KAMPALA ESTATE

Page 11

by @68billygaladanchi

*KAMPALA ESTATE*


NA


*BILKISU GALADANCHI*


*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*


11


Yau da dare Zarah tana zaune tana faman aikawa Leo messages taji knocking a ƙofar ɗakinta da sauri ta fita a tiktok ta fara goge App ɗin me gaba ɗaya sannan jin dukan ƙofar ya tsananta ya sanya tayi hanzarin zuwa ta buɗe ƙofar bathroom ta kuma rufewa don tana so yay tunanin daga bathroom ɗin ta fito da sauri ta buɗe masa tana masa murmushin ƙarfin hali amma ganin yanda fuskarsa take a haɗe ya sa taɗan sha jinin jikinta a hankali tace


"Yi haƙuri ina bayan gida ne." Hargitaatsen kallonsa ya kuma watsa mata kafin ya ce


"Bani hanya mana." Janyewa ta yi ya shigo ciki yana muzurai


"Zo ki ragemun zafi ke." Ƙirjinta ne ya wani irin bugawa tunawa da baƙar azabar data sha a hannunsa satinsu na farko da aure, nan da nan idon ta ya kawo ruwa ta fara ja baya muryarta har na rawa ta ce


"Yaa bukar kayi haƙuri." Wani kalan mari ya ɗauketa dashi yana fizgota kamar zai ɓallata ta fashe da kuka, da ƙarfi ya mannata da ƙasa akan gwiwowinta sa yana sake wanke fuskarta da wani gigitaccen mari me ratsa jiki launin idon sa sai daɗa canjawa suke suke hargowa ya ke magana


"Ban hanaki yimun musu ba jaka kawai aka gaya miki nan da wa'adain da na ɗeba na fantalawa dake zaki wuce in haiƙe miki ta baya da gaba ne duk dare? Wallahi kina mun musu zan iya shaƙeki har lahira wa zai nemeki a duk duniya wa gareki banda uwarki gawa taƙi rami." Jikinta bandanrawa ba abin da yake yi ya jefar da towel dake ƙugunsa ganin abarsan a fili haka ba ƙaramin ruɗata ya ƙara yi ba firgita zata miƙe ya sake ɗauketa da wani marin sai da gefen bakinta ya fashe sai jini, tsawa ya daka mata


"My friend will you do as i say." Da sauri tasan me yake nufi ta buɗe bakinta jikinta banda ɓari ba abin da yake ya wani cura mata aciki har wurin maƙoshinta ta shiga neman ceto ya riƙe kanta dam yana bugasa sai amai ya ɗauke sama da awa tayi amai har ƙarfinta ya ƙare maƙoshinta ya tsatsage sai uban zafi yake mata, cillar da ita ya yi tana wani zazzafe Mayun jajayen idon ta kafin ya ɗauke kai ya juya yabarta awurin cikin azaba mai raɗaɗi da ƙyar ta ja jikinta a ragwaɓe zuwa Bathroom acan ta yi wanka ta gasa bakinta daya fashe ya yi suntum ta wanke bakin sannan ta fito da zallan towel ta wuce kitche ta samu ruwan ɗimi da gishiri ta kuskure can maƙoshin da take ji jamar ya tsatsage kafin ta baro kitchen zuwa ɗaki sai da ta haɗa da paracetamol tukunna ta kwanta tana sauke wani numfashi mai ciwo da raɗaɗi wasu zafafan hawaye suka shiga zarya a idonta tana tuna rayuwarta me daɗi da mahaifiyarta, tana tuna irin yanayin kariyar da take bawa kanta da wacce mahaifiyarta ke bata, ita babban burinta shine ta zama likita yayinda bakin mahaifiyarta be taɓa gajiya da mata addu'a da fatan samun miji na gari ba, ance addu'ar iyaye batada shamaki meyake faruwa da tata addu'ar da mahaifiyarta ke mata? Ko bata yi daidai ne? Babu shakka tana cinin tsantsar tashin hankalin zama da Bukar gwara yau ace mutuwa tayi akan zama da Bukar amma ranta fansa ne ga rayuwar mahaifiyarta muddin bazai saɓawa shari'a ba zata daure abu ɗaya ne ta sani bazata taɓa uta ɗauka ba sai idan da gawarta zeyi shine nemanta ta baya ko ta gaban ma don haƙƙinsa ne amma wannan iƙirarin banzar da yake shine zeyi musabba na hadda gobara da zata ƙona dukansu don bazata iya ba!


