2
by @nanadiso10
LATYFAH IMAM
BOOK 2
NA
BILLY S FARI
NANA DISO
SHAFI NA BIYU...
Da kallon mamaki Hameed yabi Momy yadda take tsananin kuka kai kace yaronta ke cinkin yanayin da Abdulkarim ke ciki, shi acikin mata masu kissa ma yanada tabbacin baza'a samu irin Momy anan kusa ba, yadda ta zauna abakin gadon Abdul tana rushe kuka sosai ya sanya Dady goge shima hawayen dake kan fuskarsa. Tabbas ɗa da mahaifi sai Allah don wani raɗaɗin bazai taɓa faɗuwa ba ko gogewa a zukatan iyaye idan suna kallon ƴaƴansu acikin lalurar da bazasu iya yi masu magani ba, duk kuwa yadda iyaye suka kai ƙololuwa wajen soyayyar ƴaƴansu bazasu taɓa iya canza komai Allah ya ƙaddara akan su ba, duk yadda Dady yake adawa da halayyar Abdulkarim amma yau shi ne ya tsayar da kowanne harkokinsa yakasa matsawa ko nan da can yana tsaye kansa yana masa fatan samun lafiya inda Ammin su gaba daya tafita hankalinta. Sautin kukan da Momy keyi da Addu'a ne kamar da gaske har zuciyarta yasa Dady yatsayar da tunaninsa yana sauke idanuwa akanta.
"Wayyo Allah Abdulkarim Ubangiji Allah yabaka lafiya tafiyar dakai wannan hali, tun jiya na kasa samun cikakken bacci tsabagen tashin hankali yaro lafiyayya gashi yazama cikakken mahaukaci." Abdulhameed ne ya kalleta cike da karfin halinta yace.
"Momy don Allah ya isa haka, ba kuka zakuna yimasa ba Addu'a yake buƙata garemu."
"Hameed tayaya bazamu kokaba? Tayaya kaduba kaganshi fa." Tafaɗa tana mai rushewa da wani kukan. Ganin dai babu mai sauraronsa ya sanyashi fita daga dakin zuwa harabar Asubutin. Wasu haye yaji shima a fuskarsa dabai shirya zuwansu ba sun sauko masa tunawa da Latyfah, duk yadda yake ƙaunarta sai yaji ya karaya gabaɗaya zuciyarsa tayi rauni tana bugawa da sauri da sauri. A yanzu ya gama yarda da cewa ɗan uwansa na mutukar bukatarta fiye dashi, ya gano kiyayyar da Abdul keyi mata ada gaba ɗaya ta juye ta koma soyayya. Dafe kansa yayi jin yadda yake sara masa yana mai addu'a ko zai samu sassaucin abinda yake ji a zuciyarsa.
"Yaa Allah ina neman mafita agareka akan abinda bana da ikon hana zuciyata, Yaa Allah ka duba lamarin ɗan uwana kabashi lafiya alfarmar fiyayyen halitta". Ya ƙare addu'ar haɗe da jingina ajikin bangon ginin dake kusa dashi haɗe da kunshe idanuwansa ya rufe...
*******
Wani lokacin nauyin duniya yana iya zama mai wahala sosai. Kana murmushi da rana amma da dare sai kaga ka koma hawaye. Hakika manya sunyi gaskiya wani tabo bazai taɓa goguwa ba wani raɗaɗin kuma baya taɓa ƙankaruwa a cikin zukatanmu sai dai yau da gobe ta danne su. Sauke idanuwana nayi akan yarona cike da tausayin wacce kalar rayuwa zaiyi idan yasan waye mahaifinsa kuma ya taso a inuwar da iyayensa basu rayu waje ɗaya ba,
_ "Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun". Na faɗa ina mai goge hawaye na tare da ɗaukar zanin goyansa ina sakashi abayana, sauran bakko dinmu dana haɗa kayanmu aciki na dauka na fiddasu wajen sararin gidan ina ajiyesu, ina kallon yadda iyami take bada umarnin ashigo a kwashi kayayyakin namu da idanu duk na bisu muka fita, Allah ya sani idan tanine to kada mu taɓa musu komai dake cikin gidan mu ɗauki kawai kayan jikinmu, Amma babu yadda na iya tunda Iyami ta nunamin cewa wannan kuskurene da rashin godiya ga Allah dan haka na kau da idanuwa na daga kansu, can na tsinkayo muryarta tana faɗin.
