Page 8
*KAMPALA ESTATE*
NA
*BILKISU GALADANCHI*
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
08
Fatima gaba ɗaya acikin rashin walwala ta kasance duk wannan lokacin, kamar kullum ganin ba aikin da take ya sanya tayi wanka ta kimtsa kanta sannan ta ja wayarta zuciyarta daɗa gaya mata yake kawai ta buɗe Tiktok koda ma ace ba username irin yanda wasu keyi, kai tsaye kuwa ta sauke app ɗin ta shiga saita komai daya shafi abin da suke buƙata kafin su buɗe maka, bata ɓata lokaci ba wurin nemo account ɗin Leo ta shiga duban video's ɗin sa tana lumshe idonta, abin da zuciyarta take ingizata ta yi tana jin tsoro amma gani take hala wannan shi kaɗai ne abin da zai baiwa mahaifiyarta kariya ita kuma ya bata kwanciyar hankali, bata sani ba ko wannan wata dama ce Allah ya ara mata da zata damu kuɓuta daga hannun Bukar na har abada, nan da nan zuciyar ta ta amince da shawarin da ta bata kai tsaye kuwa ta shiga masa DM
_Assalamu Alaikum my captain my champion sunana Fatima Zarah, Captain kamar ko yaushe na san ba lallai bane ka kulani amma ka sani yanzu ne nafi buƙatar kulawa da kuma taimakonka sama da ko yaushe don Allah ka taimakeni kaji mahaifiyata nike so a dubamun._
Tana aika masa wannan saƙon ta rungume wayarta a ƙirjinta tana jin wani sabon son mahaifiyarta da kewarta yana huda ta, wayarta ta ciro kai tsaye ta shiga neman layin mahaifiyata amma baya tafiya yau kusan kwana bakwai tane neman layin baya zuwa tana cikin tsananin damuwa, yanzu wa yake taya Mama aiki? Wayake mata wanke wanke a wurin sana'arta waye yake bata magani? Kuma idan ta kasa bacci waye yake tayata yake rarrashinta?? Wayake mata addu'a a ruwa take sha saboda neman waraka daga indalla? Wani kuka ne taji yazo mata ga fashe da kuka ba mai rarrashinta ta shafe awa biyu hawayen idon ta ya kasa daina tsiyaya.......
Mj har dare ya rufa ya kasa bacci sai zarya yake yana zargin kansa da damuwa da matar da ba tasa ba matar auren wani, ya kasa cire ta a ransa, yanayin sanyin ta, nutsuwa da kamalarta ga kuma haƙurin da ya kula zatayi saboda yanayin yanda ta dage take zaman jiran fitowar Raheema batare da nuna gajiyawa ko ƙosawa ba, amma yanayinta yana nuna masa akwai tsantsar damuwa a tattare da ita wanda hakan ne ya tilas ta masa kasa daina tunaninta duk tsawon wuni har dare, yana tsakiyar wannan zirga zirgar Rahima ta shigo masa ɗakina kallonta ya yi yanda ta shigo tana masa wani yanga kamar zata karairaye ya bita da ido har ta kai zaune a kan ottoman sannan a yangace ta ce
"MJ na maka message kayi shiru baka ce komai ba." Cikin yanayin ƙosawa ya ce
"Look Rahima banida wannan kuɗin da kike buƙata a yanzu, ni ɗan kasuwa ne Raheemah bazan zauna inta baki kuɗi kina kashewa ba ba gaira ba dalili, just last week na baki 5.M kika kawo wasu kayan worth 2.250M acikin same week na baki kuɗinsu, you again brought a diamond necklace worth worth 7.M still ba gajiya Rahima na saya miki bayan 100k 200k da kike karɓa kullum a zuwan saka mai da daily needs yanzu kizo kice zakuyi biki in baki har 30.M wai shin hala bishiya nike jijjigawa kuɗi ja faɗowa? Ko kuma ni a a ajikin zan ƙarar da dukiyar a cikin just a week da kika kashe kusan 20.M ni ban kashewa kaina ko 1.M meyasa bakya jin tausyaina wai karya company zakiyi ko meye a kanki?" Cikin hasala ta miƙe tsaye
