Page 2
KAMPALA ESTATE
NA
BILKISU GALADANCHI
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
02.
Leo tunda ya dawo masallacin sallah subh ya kasa nutsuwa akan saƙon yarinyar daya daina samu a wayarsa duk da dama can bayan so biyu da ya buɗe saƙonta ko so ɗaya be ƙara buɗewa ba, ganin abun ya dameshi ya tilasta masa yin abin da be saba yi ba wato hawa online da rana kai tsaye tiktok ya wuce ya zarce DM's nasa ya scrolling ya nemo sunanta ya wuce zuwa message na farko data fara yi masa wanda ya taba karantawa
"Hello my favourite pilot my one and only Dr. I hope kana lafiya, just wannan say hii." Taɓe baki ya yi sai kuma na biyu da shima ya san shi
"Fav you opened my message amma ba reply Please ko da so ɗaya ne ka mun magana kaji, ni ina sonka amma nasan kafi ƙarfina Please ka ansa ni." Tsaki me sauti yaja coz dama cewa tana son sa a tun farko ya sanya kwata kwata ya daina amsa mata message shikam! Daurewa ya yi ya duba yaga bayan wannan sai da ta shafe sati 3 ba message sannan ta yi wannnan
"Fav i want you to be my brother, fav banida kowa a duniya sai mamana and she's sick seriously sick ka ma mamana addu'a kaji." Sai yaji ba daɗi a ransa yana gama karantawa a hankali ya ce "Allah ya bata lafiya."
Scrolling yaci gaba da yi yaga message ɗinta kuma
"Fav mamana munje asibiti ance cervical cancer ne da ita, Fav kai gynaecologist ne ko zaka taimaka mana Please, My Dad is late and i am the only child my mother is my everything idan ta tafi ni banida inda zanje Please Favourite help a soul kaji." Zaune ta tashi daga kwancen da yake yana duba date tun shekara da wata 8 ta masa wannan message wata iriyar zufa ce ta keto masa duk da ƙarfin Ac dake ɗakin hankalinsa ya tashi, ƙoƙarin karanta next message yake wayarsa ta yi ƙara yana ganin Dad ne da sauri ya ɗaga kiran cikin sanyi ya ce
"Daddy ina wuni." Daddy cikin kakkausar murya ya ce
"Aliyu me kake a Lagos ɗin? Ina ce tunda ka dawo bakaje Company ba? Anan ɗin idan ka zo ai akwai abubuwan yi again Nannyta ta damu ka tabbatar yau ɗinnan ka taho kano." A hankali ya ce
"Dad yau zanje Company dama ka bari gobe zan taho kanon but by road zanzo i miss travelling by road." Daddy ya ce
"Noo Leo ka hau jirgi use your private get and come home yau yau ɗinnan." Cikin sauke ajiyar zuciya ya ce "Shikenan Dad zanzo." A haka suka yi sallama ya miƙe zuciyarsa a cunkushe ba daɗi sam.
