ZIYAAN

2

by @kdeey

🦋🦋🦋🦋🦋🦋🦋

*ZIYAAN*

🦋🦋🦋🦋🦋🦋🦋

DijahAM (Oum Amani)

Daga Marubuciyar..

-NOOR

-TASWIRAR KADDARA

-ELHAJJ

-AASMAA

-JUYIN RAYUWA

-ALKALAMIN SO

-NOURAH

Day 2

The Prophet (S A W) said:

"Whoever recties Ayat Al Kursi after every obligatory prayer then nothing stands on his way to paradise except death."

Al-Mu'jam al-Kabir 7406

Page 2

TRUE LIFE STORY

بسم الله الرحمن الرحيم

Kayana na maida sannan na fito rike da ankon, akan gado na ajiye mata Ina murmushi na ce “amma dam nagode sosai, don da ni kika ce na siya da Kai na ban san wa zai siya mun ba”

“Shiyasa ai nake so na dora ki a hanya ta yadda ko nawa kike bukata zaki samu, ba tare da kin tambayi gida ba”

Da mamaki na ce “kasuwanci zan fara neh? Kin san nifa in aka bani jari cinye wa nake yi”

Dariyar shakiyanci Surayya tayi ta ce “ke jarin da kike da shi ai ba wanda zaki iya ci bane sai dai a miki kawai”

Tabe baki na nayi na ce “matsalar ba komai kika ce nake gane wa bah”

“Zaki fahimta ne yarinya a hankali ma kuwa”. Surayya ta fada tana kallon le’be na da ta sha fada min suna mata kyau Ina na tabe su.

Na jima sosai muna hira, sai da aka Kira la’aşar na mata sallama na nufi gida Ina juya kalmar ta da ta ce ban da lafiya, dole na fada wa Maman Amir don ta rakani asibiti.

Gıda na nufa da sauri sauri, sbd na daura abincin dare. Duk fita ta ana la’aşar nake koma wa gida. Sa’a ita dama yawanci tana gidan kanwar Abba, Anas da Abdullahi kuma bayan rasuwar Umma Abba ya saka su a makaranta mai hade boko da islammiya. Tun bakwai basu dawo wa sai ana magriba. Shima Abba din dai sai bayan Magriba yake dawowa ya ci abinci ya sake fita. Ni kadai ce a gidan in kuwa ba wai anyi hutun makaranta bane Sa’a tazo, shiyasa nake zuwa gidan Maman Amir sosai.

Mukulli na saka na bude kofar gidan, da sallama a bakina na shiga, tsakar gidan nan fess a share, wannn aikin su Abdullahi ne su suke gyara gidan tas kafin su tafi makaranta ni aikina kawai nayi girki na kuma wanke bandakin palo dana dakin Abba.

Direct kitchen din mu dake tsakar gida na nufa, mayafi na sakala a rijiya na shiga aikin dora danwake. Kafin magriba tuni na gama kwashe wa a flask na dafa wa su Anas ruwan zafin wanka.

Ban shiga cikin palo ba sai da aka Kira Magriba. Alwala nayi na shige dakin mu ni da Sa’a amma yawanci nawa ne ni kadai tun da dai Sa’ar ba mai zama ba ce.

Ina cikin sallah su Anas suka shigo, Ina jiyo kararniyar su suna fadan wanda zai fara shiga wanka kamar yadda dai suka saba. Abba daya shigo ne ya musu tsawa sannan suka nutsu.

Murmushi nayi bayan na gama addu’oina, Ina son kanne na sosai da gaske, yadda Umma ta tarbiyyantar da mu abin burge wa ne da ban sha’awa. Allah ya jikan ki Umma yasa kina cikin Aljannah(Ameen🥹)

Fito wa palo nayi na samu duk suna zaune suna cin abinci a plate daya har Abba. Gaishe sa nayi Nima na zaune muna ci tare gaba daya.

Sai da muka gama ci Anas da Abdullahi suka kwashe kayan suka fitar da su kitchen suka wanke sannan Abba ya ce duk yana son magana da mu.

