KAMPALA ESTATE

Page 6

by @68billygaladanchi

*KAMPALA ESTATE*


             NA


*BILKISU GALADANCHI*


*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*


   06.


Aaliya dake zaune a parlor tana kallo ce ta taso tana tambayar waye anan?" Zarah muryarta yana rawa tace "Yaa Leo it's me Zarah please Open the door." Tana shirin magana Leo ya ƙaraso wurin ya sakko daga sama yana cewa


"Ke da waye a wurin?" Aaliya ta juyo ta kallesa "Tace sunanta Zarah she is looking for you." Ƙarasowa ya yi ya buɗe ƙofar da tafin hannunsa ta faɗo cikin gidan kamar an cillota ta tsaya tana haki ya bita fa kallo doguwar rigar material ce kawai a jikinta se hula a kanta irin inner cap ɗinnan


"Zarah lafiya kuwa?" Ya tambaya yana mata kallon mamaki da tsoro, Tana shirin zaunawa a ƙasa tace "Habib ne beda kirki banson zama a wurin da yake kwata kwata." Ta ƙarashe maganar idon ta fal hawaye. Duƙawa ya yi yana kallonta duk a firgice take  hakan ya tabbatar masa kome menene to yafi ƙarfin tunaninta da iyawarta, yana zauna a ƙasan shima ya ce


"Waye Habib me Habib ɗin ya miki?"


Kallonsa ta ɗago tayi sai kuma ta dauke idon ta ƙasa ta gaza cewa komai sai hawaye sharr kamar an kunnata, muryarta yana rawa ta ce "Abokin Yaa Bukar dake zama a gidan yana takuramun da yawa ni tsoronsa nake ji." Aliyu shiru ya yi yana nazarinta sosai a ransa saƙawa yake shin ita wannan wane irin mahaukacin Family ta fito daga ciki da basuda hankali? Yaya zasu bar baligar yarinya da ƙarti wanda va muharramanta ba a cikin gida to gidan arna basa haka bare musulmai Hausa fulani, A nutse yana tsatsaret da ido ya ce


"Wane kalan takurawa yake miki?" Jikinta yana tsananta rawa a hankali tace "He is always trying to touch my body kuma ni matar aurece." Da mamaki ya ke kallonta baki a hangame kafin ya mayar da dubansa zuwa ga Aaliya da itama ta yi tsayi ta gaza gane komai ya ce


"Aaliya Please take her to the guest room ta kintsa ta kwanta if she need anything ta gaya miki ki bata." Mayar da dubansa ya yi zuwaga Zarah sannan ya ce


"And you  Zahrah gobe zamuyi magana da ke yanzu je ki kwanta rabu da shi kawai." Gyaɗa masa kanta tayi sannan ta miƙe tabi bayan Aaliya da har tayi gaba suka isa ɗakin a tare, da sauri ta zube akan gwiwowinta tana rirriƙe bedsheets da hannunta ɗaya sannan ta saka ɗayan hannun tana yarfe hannunta ɗayan, kallonta Aaliya ta tsaya yi kafin ta ce


"Is something wrong with you?" Cikin ƙoƙarin daurewaa ta ce


"No am ok." Sai kuma cikinta na juyawa da ƙarfi ta ce "Yea yea am sick and in so much, am having cramps." Aaliya yar ƙaramar dariya ta yi sannan ta ce


"Ohh Sorry eehn,  lemme get you some medicine." Sannan ta juya nan ta zauna taci gaba da juye juye daga bisani ta tattara ma ta wuce Toilet ta samu ta yi amai ta kimtsa kanta, tana fitowa Aaliya na shigowa a bayanta kuma Leo ne amma be ƙaraso ba yana jiran izinin se da Aaliya ta duba yanayinta tace ya shigo sannan ya shigo ɗin ta bata cup ɗin Lipton me zafi tana kallonta, ƙin karɓa ta yi ta tsaya ta yi narai narai da ido kamar zata fashe da kuka, Aliyu yana daɗa harɗe hannayensa a ƙirji ya ce mata


"It's just a tea karɓa kisha mana se kisha magani." A hankali ta ce


"Zanyi amai idan nasha." Cikin harɗe fuska da murya a kausashe ya ce


"Say's who? My friend karɓa kisha kana ki ɓatamun lokaci." Badan taso ba haka ta karɓa tasha rabin cup ɗin duk suna tsaye sannan ta ce wa Aaliya "Sister na ƙoshi." Magani ƙwaya biyu Aaliya ta ɓalla ta miƙa mata ta karɓa ba musu da Lipton ɗin tasha sannan ta miƙa mata cup ɗin ta karɓa ita kuma ta soma shirin amai ya kalleta sosai ya ce


