KAMPALA ESTATE

Page 3

by @68billygaladanchi

KAMPALA ESTATE


    NA


BILLY GALADANCHI


ADABI WRITER'S ASSOCIATION


     03


Kiran sallan asuba a masallacin cikin Estate ɗin ya tilasta mata tashi a ɗan razane, ƙarewa wurin kallo tayi aranta tana jajantawa rayuwarta zama wurin, kallon pool ɗin ta yi dake a rufe sannan ta miƙe tana tunano mafarkin da tayi wai ta faɗa a ruwan kuma bata iya ruwa ba ta nutse, addu'a ta karanto lokaci guda mahaifiyarta ta faɗo mata nan da nan idon ta suka yi raurau kamar zata fashe da kuka kwana biyu bata san halinda take ciki ba tunda ya karɓe wayarta, wani ƙololon baƙin ciki ne ta tokare a wuyanta bata taɓa zaton cewar auren da tayi don ceton ran mahaifiyarta zai zame mata masifa ba ita kam! A hankali ta juya zuwa gida tana addu'ar Allah yasa be farka ba, tana shiga parlour ta ganshi a tsaye kamar me neman abu jikinta ne ya fara rawa ta zube akan gwiwowinta muryarta har na rawa ta ce


"Ya Bukar ina kwana." Da wannan gwardagar muryar tasa ya ce "Lfy lau daga ina kike?" Tana sosa kai tace


"Yaa Bukar daga kitchen nike naje in zubar da abu a dustbin." Ƙare mata kallo ya yi sannan ya ce


"Zan tafi Malasia daga nan in wuce China wata biyu zanyi saura inji ance kin fita wallahi karkije ko ina har in dawo kuɗi kuma kinsan inda suke idan zaki tafi kasuwa ki tabbatar da driver kuka je saura kuma ki hanawa abokaina zuwa inci ubanki wallahi."  Jikinta yana rawa tace


"To ubangiji Allah ya kiyaye hanya in shaa Allah zan kiyaye." Yana shafa cikinsa ya ce "Akwai abin da nike jira nan da shekaru biyu zan fara tarawa da ke yanzu akwai abin da  yasa dole in kalleki in ɗauke ido, kuma inga idon ki akan wani ɗa namiji inban tsiyayar da idonki ba." Shiru tayi saboda nauyin da maganar ta mata yana lashe lip's kamar tsohon maye ya ce


"Mahaifiyarki idan muka dawo zan kaiki ki ganta." A hankali ta ce "To." Yana barin wurin ya ce


"Make me something for me to eat and ga sabuwar wayarki can da new sim na saya miki, number Mamankine kawai a ciki bana son kina waya da 'yan iskan layinkunnan kuma inji labari ance kinje gidan kiga yanda zamu kwashe da ke a gidannan kin sani sarai duk inda kika motsa ina da yalwar masu saka miki ido." Muryarta yana rawa ta ce "To." Da sauri tabar wurin ta wuce ta ɗaura alwala a ranta ba ƙaramin jin daɗi ta yi ba jin cewar zeyi tafiya duk da tasan abokan holewarsa zasu riƙa zuwa ko da hakan ma ai tasan tabbas ba wanda ze dake ta, a ɗayan ɓangaren kuma  tana jin zafin watannin daya ƙara akan wanda tayi batare da ta tafi wurin Mahaifiyarta ba, a haka tayi sallah a kitchen ta yi azkhar a bayyane sannan ta yi chips kawai da egg se ruwan shayi me ƙamshi..


