12
by @oumfatima33
💞💞💞💞💞💞💞💞
*AMATURRAHAMAN*
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
💞💞💞💞💞💞💞💞
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*BOOK 1*
*PAGE 12*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
Lokacin da su Amaturrahaman suka isa ƙofar gidansu ta fito tana share hawaye ta nufi cikin gidan nasu don sanar da Kawunnan nata, sai dai har cikin zuciyata fargabar wulaƙancin da za'a yiwa gawar mahaifiyarta take yi. Da ace ta san wasu da zata kai gawar Umma a suturtata to da baza taɓa tunkarar su Kawu Isa ba don yanda suka nuna basa son su itama haka ta tsane su a zuciyarta, tsana mafi muni ma kuwa.
Fitowa Doctor Farhan yayi ya matsa kusa da ita yace taje tayi masa sallama da mutanen gidan, kai ta gyaɗa masa ta shiga gidan tana share hawayenta.
Ɓangaren Kawu Isma'il ta nufa ko kallon sashen Kawu Isa bata yi ba sabo da mummunar tsanar da tayi masa shida ɗan iskan ɗansa akan abinda yayiwa Yayarta suka juya maganar suka ɓata mata suna. Tana zuwa ɗakin Aunty Rakiya ta shiga ta sameta a zaune tana ƙullin kayan miya da take sayarwa. "Aunty Rakiya Ummanmu ta rasu, ga gawarta can ƙofar gida a mota!". Tayi maganar cikin dakiya da bushewqr zuciya.
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un!, Ta rasufa kikace Amatu, duk da cewa ran bawa ba a hannun mutum yake ba amma yanda naga an fita da Asiya zai yi wuya ta dawo gidan nan a raye... Allah yaji ƙanta ya mata rahama, yasa mutuwa hutuce a gare ta!." Ta ƙare maganar cike da jimami da tausayin yaran.
"Gashi kuma Malam baya nan amma muje muga yanda za'a yi a shigo da ita a mata sutura." Ta kuma faɗa tana ɗaukar hijabinta dake saman ƙyauren suka fito ita da Amaturrahaman. Sashen Kawu Isa Aunty Rakiya ta nufa da Sallama. Matarsa Maimuna ta faɗawa abinda ke faruwa tace kiyiwa Yaya (Kawu Isa) magana ya fito a shigo da gawar a suturtata."
"Ai kuwa Malam baya nan ya fita." Ta ƙare maganar jikinta a sanyaye domin duk yanda suka tsaneta ita ɗin bata taɓa tsare musu komai ba, hasali ma sai dai ta kyautata musu. Tunda Allah ya haɗasu zama da ita take ƙoƙarin ganin ta zauna lafiya da kowa ta kuma fita haƙƙin duk wanda Allah ya haɗata zama da shi.
Gidan wani Malamin addini dake nan maƙotansu Aunty Rakiya da Amaturrahaman suka shiga suka yi masa bayanin abinda ke faruwa, cike da jimami ya umarci Matarsa da suje a gyara ɗakin mamaciyar inda za'a ajeta. Shi kuma ya fita ya sanar da jama'ar dake unguwar aka taru aka amshi gawar aka shiga da ita ɗakinta. Baba Juma matar Malam Sani ita tayi mata wanka da taimakon Aunty Rakiya aka shiryata. Sai a lokacin Kawu Isma'il ya dawo sabo da yaronsa daya ruga ya kirawo shi. Dashi aka sallaceta bayan an ba Amaturrahaman damar zuwa suyi bankwana.
Sai a lokacin hankalinta ya koma kan Yayarta ta shiga tambayar inda ta tsaya bata dawo ba. Data tambayi Aunty Rakiya ta sanar mata tazo neman taimako wurin Kawunanta bata samu ba ta fice bata ƙara dawowa ba har yanzu. Nemanta aka shiga yi ba'a gantaba dole aka haƙura aka kaita makwancinta yayin da tsananin damuwar da Amaturrahaman take ciki da kuma tunanin inda ƴar'uwarta ta shiga suka haɗu suka zuba mata zazzaɓi mai zafi.
Mutane basu wani tsaya zaman makoki ba sabo da ba abinda aka ɗora domin a basu, don haka kowa ya kama gabansa sai wadanda ba'a rasa ba.
~~~~~~~ Da ƙyar ta iya ƙwarara kanta ta miƙe bayan ta samu ta zare abinda suka ɗaure mata hannu da shi ta cire salatif ɗin da suka rufe mata baki da shi. Zuwa lokacin tayi kuka har hawayenta ya ƙafe don haka ta miƙe da ƙyar duk da irin azabar dake ratsa jikinta amma ta daure sabo da tunanin ta baro Amah ita kaɗai a Asibiti tana kula da Umma, dole tana buƙatar zuwa gida ta taimakawa kanta ta koma Asibitin duk da cewa itama likitan take da buƙatar gani.