***************

Tun lokacin da ya mata maganar barin masa abinci be ƙara waiwayarta ba har washe garin ranar, abin  ya so ya zo ya dameta sai kuma tace akan me ba ubana bane ba kuma mijina bane, da wannan tunanin kawai ta tattara al'amarinsa ta watsar, safiyar yau tana ta tunanin ta kira bolt ɗinne ko ta jira driver sa yazo kar yaga rashin kyautawarta? Shirinta ta gama tsaf tana tunanin ko da ta fita ne before ta yi reaching gate she can order bolt dake kusa da ita tunda dama suna using location with that thought ta shirya tsaf ta fito acikin doguwar rigar jallabiya har ƙasa baka wuluk me adon beads baƙake suma ta yane kanta da mayafin abayar tayi talha, as usual takalmi me tsayi ne a ƙafarta shima black ga alama black and white na lauyoyi ya shiga jikinta sosai don inner cap ɗinta ne kawai fari, tayi mamakin ganin driver a ƙofar gidanta ya fito daga motar yana tsaye yana jiranta ba tare da ɓata lokaci ba ta taka suka gaisa ya buɗe mata gidan baya ta zauna sannan suka bar mini gate suka bar Kampala Estate ma gaba ɗaya, har office ya direta ta masa godiya ko 5mns bata yi ba a office ɗin wayarta ya shiga ruri ta kalli screen ɗin ta ɗan taɓe baki saboda tasan sai ta shafe 2 good month kiran Aminullah be shigo wayarta ba ita kam rabon da suyi magana a waya tun randa motarta ta lalace ko so ɗaya be kuma kiranta ba sai yanzu kuma ta tabbatar alkhairi dai bai taɓa aikoshi kiran wayarta ba, jikinta a sanyaye ta ɗaga kiran tare da yin sallama, ba tare da ya amsa sallamar ba ya ce


"Wannan mutumin da ke zuwa ɗaukarki da mota waye shi?." Wani murmushin takaici ya suɓuce mata cikin dakiya ta ce


"Ohh Driver ne." A hasale ya ce "Yaushe kika yi driver har da wannan motar ban sani ba." Cikin katse sa ta ce


"Noo Aminullah ni dai baka isa ka addabeni ba gaskiya, ban fahimceka ba ka kirani kana tuhuma na sai kace wata yarinya ƙarama, ba ma Colleague ɗin ka ka bada aron motarka ba? To motana da baka ƙara neman jin ba'asin inda yake ba yana mechanic yaci inji kuma ba engine na motar anan sai an kawo daga waje so good Samaritan yake tura driver sa ya kawoni office da matsala ne? Ina ce kaima you helped someone ka bata aron motar da ni ake gudun a bani in ɓata." Gaza cewa komai ya yi kawai ya katse wayar ita ma cikin jin zafinsa ta cillar da wayar kawai tana jan wani shegen tsaki, a ranta kuwa wani haushinsa ne ya tarnaƙe ta ganin kamar wani shishigi yake neman ya fara mata tamkar dai ace da can ya saba damuwa ne da yanayin abubuwan ta.


Wuraren 4 na yamma tana shirin barin office saƙo ya shigo wayarta ta ja wayar tana dubawa Mjay ne


_Your car is at your chamber, key yana hannun wanda ya kawo da takardun gaba ɗaya_


Saida ƙirjinta ya wani kalan doka ganin saƙonsa, jikinta har na rawa rawa ta gama tatare komai nata ta bawa sakatariyarta ta biyo bayanta suka sakko ƙasa zuwa waje, nan ta tarar abokan aikinta da yaranta sunata zuba mata addu'a akan new car gayen ya bata key ze wuce ta bashi 100k sai godiya yake kafin ta tuƙa motar zuwa gida ta rasa dalilin zumuɗin motar haka kawai motar take shigewa can cikin ranta, sai murmushi take ta manta ma ko godiya bata masa ba, tana shigowa gidan Raheemah na shigo duk suka yi parking suka fito kallon juna sukayi kawai sannan Raheemah tabi motar da kallo, daga nesa da ita ta ɗan ɗaga mata hannu ita ma ta mayar mata suka ɗanyi mumushi tukunna kowaccensu ta shige cikin gidanta, Raheemah tsabar baƙin ciki bayan ta shiga gidanta kasa zama ta yi, banda zirga zirga da yawo babu abin da take, cikin kasa jure hasadarta ta ɗauki wayarta ta turawa Aminullah message.


