LATYFAH IMAM BOOK 2

PART 1

by @nanadiso10

LATYFAH IMAM


BOOK 2


NA

  BILLY S FARI

       NANA DISO


SHAFI NA DAYA..



Enyaa... Sautin kukan Noor shine abunda ya tashemu a safiyar yau, gaba ɗaya bana cikin nutsuwata idanuwana sunyi luhu luhu ga ciwon kai da nake fama dashi sosai nayi rama dan duk wanda yasanni abaya yaganni yanzu zai iya tsorota saboda babu kibar nan kwatakwata hatta hancina sai da yataɗa yanzu babu kumatun nan na rame nazama abun tausayi..


"Yaa Allah". Abunda na ambata kenan acikin raina ina mai lumshe idanuwana ina tuna tsanin halin dana shiga acikin prison a hankali na saka hannu na share hawayen dake kan fuskata ina mai kara jin zafin wannan ahali da halin da suka sakani idan ba Allah ya dubeni ba tayaya zan wanke kaina da laifin kissa kasancewata diyar talakawa, Sanin ba sallah zanyi ba ina cikin jini yasanyani miƙewa ina ɗan dafe kaina da jiri yake dibata na dauki Noor a hannuna. Sautin karar tukunya da naji afilin tsakar gidan namu ya tabbatar mun da abinci Iyami ta ɗaura. Daidai bakinsa na ƙafa masa nono ina ambatar sunan Allah hakan yabashi damar cafkewa yana zuka da sauri sauri tausayin yaron ya saukarmun acikin raina ganin irin rikicin da ake ciki akwana biyun nan kowanne ahali suna cikin damuwa da firgici. Iyami ce ta tsaya daga kofar daƙin tana faɗin.


"Jiya ban rintsa ba Latyfah ina ganin wannan shawarar taki ita zamu bi." Wani sanyi naji araina na kalleta sai kuma idona ya soma ciccikowa da hawaye kai rayuwa abar tsoro maraici babu dadi dagani har Iyami bansan wanda yafi wani rashin gata ba. Kallo na tayi tace.


"Ina fatan kinyiwa Noor addu'a? Na gayamiki ki daina sakacin yiwa yaron nan azkar."


"Nayi masa Iyami." Nafada ina gyara zamansa kan katifar dake kusa dani. Iyami ce ta zauna tace.


"Komawarmu garin mu bazai yiwu ba Latyfah sai dai mu bi shawarar ki tabarin gidan nan ina ganin shine kawai sauki agaremu amma bana tunanin ina da kudin da zamu iya kama haya Latyfah." Kallonta nayi ina share hawayena sannan nace,


"Yawwa Iyami mubar musu gidansu duk da kasancewa mahaifin Nana ne ya bamu amma suma watarana zasu iya wulakanta mu kamar yadda wannan ahalin sukayi iyami ina jin tsoron suyi amfani da kudi su kwacemun ɗana." Iyami bata ce komai ba sai bina datayi da idanuwanta tana mai mikewa tabar daƙin, bansan me dame tayi ba sai gata ta dawo ta dauki Noor ina gani tayi masa wanka sannan ta umarceni nima dana shiga bandaki nayi wanka. Har na kusa shiga bandaki naji tace " Wannan ruwan butar ganyen magaryane da kaninfari da ƴaƴan bagaruwa ki tabbatar bayan kingama wankan kinyi tsarki sosai dashi hakan zai sa ki kara haɗewa da kuma samun lafiyar gaban naki. Amsa mata nayi sannan na shiga bakina dauke da Addu'a har nayi komai na gama nafito sannan ta kalleni tace.


"Kinyi alwala?" Bata amsa nayi nace banyi ba nan ta rufeni da fada tace na daina wasa da alwala zama da tsarki abune mai mutukar amfani bama yanzu da bana sallah, amsa mata nayi na koma nayi alwala nafito har lokacin Noor na baccinsa goye a bayanta.