**************

   Amrah tunda ta shigo jikinta ke wani iri mazari tsabar tsoron abin da take shirin aikatawa, ta sani sarai ba lallai ta samu biyan buƙatarta ba amma shin ya zata yi da rayuwarta? Haka zata tabbata tanada aure amma kamar batada aure bayan tasan mijinta lafiyarsa ƙalau? Tana matsawa kusa dashi idon ta ya sauka akan hoton Joystick ɗinsa daya turawa wata suke kan cat wani bugawa ƙirjinta ya yi ras sai da ta dafa kan kujerar, ƙamshin jikinta ne ya sanya ya shaida zuwanta ya ɗago ya kalleta fuskarsa a murtuƙe cikin hasala ya ce


"Amma Amrah so nawa zan gaya miki cewar ki daina shigomun ɓangarena kanki tsaye batare da ma na buƙaceki ba?" Muryarta yana rawa ta ce


"Al'ameen sai yaushe zaka buƙaceni? Watanni nawa zan ɗauka batare da ka saukemun haƙkina ba bayan kanada ƙarfi da lafiyar sauke haƙƙin nawa tunda hakan be taɓa hanaka zama kana turawa matan banza tsiraicinka ba suma suna tura maka nasu, kaji tsoron Allah Aminullah ka sani duk abin da kake wallahi Allah yana ji kuma yana gani sannan kuma baya bacci." A hasale ya miƙe yana mata wani kallo kafin a zafafe ya ce


"Ina da mace mara fasali irin ki ya bazan nemi wasu matan ba, ke gakinan ba shape ɗin jiki me kyau ha Amrah, banda tulin ɗuwawu da ƙaton ciki meye a jikinki yanxu da zance kizo mu yi sex a tsaye wannan ubansun rundunar ƙaton cikin zai tokareni ga kaiwa, ke ba zurfin farji ba gakinan dai banda wayewa ba abin da ke kanki akan wannan katon cikin naki kike so in ƙare, look ina ragawa auren nan ne kawai saboda iyayenmu yau da ace basa raye banga abin da zan tsinta a wurinki ba." Cikin jin zafin maganganunsa duk da ba wannan bane karon farko najin ire irensu daga garesa ta ce


"Wallahi ƙarya kake Al'ameen ni kam nafi ƙarfin ka kirani me katon ciki don baka ganni da shi ba, se dai kai idan kaine da ƙaton ciki, ka faɗi duk abin da zaka faɗa a kaina, ka zageni son ranka but know this yanda kake biyayya haka nima nike biyyayar zama da kai, yanda kake taƙamar cewar ban maka ba wallahi baka mun ba, banda ƙaddara mace kamila irina me zan zauna ina tsinta a wurin fasiƙi mazinaci irin ka?" Wani lafiyayyen mari ya kwaɗa mata daya haddasa mata ganin taurari masu haske kafin taga giccin duhu sannan ta dawo a saiti dafe kuncinta ta yi tana kallonsa da mamaki saboda duk zafin faɗan da zasuyi da Aminu bai taɓa dukanta ba wata dariya me ciwo ta yi sannan ta ce


"Wallahi tallahi billahi Aminu duk ranar da ƙaddara ta kuma aikoka ka saukemun hannunka a jikina wallahi sai na gayawa Hajjyarku kuma ka rubuta ka ajiye kotu zata rabamu da kai, i know my right Aminullah nafi ƙarfin fasiƙin gardi irinka ya dakeni ya kwana lafiya i will let this slide saboda shine na farko amma wallahi ka kuma gigin kai hannunka jikina da sunan duka sai na tabbatar ka ruɓe a gidan yari, maganar sex kuma daga yanzu har abada bana buƙatarka Aminulla ka tafi kaci duk ma matan da zaka iya ci ba sex call ko sex chat ba do what ever you want, and wallahi na gama bibiyarka akan maganar sex." Ta juya fuu kamar zata tashi sama dariya ya kwashe da shi sannan ya ce


"A a tafi dai bana ci, kiyita ajiyarsa acikin pants mayya." Bata ko waigo ba har sai da takai ɗakinta ta rufe da key sannan ta fashe da wani rin ragwaɓaɓɓen kuka, ta sani tabbas a duk duniya babu macen da hala aurenta ya kai ruɓewar nata bata taɓa jin ko da labarin wanda a rayuwa ya taɓa kallon matarsa ya bita da mugayen kalamai kamar yanda Aminullah yake mata ba, cikin wannan yanayin ta fara jiyo surutan neighbours ɗin ta da suke isarta da shi kullum dare wanda a take  ya sanya mata wani muguwar sha'awa da sauri ta bar cikin ɗakin zuwa ɗayan ɗakin sabida ta daina jiyosu.


