Page 4
*KAMPALA ESTATE*
Na
*BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
04.
Majid battle water ya fara ɗauka a fridge ya sha sannan ya zauna a cikin parlor ba tare da ya cire shoe dake ƙafarsa ba, resting back da head nasa gaba ɗaya ya yi a jikin kujerar yana sauke numfashi a hankali me fita da wani sihirtacce kuma gigitaccen ƙamshi me kwantar da zuciya, Majid Merah kyakyawan matashi ɗan kimanin shekaru 36 a duniya me ji da nera, ƙirarr jikinsa irin ƙarfafan mazan nan ne masu kula da exercise yana nan da wani faɗi da kuma jiki a murɗe yanada tsayi kam da dark skin colour da gyaran da take sha ya tilasta mata yin shige da ruwan skin na Black Americans! Yanada ƙananun idanu wanda daga nesa zaka ce hala wane idon sa a rufe suke seka matso shanyewarsu da yanda yake kallon mutane zai kusan sumar da me kallon saz yanada ƙananun lashes da suka yiwa ƙananun idonsa kyau saboda dacewarsu, majid bashida dogon siririn hanci sedai ba a dame yake ba ƙofofin hancinsa sunada ɗan faɗi, yanada faɗin fuska da tsawon haɓa me ɗauke da saje da gashin baki daya zagaye laɓɓansa masu kauri da girma kuma pink shar! Baya tara suma a kansa kowane lokaaci zaka ganta a aske tana wani haɗa step after step me shaƙi da kyawun kallo, Majid irin mazan nan ne masu nonuwa a ƙirji wanda workout ya ƙara taimaka musu suka fito cas da su! Akwai kuɗi duk da iyayensa da bazarsa suke rawa saboda mahaifinsa tsohon lakcara ne a jami'a amma shi Allah ya bashi duniya tun yana ɗan shekaru 24 saboda ya tashi da huzling sosai baya wasa da nema kafin yakai wannan matakin ba irin wahalar da bai sheba amma yanzu abubuwa sun buɗe masa don kampanoninsa uku, kuma yana shan wahalar tsayar dasu, A birnin Lagos ya haɗu da Rahima shekaru 8 baya yanzu aurensu shekaru 6 amma bata taɓa haihuwa ba a cewar ta ina zata kai body structure ta idan ta haihu? Wani kalan azababben son duniya ne da Rahima idonta a buɗe yake saboda ba laifi ita iyayenta suna da kuɗi, Ehmm zakuyi mamakin jin cewar duka matan Kampala Estate sake cikin mini estate feminist ne banda Amrah kacal amma dukansu Rahima tafi sauran ɗauka da zafi! Duk wannan fitinar shan kayan mata da ihun kuɗi Rahima idan kukaga ta basa Majid jikinta to tabbas kuɗinsa take buƙata, kwata kwata bata bashi jikinta sai sanda take so gashi shi kuwa Majid ya taso ne a gida irin na dattako da sanin ya kamata da kuma addini don ma Lagos ta ɓatashi, Haifaffen garin Kaduna ne bahaushe ne zallansa ba sirki, She is practically sex starving him don kawai yanada dauriya ne amma yanayin busy life ɗinshi sam baya bari ma sha'awa tayita taso masa wani zubin se ya shafe sati abin be zo kansa ba sedai duk sanda yazo masa da kyaututtuka da lallami yake samun kanta kafin ta bashi haɗin kai, bata bashi abinci sam shi ze iya cewa be taɓa cin girkinta ba don batayi sam! Kai gaba ɗaya rayuwar auren nasa abin tausayi ga mahaifiyarsa kullum burinta taga jikokinta a ɓangaren Majid amma abin yana neman faskara saboda muguwar matarsa.