******


    Tsananin tashin hankali su Dady suke ciki kwana biyu zuwa uku yanzu gaba daya dan allura kusan biyu aka yiwa Abdulkareem amma baya cikin hankalinsa hauka sosai ya tabbata garesa wanda acikin ihun nasa babu abunda yake kira sai Latyfah ta dole aka rufeshi acikin wani daki.


Babban ɗakin jinyar ne Babu abunda yake Tashi sai sautin kuka da gurnani da kuma wani irin ƙaraji dake cika zuciya da tsoro. Wata irin larura ce da ta ɓoye duka ƙarfinsa da kyawunsa a tare dashi wato larurar hauka data kasance ba abu mai sauƙi ba. Duk yadda liƙitocin suka kai da riƙonsa amma sun kasa sun gajiya sai kallonsa kawai da sukeyi ciƙe da tausayi daga gefe kuwa mahaifiyarsa ce tsaye tana kuka sosai cike da tausayin ɗan nata. Sautin muryar Dady ce daga bakin kofa yana cewa.


"Ku koma gida kai da ƴar'uwarka." Yaƙare zancen yana kallon Hameed da idanuwansa suka kada sukayi jajir.  Kafin ya bashi amsa suka ji ɗaya daga cikin Nurse ɗin na cewa.


"Likita ko za'a ƙarayimasa Allurar ne?" Likitan baice komai ba yaƙara buɗe karamar jakarsa yana mai dakko alluran nasa yayi masa. A hanƙali sukaga yafara lumshe idanuwansa yana sauke ajiyar zuciya kusan mintuna goma sai kuma bacci ya ɗaukesa. Ranka yadaɗe ba kuka zakuyi ba haƙuri zamuyi muci gaba da yimasa addu'a wannan lamarin larurar tasa ina baku shawara da adage da Addu'a domin kuwa kwalbar da ta shiga kansa ita tahaifar da haka ko kuma wata larura ce daban daga Allah idan kun barsa asibutin ma babu abunda zamuyi sai allurai wanda hakan zai iya haifar da matsala sosai ga lafiyarsa tunda naga bayanan fitarsa asibiti India komai sunyi masa, saboda haka aci gaba da basa maganinsa, idan yadan samu nutsuwa zanyi iya sallamarsa amma ayanzu kam babu mai iya yimasa komai."


"Yanzu doctor yarona ya zama mahaukaci kenan? Kana nufin bazai warke ba?" A hankali dady yakalleta cike da tausayinta tunda ta dawo sai yanzu yayi mata kallon nutsuwa gaba ɗaya ta fita hanƙalinta tayi duhu har da yar rama." Ranki yadade ai bawa bai isa ya warkar ko yasaka ciwo ba! ciwo na wanzuwa ne bisa ikon Allah. Nafaɗi gaskiyar abunda yakamata ku sani ne akan lalurar dake tattare da dan ku." Doctor ɗin ya faɗa yana ƙoƙarin barin wajen, har ya sanyi gaba sai kuma ya tsaya haɗe da juyowa yana kallon su yace


"Amma wacece LATYFAH ? ya kamata ace tazo ta zauna dashi hakan shine kadai zai taimaka ta wani bangaren saboda yadda bakinsa yakasa dena ambaton sunanta, hakan kuma na nufin akwai wata alaƙa tsakaninsu ta zuciya." Kuka tasaki tana mai ƙarasawa gaban gadon nasa tana rike hannunsa ciƙe da tausayin halin da yake ciki. Dadyn Umar dan Allah dan Annabi kaje kazo da Latyfah, ka dawo masa da ita ko hakan zai fidda shi yanayin dayake ciki". Alhaji mai Lena bai ce komai ba yasaka kai kawai ya fice daga ɗakin. Tun da Dady ya shiga mota yaji gaba ɗaya zuciyarsa ta karye, a iya shekarunsa zai iya faɗar rabon da yayi kuka tun yana yaro. Amma yau ganin Abdulkarim cikin wannan halin gabadaya yasare ya sashi zubar da ƙwalla.