  Leo yana kwance a saman makeken ganinsa yana dannan wayarsa hankalinsa yaje a wani comment daya gani a wani video da ya yi magana akan matsalar infection a IG comment na yarinyar da ta yi masa karan tsaye


"I hope zaka amsamin magana na koda a comment section before it's too late for me, nasan abubuwa sun maka yawa but jikina yana bani cewar kaine macecin da Allah ya aiko ya ceceni, ina shirin aikata wani abu da zuciyata taƙi amincewa da shi sam Please help me Leo." Sunan ya ƙara kallo da kyau tabbas ita ce Fateema_Zarah! Lumshe idon sa ya yi ya ƙara buɗewa sannan da sauri sai ya tafi wurin DM's ɗinsa na tiktok ya ci gaba da karatun messages ɗin ta.


"Duk inda naje neman taimako a birnin Lagos ban samu ba Leo, jikin mahaifiyata sai daɗa rikicewa yake ina tsoron in rasata banida kowa, na koma asibtin da suka bamu taimako sunce free treatment ya ƙare, idan mahaifiyata ta rasu banida kowa nima hala mutuwa zanyi." Lumshe idonsa yana tunanin Ohhh shin after that free treatment ya zata an wuce wurin koda yake ya san cewar cancer sai masu hali, a hankali yaga bayan wannan ta shafe wata biyu kafin ta turo masa wani message daga nan messages iri iri masu ban tausayi fin hamsin har na ƙarshe ƙarshen suka ɗaga masa hankali.


"Wani mutum dake zuwa wurin Mamana siyan boli na roƙeshi taimako yace sai idan zan aureshi, I'm just 18 kuma ban sanshi ba ina jin tsoron in aureshi ya cutar da ni, amma yace idan na aureshi zai taimaki mamana harta samu lafiya don Allah ka bani shawara in aureshi ?" Bayan kwana biyu ta ƙara turo wani


"Bakace komai jikin mamana yanata tsanain my pilot, bansan yanda zanyi ba amma zuciyata bata kwanta da mutumin nan ba, duk da haka zan aureshi saboda mamana." Gaba ɗaya ficewa yayi daga DM ɗin saboda ba zai iya ci gaba da ganin waɗannan saƙunan masu kare zuciya ba, shi ya tasone a cikin dukiya da gata me yawa be taɓa sanin cewar akwai mutane da suke rayuwa a haka ba, ya sani tabbad akwai talakawa don yasan akwai arziki akwai talauci, amma shin ƙuncin da ake magana haka yake? Ba mahaifi  ba kuma 'yan uwa sai tarin damuwa? Cikin ɗaurawa kansa alhakin komai ya ce


"Fateema Zarah Allah yasa kina hannu na gari kuma Allah ya bawa mamankin lafiya." Kifar da wayar yayi yana tunanin ta ina zai fara neman ta? Anya ma ze iya kuwa? Cikin lumshe ido da buɗewa ya ce "Da safe i will talk to Nannyta about you Zarah please wait for me." Ya ƙarashe maganar jikinsa duk a mace


**************

Bukar ya bata wayarta ya tafi abinshi ita kaɗai a irin wannan katafaren gidan ba kowa se waya da tv da wutar da bata ko gyangyaɗi, ada kullum tunaninta masu kuɗi suna jin daɗinsu amma she now come to realise cewar dukiya bata baka jin daɗi, Bukar be rage ta da komai ba, ya bata dukiya don akwai Atm a hannunta har guda biyu se dai yana kule da abin da take ɗauka a bankin, akwai zunzurutun kuɗi a hannunta cash, akwai manyan motoci da yace nata ne, kawai kuma driver duk inda zata je yana kaita, Bukar duk inda yaga abu komai tsadar sa yakan saya mata, suturu kam batama san inda zataje dasu ba, kayan shafa kuwa shine yake nuna mata yanda zatayi using idan ya kawo fatar nan ba kalar ƙyallin da batayi, ya kance taci abubuwa masu kyau ta ƙara girma nan da shekaru biyu ze angwance da ita, abu ɗaya zuwa uku ne damuwarta a gidan Bukar,

