14
by @oumfatima33
💞💞💞💞💞💞💞💞
*AMATURRAHAMAN*
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
💞💞💞💞💞💞💞💞
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*BOOK 1*
*PAGE 14*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
*****Cikin natsuwar da take halittarta ce tayi sallama da zazzaƙar muryarta cikin station ɗin da aka shaida mata cewar Yayarta tana ciki. Gaba ɗaya ƴan'sandan dake saman kanta suka zuba mata ido suna kallon tsananin kyau, da kwarjini harma da natsuwar dake tattare da matashiyar yarinyar da ta shigo.
A natsenta ta gaishesu suka amsa mata da fara'a da mutuntaka "Dame zan iya taimaka maki ƴammata?". Wani matashin saurayi ɗaya daga cikin ƴan'sandan ya tambaye ta da kulawa. "Nazo amsar Yayata ne da suka yi faɗa aka kawo su nan." Ta faɗa tana sadda kai sabo da ɗacin da take ji na zaman Ya Nafinta a cell.
Cike da mamaki suke kallonta jin abinda ta faɗa, ganin yarinya nutsatstsiya mai kwarjini da tarin nutsuwa kamar wannan tace wai da Yayarta a cikin waɗan can sakarkarun da basu san ciwon kansu ba. "Miye sunanta?". Matashin daya fara mata magana a farko ya kuma tambaya, tunda yarinyar ta shigo yake kallon tsananin kyau da kwarjinin da take da shi, sosai yaji ta burge shi ta shiga zuciyarsa.
"Sunanta Nafisa Mukhtar Jiƙamshi". Amaturrahaman ta faɗa wanda hakan ne ya maido matashin daga duniyar tunani daya tafi.
"Ok bari a fito da ita". Ya faɗa yana nufar inda cell ɗin yake. Matashin mai suna Yahaya shi ya tsaya mata aka yi settling case ɗin aka fito da Ya Nafi suka wuce gida ba tare da tace mata komai ba.
Suna shiga gida ta wuce ɗaki bata kula taba ta fara cire Uniform ɗinta domin shiga wanka, ganin ta ɗauki kayan wankanta ta nufi waje ba tare data kula taba yasa Nafisa ta riƙo hannunta tace "Wai baza ki kula ni ba ne? Kice wani abu mana".
Juyowa tayi ta zuba mata waɗannan idanun nata masu tsananin kyau da kwarjini tana kafeta dasu "Ni ki bar kafe ni da Waɗannan idanun naki masu shegen kaifi, kiyi magana kawai". Ya Nafi ta faɗa tana janye idonta daga cikin na Amaturrahaman data kafeta dasu. "To me kike so ince maki Yaya Nafi? Ai shike nan tunda haka kika zaɓa mana, shike nan tunda so kike dole sai mun amsa sunan ƴan'iska karuwan da ake kiranmu dashi. Me yasa zaki wulaƙantar da kanki ki riƙa dambe da wasu sha-sha-shu ƙazamai waɗanda basu san ciwon kansu ba, haba don Allah wacce irin rayuwace wannan? Me yasa baza ki bar mu muji da abinda Abbanmu ya aikata ake zaginmu dashi kawai ba?!". Ta ƙare maganar cikin matsanancin kukan da sautinsa kaɗai zai shaida maka ƙunar da mai fitar da shi take ji.
Janyota tayi ta rungume tana fashewa da kukan itama ta fara magana "Kiyi haƙuri Amahh nima ba'a son raina komai yake faruwa ba ƙaddarace, amma in sha Allah zan yi ƙoƙarin ganin na daina... Ki sani har cikin zuciyata bana son irin rayuwar da nake ba yanda zan yi ne wannan itace ƙaddararmu, kila ina girbar abinda Abbanmu ya shuka ne, dama ance ita zina bin jini take yi tayi ta yawo a zuri'a, to nice zakkarku kamar yanda Abbanmu ya zama zakkar gidansu, sai dai bana fatan ko kaɗan wannan mummunan aikin ya shafe ki, nayiwa Umma alƙawarin kula dake da dukkan ƙarfina, nayi mata alƙarin baki kariya akan ko wane irin kalubalen da zai tunkaro ki ni zan tare maki shi matuƙar ina numfashi a duniya. Ina roƙonki dan Allah karki bari ki faɗa irin rayuwar dana faɗa ko mai zai faru, mu kaɗai Iyayenmu suka haifa don haka ina so ke ki tsira, ki zama tsarkakakkiya kamar Ummanmu kada Abbanmu yayi galaba a kanta ta hanyar janye mu i zuwa tsagensa!". Ta ƙare maganar da ƙyar tsabar yanda kuka yaci ƙarfinta.