"Don't you dare try it mayar da aman nan." Da mamaki ta kallesa tana dafe bakinta da hannu ya ƙara harɗe fuska,


"Karki mana amai anan mayar dashi." Ƙoƙarin kwanciya ta shiga yi ya ce


"Don't lay down stay still." Da mamakin daya ƙaru tace "Pardon?" Ya ce


"Sit." Zama ta yi tana ƙoƙarin mayar da tashin zuciyar da ya zo mata, gefe guda ga wani ubansun kwarjini daya haddasa mata shakkar sa a lokaci guda, ta zauna shiru Aaliya ta juya shi kuwa ya tsaya a kanta kusan 10mns bece mata uffan ba duk ta gama tsarguwa se can ya ce


"Gyara kwanta da kyau yanzu." Da sauri taja baya ta kwanta tana jan bargon dake kan gadon zuwa jikinta a hankali ya ce "Good night, kiyi addu'a kafin ki kwanta." Da sauri tace "To."  Shi kuwa ya juya ya rage mata ƙarfin fitilan ɗakin sannan ya fice yana jan ƙofar, sama ya taradda Aaliya tana jiransa yana karasowa ta ce


"Yaya who is she." Tsatsareta da idonsa ya yi kafin ya ce


"She is our neighbour." Yana kaiwa nan ya wuce abin sa zuwa ɗakinsa ta bishi da kallo a ranta tace "Shi be taɓa dena kwashe kwashe a rayuwarsa har abada Allah yasa kar wata rana ya kwaso jaraba. Itama nata ɗakin ta wuce ta kintsa ta kwanta abin ta.


************

  Washe gari Sassafe Zahra ta farka cikin ƙarfin jiki ta samu sauƙi sosai, se dai tana so ta canja sanitary pad amma batada shi duk ta shiga takura, tana tunanin yanda zata yi taji ana mata knocking ansawa tayi wata matashiyar yarinya ta shigo daban da uniform a jikinta wannan ga alama 'yar aiki ce irin cleaners ɗinnan, tana russunawa tace


"Good morning ma." Zarah tana kallon ta amsa da "Morning." Yarinyar tace


"Ma it's madam Aaliya that ask me to bring this to you and tidy up your room." Sakkowa tayi daga kan gadon tazo ta karɓi kayan tana ganin sabon pant da pad da kaya har ƙwaya biyu ta fara murmushi nan da nan ta zare towel da aka haɗo dashi ta wuce toilet ta yi wanka sannan ta fito ta tarar da perfumes da oil ta shafa ta canja kayan sannan cikin hanzari ta wuce kitchen saboda lokacin 7 ya gota, ba kowa a parlour don haka kai tsaye kitchen ga wuce ta duba available abin da suke da ta ɗaura breakfast simple Chai tea tayi da club sandwich sannan ta ɗaura Chinese Egg rice da salad ta gaza chicken Wings data gabi duk da sam sam bata samu spices satake so ba sai ginger and garlic taketa using kuma komai yayi so ma shaa Allah. Wuraren karfe 10 ta kammala komai ta sake wanke plates ɗin da zasuyi amfani dashi ta kai dining da komai sannan ta iso cikin parlor tana shirin ficewa ma Aaliya na sakkowa ta tsaya suka gaisa take tambayarta ya jikinta ta gaya mata ta samu sauƙi a hankali ta ce


"Zan tafi gida na kammala breakfast na haɗa da Lunch ma." Da mamaki Aaliya ke kallonta tana shirin magana Leo daga bayanta ya ce


"Yau ɗinma breakfast kika yi da dinner Zarah ke da bakida lafiya." Kallonsa ta yi tana sauke kanta a ƙasa, sautin muryarsa me faɗi kuma a very slow yana haifar mata da kasala me yawa, cikin ƙarfin hali ta ce


"Ina kwana Yaa Leo." Yana zaunawa akan kujera "Lafiya lau, ya zaki tafi bakici abinci ba? Bayan haka kuma ai nace zamuyi magana ko?" Shiru ta yi kanta a ƙasa ita dai bata ce komai ba, ya sake cewa


"Aaliya muje dining let's have breakfast together." Ya sake miƙewa duk suka bi bayansa, da kanta tayi serving na kowa ta zauna itama ta fara cin abincin a nutse wurin ya ɗauki shiru kowa ya mayar da hankalinsa ma abincin da yake ci sai bayan wani lokaci sannan Aaliya na kallonta ta ce


"How do you manage to do all these a cikin ƙanƙanin lokaci this chai tea is in another level." Tana ɗan murmushi ta ce


