ZIYAAN

4

by @kdeey

🦋🦋🦋🦋🦋🦋🦋

*ZIYAAN*

🦋🦋🦋🦋🦋🦋🦋

DijahAM (Oum Amani)

Daga Marubuciyar..

-NOOR

-TASWIRAR KADDARA

-ELHAJJ

-AASMAA

-JUYIN RAYUWA

-ALKALAMIN SO

-NOURAH

Day 4

Narrated Umm al-Ala (R A) : The Messenger of Allah (SAW) visited me while I was sick. He said: Be glad, Umm al-Ala' for Allah removes the sins of a Muslim for his illness as fire removes the dross of gold and silver. [Abu Dawud

3092,

authenticated by shaykh

Al-Albaanee]

Hisnii

Page 4

TRUE LIFE STORY

بسم الله الرحمن الرحيم

Zaman gidan Inna ba wai zama ne da ke mana dadi ba gaba dayan mu, bare ma ni wacce aka mayar kamar jaka wajen aiki. Zaku yi mamaki matuka ganin cewa mahaifiyar Ummanmu amma bama jin dadin zama a wajen ta.

Ita Inna mace ce mai sanyin hali da kawaici, baxan ce bana jin dadin zama na tare da ita ba. Amma iyalan gidan ne bamu jin dadin zama da su. A kaf kannan Ummanmu tun da ita ce babba Aunty Aisha ce kawai tamu ta zo daya, kuma ita ce wacce take bin Ummanmu. Sauran kam sai a hankali bama karamar su Aunty Binta taji labari, sam ban san mai na mata ba tafi kowa muna min tsana a fili. Ba dama ko wuce wa nayi ta dinga harara ta tana cewa ita fa bata yadda da yadda jikina yake bude wa ba.

Sa’a dama bata zuwa, rabon ta da gidan Inna wata takwas kenan, tun da sallah data zo Uncle Usman ya mata mugun duka sbd ta fara bleaching, shikenan ta daina zuwa.

A daddafe dai muka yi sati daya muka koma gıda.

Amaryar Abba sam bata da damuwa, yarinya ce ma baxa ta wuce 21 zuwa da biyu ba. Ta dauke ni tambakar kanwar ta, komai tare muke yi gashi bata jin kunya ta in har zata hada maganin mata a gaba na take tana min bayani. Wani lokacin ma ni ce mai nuna jin kunyar ta, ita kuwa ta ce ai dole ta koya min in aka min aure na huta ita ma ta huta.

Wannan maganin sanyi in zata sha tare muke sha, ga gyaran jiki in har zata yi sai ta min Nima. Sosai nake Jin dadin zaman mu. Su sa’a ma da Anas ganin bata da damuwa yasa duk suka saki ran su suma.

Abba kuwa yafi kowa murna ganin ahalin sa sun hade kansu.

***A haka na gama WAEC dita, sai zaman gıda da jikan sakamako. Surayya kuwa ni manta wa ma nake da ita. Sai dai fa duk ranar da maganar ta ta fado min wuni nake cikin sanyin jiki da faduwar gaba.

Dole na fada wa Maman Amir yadda muka yi, fadan dana yi tunanin zata min cikin ikon Allah bata min ba, sai nasiha data dinga min ta kuma bani shawara na dage da addu’a In sha Allah bakomai.

Yadda na samu kwanciyar hankali na dauka shikenan matsalar dana fara fuskanta ta wuce ashe yncu ma zata fara. Matsalar da zata zame min karfen kafa, wacce kuma zata kasance zubar hawayen duk wani masoyina.

Yau a gidan Maman Amir na wuni tun safe. Ynxu ba ruwana da tunanin girki shiyasa har wani dan Kara bude wa kasa na yayi. To na samu kwanciyar hankali.

Sai bayan la’asar na mata sallama na tafi gida.

Da sallama a bakina na shiga palon mu, na riga dana saba ina shigowa nake cire mayafi ko hijab don haka yncu ma Hijab din na cire na rike a hannu, gashi ba wata rigar arziki ce a jikina ba, doguwar riga ce ta roba mai karamin hannu. Gaba daya halıttu na a bayyana suke, bama sai na tsaya fada muku ba.

Jin ido na yawo a jikina yasa ni juyo wa, wani irin buga wa kirji na yayi ganin namiji ko na ce gardi ma kawai zaune cikin manyan kaya. A kallo daya na hango kamannin sa da Aunty, amaryar Abba kenan.

Jikina yana rawa na mayar da hijab dina jikina. Sbd yadda jikina yake rawa ne yasa ni zama akan kujera kai na a kasa.

Fito wa Aunty tayi daga daki tana cewa “Mahmud ka cewa Mama zan aiko mata da sakon in na karbo”

Gani na da tayi a zaune yasa ta cewa “Ziyaan yaushe kika shigo?”

Kafin na bata amsa wanda ta kira da Mahmud ya riga ni cewa “ai bata dade ba”

Gyada mata kai nayi ina Murmushin dole. Ita ma Murmushi tayi tana zama a gefen Mahmud ta ce “ita ce Ziyaan din da nake fada maka, kanwar ta ba anan take zaune ba. Ai kasan su Anas dama koh?”

Idon sa a kai na ya ce “eh su na san su mana”

“Yauwa, Ziyaan wannan Yayana neh, shine babba a gidan mu. Sunan sa Mahmud”

Kakalo Murmushi nayi na kalle sa cikin sanyin murya na ce “ina wuni”

Murmushi mai fadi yayi ya ce “lafiya qalau Ziyaan, sunan ki mai dadi sosai”

“Ngd” na fada ina mike wa na shige dakina.

Ban san lokacin daya tafi ba don ban fito ba sai da Aunty tazo ta kira ni, sannan na fito zuwa Palo muka sha hira.

Tun daga ranar Mahmud ya tsiri zuwa gidan mu, kusan kullum ma anan yake wuni. Da sassafe a zai zo, a gidan mu zai karya sannan ya tafi aiki. Karfe 5 zai sake zuwa gidan mu baxai tafi ba sai wajen goma na dare.

A takure nake matuka da gaske, ko yau she cikin hijab nake yawo sbd irin kallon da Mahmud yake bina da shi.

Yau zuwan na sa da akwati yazo, wai kwana hudu zai mana. Nayi tunanin Abba sai masa magana amma sai naga akasın haka don kamar murna ma yake da zuwan nasa. A dakin su Anas dake palon aka sauke sa.

Shikenan na sake takura, fitsari ma da kyar na ke yin sa, tun da shi da aka sauke a dakin su Anas baya shiga, in ka gansa ya shiga to kaya zai saka, a palo yake kwana a cewar sa Abdullahi yana munshari baya iya bacci.

Yau kwanan sa uku a gidan mu, kuma kullum kofa ta a rufe take in zan kwanta.

*****cikin bacci naji ana bude kofar dakina, gaba daya ban kawo da gaske bane sbd sanin da nayi na rufe dakina da hannu na. Don haka na sake gyara kwanciya ta, duk na yaye bargon dana lulluba.

Shafa ni naji ana yi, tun ina tunanin mafarkin dana saba yi ne a kwanakin nan har naji abun dai yafi karfin mafarki. Yaye min rigar baccin da aka yi ne yasa ni bude idona a firgece…………

Wannan book din na kudi neh✍🏻

Ki biya 500 din ki, ki karanta cikin nutsuwa.

Account number

9066728387

OPay

Khadijah Dan’asabe Adamu

Ko katin wata ta wannan numbern

***

A turo shaidar biya ta numbern nan

***