Kallon nutsuwa Meena ta saukewa Rahima kafin tace "Madam yau oga ya karya record shi ya fara dawowa ki tashi ki tafi mana." Wani kallo ta watsa mata kafin ta taɓe baki "Lallai ma Meenah kin rainawa ajina se kace wacce batada yanda zata yi se a wurin namiji? Nifa ko kyauta Majid ya bani sena raina masa a gabansa don ya san nafi ƙarfin duk wani abun tsiyarsa, in tafi akan ga ubana ya dawo? Can yaji dashi." Dukkansu dariya suka kwashe da shi Sameerah ta ce "Kina burgeni wallahi ƙawata ni abin da yasa kuke burgeni ko gaba ɗaya ke da shi kowa aji, ji yanda ya ɗauke mana kamar be san Allah ya ajiye wasu kyawawan halittu masu aji anan ba." Tsaki taja sannan ta ce
"Ku yake nunawa wannan amma ni yanzu da zanje masa ai sujjada ne kawai ba zemun ba." Suka sake kwashewa da wata banzar dariya a wurin, suna zaune suna ihunsu da hire hire har duka mazajen suka dawo a lokacin isha ta yi amma acikin su ba wacce tamayi maganar yin sallah bare aje gayi daga baya duk suka yiwa juna sallama suka wuce gidansu. A parlour ta tarar dashi ya bita da wani kallo kafin ya ce
"Amma Rahima ban gaya miki duk daɗin hirar da kuke yi ba ku daina miƙe ƙafa magrib ya wuce har isha ya riskeshi ba baku tashi kunyi salla ba." Wani irin mugun kallo ta ɓalla masa kafin ta ce "Saboda gani masalla ba wacce ta tashi ko tayi maganar se kawai in wani ce atashi a yi? Nace bazanyi sallan bane tukunna ma bare kace zanyi idan nayi wanka zan haɗa dama ko asr banyi ba ai." Bakinsa ya hangame yana kallonta har ta ɓacewa ganinsa sannan kawai ya jinjina kansa yana tunanin yanda akayi be ankara da rashin son ibadar Rahima ba se daga baya tayi nisa batajin kira sam!
Leo ya shirya tsaf ze dawo Lagos saboda abubuwa biyu na farko akwai sabon Estate ɗin su a Banana Island da ake kan aikin ze duba aikin, na biyunsu kuma Zarah! Zarah ta hanashi bacci tunaninta ya masa yawa ainun bashida sukuni yana neman zarah koda zasuyi yaƙin duniya na biyu da mijinta saboda ya aureta akan tilas taimakon ba dole bane saboda haka a sake masa zaransa, zara tasa ce ba yanda wani ya iya da ita, ze nemi zarah indai internet yana aiki zeyi akan acc ɗin zara na IG da Tiktok da kuma number wayar da ta rubuta masa a DM na IG a cikin wani saƙo da take cewa"Leo call me i am dying slowly ina neman taimakonka ido a rufe."
Ya iso very late a Estate ɗin saboda ba nan ya fara tsayawa ba, wuraren 11 na dare ya iso Estate ɗin driver ya ajiyesa a bakin gate kamar yanda ya yi umarni ya ce ta tafi yaje ya nema masa Youghurt da gasashiyar kaji don haka da ƙafa ya iso yana mamakin dama cleaners ɗin basu rufe masa gate ba? Taɓe bakinsa ya yi duk da akwai tulin securities but her prefer ace gate ɗin sa a rufe yake ko yaushe, takawa ya yi zuwa main entrance na gidan har zuwa ƙofa inda ya kafe abin da ya gani da ido cikin mamaki, kafin cikin nutsuwa ya ce "Waye a wurin?" Da sauri ta zabura tana kame kame ta kasa kallonsa idon ta da kanta a ƙasa jikinta ya soma rawa cikin tsoro muryarta yana rarrabewa ta ce
"Kakkkayi Haƙuri nna kwanta maka anan." Da mamaki ya ce
"Wacece ke kuma me kike anan?" Tana sussunne kai ta ce "Kayi haƙuri." Wani kallon takaici yabita da shi kafin ya ce "Im asking who are you and you are telling me sorry yanzu yanzu zan kira Estate security suyi waje dake." Jikinta ya ƙara shiga mazari ta fara magana a rikice