Bukar Gay ne banda kawo maza a gidan ba abin da ya iya idan yaga koda alamar ta kalli yaron daya zo dashi ya dinga dukanta kenan kamar jaka akan tanaso ta lallace tana neman maza, na biyu kuma saurin fushi komai duka komai zagi se na uku hanata fita, hanata ƙawaye, hanata hulɗa da kowa a ciki har mamanta! Bata zuwa ko ina baya kuma bari a zo mata, karatun data ƙwallafa a ranta ya hana ƙarasawa saga secondry da dama ta kammala shikenan, duk waɗannan abubuwan yace idan ta gayawa wani se ya kashe ta ya kashe uwarta, ba laifi ya taimaki mamanta kuma ta samu sauƙi har ya ƙarawa wurin sana'arta girma amma kullum tunanin Zarah mecece makomarta? Rayuwa da fasiƙi haka zata rayu a cikin ƙuncin? Tasan dangin Bukar don ya kaita kowa ya ganta kuma sunzo biki wasu daga ciki amma shin menene ma dalilin daya sanya gaba ɗaya baya son hulɗar ta da kowa ciki hadda danginsa! A hankali ta furta


"Leo pray for me and my mother please." Ta kalli wayarta da kyau da zaran ta yi yunƙurin buɗe koda whatsapp ne Bukar na kallonta ta rasa da me ya haɗa abin wayarta baya barinta yin social media ko kaɗan abin da tafi sabawa dashi the most kenan.


ALIYU


Yau bayan sun kammala breakfast Leo bin bayan Nannyta ya yi zuwa ɓangaren ta, a saman cinyarta ya ɗaura kanta yana kallonta yana wani tunani, cikin hikima tace "Wani abu yana damunka ne Aliyu?" Murmushi ya sakar mata har seda haƙoransa dake nan a jere farare tas suka bayyana, dimples ɗinsa na duka side biyu suka loɓa masu faɗi da zurfi, yatsa Nannyta ta zura a cikin ramin dimples ɗin tana dariya ƙasa ƙasa "Kana mamaki idan nayi saurin ɗago halin da kake ciki ko? Hmmm nice fa na renaka Leo gayamun menene." Dariya ya yi me sauti kafin yace


"Ina shan gori akan wannan renon amma ba komai zan rama, Nannyta idan mutum baka sansa ba ya dinga turo maka saƙonni ta socila media kusan shekaru biyu ya shafe yana bibiyarka baka taɓa kulawa ba kuma sai rana guda kawia kaga mutumin ya daina maka saƙo wata kusan 6 daya wuce daka bibiyi tsofaffin saƙunan sa sai kaga duk neman taimako ne akan lalurar mahaifiyarsa da bata lafiya kuma basuda kowa ga me tura saƙonnin macece, daga bisani ma sai tace zata auri wani akan sharaɗin ze taimaka wa mamanta ta samu lafiya shin ya mutum zeyi?" Nannyta ta yi shiru kamar me tunani sannan can bayan shuɗewar wasu mintuna ta ce


"Ka nemeta, macece ko namiji ne ka nemeta Leo koma a ina take ka taimaka mata, wato duk tsananin ciwon da zaisa mace ta auri wani don yace zai taimakawa mahaifiyarta mata lafiya kayi tunanin irin ƙuncin da kutumin nan ze shiga, kai ai kaga kanada ambition, kanada burirrika da wasu kayi achieving wasu kana neman kayi to kwatantawa macen dake da burka batada kowa se mahaifiyarta zata sadaukar da komai nata ta tafi auren da babu tabbas akan sa saboda uwarta ka nemeta ka kuma taimaka mata Fisabilillah." Wani irin gauron numfashi ya sauke kafin ya ce


"Nannyta i felt bad, jikina yana bani cewar duk abin da ya sameta laifina ne, tace mun she is just 18 how can 18 years old girl make this huge decision on her own." Nannyta ta ƙara jinjina al'amarin tace "Because that is huge! Koma menene yafi ƙarfinta Leo." Yana ƙara gyara kwanciyarsa ya ce