"Yanzu nake kokarin shiga gurinki nace kifito na samo masu mota zamu bisu mushiga cikin garin saboda mu isa da wuri kinga kusan awanni 8 zuwa 9 ne ahanya, Sakko da Noor din na goyasa ko?" Kallonta nayi cike da tausayi komai nata ya ƙare saboda kulawa dani da maraicina, tabbas da za'a samu kaka irinta da iyaye basuyi kuka ba alokacin da ƙasa zata rufe musu idanuwansu, Sosai ta sadaukar da kusan rabin rayuwarta dan kulawa dani gashi yanzu kuma tana kulawa da gudan jinina. Muryarta naji ta sake cewa,
"Latyfah rayuwa bazata taɓa yiwuwa ba sai da jarabawa, matukar baki ajiye wannan tunanin ba kin fuskanci abunda ke gabanki ki kuma manta da wutaccen abu na bayanki to fa rayuwa zata yimaki wahala yadda kike so, kiyi kokarin inganta rayuwarki ta yanzun ke da ɗanki Latyfah Imam ki ajiye komai kamar bai taba faruwa ba, hakan zai sa ki kasance mai nasara haɗe dayin galaba a rayuwa.
"Kò sí ẹnikẹ́ni tí ó lè sálà kúrò ní àyànmọ̀ rẹ̀ Latyfa (Babu bawan da ya isa ya tsallake kaddararsa Latyfah)." Karo na farko da nayi murmushi na miƙamusu sauran bakkon namu dake hannuna dana dauka da nufin bin bayansu sannan muka fita ina cewa. "Iyami bar shi a bayana ki huta kema, yanzu wa zamu bawa mukullin gidan Iyami?" Wani shago na gefen gidan Iyami ta kalla tana cewa,
"Bari mu bawa wannan koda sun zo zasu nememu." Karba nayi na datsa kwaɗo ina cire mukullin na ƙarasa gurin mai shagon ina gayamasa danAllah idan wani yazo daga yaran gidan Alhaji dogo yabasa, kasancewar sanannen mutum ne kuma mai shagon yasansu ya karba yacemun to Inshaa Allahu zai basu, na juya mu kuma muka shige mota muka tafi ina sauke wata irin ajiyar zuciya tare da lumshe idanuwa lokacin da motar ta tashi muka miki hanyar ficewa daga anguwar.
********
Tun tashinsa daga baccin da ya ɗan rintsa daga bayan asubuhi yaji ransa bayayi masa daɗi, Addu'ar tashi yayi daga bacci sannan ya nufi banɗaki bakinsa cike da ambaton Allah ya shiga, sai da yatabbatar yagama wankan ya fito ya shirya sannan ya sanya kayansa marasa nauyi da suka yi masifar ƙarbar jikinsa.
Tun daga matattakalar benen Ummy take kallonsa har ya ƙaraso cikin babban palourn na Abbiy, fuskarsa ɗauke da sallama sai da ya gaisa da Abbiy sannan yayi hugging Ummy haka yakarasa kusa da Anty itama yayi hugging ɗinta daga nan ya rungume Nana da kanwarsa da suke gaishesa ya samu guri yazauna. Abbiy ne ya sauke ajiyar zuciya sannan yace.
"Don fisabilillahi yanzu sai 11 zaka tashi bacci bayan kasan kana da meeting ɗin dana gayamaka."
"Kayi hakuri Abbiy jiya sai 12 na baro gurin kayana shiyasa nagaji sosai ina dawowa daga subhi na kwanta." Murmushi yayi Abbiy yai yace.
"Dama yanzu suke mun zancen kudi don haka sai ku tambaye shi ya baku tunda dai kun ji kayansa daya dari sun ƙaraso, na kuma tabbata an samu tun mi yawa ko ba haka ba?" Anty ce tace.