"Ai it take a while kafin na gama." Aaliya tana murmushi ta ce


"I must confess you are a good cook, am impressed." A hankali ta ce


"Thank you." Aaliya ta sake cewa


"Next time idan zakiyi girki zan koya irin abubuwan nan." Nan ma dariya kawai tayi har suka kammala ita ta fara miƙewa ta ɗauke nata plate sannan ta shiga kitchen ta wanke ta ƙara gyara wurin sannan ta fito, Aaliya ma ta hada nata dana Leo ta wuce kitchen. Bayan sun zauna parlour ita tana ƙasa Leo sai da ya gana nazarinta sannan ya ce


"Jiya kince ke matar aure ce to waye mijin naki daya barki anan kina shan wahala kuma tare da wasu mazan." Sai da ta ɗan saci kallonsa ƙirjinta yana wani irin bugawa sannan muryarta yana rawa ta ce


"Yaya bukar ne."


"Waye Yaya Bukar?." Ya cillo mata wannan tambayar batare da ya ma bari ta sauke numfashinta ba, cikin ƙara ruɗewa ta ce "Shine me gidan dake kallon naka ai wannan ɗin gidansa ne." Gyaran zamansa ya yi yana mata wani kallon mamaki cikin neman sanin wannan kwamacalar ya ce


"Kina so ki gayamun mutumin danaga ranar yana dukanki mijinki ne ba yayanki bane ba.?" Sauke kanta ƙasa ta yi jikinta zuwa yanzu ya fara rawa cikin dakewa ta ce "A shine mijina."


"To meyasa yake dukan ki? Akan me yake barinki a gidansa ke kaɗai da ƙarti yanada hankali ma kuwa? Ina mahaifinki da sauran 'yan uwanki kuma shi ɗin ina yaje da ze barki da gardawa agidansa ke kaɗai." Nan da nan idonta ya kawo ruwa ta shiga ruɗani da tashin hankali muryarta yana rawa ta ce,


"Ya tafi Malasia wata biyu zeyi, ni banida Baba banida 'yan uwa amma inada mamana itama batada lafiya koda yake yace ta samu sauƙi yanzu har ta fara fita wurin business ɗin ta." Ƙureta da ido yayi na wani lokaci kafin ya ce


"Fatima." Ɗagowa idon ta tayi da suka yi kace kace da ruwa ta kallesa cikin dakakkiyar murya shikuwa ya ce


"Shi mijin naki nace wane iri da zai yi tafiya yabarki da gardawa agida suna neman haiƙe miki kuma mecece alaƙarshi da su mutanen dake gidan don nadai san bazaku wuce Hausa fulani ba to ko agaban gaɓa gaɓa koda ace yau su ɗin ƙannensa ne an saɓawa shari'a bare akai ga maganar abokai." Shiru ta masa ta gaza cewa komai sai kuka shaaa a fuskarta cikin takaici ya ce


"Fatima are you hiding something from me? Meke faruwa akan me ne zai rika dukan ki bayan haka zeyi tafiya why can't you go to your mom kafin ya dawo and why are you saying yace ta samu sauƙi ke baki sani bane ko ke bakya zuwa wurinta." Yanzu kam ta fara shiga ruɗani jikinta sai karkwarwa ya ke tana wani kalan kuka da ƙyar ta iya cewa


"You are asking too many questions Yaa Ali, don Allah kayi dukkan tambayoyinka banida amsarsu wallahi because magana kaɗan ze iya saka in rasa komai ciki hadda mahaifiyata, just pray for me kaji." Tsatsareta da ido ya yi kamar ze cinyeta kafin cikin jinjina kansa ya ce


"Fateema Zarah ki saki jikinki don Allah, ki gayamun mecece matsalarki." Jikinta yana rawa tace "Ni Mamana kawai nakeso ta warke banida komai banida kowa sai ita Please don't ask any question wallahi mamana zata iya rasa ranta idan bakina ya furta kalma guda ɗaya akan yaya Bukar." Leo shiru yayi yana nazarin ta kafin a hankali ya ce


"Karki damu Fatima since you are not ready to talk ba sai kinyi magana ba amma if you ever need any shoulder to cry on i will be there for you, karkiyi ƙasa a gwiwa, i promise to be a brother in shaa Allah." A hankali tace na gode sosai Allah ya saka da alkhairi." Ta miƙe tsaye kawai ta nufi waje ya bita da kallo ita kuwa tabar gidan da zummar komai girman matsala bazata ƙara zuwa gidan ba hala so yake ya janyo mata matsala bayan dogon warning da Bukar ya bata akan ambatar duk wani abu daya shafi gidansa ma wani a waje yace wallahi sai ya kashe ita da uwarta har lahira basuda kowa bare ma ace wani ze nemesu!!


Mom Nuaiym.