5
by @kdeey
🦋🦋🦋🦋🦋🦋🦋
*ZIYAAN*
🦋🦋🦋🦋🦋🦋🦋
DijahAM (Oum Amani)
Daga Marubuciyar..
-NOOR
-TASWIRAR KADDARA
-ELHAJJ
-AASMAA
-JUYIN RAYUWA
-ALKALAMIN SO
-NOURAH
Day 5
The Prophet (SAW) said:-
"Have Taqwa (Fear) of Allah wherever you are, and follow an evil deed with a good one to wipe it out, and treat the people with good behavior."
Jami' at-Tirmidhi 1987
Page 5
TRUE LIFE STORY
بسم الله الرحمن الرحيم
Mahmud ne zaune a gefen katifa ta, daga shi sai gajeran wando. Cikin lokaci kankani jikina ya samo rawa, yadda bakina yake rawa ne yasa ni kasa furta ko kalma daya.
Murmushi ya mun yana bin jikina da kallo, cikin kasa kasa da murya ya ce “Ziyaan, ba wai sai na tsaya bata mana lokaci ba wajen fada miki yadda nake tsananin begen ki, a idona ma kadai zaki gane haka. Ke ba yarinya ba ce, ki saki jiki kawai mu shayarwa da juna dadi”
Girgiza kai nake cikin rawar jiki, da kyar na samu bakina ya bude, cikin rawar murya na ce “ka ji tsoron Allah”
Murmushi yayi yana janyo cinyoyina ya ce “zan ji in na gama”
Ina ji ina gani ya bankare ni ya cire rigar jikina. Ban taba jin takaicin kwana da karamar riga ba irin yau. Duk turjewar da nake ina kokarin kai masa duka ko kadan bana samun sa, tuni dama ya danne kafafuna da tasa kafar, yayin da ya bankare min hannaye na baya.
Yadda yake min ban bari yayi tasiri a jikina ba sai kokawa nake, ganin kokawar ma kamar kara masa nishadi yake yasa ni sakin jiki na kawai ina wani irin kuka. Kuka nake wanda tun rasuwar Umma ban sake yin makamancin sa ba.
Kokarin cin ma burin sa da naji yana yi ne yasa cikin ikon Allah wani karfi yazo min, kafata da ke kasan sa na daga na daki zuwairar sa d ita.
Sırıriyar kara yayi yana tashi da mugun sauri. Wani irin mugun kallo yke min wanda yake kara hausina min tunani. Cikin tsananin bacin rai Mahmud ya ce “ki ta guje gujen ki, amma tun da na fara sai na ida sa” daga haka ya saka kai ya fice.
Hade jikina nayi na dunkule wani kuka mai ciwo yana sake kwace mun. Duk yadda zan muku bayani baza ku gane abinda nake ji ba. A gidan mu fa har cikin dakina namiji ya shigo yai molesting dina ya fice. In a gidan mu I’m not safe ina ne zan je kuma na tsira?.
Kuka na dinga yi cikin rashin mafita har aka kira sallah. Kasa ma tashi nayi sai da aka idar sannan na mike da kyar ina jin yadda jikina yake min ciwo, musamman hannayena da fuska ta wacce ta sha mari.
Doguwar riga na zira na saka hijab na fice a gidan, sai da na tabbatar ba wanda ya ganni sannan na nufi gidan Maman Amir. Buga wa nake a hankali don har lokacin jikina rawa yake.
Maman Amir ce ta bude bayan ta tambayi waye na ce ni ce. Yadda ta ganni ne yasa gaban Maman Amir faduwa, cikin tsananin tsoro ta riko hannu na, sai da ta rufe gidan sannan ta ja ni har dakin ta.
Muna shiga ta riko fuska ta tana duba wa, cikin rawar murya ta ce “yan daba ne suka shiga gidan ku Ziyaan?”
Girgiza mata kai nayi ina zama a kan gadon ta. Cikin dacin murya na ce “Mahmud ne ya shigo min daki”
Zaro ido tayi ta ce “Yayan amarya, bai miki komai ba koh?”
Murmushi nayi wanda kana gani kasan bana dadin rai ba ne na ce “zai shigo ne ya kasa mun komai Maman Amir”
Cikin tashin hankali ta ce “kar ki ce wani abu ya faru Ziyaan, Innanillahi wa inna ilaihir Rajiun”
“Allah bai basa ikon Kai wa ga babban burin sa ba Maman Amir, amma yayi molesting dina in a way da ko makiyi na bazan ma fatan yayi going through ba” na karashe hawaye na zubo min.