Tana ƙoƙarin wucewa idanunta suka faɗa saman ɗaurin kuɗin da suka aje mata, wani irin ɗaci taji zuciyarta na mata akan dalilin da yasa suka bata kuɗin. Duƙawa tayi da ƙyar ta kwashe kiɗin sabo da tana tsananin buƙatarsu, kuma koda ta barsu bata ɗaukaba ba abinda zai sauya daga abinda suka mata, bazata taɓa dawowa yanda take ba har abada, don haka ta ɓoye kuɗin a cikin jinkinta yayinda zuciyarta ta gama bushewa ta ƙeƙashe gaba ɗaya, hanyar gidansu ta kama zuciyarta cike da alwashi iri-iri akan irin addabar da zata yiwa duk na mijin daya kasance bunsuru.
Da ƙyar taci gaba da takawa tana fita daga lungun, duk taku ɗaya sai taji kamar zata suma tsabar azabar dake ratsa illahirin jiki da ƙwaƙwalwarta. Lokacin data fito sarari ta fara haɗuwa da mutane sai ta zama abin kallo, duk inda ta wuce sai an nunata ana magana ƙasa-ƙasa. Bata damu da duk masu kallonta ko kuma abinda zasu faɗa a kanta ba domin ta riga da ta gama sallamawa.
Sanda ta shigo layin gidansu ta fara haɗuwa da mutane sai taga kamar kowa kallon ƙyama yake Binta da shi ana zaginta da faɗar magan-ganu mara daɗi a kanta. Bata damu ba taci gaba da lallaɓawa har zuwa kofar gidansu data samu Malam Musa da wasu tsirarun mutane da suke karɓar gaisuwa.
Bata samu zarafin gaishe su ba ta shige sabo da ita kaɗai ta san halin da zuciya da gangar jikinta ke ciki. Da Kawu Isa ta ci karo a zaure zai fita ya bita da wani mugun kallo yace "Sai yanzu zaki dawo daga yawon karuwancin da kika yi gado wurin Ubanki?, ai sai ki ƙarasa ki fara zaman makokin uwar taku don ta ƙarasa kina can kina gantali a titi." Yana gama faɗa yayi gaba abinsa bai ko tsaya ya kula da halin da take ciki ba.
Kai tsaye sashensu ta nufa ba tare da ta tsaya ko kallon mutanen dake tsakar gidanba waɗanda suke ta binta da kallo suna ƙus-ƙus. Da matar Malam ta fara cin karo ta fito daga banɗaki da buta a hannunta, itama kallon ta bita dashi tana nazarinta, sabo da yanda take taka ƙafa da ƙyar da kuma yanda take tafiya tana buɗe ƙafa kamar yar kaciya ya bata mamaki. Aje butar hannunta tayi tabi bayanta ɗakin don jin mai ke faruwa.
Samun su tayi rungume da juna ita da ƙanwarta suna wani irin kuka mai ban tausayi ga ɗaurin kuɗi har biyu na ƴan dubu ɗaya yashe a ƙasa. Kuka take yi, kukan dake fitowa tun daga ƙasan zuciyarta tana sabbatu, "Me yasa zaki tafi kema ki bar mu a wannan duniyar da babu komai cikinta face tsan-tsar zalunci da son zuciya..., Duk irin roƙon da nayi musu ba wanda ya taimake ni Umma korata sukayi na rasa ina zan dosa domin a taimaka mana har naje inda aka wulaƙanta rayuwata..., Aka tozartani aka jefe ni da kuɗi bayan an min barazana da rayuwata..., Shike nan kema kin tafi kin barmu bamu da uwa bamu da uba..., daga yau daga yanzu na ɗau alƙawarin babu wanda zan saurarawa, na shirya fito na fito dako wane ɗan iska, sai na karar da arziki duk bunsurun daya yarda ya nuna min halinsa!."
Irin waɗannan kalaman su suke fitowa daga bakin Nafisa cikin gushewar hankali yayinda jikin Amaturrahaman ke karkarwa tana fassara dukka kalaman Yayarta dake nuna cewar ta rasa mutuncinta a dalilin neman taimako, mutuncinsu da Ummansu take kare musu shi da duka ƙarfinta, ta kuma roƙe su dasu tayata karewa ko bayan ba ranta. Ko a lokacin da zata amsa kiran mahaliccinta sai da ta jaddada mata wannan maganar ta kuma ce ta faɗawa yayarta.