_You such a good husband, i saw the new car you bought for your wife, Gaskiya na mata murna._


Aminullah yana office ya ci karo da wannan saƙon cikin ruɗani da mamaki ya mayar mata da amsa


_New car? My wife? Me? When?_


Sai da ta gama tunanin amsar bashi don taga yana so ya raina mata hankali sannan ta ce


_Abu a fili ga mota tear leather ma._ Be ƙara komawa ta kanta kawai ya fara aikinsa after 15 minutes ya kira Amrah a waya har so biyu bata ɗaga kiran nasa ba saboda tana wanka ne a lokacin, cillar da wayar kawai ya yi ya shiga sabgoginsa don kuwa a ransa ya tsani ya kira mutum be ɗaga masa waya ba.


A ɓangaren Raheemah kuwa ƙaramar hauka ne kawai bata yi ba a wannan lokacin saboda wani irin baƙin tuƙuƙin ɗaci da hassada mara misaltuwa dake addabar zuciyarta, jikinta banda ɓari ba abin da yake burinta kawai ta samu damar da zata ciwa Amrah mutunci, tana takaici da hassadara Amratu sama da kowa, ganin maganar zai iya kashe ita kaɗai idan bata furta ba ya sanya ta ɗaga wayarta ta kira Meenah, ita ma a wannan lokacin ta shigo don haka a kasale ta ɗaga kiran.


"Bacci kike wai?" Raheemah ta wurgo mata wannan tambayar." Ɗan taɓe baki ta yi tana daga kwancen kafin tace


"Ba baccin da nayi wallahi kawai gajiya sai wuraren 3:30 na shigo." Tsaki Raheeman taja


"Ni ai kinma rigani shigowa ina ga da ke zaki ga abin da na gani wai kinsan Meenah Amrah munafuka ce yau kusan a tare muka shigo kinga wata arniyar farar Roy's roll's data shigo da ita sabuwa gal? Don kutumar ubanta ma wai kinsan waving nawa kawai tayi ta yi shigewarta Billahi ganinan zuciyata kamar zata faso ƙirjina ta fito tsabar baƙin ciki, a rayuwar Meenah na tsani inga waccen mayyar da abin da ni ban mallaka ba." Meenah dake daga kwance ta miƙe zaune cikin jin zafi da takaici bugun zuciyarta sai ya daɗa ƙaruwa a razane ta ce


"Wace Amrah? Kam bala'ee." Raheemah da ke jin kamar zata kwarma ihu ta ce


"Iya wannan kika sani, ki daure ki fito da wuri yau a sport mu caccaki matsiyaciya mu ɓata mata mood, don kinsan tsinanniyar ba magana take ba, bakiga yanda nake jin haushin ta ba kullum se nai baƙin cikin kasancewarta 'yar da ubanta da zuri'arta suka fi nawa kuɗi, miji kuɗi ga kuma ita kanta kuɗi, chamber ɗin kafirar matarnan layi ake da cases last case da na kawo mata sauraran matsalar da zatayi sai da ta karɓi 10.m ba kuɗin aiki ba batada imani son duniya ya mata yawa ko don fana wining cases take wa mutane fi'ili waya sani." Meenah da tuni zufa ya karyo mata ta ce


"Yanzu zan tashi in fara shiri yau in shaa Allah sai na ci zarafinta akan motar nan, ita komai se dai mu ganta dashi namu shine abin da kowa ze ji ko wato mu ga sakarkaru."