Wanka ya yi ya shirya kansa acikin wata suit cream color me shegen kyau sai sheƙi take tie ɗinsa da takalminsa black cover shoe suit ɗinsan company mara choe ne har takalmin kitson kansa yake kallo ya ɗan tsufa masa a hankali ya sakarwa kansa murmushi har saida one sided dimple ɗinsa ya wani kalan loɓa da zurfi, dayan side ɗinsa akwai but be kai ɗayan zurfi ba, zallan wayarsa ya ɗaga ya fito parlour sa body guards ɗinsa biyu ya tarar a tsaye a hankali ya ce
"Bush get my stuffs, And you Hygiene lead the way." Duk suka fara takan abin da ya saka su, Hygiene ya rakoshi waje ya buɗe masa yana shirin saka ƙafarshi sai ga nan yarinyar jiya ta fito yanzu ma a hautsine tana kuka me sauti wani sharɓeɓen namiji ya fito da dorina a hannunsa yana huci tsayawa Leo ya yi yana kallon su da mamaki ɗauke akan fuskarsa jikinsa ganin cewar wannan ba yoruba ko igbo bace as he expected kai har mijin ma ba wani yare bane face Hausa fulani! A hankali a tako zuwa gate ɗin shikuma wancen sai banbami yake tana gefe tana kuka
"How dare you meddled in my affairs ban gaya miki sharaɗina ba kafin ki shigo cikin gidannan? 'yar iskar wulaƙantaciya nace ki matso kafin in kama ki." Tana ƙarawa kukanta sauti ta ce
"Don Allah Sir kayi haƙuri don Allah ka rufamun asiri bazan ƙara ba wallahi kaji ka taimakeni don Allah." Yana huci ya ce
"Those Filthy hand's da suka taɓamun kayana wallahi sai na saka wuƙa na guntule su yau you will c the other side of me banza kawai." Tana ƙarawa kukanta sauti ta ce
"Ka yafemun Sir don Allah ka ji tausayina na yadda idan na ƙara ka yankani ma don Allah." Leo kamar ba zaiyi magana ba amma sai ya taka zuwa wurin mutumin cikin sigar rarrashi ya ce
"Oga i don't mean to intervene or disrespect you but please ka yafe mata kayi haƙuri kaji." Mutumin ya bi Leo da kallo nan da nan ya fara turo harshe yana murmushi lokaci guda ya shiga lashe lip's a nutse ya ce
"It's fine Cute boy ya wuce shikenan amma taci albarkacin ka." Kalmar Cute boy ɗih ta daki ƙirjin Leo amma se ya saka a ranshi hala haka yake magana shi? Ya ƙaƙalo murmushi ya ce "Thank you sir." Ya juya ya kalli yarinyar shikuwa Leo ya ce
"Ke meyasa kike yiwa yayanki laifi ne kullum? Jiya da dare ma i believe sai da kika sha duka yanzu ma kin kuma, you better behave yourself and be a good girl kina jina." Da sauri ta gyaɗa masa kai har lokacin dai bata kalleshi ba bazata ce ga fuskar wanda ke mata magana ba duk da his voice sound familiar sosai, haka ya barsu ya juya abin sa.
**************
Rahima wuraren 4 ta shigo compound ɗin acikin Kampala Estate, ana taci karo da mijin Meerah ya dawo gidan shima with surprise take kallonsa don tasan ba lokacin dawowarsa ba kenan duk mazajensu sai yamma, wani kallon ƙurulla ta bisa dashi a ranta tana tunano yanda ake basu labarin tsawon lenght ɗinsa da ƙwarancewarsa a shinfiɗa wani abu daban ya tsarga mata ta kawar dashi a ranta da sauri tare da gayar dashi
"Ina wuni Sir." Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa ba zai iya cewa ma ga sunanta ba shikam ya ce "lafiya lau kina lafiya." A hankali ta ce "Lfy lau." Ta wuce cikin gidanta sum sum kamar ba ita ba ya ɗan saci kallonta a ranshi ya ce "Duk dai haka suke fita kamar wasu arna Allah ya shirya." Tana isa wanka ta farayi sannan ta kira me aikin gidanta ta nemi abinci taci ta baza online abinta tana nishaɗi, by 5 na yamma gidan ya cika da matan compound ɗin nan da nan suka fita suka kafe daba.