Ƙara riƙeta Amaturrahaman tayi suka sha kukansu suka gaji suka rarrashi kansu kafin ta tashi ta nufi wanka cikin sauri domin lokacin sallah ya ƙure mata sosai har ana gab da kiran sallar la'asar.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Zaune yake a cikin ofishin nasa yayi nisa a cikin tunanin daya lula, ga tarin files jibge a gabansa na marasa lafiyar da zai duba amma ya kasa bada damar da zasu fara shigowa domin gudanar da aikin da shi ya kawo shi Asibitin. Bai taɓa tunanin soyayyar mitsitsiyar yarinyar da bata wuce autar ɗakinsu ba zata masa irin wannan mugun kamun ta hana shi sakata, har take ƙoƙarin shiga aikinsa ba. Doctor Farhan kenan babban likita kuma kwararre dake aiki a babban Asibitin gwamnati dake cikin garin Matazu, shi ɗin Haifaffen garin Katsina ne kuma mazaunin can. A duk sati sau ɗaya yake shigowa Asibitin domin duba manyan Cases wanda ƙananun likitoci baza su iya settling ba.
Yana da aure Matarsa ɗaya da yara biyu amma hakan bai hana shi neman Matan banza ba, mugun ɗan neman mata ne duk budurwar daya ƙyalla ido ya gani ta biya masa sai ya taya sai dai in bai samu ba. Yana da Asibitinsa ta kansa a cikin garin Katsina wanda a can yake sheƙe ayarsa da ƴammata.
A irin haka ne ranar dasu Nafisa suka kawo Ummansu yana Asibitin ta nemi taimakonsa ya nuna mata ainahin kalarsa amma bata bashi haɗin kai ba, batare data san ƙaddarar hakan na jiranta a gaba ba.
Tunda ya ɗora idonsa akan Amaturrahaman soyayyarta mai girma ta kama shi so kuma na gaske wanda yake jinta can ƙasan zuciyarsa. Bayan ya kaita gida da gawar mahaifiyarta ya tafi ne da niyar dawowa bayan kwana biyu ya fuskanci Yayarta ya bata haƙuri ya kuma roƙeta ta bashi Amaturrahaman zai jirata har lokacin da ta buƙata in dai za'a bashi ita ya aureta.
Sai dai yana komawa gida tafiya ta taso masa mai muhimmanci akan aikinsa wacce ba zai iya tsallakewa ba, dole ya wuce da ƙudirin yana dawowa zai je ya fuskance su. A jiya ya dawo yau kuma ya taho Matazu, sai dai bai samu ganin ko ɗaya daga cikin su ba don an shaida masa Yayar ta tafi yawon gantalinta ƙanwar kuma ta tafi makarantar boko.
Jiki a sanyaye ya dawo da niyar zai koma idan ya gama duba marasa lafiyar da zai duba, sai dai ya kasa taɓuka komai. Ƙwan-ƙwasa ƙofar da akayi ne ya maido shi daga duniyar tunanin daya tafi, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya bada izinin shigowa.
Doctor Zubairu ne ya shigo don ganin ko lafiya patient sun taru ana ta jiransa amma shiru ba wanda aka fara kira.
"Doctor kana lafiya kuwa?". Ya tambaya da kulawa.
"I'm ok". Kawai ya faɗa yana bashi umarnin fara shigowa da mutane, ture komai yayi yaci gaba da duba marasa lafiyar da suka fara shigowa.
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
Katsina....
Dokajo Mansion...
Fitowarta kenan daga wanka ta zauna gaban makeken dressing mirror ɗinta tana shirya kanta cikin farin ciki da annashuwa sabo da dawowar mutumin da take tsananin so a yau. Don haka take ta sauri don ta kasance ɗaya daga cikin wacce zai fara gani don ta lura idan ba ƙara cusa kanta tayi a gare shi ba haka zai yi ta zuwa yana tafiya ba tare daya san da zamanta a cikin gidan ba bare soyayyar da take masa ba, duk irin shishshige masa da take yi sai ya rinƙa nunawa bai ma san me take nufi ba. Gashi ita kuma a kullum ƙara matowa take a kan son sa kamar zata yi hauka, bata da aiki sai ɗora hotunansa a social media da malaman dake nuna tsan-tsar son da take masa. Hakan da take yi ne yake ƙara harzuƙa Anisa har ta kasa jurewa tayi mata magana ranar sai da aka raba su.
A ɓangaren Hajiya Busaina ma tunda gari ya waye ma'aikatan sashinta suke ta kai-kawo n gyare-gyare da shirin dawowar babban ɗanta mafi soyuwa a gare ta daga doguwar tafiyar da yayi wani aiki, da kanta ta shiga kiching Ita da Haneen dake taimaka mata suka haɗa masa abinci mai rai da lafiya sabo da baya cin abincin ƴan aiki.
Tun da Safen ta tura Muzaffar da Haneen suka gyara ɓangarensa suka saka ƙamshi, sai da komai yayi kamar yanda suka san yana so suka rufo sashen.