"Kayi haƙuri kaji ga gidanmu can abin da ake a ciki baya barina bacci ina jin tsoron kwana a wurin shiyasa nake kwana anan kullum ko wurin pool yanzu ma naga hadari na kwanta anan." Cikin mamaki ya ce
"Me ake agidan naku da ke hanaki bacci?" Ya gano ƙanwar wancen mutumin ne da yake dukanta kullum, ita kuma se da ya wurgo mata wannan tambayar sannan ta gano cewar ta gama kwafsawa, cikeda tashin hankali ta na dafe bakinta ta ce
"Wa ni? Me kuwa akeyi ba fa komi kawai cikin gidan ne ana bani tsoro nafison waje." Binta ya yi da kallon nutsuwa a ranshi ya ce "Wannan child abuse ne ba komai ba, a sarari kuma ya ce
"Ina mamanki da babanki da zasu barki ki fito anan ke kaɗai acikin dare." Tana share hawayen daya zubo mata don ta fara tsorata sosai ta ce
"Kayi haƙuri ai ni mamana batada lafiya babanmu kuma ya rasu tun ina ƙarama, ni da yaya Bukar ne kawai anan se abokanshi dake zuwa suna kwana shi ya yi tafiya ni kuma banson kwana tare da su ni kaɗai." Da mamaki ya ce
"What yayi tafiya ya barki ke da wasu maza shi wane irin yaya ne wai? To ina mamanku.?" Hankalinta a tashe ta ce
"Bata tare dani." Shiru ya yi yana ƙoƙarin yin kyakyawan tunani akan wannan al'amarin me rikitarwa shin wannan wane irin haukane a banza?" Ganin zata ɓata masa lokaci ya sanya ya ce "Miƙe ki koma gida." Hannayenta biyu ta haɗa wuri ɗaya kafin ta ce "Ai rufamin asiri zakayi in kwanta nan abina wallahi tallahi ban iya sauraren surutun da suke kuma ina bacci bayan haka tsoronsu nake ji don Allah ka barni anan in kwana." Sauke wani wahalallen numfashi ya yi sannan ya ce
"This place is not zafe for you dear, akwai kunamu, macizai, cinnakai da sauran ƙwarin da ba lallai security Estate su kula da su ba, you will end up getting hurt if you continue being stubborn now get up ki kwana a gidan nan kafin safe ki koma gidanku but gaskiya you are too small da ze barki ke kaɗai on top ma da wasu mazan da besan halinsu ba yanda duniya ya lalace." Bata masa musu ba sabo Habib he is trying so bad to rape her shiyasa tun magrib take zuwa nan da Bukar ya yi tafiya take bankwana da kwanan cikin gidan don far mata yake ƙokarinyi ba abin ta gayawa Bukar ba tafishi shan wahala ze ce ta iskance kar tayi wasa da rayuwarta ita ce Luck ɗinsa a duniya. Suna shiga cikin gidan ya nuna wani ɗaki a ƙasa da hannunsa
"Don't make any noise anan malama banason surutu, and banson ƙazanta ki gyara toilet da bathroom idan kin tashi." Godiya ta masa har ta juya ya ce "Kinci abinci?" Cikin fargaba ta ce "Banci ba saboda tun magrib nake wurin." Fuskantar ta ya yi gaba ɗaya kafin yace "Akan me." Muryarta yana rawa ta ce
"Don Allah malam ka daina tambayana abubuwa wallahi zaka sa in faɗa maka abun da zeyi sanadin rai na dana mahaifiyata ni dai ka taimakeni in riƙa kwana a waje kafin bukar ya dawo wallahi Habib ɗincan ɗan iska ne." Shiru yana kallonta duk da taƙi ta kallesa se can ya ce