Meena ta ce "Ban samu kan Dr. Ba jiya so bansan amfanin sakeni in sarara ba but i had to use panty liner sabosa yanda nake yoyo." Meerah ta ce
"Wallahi jiya na durzu a hannun Oga Bashir again i used that power ranger's a cikin shayinsa na dare lenght ɗinsa har wani tsawo ya ƙara gaskiya yana aiki sosai thanks to our dearest madam me kayan mata i enjoy every bit of it." Suhaima ta ce
"Jiya muka fitar da new products a shop sunansa ci ka laƙe very affordable kuma taho muku dashi yanzu zamu sha 2 pieces ake sha kullum mu gwada mu gani ko?" Sowa wurin ya ɗauka kafin ta kira me aikinta a waya yazo ta kawo ubansun Youghurt da mini bowls and spoons very clean one's guda shiga suka fara haɗa masifar da suka saba, Suhaima na kallon Meena ta ce
"Madam Zuby yaufa ni da nake manne daku zanji zantuttukan shirme sa santi masu yawa kun ganku sam bakuda dama." Meena na dariyar shaƙiyanci ta ce
"Sa'ar namiji me lenght da kauri ga ubansun jarumin ƙatoton crowns sai an tona dole ma zakiji ihun mu ni daɗi shi daɗi." Amrah dai bata ce komai ba she hardly talk akan girman lenght ko harkar jima'insu a duk jikinsu nata saurara idan an kawo abin sha tasha, ita kaɗia ce me kamun kai a jikinsu duk sa tulin wayewar dake kanga but tana kwatantawa she always dress decent batada wannan shirmen hakan ya saka ma kamar zaman dole suke da ita majority a Click ɗin sukance tana kwafsa musu amma ita bata damuwa tace ma kansu suka yiwa ba ita ba, Heemah tana kallonta ta ce
"Ke madam kullum aka zo kiyita jin sirrinmu amma ke bakinki shiru anya kinada mutumci ma kuwa." Dariya siririya ta yi kafin ta ce "Ni dai ban tilastawa kowaccenku kawo hirar girman lenght ko hours da yake lasting a gado ba meyasa zaku tilastani faɗar nawa? Ra'ayi ne kawai banayi madam." Ɗan shiru wurin ya ɗauka ga alama ba wanda yaji daɗin maganar ta a wurin, Sameerah ta ce "To meyasa kike fitowa jin namu sirrin?" Jinjina kanta tayi sannan ta ce
"Ai ba wai zaman hirar abin da muke yi ba kenan a kullum koda yake ke maganarki da rayuwarki gaba ɗaya akan jima'i ne idan bakwa buƙatar zamana a cikinku saboda kawai bana tofa albarkacin bakina akan shinfiɗar aurena sai in daina zuwa look its not as if banida abin yi fa." Da sauri Suhaima ta ce
"Noo behave yourself mana big girl's after all it's her life mu da muke faɗa ba tilasta akai mana ita idan ta zaɓi shiru kawai a rabu da ita." Rahima cikin takaici tace
"To tunda kuka ga its obvious shinfiɗar gidanta ba armashi tukunna wama ya sani ko hala girman abar ƙarama ce shiyasa take tsit." Cikin jin haushi boss ɗinsu Suhaima ta ce "Heemah meye haka wai? Bata ra'ayin yin maganar shinfiɗar aurenta ana so be it." Amrah dai bata sake cewa komai ba daga nan kamar ko yaushe aka kawo wata hirar ta designers inda Meena ke kawo musu kayan data kawo sababbi aka shiga ɓarin kuɗi ana siya.
***************
Tunda ya iso filin jirgin Aminu kano yaji wani sanyi ya mamaye sa haƙiƙa ya yi missing gida dama jihar sa baki ɗaya, da fara'arsa ya isa kusa da Nannyta da ta shafe awa a filin jirgin zaman jiransa, faɗawa ya yi jikinta yana mata murmushin so a hankali da muryarsa me sanyi yet husky ya ce "My Nannyta i miss you so much I'm so happy to see you me kika ajiye mun?" Tana shafa kansa ta ce
"Lion muje gida tukunna ko." Nan ya riƙo hannunta wani irin kama ya ke da ita kamar an tsaga kara, gaba ɗaya ya shammaceta don ko ubansa data haifa baya kama da ita yanda Leo keyi, suka ɗunguma mota se gida. Mahaifiyarsa kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kanta sabida tana fushi dashi sosai akan rashin amsa tayinta na auren 'yar ƙanwarta kuma Nannyta tace ba dole ba wanda ze yiwa jikanta auren dole, shi dai be damu ba ya tafi ya rumgumeta yana dariya ƙasa ƙasa yana saketa ya kwanta ya ɗaura kansa akan cinyarta ya ce
"Mami i missed you." Ɗauke kai ta ƙarayi yana murmushinsa me kyau ya ce "Shikenan ko yanzu na faɗi na mutu nasan wuta zanje tunda na ɓatawa Mami na rai har tana fushi dani Allah kada ka ɗauki raina se Mamina ta sakko." Murmushi ya suɓuce mata ta kallesa tana yi sannan ta ce "Ni nace ina fushi da kai?" Yana dariya ya ce
"Ba gashi kin kulani ba Mami kiyi haƙuri kinji Please karmu fara haka da ke don Allah." Kansa ta shafa "Shikenan gaye ba wanka kalli sumar kan jikan Nannyta?" Murmushi ya ƙara yi kafin yace
"Nannyta zatamun kitso ai." Mami ta girgiza kanta kafin tace "Alhamdulillah tunda ance gyaran gashin ba haramun bane amma ni kitson da kake ne bana so my pilot." Yana murmushin sa me kyau ya ce
"Mami kitson ma ba haramun bane ai." Shiru ta yi kafin ta jasa zuwa dining duk aka zauna Nannyta sai bashi alkubus take a baki kamar wani ƙaramin yaro, Daddy dai se murmushi yake don yasan Leo se matarsa tasha haushi don ba ranar da zai girma hala?..
