Page 12
*KAMPALA ESTATE*
NA
*BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6790e01cf524f8dc4eabb9dd
Arewa books kullum zan sauke musu 2pages so zasu wuceku da pages masu yawa ku shiga wannan link don sauke app na arewa books.
12.
Ta rubuta saƙon godiya wa Mjay yakai so goma tana gogewa ta rasa da wanne kalaman zata yi amfani wurin masa wannan godiyar ita kam. Ba yau ta fara samun kyautar mota ba, zata iya cewa tunda take bata taɓa saka kuɗinta ta saya mota ba, sanda take gida mahaifinta ne yake siya mata motar hawa ko da ma ace batada motar akwai motoci burjik a gidan, bayan ta zama kauya client nata so shida suna bata kyautar motoci but why is this different? She never saw this comming ko so ɗaya bata taɓa tsammanin cewar zata iya samun wani abu a wurin Raheema ba ma bare mijinta, wannan borin da Raheemah keyi idan tasan hala mijinta ne ya saya motar yaya kenan? Shin mijin Raheeman zai gayawa Raheema cewa ya sayar mota? Kai abu ne da wahala duk da haka zata masa magana tabbas taji saboda gudun fitina, ganin be kyautu ba ta masa banza ya sanya cikin tsananin jin kunyar sa ta rubuta masa saƙon
_Salam, Good evening, i recieved your gift Sir, bansan da wane bakin zan maka godiya ba Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi da rufin asiri me yawa, i really appreciate it. The car is super nice i literally like everything about the car, na gode._
Mjay daya karanta message ɗin murmushi ya ƙwace masa, after Raheemah be taɓa bawa mace mota ba, ƙanninsa na gida duk maza ne se autarsu ƙwalli ɗaya mace da bata fara tuƙin bama bare kalar godiyar ta amma shin dama kowace mace ba iri ɗaya bace, duk sanda ya sayawa Raheemah abu sai ta kushe koda kuwa ita ta zaɓa, bayan haka kuma bata taɓa masa godiya da addu'a ba tayi wuta ta ce thank you, reply ya shiga yi mata
_Never mind it's my pleasure Barrister, do me a great favour of not letting anyone know about it don Allah, i mean no harm khair in shaa Allah, na gode da addu'a._
Jin hakan na ƙaramin kwantar mata da hankali ya yi ba ta shiga zuba murmushin jin kowa baya so kowa ya sani that means bazai gayawa kowa ba kenan what a relief!
Raheemah kuwa tanacan tana zuzzuga Aminullah bayan sakaran ya gama gaya mata ya tsani ganin Amratu a cikin walwala, yace shi bazai taɓa iya kashe mata 100k ba don batada maraba da ladan noma, yake cewa ai shi fa da akwai budurwarsa da yaso ya aura amma da iyayensn suka ga ita Amrah ta yi kwantai se suka ce ya rufa mata asiri ya aureta da kuwa ya matsa akan ba zai shigo ba yana tunani ita da uwarta suka shiga malamai da bokaye mahaifiyarsa ta ce zata tsine masa ta kuma sha al'washin cewar muddin har ya sake ta ba ita babu shi, ya ce ai shi tunda ya aure ta be taɓa son ta ba kuma ya tsaneta saboda ita ce tayi sanadiyar rabashi da masoyiyarsa abar sonsa har tayi fushi dashi taje ta auri wani, ya ƙara da cewar duk sanda ya tuna da masoyiyarsa tana can tare da wani tsabar kishi ji yake kamar ya maƙure wuyan Amratun ya hallakar da ita har lahira. Raheemah cikin tayashi jimami ta ce
"Ohh kayi haƙuri my meen kasan wasu mutane kansu kawai suka sani, mu kanmu kullum cikin bata shawarwari muke game da ragewa kanta biye biyen bokaye, ɗazun ma akan hakan sai da muka yi kaca kaca da ita nasan zata kwana biyu bata fito majalisar ba saboda yanda aka watse duk cikinmu ba me zuwa gidan boka sai ita Allah ya shiryar da ita."