"Lallai ma Mj ka gama rainan hankali wallahi, yanzu duk akan waɗannan ƙananun kuɗaɗen da kake bani kake gayamun magana har haka? Rainin hankalin ya kai ace ina shirin yin biki in tambayeka kuɗi ka tsaya lissafamun nawa ka kashemun a sati? Ka dubafa ka gani Anty Maryama fa mijinta 100.M ya bata kuɗin bikinnan so kake inje bikin a raina ajin mijina?." Cikin katseta ya ce "Look Raheemah koda ma ace mijin Anty M CBN ya bata ni ba abin da ya shafeni bane ba, Honourable ɗan siyasa ne yanada kuɗi ni kuma ɗan kasuwa ne ko inada kuɗin dole insan yanda zan kashe su." Nan da nan sai ta taro hawaye a idonta, cikin saiɓi da sakalci ta fara rera masa wani sakaltaccen kukan shagwaɓa
"Haba Mj na ka taimakeni mana, ni nasan kanamun ƙoƙari amma don Allah ka ƙara haƙuri nima a nawa business zan cire 20.M na ƙara ayi shagalinnan kowa gayamun yake ansan daga Anty M sai ni a shagalin bikin nan saboda kowa yasan my husband is a successful business owner, yanada running 3 different companies da ake ji dasu a Nigeria, My Mj kafi ƙarfin yin raki akan ko da ace billions ne ma bare ma millions babyna please ka taimakeni kaji " shiru ya yi yana ɗauke kansa daga dubanta saboda ya tsani hawayen idon ta sam baya so ko kaɗan! Matsasa ta yi kusa da shi tana shafa mai ƙirjinsa cikin shagwaɓewa da sakalci kamar zata koma cikinsa
"Mj Please kaji." Hannunsa ya kai bayanta ya ɗan bubbuga a hankali cikin sigar rarrashi ya ce
"Ok but promise me zakiyi shigar mutunci a bikin nan?" Tana share hawayen idon ta tace "Sure mana Mjay i promise i will." Yana jinjina kansa ya ce
"Then i will credit your account with 50.M but karki ƙara tambayana kuɗi sai after a month." Rungumeshi ta yi tana murna
"Thank you Mj." Kafin ta wani fara bashi kiss me shiga jijiya!
Washe gari da tsamin jiki ya tashi saboda gajiya da ɗawainiyar Raheemah ya kuma tura mata kuɗin tun jiya amma ya rasa dalilin hanasa sukuni da take, shi yasan idan ba kuɗi take so ba bazata taɓa bari ya mora daga jikin nata ba, ita feminism ɗin nata be gama shigarta ba tun ta kasa zama independent ma kanta. Ta rigashi ficewa a gidan ma shi sai wuraren 10 na safe sannan ya fito, yasha wani lallausan yadi fari ƙal transparent da har ana iya hango singlet ɗinsa dake nan itama fara ƙal aciki yayi kyau sosai sai tashin haɗaɗɗen ƙamshin turaren sa na Lacoste yake yi me kwantar da zuciya....
Barin cikin Estate ɗinsa befi da mintuna 5 ba ya hangota ta buɗe bunnet tana dube dube lokaci guda tana daɗa duban agogon hannunta, gangarawa ya yi yay parking daf da ita ta gabanta kaɗan saboda ya wuce tane sanda ya shaida ita ɗin ce, sakkowa yayi daga cikin motarsa ya tako zuwa iinda take, duk da taji taku a bayanta hakan bai sanya ta juyo ba har ya iso daf da ita a hankali ya ce
"Barrister lafiya dai?" Wani irin faɗuwa gabanta ya yi jin sautin muryar Mj da sauri ta juyo wanda hakan har sai da ya nuna a yanayinta, wani sasanyan murmushi ya ajiye mata kafin ya ce
"Sorry i frightened you." Tana saisaita nutsuwarta ta ce
"Good morning sir." Murmushin fuskarsa ya ƙara faɗafawa kafin yace
"Good morning Our Barrister meyene ya samu motar?" A hankali ta ce
"Jacking take yi tunda na fito and its unusual ma, yanzu ma tanayi sosai." Zagawa ya yi zuwa cikin motar ya ɗan buga motar ya bata wuta sai ya fito ita kuma tana tsaye daga gefe, a hankali ya ce "Duk da ni ba bakanike bane Barrister amma kamar fanfonki ya yi datti inaga you call your mechanic ni kuma saina saukeki a office." Kallonsa ta ɗanyi sai kuma ta sauke numfashi kafin ta ce