"A'a Abbiy ai bamayi haka ba kwanan nan ya canza mana wayoyin mu fa." Nana kam ta langwabe kai tana faɗin,
"DanAllah Abbiy." Akaro na farko da yadago kansa yana kallon Ummy jin batace komai ba. Abunda ya lura ma gaba daya hankalinta baya kanta kwata kwata. Baice komai ba dai har suka gama hayaniyar su Abbiy yayi sallama dasu kasancewar Anty ke dashi ta tashi ta rakashi Ummy kuwa cewa tayi.
"Allah yakiyayye". Nana kam bin mahaifin nasu baya sukayi, Ganin duk sun bar gurin ya sanya Yusuf miƙewa daga inda yake yakoma kusa da mahaifiyar tasa yana faɗin.
"Ummy lafiya kike kuwa?" Kallonsa tayi tana tausayin yaron nata tace,
"Lafiya kalau ba komai Abni, kawai dai Abbiy ne..." Sai kuma takasa ƙarasawa.
"Me yayi miki Ummy?" Kallonsa tayi tana ganin damuwar data ƙara lullube fuskarsa. Sai tayi murmushi tace.
"Yana ganin kamar nice na hanaka auran Kursum jiya da dare bakaga yadda yaɓata rai yanamun faɗa ba."
"Wai Ummy duk akan Kursum ɗin kike jefa kanki a damuwa haka?"
"Abni kasan yadda mahaifin Amina yake da mahaifinka ina da tabbacin shine ya kirashi dakansa ya yimasa zancen Kursum ɗin tunda su suna ganin sun gaza."
"Indai wannan ne dan Allah kidaina daga hankalinki Ummy banson inga kina saka damuwa akan Abbiy, In dai wannan zancen ne kibarni dashi danAllah."
"Abni.." takalleshi cike da soyayya irin ta mahaifiya sannan taci gaba da cewa,
"DanAllah indai har kanason auren ka aureta kawai." Wayarsa ya dauka yashiga instagram nan yayi searching sunan Kursum atake sai ga shafinta ya bayyana wasu video din babu kyan gani ko daya shigar tata ma babu wani tarbiya ko kunya ciki ya nunawa Ummy
"Subhanallahi Kursum ɗince wannan?"
"Eh Ummy wannan ma kaɗan kikagani wallahi sai kinga shafin ta na tiktok, yanzu zakiyi mani sha'awar tazamo uwar ƴaƴana? Zaki so ya'yan da zan haifi su zama haka fisabilillahi Ummy? Idan da ace tana da ɗabi'u masu kyau kamar Yayarta ko da bata kaita ba to tabbas zan aureta Amma Ummy a haka da take ni gaskiya kome Abbiy zaiyi bazan aureta ba." Ummy data cika da mamaki tace,
"Ubangiji yazaɓa maka mafi Alkhairi." Ya amsa da "Ameen yaa Allah". Yana rungumeta cike da jin daɗi ganin ta fahimcesa.
******
"Ki kwantar da hankalinki Mahaifinki yace ya kirawo mahaifinsa sunyi magana, Kursum ni wannan aikin na bokan nan fa kamar bayaci, nayi iya yina amma kunkasa samun daidaito tsakaninki da Yusuf idan fa kika auresa mun warke yarinya amma naga ke ko a jikinki abun nan tamkar baya gabanki sai shegen latsar waya".
"To wai Mama shikenan aikina bin namiji yana wulakantani gaskiya bazan iyaba daman tun farko na gayamiki bamu dace dashi ba idan na kirashi yana gayamun maganganu marasa dadi, yanzu ma haka inaga yayi blocking ɗina, Ni kuma dama a takure nake ina da wanda nakeso dan haka kidaina ɓata lokacinki gurin wasu makaryatan malamai." Da mamaki uwar tata ta tsaya tana kallonta tace,
"Dan ubanki ni kike gayawa kalmar nan?."
"Naga gaskiya nagayamiki ai wallahi ban auransa dan nasan ba kaunata yakeyi ba ina da wanda nakeso."
"Dan ubanki wannan dan iskan yaron da bashida ko sisi kike fatan aura Kursum? Anya kina da hankali kuwa?"