Janyo ji jikin ta Maman Amir tayi tana rarrashi na cikin tsananin kunar zuciya. Mun dade muna kuka kafin ta ce “ki fada wa Abbanku, in kuma baxa ki iya ba ni na fada masa”
Da sauri na girgiza Kai na ce “baxai yadda ba, ko kadan, cewa ma zai yi karya nake masa”
Fuska ta ta riko tana kallon yadda ta kumbura ta ce “ita fuskar taki cewa zai yi ke kika na kan ki”
Ajiyar zuciya na sauke na ce “baxai yadda ba Maman Amir, kin tuna na taba fada masa bai kamata Mahmud ya dinga zuwa mana gıda ko yau she ba tun da ba muharrami na bane ba? Amma me yayi Maman Amir? Fada ya Kama ni da shi yana cewa Ina so na bata masa gida, wato matar sa nake wa bakin ciki tun da naga dan uwan ta yana zuwa ai lokacin da Ummanmu na raye itama yan uwan ta suna zuwa, kuma bai tsaya iya nan ba sai da ya fada wa Aunty cewa bana don Mahmud yana zuwa ita kuma tazo ta mun tass. Kina ganin in na fada masa zai yadda, cewa zai yi karya nake kawai sbd dama tun da bana son Mahmud”
Numfashi mai zafi Maman Amir ta fesar ta ce “Allah ya shige mana gaba kawai, Allah ya kare ki da kariyar sa Ziyaan”
“Ameen” na fada Ina zame wa kan gadon na kwanta.
Ruwan zafi Maman Amir ta dafa mun nayi wanka sannan nai sallar asubar da ban yi ba. Ina idar wa na kwanta nan da nan wani wahalallan bacci ya dauke ni.
Ko da na tashi kiran Abba nayi na ce masa na tafi gidan Aunty Aisha zan kwana biyu. Fada dai na sha sa akan me yasa na fita tun asuba ban fada masa ba…
****
Sai da nayi sati guda a gidan Maman Amir ki kofar gida bana lekawa. Yau dai bayan magriba nai mata sallama na tafi gida bayan ta kara min wasu nasihar sosai akan naji tsoron Allah na kuma ta addu’a.
A palo na samu Aunty, gaisawa muka yi sai dai yadda take amsa min sama sama yasa ni mike wa na shige daki. Ko minti daya ban ba na dawo palo fuskata dauke da madaukakin tsoro na ce “Aunty waye ya lalata min wajen mukullin daki na”
Kallona tayi shekeke ta ce “gadin daki nazo yi miki dama Ziyaan”
Tuni idona ya fara cikowa da hawaye. Cikin sanyin jiki na koma dakina Ina duba kofar naga ko zan iya yin dabara amma babu dama don gaba daya a bata gurin key din.
Zama nayi a gefen katifa ta na kifa Kai na akan cinya Ina sakin kuka mai ban tausayi. Ban san adadin lokacin dana dauka Ina kukan ba.
Jin shigowar su Anas ne yasa ni mike wa Ina goge hawayen fuska ta. Da Hijab dina na fito don gaishe da Abba.
Maganar tawa makale wa tayi a makogorona sbd tozali da nayi da Mahmud, bai tafi bane ba? Amma ai kwana hudu aka ce zai yi. Sanin ba mai bani amsa yasa ni cikin sanyin jiki juyawa na gaishe da Abba, wanda ya amsa min yana tambaya ta ya na baro su Aunty Aishan. Kun gani shiyasa nayi karya da cewa Ina gidan Aunty Aisha sbd nasan Abba baxai taba kira wo wa don yayi confirming da gaske na je gidan ko ban je ba.
Ajiyar zuciya na sauke ina kallon Anas wanda ya zuba min ido kamar mai son karanta ta. Murmushi na masa Ina dauke idona akan sa.
Ba yadda na iya dole na zauna a palon, tun da nasan Abba Ina kokarin shiga daki zai ce na dawo da zauna shi baya son sabuwar dabi’ar dana koya ta zaman daki.
“Abdullah, ka kwana a dakina yau kaji” na fada Ina kallon Abdullahi daya fara hamma alamun bacci.
“Ai Umma ta hana mu kwana a daki daya kin tuna” Abdullahi ya fada yana mutsika idon sa.
Kafin nayi magana Abba ya riga ni”kamar ya ku kwana daki daya”
Murya ta na rawa na ce “tsoro nake ji Abba”
“Ban gane tsoro ba”
“Wani film muka kalla a gidan Aunty Aisha na Aljanu”
“Allah ya Kara, gobe kya sake kallon irin fina finan, amma babu yadda za’a ki ku kwana daki daya da Abdullahi”
Tuni idona ya fara tara hawaye, dan kallon inda Mahmud yake nayi naga idon sa a kan wayar sa amma fuskar sa dauke take da murmushi…..
Wannan book din na kudi neh✍🏻
Ki biya 500 din ki, ki karanta cikin nutsuwa
Account number
9066728387
OPay
Khadijah Dan’asabe Adamu
Ko katin waya ta wannan numbern
***
A turo shaidar biya ta numbern nan
***