyen ma sun waye, sannan yadda na siyo kayan nan n kuma bada kudin dinki Allah baxan yi asara ba dole na ki saka su”

Ganin ta dauki fushi yasa ni cewa “na ji, amma ko za’a bude min ita”

Fuska a hade Surayya ta ce “baxa a bude ba”

Shiru nayi kafin daga baya na wuce toilet.

Wasu lokutan ni Kai na Ina mamakin yadda bana iya wa Surayya musu, in ta ce nayi abu kaza a take nake cewa Toh, in kuma ta ce na bari shikenan ba bari. Ko zuwa Islamiyya ta Ina ajin sauka ta ce “na hakura haka mana ai na samu wanda na samu tun da kuma Maman Amir na Kara mun, ita baza ta iya wannan jigilar ba. Shikenan na ajiye Islamiyya a gefe. Inda Allah ya taimake ni ma na hade sittin littafai ne kawai bamu karasa ba zamu yi sauka. Shine Maman Amir take Kara mun su amma ba yadda ba tayi da ni ba akan na cigaba da zuwa makaranta naki.

Wannan book din paid book neh✍🏻

Ki biya 500 din ki, ki karanta cikin nutsuwa.

Account number

9066728387

OPay

Khadija Dan’asabe Adamu

Ko Katin waya ta wannan numbern

***

In an tura sai a turo da shaidar biya ta wannan numbern

***