"Rabu da banza, ina takaici komai nata designer ina takaici yanda ko me ta saka zata yi kyau, ina takaici yanda take da aji wallahi haushi take bani always pretending to be holly." Cewar Raheemah nan suka shafe wasu good 10 minute suna zagin ta tare da kushe da hassadar duk wani abu da zai kawo ci gaban ta a rayuwa kafin suka yi sallama kowacce ta hau shirin zuwa Centre su na shirme.


***********

Zuw 5:23 pm kowaccensu su 6 sun hallara a farfajiyar gidan a sport nasu banda Amrah, dukkansu hankalinsu yana kan arniyar motar dake park a wurin parking lots na su Amrah, Sameerah cikin gaza haƙuri ta ce


"Wai Uwar daba yaushe Amrah ta saya waccen motar ne? Shin haka zamu dawwama mu duk abin da zamuyi ko tusa ce sai mun gayawa kowa anan amma ita kullum tana ɓoye mana abu." Cikin takaici uwar daba ta ce


"Duk ku zuba mata ido ai zata zo ne." Suna ta zuba zanje sai ga tanan ta fito, sanye da Compy Bubu gown ta asalin silky and shaky material sai jercy vail data yi rolling kanta da shi ta yi kyau sosai, flat shoe ne yau a ƙafarta don haka nan da nan zaka iya hango gajartarta daga nesa duk da ba cancan bane, da fara'a ta ƙaraso wurin ta zauna tana dubansu yanda duk suka zubo mata ido wayancewa tayi duk da ƙarya ba ɗabi'arta bace ba haka ta kasa cewa mijin ƙawarta ya bata mota tana dariya tace


"Guys albishirnku ina zaune a office sai ga gift na waccen motar from my Dad bankosan zai aikomun mota ba tun ɗazu nake sauri in gama shiri in fito in nuna muku." Ba haka suka so ba dukkansu sun so ace sune suka fara mata ƙorafi don su ci zarafinga sai ta musu na lauyoyi ta lauye su tamau, Raheema cikin basarwa ta ce


"Kai we thank God for the kind of husband Allah ya bamu very supportive please Amrah koda babanki ya siya miki abu ki riƙa ɗan rufawa mijinki asiri kina cew a shi ya saya miki ke ko kunya bakya ji komai Daddy." Cikin jatse ta Amrah ta ce


"I am not like you Raheemah, you are always claiming feminist but komai se miji ya miki, learn to be self independent mana, i am not a feminist but I don't fucking need anything from my husban i can setisfy my need ko da ba mahaifina shiyasa maza duk suka raina ku sunsan da bazarsu kuke rawa ƙaryar feminism ɗin ne kawai." Raheemah bata taɓa zata Amrah zata mayar mata magana haka ba cikin masifa ta ce


"Ni kinsan wallahi nafi ƙarfin ki gayamun haka, meyasa zan damu da dukiyar Jay kawai kinsan shi ba kamar matsolon mijinki bane he likes doing komai ma matarsa so is not as if ina son wata tsiya a hannunsa ne." Amrah da bakinta baya shiru ta ce


"Then show me one single thing da kika taɓa saya ma kanki? Nan fa ko kayan mata Uwar daba ta kawo mana cewa kike Mjay zai bayar, ke kullum idan baki haddasa fitina ba bakya jin daɗi ne wai?" Cikin fitina Raheemah ta ce


"Ke dai kawai bakida power a wurin miji, gakinan ba ƙaunar ki miji yake ba sai iyayi da ƙaryar banza kina taƙama da kuɗin uba." Amrah kawia miƙewa ta yi tana wani murmushi


"I can see that hassada yana damunki, and har abada ba zaki kamo ƙafata ba." Uwar daba ce ta miƙe


"Please meyasa kuke haka wai? We are far far far very far da yin wannan shirmen, Amrah calm down please Allah ya sanya alkhairi we are happy for you Allah ya raya mana Daddy ya ƙara lafiya." Amrah shiru kawai ta yi ita kuwa meena ta ce


"But tsakani fa da Allah Amrah bakya kyautawa yanzu me ya kawo maganar rashin zama self defendant idon kika duba ai shawara kawai ta baki don ko wace mace tana so ace yau mijinta yana nuna bajintarsa a kanta." Raheemah ta caɓe da cewa