"Koma ita ce zata zama bokar bazata taɓa samun kai na ba, taje can ta ƙarata." Cikin kissa tace
"Dole zan saka wani malami na ya tayaka da addu'a my friend ai bazaka zauna a banza ba, mu mata ba'a sakin jiki damu gaskiya, ko a abinci sai ta girka maka kaci ai." Yana wani kalan dariya ya ce
"Wa yake cin abincin wata Amrah ni ? Yo hauka ake? Ni ko ruwan zafi ta tafasa bana sha, in ƙare miki magana ni sam ko ɗakina Amrah bana bari tana shiga har me aikin gidan bata shigarmun, da kaina nike hidimana i just don't trust her." Wani shu'umin murmushi Raheemah ta yi kafin tace
"Kenan i can use the back door to your master's bedroom ko duk dare nike son zuwa." Yana dariya me sauti ya ce
"Yea You can use the elevator ma." Shiru suka ɗanyi kafin a hankali ta ce."
"Aminullah nasan cewar kana son girlfriend ɗinka da tayi aurenta but Please ka bani dama a matsayina na friend ɗinka in kwantar maka da hankali hankalina baya kwanciya idan kana cikin damuwa kaji."
"Ai ko yanzu kina kan kwantarmun da hankali, maganar da nike ɗanyi da ke ba ƙaramin kwanciyar hankali nike samu ba, nagode kinji."
"Ba komai My Meen ni kwanciyar hankalinka shine burina a ko yaushe, shiyasa raina ma fansa ne akan farin cikinka, zan iya baka dukan jikina ma da zuciyar har ruhin." Yana wani murmushi ya ce
"For this alone i will have to give you something to recharge your phone, kafin mu tafi shopping ko zaki bini muje dubai next month 2weeks kawai zamuyi mu dawo." Cikin wani farin ciki tace
"Sure mana zan bika, dama akwai kayan da zan siyo na shop ɗina to da zanje uk ne da Egypt but na fasa muje dubai ɗin kawai." Yana jinjina kansa ya ce
"Alright on 12 next month ne tafiyar idan ki fara neman visa."
"Ba damuwa Mjay will do that ba kuma zai gane mun wani tafi tare ba idan na nuna on 12 nake so zanje dole zeyi abin da ya dace na sani." A hankali ya ce
"Alright Raheemah na gode sosai Please send your acc details in saka kuɗin recharge card." Godiya ta masa sannan ta ajiye wayar tana ayyana yanda zata tabbatar Amratu ta haukace akan baƙin cikin da zata riƙa cura mata saboda Aminullah, se ta ƙara haddasa rashin zaman lafiya a tsakaninsu nan da nan ta tura mata masa acc details shi kuwa immediately ya crediting acc nata da 3.M ita kanta taji tsoro, saboda tasan maza basa kyautar banza wato ta saka katin wayar 3 million to idan suka je dubai ashe daga ranar ta zama millionaire kenan hmmm..
*BAYAN SATI ƊAYA.*
Bukar kamar abin tsafi tunda ya dawo daga tafiyarnan banda sha'awar Fatima ba abin da yake ji a ransa, sha'awar yarinyar ta addabesa har bashida wani sukuni saboda rashn kasancewa da ita, ko kaɗan kuma baya samun gamsuwar da da yake samu a wurin mazan da yake bibiya wanda dama ba wai ɗabi'arsa bace ba hakan shi ɗin manemin mata ne na bugawa a jarida, neman kuɗi ne ya kaishi ga hallakar da yake ciki kuma dama idan kaje zasu tambaya abin da kafi so da zaran ka faɗa zasu rabaka da abin nan na tsawon shekaru biyu da rabi zuwa shekaru uku ko da kuwa cewa kayi kafi son kasancewa da uwarka zasu ce lallai ka gujewa duk inda take har na tsawon shekaru biyu da rabi ko uku, to shi Bukar ba wai ya sani bane da ya je neman dukiyar suka ce me ya fiso a duk duniya ya ce Mata sune abin sonsa yana son ya ganshi yanata amfani da mace shine aka bashi sharaɗin farko akan yin luwaɗi Allah ya kiyashemu, akace kuma an haramta masa kwamciyar ya dai shiga ramin mace har na tsawon shekaru uku kuma ya tabbatar ya nemi mace Virgin ya aura ya ajiye baya komai da ita har na tsawon wa'adin da aka ɗebar masa kafin daga baya suyi mu'amalae aure ita ce luck ɗinsa muddin ya tara da wacce ba virgin ba laƙaninsa ya karye, sai da ya shafe 5month neman virgin don sai ogansu ya duba da tsafinsa duk wacce aka kawo idan virgin ce har yaci karo da Fatima yakai sunanta aka tabbatar masa da hakan daga nan kuwa ya daddage ya shige musu ganin suna neman taimako ya nuna ze taimaka musu ya auro yar mutane yana nuna mata baƙin hali don a cikin sharaɗin ance lallai yarinyar da zai taran da ita dole sai tasan yana aikata gay ɗin shiyasa ya samu sa'ar ta. Shi kuma Habib ya kasa samun virgin so ɗaya ya samu amma fir ya nuna kuɗin ya nuna kuɗin amma taqi ta amince ta aure san ba yanda be buga ba da wannan takaicin ya haƙura kawai amma sai ya kuɗiri niyyan ganin bayan abokin cin mushensa bukar don haka ya tafi wurin wani malami aka cinnnawa Bukar sha'awar Fatiman don ya haiƙe mata kafin lokacin ya cika komai ya kalace tun da shi ya kasa samun haɗin kanta! To yanzu da Bukar yaga zai lalata aikinsa sai ya yanke shawarar turata kano karatu don ya fahimci zamansu a wuri ɗaya ba alkahiri bane ba kuma ya vcc Fatima bazata taɓa bin maza ba duk da zai ƙara ja mata kunne sosai wannan kenan.....