"Da hankalina kuma idan shi ɗan iska ne to Mama nima yar iskar ce ai, da dai na auri Yusuf da baya sona wallahi kara auren mara kuɗin tunda yana so na". Takarasa faɗa tana barin palon gaba daya ranta aɓace. Mamaki sosai ne yacika mahaifiyarta hakan yasanya ta dauki wayarta atake takira Anty dan wallahi akanta zata huce wannan takaicin da rashin mutunci dan tasan fitsarar Kursum yanzu sai tace zata sanar da mahaifinta tursasata akeyi.
"Yaya barka da rana."
"Kinga karki kara cemun yaya ki kirani da Kubrah ta ina ganin hakan zaifi ko? Tunda ke kin samu gidan attajiri kin nannade ƙafa diyata kuma kin kasa samar mata mafaka."
"Haba Yaya me isa kike mun haka sai kace ba jininki ba kinsan fa wannan yaron ba ɗana bane ba kuma yanzu da nake gayamiki bakiga yadda na zuga mahaifinsa ba haka yanzu basa maganar Arziki da ita Ummy ɗin sabida ya nuna mata ɓacin ransa sosai akan lamarin tunda naji yaya ma yakira sa jiya."
"Ohon miki dai Wallahi bazanyi kaffara akan maganata ba tunda.."
"Kinga Yaya ya isa haka danAllah kiyi duk abunda zakiyi mana sai me? yusuf yaronane? Ko kuma ni na haifesa da zaki uzzura Mani duk ƙoƙarin da nake bakya gani, haba! Wannan ai son kai ne" Ta kashe wayarta hakan yasanya hajiya Kubrah firgita da maganganun Anty dan haka tamiƙe ranta ciki da bakin ciki tana kunduma ashar tare da tunanin matakin da zata dauka akansu duka.
******
Tunda Momy ta shigo mota ta nufo gida taji zuciyarta namata wani irin sanyi dariya tasanya a motar a zuciyarta tana faɗin ga dai yaro lafiyayye amma yazama mahaukaci tuburan kai wannan labarin zaifi daɗi da kawata wallahi. Nan tashiga dialing numbar Hajiya Marsi atake kuwa ta ɗauka tana mai faɗin,.
"Kawata kiranki ba alkhairi wacce tsiyar kuma kika tufka."
"Wannan karan ai babuni babu maganar malami yanzu na yarda duk makaryatan banza ne wannan abunda yasamu Abdulkareem nasan har yamutu bazai taɓa warkewa ba wannan baƙin cikin kuwa bazai taba sanya mahaifiyarsa ta samu walwala ba wallahi yanzu ma bakiganta ba kamar korarriya wallahi na shiga inata rusa uban kuka cike da tausayi bakiga bafa shi kanshi Dadyn rungumeni yayi yana lallabata wai addu'a zamuyi masa araina nace addu'ar ubanwa ai Allah ya kashe shi haka ai ganin bakin cikin kishiya akwai dadi." Dariya Hajiya Marsi tayi tace,
"Ai daman na gayamiki kawata kefa makircinki kadai ya isa ki mallake gidan gaba daya malaman nan babu inda zasu kaiki sai ga halaka."
"Ai kawata na fahimta batun iyayenta nake so nayi miki gulma ma wai tataho da iyayenta birni yanzu suna akusa damu fa."
"Kice mun dai yanzu tasan mahimmancinsu kenan?"
"Hegiya bakiga yadda dariya takusa kufcemun ba danaga tana kuka wallahi."
"Ƙawata bakida kyau nifa nazata yaron ya mutu da gaske?"
"Wallahi naso haka, Ah to ƙawata ba gwara ya mutu ba akan wannan halin da yake ciki tabbijan ai gobe ki fito kiyi kallo."
"Ai dole na ita ina Matarsa."
"Waya sani musu naga dai uban ya daga hankalinsa akan soyayyar yaron, zan san yadda zanyi in nuna masa ba komai bane ba dan bana so naga soyayya tsakanin Dady da Abdul dan wannan shine asalin kiyayyar mu bari dai kawata nakarasa gida na kiraki."
****
Ammy kuwa da tasa Aliyu ya ɗaukota tazo ta roki Latyfah ko da suka ƙaraso gidan kwaɗo suka gani ajiki wanda yasanya gaban Ammy bugawa sosai.