"Just let her be, ita ai gani take kamar tafi kowa wayo da basira saboda tayi wani gurguwan master's da su sauran shirmen, jami'arnan duk munje ko yanzu nike so in zama lauya sai in zama." Amrah wata dariya ta kwashe dashi don ita abinma dariya ya bata kafin tace


"Look Babe ki zama lauya yanzu yanzu but know this you will for ever be my junior har abada level kam ina gabanki, and soon enough sai dai kiji ana maganar judge ba lauya ba." Nan sabon rigima ya tashi da ƙyar aka rabasu, Raheemah banda surutai ba abin da take tana ƙara gaggasawa Amrah maganganu akan abin da taji a bakin mijinta na tsanar tan da yayi a kaikaice, ita dai Amrah da taga kamar su ukun jiranta suke banda Uwar daba dake ƙoƙarin kashe wutar ko don business ɗinta sai ta bar wurin da niyyan har abada ita kam ta gama wannan zaman tunda ba dole ba zaman Allah ake da juna ba.


**********


Wuraren ƙarfe 8:30 na dare Amrah tana zaune Aminullah ya shigo ya sameta har bed room ɗinta ɗago kanta ta yi daga duban screan da take na laptop ɗin ta tana aiki ta mayar da sumar kantan daya zubo ta saƙale a bayan kunnenta tana masa wani kallo, be ce komai ba sai wani harara yake banka mata, a hankali ta ce


"Aminullah you are welcome." Tsaki yaja acan ƙasan maƙoshinsa be amsa mata ba ya ce


"Who own that car?" Tana ƙoƙarin saisaita faɗuwar da gabanta keyi ta ce masa


"Ni ni nike sa motar." Cikin takaici ya ce


"And shine kika je waje kina gayawa ƙawayenki cewar ni lusarin namijine ban iya tsinana miki komai kike cewa yanzu ma haka motarki ta samu matsala shine mahaifinki ya aiko miki wata me kike so su ɗaukeni kince in saya miki mota ne?" Tana wani basarwa tace


"Tunda nike da kai ka taɓa siyamun mota? Ko kuma da ƙafa nike yawo sanda nazo gidanka? Duk bama wannan ba wane ƙawayen nawa ne suka gaya maka haka do you have any business with matan compound ɗinnan cox nasan nidai da su kaɗai nai maganar Dad ya sayamun mota." Wani kallo ya watsa mata kafin yace


"Ki gayawa uban naki mijinki yace bazaki karɓi motar ba don banga dalilinsa nayimun shishigi ba." Wata shakiyiyar dariya Amrah ta yi sannan ta ce


"Look Aminullah please mind your business, kasani na sani muna zaune ne da juna akan yarjejeniyar ba zamu shiga hurumin juna ba zamu rufawa juna asiri saboda biyayyar iyaye amma idan ka gaji just send me to my parents ni da motar, kajimun mutum fa, tunda na gaya maka motana yanada damuwa ka taɓa kulawa? Ka taɓa tambayana bawan Allah ko duk dukiyar da Allah ya maka kana mun cefane? Se kayi shekara baka yi restocking komai a gidan ba a sunan baka cin girki na, kai nike yiwa favour idan ka shirya in tona duka wannnan sirrukan ma parents namu sai ka gayamun mana." Yana mata wani kallo ya ce


"Are you threatening me?"


"How is this a threath? Nagane kana so ka karya alƙawari ina ruwanka da motana? Ina ba kuɗinka bane ba to ina ruwanka dani yaushe muka fara haka da kai?." Jinjina kansa kawai ya yi ya juya a fusace ita kuwa ta zauna tana tunanin hala yaushe ya fara damuwa da al'amarinta, wace ƙawar tata? Shin ko dama yana magana da wata ne a cikin matan KAMPALA ESTATE???? DA wannan tunanin kawai ta rufe aikin da take ta zari wayarta don rubutawa Mjay saƙon godiya.


Hmmmm wai kuna ganin daidai ne Amrah ma take yi?? Ina ruwan matar aure da alaƙa da wani?


*KAMPALA ESTATE*

*BILKISU GALADANCHI*

2025.

***.