"Akwai Client dake jirana ga lagos baka isa kabar mota a gefen titi haka kawai ba kuma ni banida mechanic." Ɗan shiru ya yi sannan ya ce "Call your husband muji ko zai turo me muku gyara." Cikin tsoro daya nuna a fuskarta ta zari wayarta ta shiga kiran wayarsa ringing biyu ya ɗaga, a hankali ta ce
"Aminullah na ce don Allah ko zaka taimaka ka turamun makanikenka motana ya tsaya a hanya and client suna jirana a office." Cikin ɗaga murya ya ce
"Akan me zan turo miki wani mechanic nine nace bakya servicing motocin gidan? Ni ina meeting ki san yanda zakiyi." Cikin daurewa wulaƙancinsa ta ce
"But Aminullah kasan nan Lagos ne ba kano ba yaya zan bar mota anan kasan halin ma'aikata." Tsaki kawai ya yi ka kashe wayar sa, ta zaro wayar daga kunnenta ta bi screen ɗin da kallo cikin tsananin ɓacin rai. MJ ya ɗauke idonsa daga dubanta kafin cikin basarwa ya ce
"Look Barrister i guees your husband is busy Kinsan me zai faru, zo mu tafi in saukeki mechanic ɗina zezo ya ya tafi da motar." Cikin dauriya ta masa godiya sannan ta kwashe kayanta a motar suka shiga motarsa ya kira mechanic yace su haɗu a office ɗinsa. Har Chamber ɗinta ya kaita ya ajiyeta ta waigo suka haɗe ido a hankali ta ce
"Na gode sosai Sir Allah ya saka da alkhairi." Yana mata murmushi ya ce
"To Barrister lemme have your number ko? Idan mechanic ɗin ya kammala zan kiraki ko in dawo in ɗaukeki ne se ya kai miki motan gida?" Tana murmushin ta me kyau ta ce
"Noo Sir ya kai motan gidan zan yi order bolt ya kaini gidan idan na kammala."
"A a bazamuyi haka ba Barrister zan zo in ɗaukeki idan kin tashi idan kuma ban zama free bama zan turo driver ya kaiki gida amma ai kin wuce hawa Bolt ai." Tana daɗa jinjina masa kai ta ce
"Na gode sosai da karamci Allah ya bar zumunci." Sannan ta miƙa hannunta tana cewa "Barin saka digit ɗin Sir." Wayar ya bata ta karɓa ta zuba digit ɗinta sannan ta masa godiya ta sauka bayan ya kirata taga number sa amma bata tsaya wani saving ba.
Wunin rashin sukuni Mj ya yi a office ɗinsa yau saboda tunanin Amrah gaba ɗaya shi yama rasa takameme shin tunanin me yake akanta? Itama a ɓangarenta gaba ɗaya ko motsi ta yi sai ya faɗo mata faɗi take a zuciyarta he is so caring har zuwa lokacin tashi daga aikin da aka yi tana shirin order Bolt ya kira wayarta gyara zamanta ta yi sannan ta ɗaga kiran haɗe dayin sallama, amsa sallamar ya yi kafin ya ce
"Barrister Majeed ne ya aiki?" A nutse ta gaidashi ya amsa a sake kafin ya ce "Ina wani aiki me muhimmanci Barrister amma driver yana waje duk sanda kika tashi a aiki ze kaiki gida, me gyara ya ɗauki motar tun ɗazu amma yace gyaran se ya kai gobe." Cikin sauƙin murya ta ce
"Na gode sosai Sir Allah ya saka da alkhairi sannu da ɗawainiya." Yana faɗaɗa fara'arsa ya ce
"Ba komai take care." Gaza cewa komai ta yi ta kashe wayarta tana me jin wani iri. A ranta tace "Wannan tattalin ne ya sanya dole Heemah ta rikice akan Mjay he is so caring."
A ɓangaren Leo kuwa kasa sukuni ya yi kwana ɗaya kacal da be ƙara ji daga gareta ba, ya shiga damuwa sosai har ya fara tunanin hanyar da zai bi ya gana da ita ko yaya ne, wani ɓangaren na zuciyarsa yana gargaɗinsa sosai akan fita sabgarta tunda ita ɗin matar wani ce, daga ƙarshe ya raya a ranshi cewar shikam ya daina shiga sabgarta duk sanda take neman taimako ta kawo kanta ze taimaketa amma idan bata kawo kanta ba bazai ƙara shiga huruminta ba, a wannan daren ma ya kimtsa kansa Don washe gari Aleayah zata tafi kano shikuma zai ɗaga zuwa US.