Nan da nan ranta yayi mummunan ɓacin daya lunka na yayarta, kasancewarta mai haƙuri yasa bata iya ɓacin rai ba, tana da wata irin zuciya da Ummansu ke tsoron abinda zai motsa mata ita. "Na rantse da Allah sai na ɗauki fansar abinda aka miki yaya Nafi..., Wallahi wallahi sai na wulaƙanta rayuwar kowaye yayi gan-gancin taɓaki..., sai na addabi duk wanda ya raɓi rayuwarmu da niyar cutarwa..., sai na tsiyata duk na mijin daya kuskura ya kusanci yaruwarmu..., na rantse sai na hukunta duk wani mai hannu a cikin ƙuntata rayuwarmu, sai na addabi kowane azzalumi..., sai na ɗauki fansa... Ba zan ƙyale ba ba zan ƙyale b..." Ɗif ta ɗauke wuta ta zube a sume wanda shine silar dakatawarta daga furzar ta tafasassun kalmomi masu ban tsoro dake fitowa daga zuciyarta waɗanda hatta Nafisa sai da suka tsoratata ta tsaya tana kallonta cike da tsoro da kuma shakkar zafin zuciyar ƙanwar tata.
Da gudu suka yi kanta ita da matar Malam suna jijjigata da kiran sunanta. Tun fara magan-ganunta cikin ɗaga murya hankalin duka mutanen gidan ya dawo nan don haka suka cika ɗakin don ganin abinda ke faruwa.
"Ku miƙo ruwa a zuba mata mana kuka tsaya kallonta." Matar Malam ta faɗa, Aunty Rakiya ce ta miƙo ruwan aka zuba mata a fuska aka samu ta farfaɗo. Ɗaya bayan ɗaya mutanen ɗakin suka fice suna faman ƙus-ƙus akan abinda ya faru.
Tunda ta farka ta maida ido ta rufe ta juya musu taƙi cewa komai, tana jin sanda Baba Juma ta fita ta ɗora ruwan zafi ta gyara Nafisa sosai ta kula da ita sannan ta tafi bayan ta bata abincin da aka kawo sadaka. Amaturrahaman kuwa duk yanda aka yi da ita taci wani abu ƙiyawa tayi, bata sa komai a cikinta ba sai da dare da Nafisa ta saka mata kuka sannan ta amshi abinci tayi loma bata fi biyar ba ta aje. Magani suka sha dukansu wanda Aunty Rakiya ce ta nemo ta basu suka kwanta.
``````Ba'ayi wani zaman makoki ba sabo da yanda abin ya zama yanzu, mutane basa zama inda suka san baza su mori komai ba. Don haka har aka yi kwana bakwai daga su sai Baba lami da Malam ya bawa umarnin zama dasu, sai ko masu shigowa gaisuwa jefi-jefi.
★Washe garin data cika kwana bakwai da rasuwa Malam ya buƙaci zama dasu Kawu Isa akan kula da marayun da suka kasance nauyinsu. Mutuncin Malam da suke gani ne yasa Kawu Isa amincewa da zaman daya nema, don haka bayan sallar magrib suka haɗu a bangaren Mukhtar Nafisa ta shimfiɗa babbar tabarma suka zauna.
Bayan gaishe-gaishe Malam ya buɗe taro da addu'a sannan ya fara dayi musu nasiha akan girman zumunci da yanda Allah ya haramtawa masu yanke shi shiga aljanna... Sannan ya ɗora da kwaɗaitar dasu ladar riƙon maraya ya rufe da cewa "Waɗannan ƴa'ƴanku ne har a wurin Allah domin Mukhtar (Allah ya masa rahama) jininku ne Mahaifinku ɗaya, yanzu da baya raye nauyinku ne kula da iyalinsa. Don haka ina roƙonku da kuji tsoron Allah ku riƙe yaran nan amana tamkar yanda zaku riƙe ƴa'ƴan da kuka haifa."
Tunda ya fara maganar kawu Isa ya zumɓuri baki ya kauda kai maganar Malam na shiga ta dama tana fita ta hagu, yana ayyana cewar ɓata baki kawai Malam keyi don bazai taɓa riƙewa Mukhtar yara ba har abada. Mukhtar ɗin da ya shige musu hanci ya hana su sakat, Mukhtar ɗin da Mahaifinsu ya fifita shi fiye dasu, suna ji suna gani sai a bashi jari sau goma zai lalata sau goma za'a kuma bashi wani. Mukhtar ɗin da ko mahaifiyarsu baya ragawa bare su, kai ina da sake.
Amma da Malam ya buƙaci jin ta bakinsu sai basu musa ba suka amince sabo girman da yake dashi, kuma sannan Aminin Mahaifinsu ne. Da haka Malam da matarsa suka yi musu sallama suka wuce bayan sun ƙara yiwa su Amaturrahaman ɗin nasiha sosai da ban haƙuri.....
Oum Fatima