Yadda wayarsa tashiga ringing ya sanya ya dubeta yana ganin sunan Momy akai a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana mai goge hawayen daya zubo masa ya kara akan kunnensa.


"Dady dafatan jikin nasa da sauki? Wlh gani nan hankalina duk ya tashi na kasa samun natsuwa na kuma rasa sukuni, ko dai na biyo ku asubutin ne?" Sai da yayi gyaran murya kamin yace.


"Jiki da sauki za'ace amma Abdulkarim na bukatar addu'ar mu." "Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun ubangiji ya basa lafiya mai ɗorewa, Allah yasa dai Dady ba kuka kake yi ba, Kawai ni kam ka bari nataho."


"No ba sai kinzo ba dan Allah kuka kuma duk wanda yaga Abdulkareem a wannan halin dole ne yayi masa yarona mai himma mai kwazo amma yanzu babu ko ɗaya, ai dole ya zama abun ayi masa hawaye." Sosai wani abu ya tsaya mata arai, wato ƙaunar da yake yiwa yaron nan kenan har yanzu tana nan? amma tsabar kissa bata nuna masa jin zafi ta ba sai cewa tayi. "Ba damuwa Dady Allah zai yaye masa albarkacin al'qurani, ga Umar nan ya kasa samun nutsuwa shima zazzabi ya rufeshi."


"Subhanallahi ". Kaɗai Dady ya iya faɗa sannan ya yimata Sallama ya ja motar zuwa gidansu Latyfah dan yanason zantawa da'ita. da kuma ya ƙarasa gidan sai yaji wani iri acikin ransa amma haka ya danne zuciyarsa yana aika yaro akan ya shiga ya sanar dasu shine yazo. Iyami dake kintsa tsakar gidan ta bashi dama akan yashigo tana mai shiga ƙaramin palon dake ɗauke da kujeru. Duk sallamar da sukeyi gabadaya Latyfah bata jinsu saboda ta shiga tunani har sai da iyami ta dan taɓata sannan ta juyo a ɗan firgice tana gaida Alhaji mai lema a hanƙali. Ita ma Iyami suka shiga gaisawa cike da girmamawa kafin yace.


"Ina mai sunan nawa?" Ni dai da idanuwa na na bisa bance komai ba sai naga Iyami ta miƙe tashiga daƙi ta dakkosa yana bacci ina jinsu suna ɗan taba hira nan yake sanar mata akan sunnah da kuma ragon da za'a yanka, batace komai ba dai naga tayi murmushi ni kuma ina mamakin rayuwar wasu ɗan Adam ɗin, Nasan wannan zaman da yayi bai wuce akan ɗansa ba don haka sai ma nayi kokarin miƙewa nabar musu gurin gaba ɗaya. Cikin sanyin murya naji yace.


"Yarinyata gurinki nazo ya kuma naga kina kokarin miƙewa." Da bazan jiyo ba amma tunawa da nayi da faɗan Iyami akan girmamashi ya sanyani dawowa na samu guri akasan carpet din na zauna. Ina kallonsa ya dago kai yana rungumar Noor a kirjinsa yace.


"Iyami dan Allah dan Annabi nazo da alfarma ne nasan kowannen mu baiji dadin abunda ya wakana ba tsakanin Latyfah da Abdulkareem amma ina so kusani bawa baya taɓa tsallake kaddararsa ayau banzo dan in tilasta miki akan ɗana ba nazo ne na tabbatar da batun sakin da kikace yayi miki Latyfah, don girman Allah ki faɗa mani gaskiya shin da gaske ya sakike?" Mamaki ne ya cikani da baƙin ciki sai ga hawaye yana bin fuskata wato idan bai sakeni ba in koma in zauna shikenan ita macce ba tada ƴancin da ya wuce tayi hakuri da wulakancin namiji da tozarcin sa, haba Auta daga taci albarkacin yaranta sai iyaye su tursasata! Jin nayi shiru yasa Iyami tace,


"Magana ake yimiki fa Latyfah." Cikin kuka nace.