"Aliyu me nake gani haka? Ko dai ba gidan bane ba? Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun."
"Ammy wallahi gidan ne fa amma ina zuwa bari nakira Laila naji dan tace mun da safe zata biyo." Ko da yakira Laila haka tace mai itama taga gidan arufene. Shasshekar kukan Ammy ne ya sanya Aliyu rikicewa yace " Ammy dan Allah kidaina kuka."
"Indaina kuka kace fa Aliyu bakaga halin da ɗana yake ciki bane ba? Aliyu ko jikana bansa a idanu na ba wannan wacce iriyar mara imanin yarinya ce Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun ina suka tafi kenan?."
"Ammy bari na tambayi mai kantin can" Sai da yayi masa sallama sannan ya tambayeshi mutanen gidan can suna ina?"
"Bawan Allah ai tun asuba suka bar garinnan."
"Dan Allah kasan garin da suka tafi?."
"Gaskiya ban sani ba dan nima sunmin sallama suna sauri ne." Ƙansa ya shafa yanajin wani irin zafin rai da baƙin ciki wato guduwa sukayi kenan? Kai ya Allah. Yayiwa mai shagon godiya yatafi.
"Ammy shima baisan inda suka tafi ba."
"Wayyo Allah na Latyfah Imam ta cuceni ta cuce ɗana."
"Ammy ki daina faɗar haka kinyiwa abun mummunar fahimta.."
"Bana don jin komai Aliyu kawai kai ni gidan baffana." Ta faɗa tana katsesa ba tare da ta saurareshi ba, kasancewar tafiyar babu tazara ya sanya shi karasawa dasu ya bude mata kofa tashiga gidan. Sosai Ammy ta shiga tana kuka. Fulany dake tsaye ta sanyata nufarta tana salati tana faɗin lafiya.
"Fulany ta cuceni ta zalunci ne ta cuci yarona Abdul ya haukace Fulany baki ga abinda yakeyi ba kuma duka saboda ita, ta gudan Mani da jika Fulani yarona ko ganinsa bai yi ba bai sanshi ba Baffa." Rungumeta tayi tana shigar da'ita cikin falon tace,
"Kayi shiru kayi shiru." Baffa dake gefe kan dadduma ne yasanyashi kallonta cike da hali irin na yarinyar tashi ga manyanta sunzo amma hankali kam bai tunanin zatayi shi nan kusa, cikin ɓacin rai sosai baffa yace,
"Karka soma ambatata wallahi Anan wajen ince bakada hankali kai kullum kana girma amma babu hankali bazaka nutsu ba Fatsima, baza kiyi hankali ba? Wannan tunanin naki na banza da kikeyi ina zayakai ki ince yaron har gidan keso kikaisa wai ke kam fatsima kinada tunani kuwa yaronka shine yaro kenan ita wancan yaron ba yaro bane ba? Yanzu kikasan da jikanki kenan bayan irin iskancin da kayimata?." Allah sarki uwa sai ta fashe da kuka fulany tace " "O waɗa mo ɗum gasaɓaɗi (me isa kake mata faɗa)."
"Au kana goya masa baya akan abubuwan da yakeyi? Ita bazata taɓa girmama ɗan adam ba kenan? Ko wanne loƙaci ganin tanada kudi takeyi kullum cikin wulakanta ɗan adam." Cikin kuka tace,
"Baffa kayi hakuri zan gyara."
"Idan baka gyara ba wahala zakayi ina tabbatar maka sai kayi kuka da idanuwanka wallahi ba baki nakeyi ma ba, ita waccen yarinyar daka cuta saboda batada gata kenan ko kuma saboda batada kudi wulakanta ta da kukayi hakkinta kina tunanin zai barki? bari kaji acikin halittun Allah Akwai bayin da Allah yake ƙauna yake sansu idan da yana ɗaga miki kafa to ina tabbatar miki saboda kin taɓasu bazai ɗaga miki ba, ki natsu ki yarda kun cuta mata kunemi yafiyar Allah da tata sai Allah yarangwanta miku halin da kuke ciki kema shine magana." Aliyu dake hawaye shima yaji wayarsa tafara ringing.