Hankalin mu muka basa muna so muji mai zai fada mana wanda alamu suka tabbatar mai muhimmanci neh.

Kallon su dayan bayan daya Abba yayi sannan ya ce “dama so nake na fada muku na fara neman aure, kuma İn sha Allah in komai y tafi dai dai baza a wani ja lokaci ba za’a daura auren kawai”

Allah ya gani ban ji haushi ba kamar yadda na sha jin labarin cewa yara suna jin haushi in irin hakan ta faru. Hasali ma ni farin ciki ne ya Kama ni ganin za’a auro wacce zata karbi ragamar gidan dan mi kam abin ya min yawa gaskiya.

Cikin farin ciki na ce “Alhamdulillah, Allah ya tabbatar da alkhairi Abba, naji dadi sosai”

Murmushi yayi ya ce “Ameen Ya Allah” kallon su Anas yayi ya ce “baka ce komai ba”

Cikin kunkuni Anas ya ce “Toh”

Da mamaki na kalle sa, ban dai ce komai ba ganin Abba shima yai shiru. Daga karshe ma tashi yayi ya bar gidan. Yana fita na kalli Anas na ce “Ynxu abinda kayi kana ganin ta kama ta kenan? Abba din zaka wa kunkuni? Aure fa ya ce zai yi Kai ba abin farin ciki bane a kawo mana sabuwar Umma”

Cikin kunfar baki Anas ya ce “ba wacce zata maye mana gurbin Ummanmu, duka duka shekarar Umma biyu da rasuwa har zai Kara aure, abokina Kamis da mamansu ta rasu baban su sai da ya shekara biyar bai aure ba, kuma ko daga baya kamis ya ce mun Kakar su ce ta aura wa baban su wata cousin din sa baya so. Shikenan mu sbd Abba ya nuna baya son Umma sai ya kara aure, ke kuma sai murna kike ko, ni nasan da Sa’a ce Wallahi baza ta taba farin ciki ba”

Daga haka ya fisgi hannun Abdullahi suka fita.

Da mamaki karara nake kallon kofa, to don Allah meye a ciki don Abba ya Kara aure(_Rashin sani yafi dare duhu, tabbas da ace Ina da masaniyar auren Abba shine mataki na farko wajen fara lalacewar tarbiyya ta da mutunci na da nayi yaki iya yaki ganin bai faru ba_💔)

Daki na shiga na dauki hijab na saka na nufi gidan Maman Amir. Lokacin dana shiga ta saka yaranta a gaba tana koya musu Quran, abin gwanin burge wa.

Sai da suka gama aka yi addu’a sannan ni da ita muka shiga daki. Muna shiga ko zama ban yi ba na ce “Abba aure zai yi, ynxu ya fada mana”

Da murna sosai Maman Amir ta ce “Kaii Alhamdulillah, amma wannan zance ya mun dadi sosai sosai”

Numfashi na fesar na ce “Anas dai sai fushi ya ce wai bai kamata Abba yayi aure ba, ni dai ban ga komai a ciki ba”

“Ke raba kan ki da maza haka suke da dan banzan kishi, ko da ace maman su ce zata auri wani daban haka zasu yi”

Shiru nayi Ina tunanin da kuma juya yadda zan fada wa Maman Amir ban da lafiya

“Qalau kike kuwa ZIYAAN?”

Ajiyar zuciya na sauke na ce “dazu ne Surayya take fada min ashe bani da lafiya”

Hade rai Maman Amir tayi ta ce “wata ce ma zata fada miki baki da lafiya?”

Dan lumshe idona nayi na ce “sbd ta ce in na kalle ta bana jin komai na ce eh, shine ta ce ko bani da lafiya wai bani da sha’awa shi yasa in na kalle ta ba kaya bana jin komai, ita kullum na shigo har na fita tana tsiyaya, meye Sha’awa din? Ni dai bana ganin tana tsiyaya amma ta ce tana yi”

Tun kam nakai karshen maganar Maman Amir ta mike tsaye tana nanata “Innanillahi wa inna ilaihir Rajiun”

Ganin yadda ta kidime ne yasa ni nima shiga tashin hankali kenan da gaske bani da lafiya. Kuma yadda naga Maman Amir ya rikice da rasuwar Umma kawai naga tayi irin rikicewar. Tuni hawaye suka shiga gudu a fuska ta. Ta tabbata bani da lafiya sosai.