"Tun kamin takardar da kuka hani yayimun ɗaya ai kuma shine ya rubuta da hannunsa wallahi ko shine autan maza bazan taɓa kara zama dashi ba dady kayi hakuri." Ba tare da ya amsa mata ba ya kara wayarsa dake ruri acikin kunnensa yaji ana faɗin.


"Dan girman Allah Dady kazo da Latyfah Abdul kada yakashe kansa kaga har ya farka yanzu yagama buga kansa a jikin bangon". Dakyar ya haɗiye wani abu yana faɗin.


"To gani nan.." Sai kuma kawai yama rasa me zaice. Iyami ce data fuskanci kamar da matsala take tambayarsa lafiya dai ko?"


"Zan dawo iyami bari naje." Dady ya fada yana bata Noor ba tare da yasan me ma zai yi ba gaba daya hankalinsa a yanzu ya koma can.


"Latyfah dan Allah ki daina kukan nan idan dan tanine bazan taɓa yimiki dole akan sai kin koma gidansa ba tunda kin nuna bakyaso to ni dai ina ganin samun nutsuwarki shine nawa dana wannan yaron zamuyi koƙari mu bar garin mu koma kalwa duk da babu nisa sosai Amma akwai wata yar uwar mai gidana dana sani sai tasamar mana ko karamun gidan hayane." Iyami tayi maganar cike da damuwa ganin irin kukan da Latyfah keyi.


"Nagode Iyami ina da kudi a hanuna wanda Abbiy ya bani da wanda yayan nana ya bani kuma suna da kauri ina tabbatar da har sana'a zasu ishemu mufara ko dillali zamu nema yasamu yasiyar da waƴannan kayan namu sai mu samu wasu can idan munje. "


"A'a wannan ai ba dabara bace ba mu dai samu babbar mota takwashemu da kayan mutafi dasu ko kinga bamu zuwa ai mu zauna akasa." Karon farko na saki murmushi dan ni wallahi tsoron mai kudi nake yi da abunsa komai yafita kaina, miƙewa nayi naje na hada takarduna na karatu kaf waje ɗaya. daman Iyami tasa Hameed ya debo mata komai na amfanina. Ban zauna ba sai da na tabbatar nagama komai na kuma haɗe komai sannan muka dafa taliya jallop cikin hukuncin Allah babu wanda yazo har dare sai ma bayan magriba ne sai ga nana tazo itama bata dade ba ta tafi. Hameed ma yakira Iyami ya sanar mata jikin Abdulkarim ne ya tsananta shiyasa bai shigo ba yana gaidani ni da Noor, ko data gayamun babu abunda nace ko naji sai ma kwanciyata danayi raina yana tsananta zafi ganin irin shisshigin da Hameed ke yimana.


********


    Numfashi yaja yana mai tsananin tsoro Akan wannan zamani da muke ciki,


"Yaa Allah!" Ya faɗa yana karanta saƙon abokinsa da yaturo masa.


_"MAN kafito yanzu nasamar maka sabbin Babies da zasu kwashe maka duk kishurwarka tunda dai auren nan ka kasa yi"_ Tsaki yaja sannan ya aika masa da


_"Bana bukata."_ Kara karanta saƙon yayi a hankali hakan ya saka shi cikin yanayi na shakku da gwagwarmaya tsakanin biyayya ga Allah da bukatunsa na zuciya. Zugar da abokinsa yake masa na iya zama wata jarrabawa da ke ƙoƙarin karkatar da shi daga tafarkin gaskiya. Duk da haka, tsoron Allah da imanin sa sun kasance garkuwa a gare shi, suna hana shi shiga cikin haram. Wannan hali na nuna darasi ga duk wanda ya tsinci kansa a irin wannan yanayin cewa ya kamata mu kasance masu ƙarfin zuciya wajen gujewa zunubi, kuma mu nemi taimakon Allah don tsayuwa da jarabawasa.