***************
Tun ranar da Amrah ta masa wannan message suka yi yar magana ita da Mjay ba wanda ya ƙara neman wani, ita dai har ga Allah duk sanda zata shiga motar ko take cikin motar a zaune tana tuƙawa yakan faɗo mata, wani zubin takanci kamar ta kirashi amma zuciyarta yana mata gargaɗi akan kar ma ta fara kiransa ita ɗin akwai igiyoyin wani akanta masu ƙarfi da ƙwari. Yau ma kamar kullum tana shiga cikin motar ta fara warming Mjay ne ya faɗo mata batare da shiri ba murmushi ya suɓuce akan fuskarta ta saka rivers kawai ta juya tabar cikin gidan hankalinta a kwance, kwananta huɗu yau cif bata saka Aminullah a idon ta ba ko meye dalili ita baga sani ba sam, yakice tunaninsa a ranta tayi kawai ta kama hanyarta ta zuwa office har ta isa, bayan ta zauna office befi da mintuna 40 ba wayarta ya soma ƙara ta ɗaga wayar tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa ganin me kiran, Sallama ta yi ya amsata cikin girmamawa kafin a hankali ta ce
"Barka da wanan lokaci Sir." Cikin kamewa irin ta kamilin namiji ya ce
"Lafiya ƙalau Barrister kina lafiya?"
"Alhamdulillah Sir ya aiki?" Murmushi ya yi kamar tana gabansa
"Ai nace ki riƙa kirana da Yaya Majid ko." Tana daɗa russunawa ta ce
"To Yaya na."
"An saka Engine mun samu Engine anan Nigeria so an ɗaura miki a jikin motar, mechanic ɗin ze kai miki motar gida ne ko office." Cikin jin nauyinsa ta ce
"Yayana na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi sannu da ɗawainiya na rasa da wane bakin zan maka godiya se dai fatan Allah ya sanya maka alkhairi aduk abin da ka saka a gaba." Murmushi ya yi saboda yaji daɗin addu'ar ta kafin ya ce
"Ameen Ameen ba komai my little sister, anything for my sister." Shiru suka ɗanyi kafin ya sake cewa
"Duk abin da yake damunki ko kikeso ki yi magana da wani akan abin kimun magana mai tsaye i will surely e there for you always." Nan ma godiya ta masa haka tace akai mata motar gida da yamma kafin suka yi sallama.
Leo kuwa acan ƙasar da yaje sai yanzu Fatima ta masa karan tsaye a zuci, duk sanda ya tuna cewar tanada aure har wani zazzaɓi yake jin ya taso masa, kwanakin nan be isa ya kwanta ba se ya yi mafarkin ta, abin ya soma damunsa don haka yake so lallai ya dawo yazo ya ganta ya tabbatar tana lafiya don yanzu haka tunanin sa idan hala wani abu ya sake taso mata ina zata je da damuwa? Wane gidan zata shiga? Wa zai taimaketa? Ire iren waɗannan tuna ne tunanen sune suka tilasta masa haɗa koma santsa ya nufo gida Nugeria.
Ranar daya diro Nigeria a wannan ranar Bukar ya ɗauki Fatima zuwa Kano don yin NCE daya samo mata acan!
*KAMPALA ESTATE 2025*
*BILKISU GALADANCHI*
***