Ganin duk na rikice yasa Maman Amir riko hannu na ta zaunar da ni. Bayanı ta min dalla dalla akan meye sha’awa, sannan ta kuma dora min bayani akan lesbian yacce mace take bin yar uwar ta, har zuwa zina. Yadda take fada min tana kuma fada min girman lefin a wajen Ubangiji yasa naji jikina yana rawa. Tsoro ya cika zuciya ta hadi da wani irin kyamar les din sosai.

“Kin ga dai Umman ki har a lokacin rasuwar ta tana sake fada muku, ku rike mutuncin ku don Allah har dakin auren ku. To Wallahi kina yadda aka yi les da ke ko zina shikenan. Ga zunubi ga shi kuma in kika yi aure ki rasa abin da zaki fada wa Mijin ki. Don gane wa zai yi sosai ma kam”.

Cikin tsoro na ce” ai tun da Umma ta ce mu rike mutunci mu duk sallah sai nayi adduar Allah yasa na Kai mutunci na dakin mijina. Kuma zan sake kula sosai, itama Surayya din in abinda take yi Kenan zan rabu da ita ko ba haka ba?”

“Eh hakan zaki yi, ki cigaba da adduar Allah ya sa ki Kai budurcin ki dakin Mijin ki ZIYAAN, addu’a ce mai kyau don ba dabarar mu ba ce ke kare mu”

Jikina yayi wani irin sanyi. Ranar dai a gidan Maman Amir na kwana, Baban Amir ba a garin yake ba dama don aiki yake a bauchi sai ya shafe wata hudu ko biyar bai zo ba ma.

Washe gari da wuri ba koma gida, sbd yiwa su Anas abincin karya wa. Wuni ranar haka nayi sa sukuku ba dadi ko gidan maman Amir ban iya zuwa

Sai da na kashe kwana uku ban leka dai dai da kofar gida ba. Wani irin tsoron maza da kuma mata ne ya shige ni na ban mamaki. Ga kuma a gefe Ina tunanin in ya kasance Surayya Tana bin mata ya Kenan?

Yau dai bayan nayi la’asar na shirya cikin lace dina dinkin Riga da zani, ya min kyau sosai sai dai duk da kayan basu matse ba hakan bai hana su fito da halittu na ba. Dogon Hijab dina na daura har kasa sannan na fita.

Sai da na fara shiga gidan Maman Amir muka gaisa sannan na fito na nufi gidan su Surayya. Nayi niyyar in na je sai bayan isha’i zan dawo tun da nayi abincin dare na zuba a flask.

Da sallama na shiga gate din gidan su, kamar ko yaushe tsakar gidan shiru kai baza ka ce gidan akwai mutane ba.

Dakin Surayya na nufa. Tun da na kusa nake jin nishi nishi kasa kasa, da mamaki na ke kara kasa kunne na amma still nishin dai nake ji. Bude kofar nayi Ina tura jikina gaba daya ciki.

Wata iriyar bugawa kirjina yake yi ganin Surayya da kawarta Lee kanat yadda naji ana kiran ta suna aikata wani Abu da ban sani ba. Amma a irin bayanin da Maman Amir ta min suna biya wa juna bukata ne. Kamar wacce aka dasa haka na zuba ido ina kallon su, Surayya ce ta fara ankare wa Ina tsaye amma Maimakon su rabu da juna sai ta Kashe min ido daya tana kuma rarumar lee jikinta(Ya Allah ka tsare mana İmanın mu, ka kare mu da kariyar ka Ameen Ya Allah)

Wannan book din na kudi neh✍🏻

Ki biya 500 din ki, ki karanta cikin nutsuwa.

Account number

9066728387

OPay

Khadija Dan’asabe Adamu

Ko katin waya ta wannan numbern

***

İn an tura sai a turo da shaidar biya ta wannan numbern

***

Comment and share 🙏