Yau gaba daya baya cikin nutsuwarsa duba da yadda Abbiy ya rufeshi da faɗa kan maganar aure da yayi masa awaya karon farko Ummy taji ba dadi dan ita anata tunanin indai iyaye nada fahimta sosai da yaransu to dan sun sanar musu da maganar suna son aure ba wani abu bane ba balle shi daya taɓa yin auren ma yasan daɗinsa, kallon mahaifin nasa yayi cike da dana sanin mai tsanani yana mai tabbatarwa akan zugasa akayi akan kursum shi kuwa ko mata sun ƙare wallahi bazai aureta ba.


"Kayi hakuri Abbiy ban tunanin zamu dai-daita da kursum ba, amma duk wacce kuka zaba Mani zan aura saboda ina da bukatar hakan."


"Yanzu Yusuf menene bambancin marigayiya da yarinyar nan da zaka ce baka sonta? Kanwarta ce da uwa ɗaya uba ɗaya".


"Abbiy ka fasan kursum kasan Amina wallahi ko hanya basu haɗa ba a tarbiya duk da zamansu jini daya daga uwa ɗaya."


"Is okay! Nafahimta yanzu sai ka kawomun wacce kakeso nayi maka auran na huta ko? Tunda kana ganin zabin nawa baiyi dai-dai ba."


"Nifa Allah babu mai yiwa yarona auren dole." Ummi tafaɗa tana jin baza ta iya ci gaba da kara da kawaicin da takeyi ba, Murmushi Abbiy yayi yace.


"To sarkin kaunar yaranta kinji nace zan masa auren dole ne?


"Ah to, Abbiy tunda naga har ya nuna baya son yarinyar nan to dan Allah kabar maganarta mana, Allah ya zabo masa ta gari wacce tafita". Cikin jin daɗi Yusuf ya saki murmushi haɗe da miƙewa yabar gurin ganin Umminsa na tare dashi dari bisa dari, A zuciyarsa kuwa Nana na shigowa yaji ya riga yaga matar aurensa inshaa Allahu tunowa da ƙawarta Latyfah da zuciyarsa tayita janyo masa tunanin ta amma yaki amincewa da hakan.


******

   Tabbas safiya ba tada da bambanci da dare, dan kuwa babu wanda ya runtsa saboda tsananin tashin hankalin da suke ciki duk dakiyar Hameed da kokarin danne zuciyarsa sai da ya kokawa dan uwan nasa, mahaifiyarsu kuwa duk ta fita daga hankalinta Dady tun yana rarrashin har yazamana shima ana rarrashinsa. Tunda ta dawo bata zauna ba duk wata dawainiya ta iyayenta duk Hameed ne yayi mata, Umar ma dakyar yabar asubutin tsabagen tashin hankali dan shima sai da aka saka masa ruwa anan yasanar da iyayensu ko dai za'a kara fiddashi waje likitan ya hanasu ta hanyar sanar dasu ko anje babu abunda zasuyi masa.


"Wannan wacce kalar yarinyace mara tausayi da imani Dady? Ni kubarni naje natawo da ita kuna kallon yadda ɗana ya zama sabida macce ku kalli hauka fa yakeyi." Dady kam yama rasa menene zaice, Hameed ne ya riko hannunta yace Ammy please calm down ki natsu Latyfah bazata taɓa zuwa da masifa ba ni kibari zanje na lallabota dan Allah amma ke kar kije."


"Kayi alkawari?"


"Eh Ammy zanje amma ki koma kuma dan Allah kici abinci Dady kai yakamata kana bata haƙuri amma kuma.." Kasa karasawa yayi ganin Momy dasu Aliyu sun shigo.