Basu kaɗai ke murna da shirin dawowar tasa ba har da ƴammatan dake haukan sonsa a Familyn, barin ma Zaheera da kowa ya san irin haukan son da take masa. Ga kuma Anisa a gefe ɗaya wacce itama ta ɗagawa Mahaifiyarta hankali a kansa, itama ta dami Mijinta akan yayi wani abu a kai.
Kafe 3:40 na yamma motocinsa suke shigowa cikin Mansion house ɗin mallakin Muhammad Dokajo. A Kano jirgin daya ɗaukosa daga Paris ya sauke shi, yana fitowa ya samu motocinsa na jiransa don haka ba ɓata lokaci suka ɗauko hanyar Katsina cikin ikon Allah sai gashi sun iso lafiya.
Motocin na kammala tsayawa babban yaronsa Samuel ya fito da sauri ya buɗe masa ƙofa, bayan wucewar mintunan da baza su haura biyu ba ya ziro lafiyayyar ƙafsrsa dake sanye cikin Boot masu kyau, kansa ya ziro kafin ƙaƙƙarfan jikinsa ya bayyana gaba ɗaya.
Sanye yake cikin asalin kakinsa na Sojoji da suka fito da cikar zatin halittarsa suka ƙara masa kwarjini, masha Allah Zayyad yaje duk inda ya kamata Namiji yaje, lafiyayyen matashi ne mai cikakken dirin halittar jiki mai tsananin kyau da kwarjini da haibar da suka lulluɓe kyawun nasa wanda hakan yasa ya ƙara zama na musamman ɗin da dole ma ƴammata su mato masa.
Gaba daya mutanen gidan sun fito tarbar sa domin doguwar tafiya yayi ta wata uku zuwa wani aiki da aka turasu mai haɗari a ƙasar Paris. Tunda ya tafi tsawon wata uku ba'a ƙara jinsa ba koda a waya ne har sai da suka kammala aikin cikin nasara suka dawo sannan. Ba ƙaramar damuwa Ammah da Abba har ma da Baba Alhaji da sauran masu ƙaunarsa suka shiga ba.
Wani irin sanyi yaji yana sauka a zuciyarsa ganin ahalinsa a gabansa suna masa maraba, a natse ya fara takawa gaban Baba Alhaji dake ta zabga murmushi yana faɗin "lale marhabin da dawowar Sadaukina." Yana isa bai tsaya jiran komai ba ya rungume shi yana sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya. Sosai yayi kewar tsohon, yayi matuƙar kewar kulawarsa a gareshi.
Ɗaya bayan ɗaya yabi Iyayensa ya gaishe su kafin ya nufi sashen mahaifiyarsa Haneen na gefensa tana masa magana cike da jin daɗin ganin ɗan'uwanta. Duk da kasancewar bai fiye fara'a ba haka ba yana nufin baya son ƴan'uwansa bane, yana matuƙar son su fiye da komai a duniya.
A natse ya zauna saman ɗaya daga cikin tsadaddun Royal chairs ɗin da aka ƙawata palon dasu ya lumshe ido yana zuƙar daddaɗan ƙamshin turaren itace da aka baɗe palon dasu. Ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe ido nutsuwa na saukar masa, "Kaje kaci abinci sai ka samu ka huta." Ammah ta faɗa tana dubansa cike da kulawa da tausayawa.
Kallo ɗaya tayi masa tasan akwai gajiya tattare da shi, sai dai tsananin jarumtarsa ya ɓoye hakan itama sabo da tafi kowa saninsa, ta san ko wane irin motsinsa.
"Zan fara watsa ruwa ne Ammah." Ya faɗa a hankali yana murza goshinsa.
"To kaje kayi wanka Haneen zata kai maka can ɗin."
"To Ammah, jazakillah". Ya faɗa yana miƙewa ya fice daga falon. Ajiyar zuciyar samun nutsuwa ta sauke tana lumshe idanunta. Tunda yayi wannan tafiyar ta kasa samun kwanciyar hankali, ance babban aiki ne aka tura su mai matuƙar haɗari, gashi tunda ya tafin aka daina communicating da shi don ba'a samumsa.
Data kasa jurewa ne tayiwa Abba magana shine ya tuntuɓi manyansu aka shaida musu yana kan aiki ne sannan ta ɗan samu natsuwa kaɗan. Addu'a taci gaba da masa kamar yanda ta saba kullum cikin sallolinta da kuma tashin dare da take tana raya shi da ibada.
Ta sani tana da maƙiya a gidan, ba kowa yake son ya buɗe ido ya ganta ita da yaranta ba musamman Zayyad da ake ganin Mahaifinsa da Kakanninsa sunfi sonsa, shi yasa bata wasa da ibada ta riƙi addu'a sabo da ita ɗin makamin mumini ce.....
*Oum Fatima*