Da dare Leo ya kasa bacci yana so ya kammala ganin tulin tarin saƙunan da ke nan a gabansa na yarinyar da Tiktok da IG handles ɗinta duka suna ɗaya ne "Dr. Pilot Fav." Ya koma can inda ga tsaya da karatunsu da safe inda ya fara da inda ya bari
"Fav nasan ance kana taimakon mutane, my fave Mamana zata mutu batada lafiya,.mamana bata iya tashi dama ita take siyar da Boli da kuma Dukunu muke cin abinci Please ka taimaki mamana." Ya girgiza kansa cikin jimami kafin ya tafi next
"My pilot naga last video naka akan masu neman taimako da asibitin da zasuje a musu free treatment thank you so much fav Allah ya saka da alkhairi mamana ta fara jin sauƙi." Murmushi ya yi a ranshi yace what a relief that means kenan sun samu taimako ko yayane ta hannunsa kuma jin Boli da dukunu ya tabbatar Lagos ne saboda iya can ne da kano aka bawa masu cancer free treatment a asibitin sa a wannan lokacin, jin wannan kawai sai hankalinsa ya kwanta yaji cewa hala shikenan ba sai yaji sauran ba tunda tace sunce asibiti da wannan tunanin he replied few messages ya ɗauki video kuma akan yanda ake kare kai naturally ma gujewa faɗawa cutar infection sannan ya yi edit ya yi posting ya shiga live inda nan da nan aka cikasa da gift mutane suka hau aka tattauna dashi kai tsaye kafin ya sauka yana duba iyayen kuɗin dayake tarawa duk sanda ya hau live koda kuwa unannounce ya hau a ranshi yace ma marayu zai sayawa suturu da abinci as always ba abin da zeyi da kuɗin shikam.
Tunda oganta ya shigo da namiji acikin daren as usual suna wannan watsewar da suke suna surutai da hargowa jikinta ya ɗauki rawa tana gani hala ita kanta sai Allah ya kamata da mijinta yake kawo mazaje yana aikata baƙar ɓarna dasu amma tana zaune dashi bata ɗauki wani matakin ba to ina matakin ɗaukar tana talaka lilis?? Ina matakin ɗauka tunda da sharaɗin ba ruwanta da rayuwarsa tare da alƙawarin duk abin da taji ta gani bazata gayawa kowa ba in return ran mahaifiyarta fansa gayin komai ita kuwa meta haɗa da mahaifiyarta a duniya kawai gwara ta fita waje ba yau ta saba kwana a waje ba idan yana watsewarsa don ta tabbatar wayewar garinma se su iya kaiwa 12 na rana basu farka ba ansha giya to an bugu! Ganin abin yafi ƙarfin kanta ya sanya ta buɗe ƙofar baya ta sulale apartment ɗin can na Leo ta zauna akan chair's ɗinsa tana kuka tana lulluɓa da hijabin jikinta tare da addu'a ubangiji ya kawo mata mafita ta alkhairi.
KAMPALA ESTATE
BILKISU GALADANCHI
2025
FREE PAGES