"Ok zanje ɗakin Aaliya in nemo miki kayan bacci you take birth and change sai ki fito ana kawo abinci kici kije ki kwanta." Ya juna yana shirya yiwa yayanta magana duk sanda ya dawo daga tafiya aranshi yana cewa wai ko beda hankaline?" Ɗakin Sister shi ya shiga dayake idan sunzo Lagos duka gidan anan suke sauka shiyasa ya nemo wata rigar bacci cotton har ta wuce gwiwa da wata inner cap ya kawo mata ta karɓa saboda har lokacin tana zaune a wurin tàna jiransa, karɓa tayi batare da ta kallesa ba still ta miƙe jikinta yana rawa ta wuce ɗakin daya nuna mata sai da ta kimtsa da kayan ta wanke nata da detergent data gani ta shanya a cikin bayin sannan ta fito ta zura dogon hijabinta tana shirin kwanciya taji knocking ta miƙe da sauri ta buɗe ɗakin ta kalleshi, da sauri taja baya ƙirjinta ya wani irin buga a ranta tace Pilot ya fara mata gizo ne? A sarari kuma ta ce "Ina whni." Murmushi ya mata da ya kusa sanya ta suma a tsaye tsabar kyaun fuskarsa da kuma tabbacin cewar Leo ɗinta ne, a hankali ya ce
"Come out and eat." Da ƙyar ta daidaita nutsuwarta ta fito tana kallonsa suka jeru har ƙasa akan carpet ya tura mata leda ɗaya da roba Youghurt tsabar yanda take satar kallonsa kasa ci ta yi sosai har ya lura da hakan ya dakatar da cin nasan ya ce
"Ki sake jikinki, wannan Estate ɗin na mahaifina ne 85 na gidajen Estate ɗin nan haya suke a ƙarƙashinmu ragiwar 15% ne muka sayarwa, hakkin mune mu kare duk wani mazaunin cikin compound ɗin nan so ki sake jikinki you are just like Aaliya my little sister so i will protect you kinji now eat your food ki daina kakkafeni da ido yayanki ma dole za'a masa magana ya daina barinki da gardawa a gida." Shiru ta yi kafin ra sadda kanta ta gaza cewa komai rayuwar yazo mata kamar a mafarki yau gata ga kuma Leo amma yafi ƙarfinta dama ance he is so kind rashin duba Dm's abubuwa ne sun masa yawa. Da ƙyar ta ci naman ta sha Youghurt ta koma ɗakin da aka ajiyeta ta shiga juyi tana tunanin rayuwarta da makomarta shin ko ta tare Leo ne da maganar halin ƙuncin da take ciki ya taimaka mata?? Da wannan tunanin tayi bacci.
Tun 4:30 ta farka ta shiga ƙaƙale gidan kamar ba gidan ba, kitchen da ko ina sama ne kawai bata hau ba jin ana kiran salla yasa ta tafi ɗakin tayi sallah da wanka ta sauya kayan ta wanke su ta saka nata sannan ta fito, tana fitowa parlour yana dawowa daga masallaci lokacin ƙarfe shida ya bita da ido ta zube har ƙasa ta ce
"Ina kwana Yaya." A hankali ya ce
"My name is Aleo you can call me Leo." Ɗagowa ta yi suka kalli juna sannan ta sauke kanta ƙasa kafin tace
"Yaya Leo an tashi lafiya." Murmushi ya yi sannan ya ce "Sannu naga kin gyara gidan na gode sosai ina son tsafta kizo ki koma gida kar a nemeki." Tana zare ido ta ce "Baxasu nemeni ba zasu iya kaiwa 2 na rana suna bacci Please letme cook for you." Kallonta ya yi kafin ya ce
"Banji akwai wani food stuff a gidannan baiwar Allah karki damu i will order." Tana gyaran tsugunonta ta ce "Noo a kitchen dana gyara akwai almost everything." Shiru ya yi yana duba tsaftarta kafin ya ce "Ya sunanki?" Tana sunne kanta ta ce "Zarah Fateemah Zarah." Jinjina kansa yaa yi kafin ya ce "Ohh nice name to zara a kula da tsafta Please ki dafa to." Tana miƙewa acikin hijabinta ta ce "Nigerian dishes or continental dish?" Tsayawa kallonta ya yi kafin ya ce
"Both." Juyawa ta yi ta soma tafiya ya bita da kallo har ta shige kitchen ɗin sannan ya haura samansa a ransa yana mamakin shikuma wannan bukar ɗin a garin gaɓa gaɓa aka haifesa ne? Ai Aaliya yau zata dawo daga Ukrain sa zauna a tare kafin wancen sakaran ya dawo.
*KAMPALA ESTATE*
*BILKISU GALADANCHI*
*2025*
***