Amrah tunda driver ya ajiyeta gabanta ke faɗuwa ganin Ameenullah a saman verandah part ɗinsu, a wani irin kasalallen yanayi ta ƙaraso kusa dashi bakinta yana mata nauyi sosai ga kallesa ta ce
"Ameenullah barka da wannan lokaci." Hannunsa ya zuba a aljihunsa duka biyu yana gyaran tsayuwarsa kafin yace "Wancen ɗin da ya ajiyeki waye shi?" Motar dake fitar a farfajiyar gidan ta kalla sannan ta mayarda dubanta zuwa gareshi a kasale still cikin ƙosawa ta ce
"Driver Me gidan Raheemah ne, ɗazu da safe shi ya taimakeni ya kira mechanic ɗinsa aka ɗauki motar yanzu da yamma ya Kirani dake ɗazu ya karɓi number na sai yace driver sa yana waje office ɗina zai maidani gida." Ƙureta da ido ya yi na wasu matasan daƙiƙu kafin yace "To ina motar taki." A hankali ta ce
"Yace me gyaran yace sai zuwa gobe in shaa Allah, kaga gobe i have to use your other car inje office saboda nawa sai gobe." Taɓe bakinsa ya yi kafin ya ce
"Mota ɗaya ne agidan ɗayan na arawa wata Colleague ɗina da yamman nan motarta ta sayar kafin a kawo mata sabuwa, se dai ko ki kira Uber ko kuma shi Mjay ɗin ya taimaka driver sa yaci gaba da kaiki tunda kinga ni dai bazan iya katsewa driver na aiki ba beside bazan ma baki motana ki hau kije ki bugamun ita a banza ba." Shiru ta yi tana kallonsa kafin a hankali ta ce
"Yanxu Aminullah ita Colleague ɗin naka bata ɓata maka motar ba sai ni, tayaya zai yiyu ace sai neighbour ne zai taimakeni kai kana matsayin mijina ka taimaki wata ni ka gagara taimakamun." Cikin katseta a hasale ya ce
"Cut the crab Amratu, shi neighbour ɗin ba don nayi taimako Allah ya jehoshi ya taimakeki ba? Ko kina tunanin cewar ba alkhairin da nayi bane yake dawo miki? Please don't spoil my precious moment madam kije can kiji dashi. Ya wuce abinsa zuwa mota ya shige driver ya tayar suka wuce ta bishi da kallo kafin ta wuce cikin gidan ranta a jagule.
Bayan ta gabatar da Asr tasan zuwa 5 matan duka mini gate na Kampala Estate zasu hallara ne a waje don haka a cikin azama ta yi wanka ta ɗauki wanka acikin kwalliyar ƙasaita doguwar rigar cotton crepe material ce a jikinta black and peach colour rigar a buɗe take sosai ba inda ta kama mata jikinta, zallan inner cap ne a jikinta sai kuma mayafi peach colour data yane kanta da shi, ba komai a fuskarta banda kwalli da sanyayyan ƙamshin da take, zama tayi ta lalubi number Mjay ta rubuta masa saƙo kamar haka
_Na iso gida Sir mjay Allah ya saka da alkhairi._
Yana shirin barin office yaga message ɗintan murmushi ya sauka akan fuskarsa nan take da sauri ya shiga reply
_Never mind Barrister it's my pleasure._
Itama murmushi ta yi sannan ta miƙe zuwa wajen inda tana fita taci karo da Meena, suka gaisa sannan suka jeru zuwa wurin zamansu, koda suka ƙarasa duka sauran sun fito, a tsaye suka gaisa ganin suma suna tsaye Sameerah ta ce "Ku muke jira mu fita muɗan motsa jikinmu, mun fi wata anan zaune." Batare da sunyi wata doguwar magana ba suka nufi gate ɗin mini estste suka fice suka doshi main gate ma Kampala Estate, sai can wurin gab da magrib suka juyo suna hira suna tafiya suna shigowa Kampala Estate ko ina ya buɗe da hasken fitilu kamar safiya, a wannan lokacin Mjay ya dawo kallonsu ya tsaya yi suna ƙoƙarin bullewa shi kuma ana duba booth nasa, bin yanayin dressing na dukkansu ya yi she is different! Ya ayyana a ranshi a sarari ya furta she dress decently, yaa Rahman ka shiryar da Rahima ta nutsu tasan menene gaskiya ta daina shiga irin wanann." Ya ƙarashe maganar yana furta Amin shi kaɗai..
Bilkisu Galadanchi
KAMPALA ESTATE
2025.