"Nannyta ina zan fara nemanta? Tayi auren fa saboda rabon da tamun saƙo 6month kenam." Nannyta na kallonsa da damuwa cike a fuskarta tace


"Jikina abu daban yake bani Aliyu look for that girl kanajina?" Gyaɗa mata kansa ya yi kafin ya ce "Nannyta Naan bread and beef danderu nake so." Tana gyaran zamanta ta ce


"Leo baka taimakawa jikin tsufan nan nawa wai Naan bread fa." Dariya ya shigayi ƙasa ƙasa kafin ya riƙo hannunta ya ce "Nannyta abincinki daban ne duk duniya ba macen da zata girkamun abu inji daɗinsa kamar naki shiyasa kiyi haƙuri kullum fatana Allah ta ƙara miki lafiya da tsawon rai me amfani." Dariya kawai ta yi sannan suka shiga wata hirar.


*KAMPALA ESTATE.*


Amrah yau fuskarta a kumbure ta tashi dashi kuma tasan halin matan kampala estate musamman na cikin mini gate ɗinsu yanzu zasu fara tuhumar ta, akan hakan yasanya ta gagara fita a sanda tasan duk zasu fita ta zauna abin ta har duk suka fita sannan ta shirya kayanta a jaka ta fice a cikin zuƙeƙiyar motarta kawai hotel ta tafi tayi logging a ranta ta ce 2 days zata yi ta huta kafin ta koma wannan Estate ɗin. Yamma sanda duka mutanen mini estate suka hallara bata fito ba sunsha mamaki but basu damu ba saboda duka matan suna ganin kamar ajinta be kai dama tana rayuwa irin wacce suke ba kawai saboda ita ɗin mahaifinta yafi na kowaccensu kuɗi ne amma she is too local for their liking kam, Raheema anan ta zauna zaman zuzuta darenta na jiya a cewarta an bata kyautar 5.m akan zata saya wani sarƙan gwal data gani online, ita ma Meenah haka ta zauna tana fallasa nata sirrin har kowacce ta tsumu da zagwaɗin son samun miji irin na wata don a zuciyar kowacce tana yaba kyautar da mijin wance ya yi ba nata mijin ba kai tsaye. Raheemah a duk cikinsu tana masifar son kasancewa tare da mjjin Meerah duk da kuwa bata taba kasancewa da wani namijin ba tun bayan aurenta amma haƙiƙa yanayin yanda Meerah ke zuzuta ƙwarewar mijinta a shinfiɗa yana ƙara sanya mata shauƙin sa kowane lokaci tana jin cewar hala idan ta sameshi ko da so ɗaya ne a shinfiɗar ta ta huce takaici?? Ba tun yauba take so take kuma neman hanyar da zata samu number wayarsa ido a rufe amma Meerah ta cika wayo. Yau suna zaune mijin Raheemah ya dawo inda ɗaukacin matan suka mayar da hankalinsu a kansa, Meenah se wani yawun sha'awa take haɗiya don a kaf duniyarta bata ga namijin daya kwanta mata a rai sama da mijin Raheemah ba his calmness is something else ya Rahman zata iya kashe aurenta sanyinsa yana burgeta ainun, haka ta zauna kallonsa su duka ma shi kuwa tunda driver ya buɗe masa ya sakko ko kallon inda suke be yi ba saboda ya tsani wannan zaman, kallo ɗaya ya musu ya ɗauke kansa ya soma takunsa a cikin wannan tafiyar ta maza masu wadataccen body structure me aji sa jin daɗi wanda duniya ta wadacesu, kamshinsa me ƙarfi da kwantar da zuciya a take ya mamaye ilahirin wurin Meenah ta lumshe idon ta a zuciyarta tana addu'ar Allah ya kai damo ga harawa! Ita ɗinma number wayarsa take nema idon ta a rufe amma ga alama ɗaukacin matan Estate ɗin basu gama yadda da juna ba hala shiyasa sam basa wasa da lambar wayar mazajen nasu hmmm.


KAMPALA ESTATE

BILKISU GALADANCHI

2025

FREE PAGES

***