KAMPALA ESTATE

Page 13

by @68billygaladanchi

*KAMPALA ESTATE*


NA


*BILKISU GALADANCHI*


*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*


https://www.arewabooks.com/chapter?id=6790e01cf524f8dc4eabb9dd


13.


Da yamma tana tashi office kasuwa ta wuce don yin restocking wasu abubuwan saboda kwata kwata Aminullah bayi yake ba, ita kuma tana yin komai ne saboda farin cikin mahaifiyarta da farko takan kai ƙararsa amma daga bisani mahaifiyarta ta nuna rashin dacewar hakan akan abinci kuma ta tilasta mahaifin Amran yake tura mata kuɗi masu ɗan kauri duk ƙarshen wata akan tayi restocking komai na gidan se dai shi mahaifin nata be taɓa sanin cewar mijinta baya ɗaukar ɗawainiyar ta ba, abin da yasa yake turawan saboda shi 'yarsa ko ɗan karuna take aure baya gajiya da yi mata hidima, haka mahaifiyar Aminullah dake shima ba laifi suna da masƙi sosai takan tura mata kuɗi duk watan duniya saboda haka be taɓa damunta ba rashin kulawarsa dama uwarsa ta aurota to ta ɗauka a hakan cewar ta yi mata lalurar, tun daga kayan lefenta kuwa da take da yaƙinin ba bu kwabon Aminullah a ciki har yau bai ƙara siya mata ko da ɗan kamfai bane ba, hasalima bata taɓa tambayarsa siyen abu ba, abu ɗaya ta sani yana yi shine harkar gidansa kuma duk mazauna mini gate a kampala estate su suka mallaki gidajen ba haya bane ba, don haka dolensa ya kula da dukiyarsa ko da baya son hakan. Sai wuraren 6 ta kammala siyayyar da take ta juyo gida tana tunanin yau irin gajiyar da tayi ga kuma shiga kotu gobe saboda akwai wani Rape case dake hannunta tana so ta tabbatar da gaskiya saboda ana so ayi cover up ma yaron da ya aikata fyaɗen saboda reputation na mahaifinsa ita kuwa abin da bazata ɗauka ba kenan, mahaifin yaron jin cewar ita zata hau case ɗin a matsayinta na lauya me kare wanda akaiwa laifi ya taka har office ɗinta and he offered to give 200.M to her akan ta janye amma fir taƙi tace ita bincike kawai zata yi a tabbatar da adalci. A gajiye ta iso compound ɗin wuraren 6:35 a lokacin ana haramar barin masallaci matan Estate na baje suna sowa, kai tsaye kuwa zuwa ta yi ta yi parking tana fitowa ko kallonsu bata yi ba ta wuce cikin gidan ta su kuma duk sun zuba mata ido, Raheemah kamar taje ta shaƙeta har lahira take ji amma tana so ne tabi komai a sannu saboda ita ma akwai case da suka bata kar ta sauke mata hawan jini su shiga uku amma da zaran an gama case ɗin 6month ya mata yawa a hannun she will definitely run mad kowa ya huta da izzar masifa.


Meenah taɓe baki ta yi ta kalli uwar daba "Kina dai ganin wulaƙancin da Amrah ke yi tun sanda suka ɗan yi hatsaniya da Heema wai na ce nikam ita tafi kowa zuciya ne da zata haɗa har mu bata yiwa magana?" Uwar daba tana gyaran zamanta ta ce


"Kuyi haƙuri don Allah zama ne ya haɗamu, and we are classy very classy ladies bazamu zauna muyita ɓatawa juna rai ba akan wani ƙanƙani abu ba, people take things differently so learn to give people space idan suna fushi its self respect da kanta zata dawo, amma idan wani ya nuna ya damu sai ta mayar da mu sakarkaru yanzu da bata nan waninmu ya kasa ne?" Nan dai aka kafe chapter aka tsigale ta tatas.


*Aliyu*


Yau kwanansa biyu a gidansa na Lagos amma ko so ɗaya be taɓa ganin giccin yarinyar ba abin ya dameshi sosai har ya sanya ya fara rasa sukunin sa don yana ji ko hala akwai wani abu da ya ke damunta da be sani ba? Juyi ya yi akan gadonsa cikeda kasala yana yamutsa fuskarsa ganin ya ɗauki dakon damuwa da matar wani ya dasa a ransa duk da yasan shi fa ba wai wani abu bane a ransa face tsantsar tausayi. Hannunsa ya miƙa ya ɗauki wayarsa yana tunanin wa zai fara bincika akan ainahin inda ta tafi amma ya gama tunanin ba wanda ze iya tambaya, Aaliya ce ta faɗo masa hakan yasa ya lalubo number ta ya fara kiranta ringing biyu kuwa ta ɗaga wayar ta gayar dashi ya amsa kafin ya ce


"Aaleeyah dama its about that girl that my neighbour a kampala estate kunyi exchanging digit da ita kuwa?" Se da ta ɗanyi tunanin na few seconds kafin tace


"Ohh Zarah nooo wallahi bamuyi ba, nima ina ga so in ganta inji ko zata dan bani recipe na girkin data mana ranar." Cikin jimantawa kansa ya ce


"Alright no wahala shikenan." Cikin kulawa tace


"Yaa Leo is everything alright?" Tashi zaune ya yi


"Noo ba komai ban ganta bane tunda na dawo and kinsan halin yayanta I'm just worried want to check on her kawai." Itama Aaleeeyah jajantawa tayi kafin tace yaushe ze zo kano yace mata in two day's time suka yi sallama. A ɗan dagule ya shiryar barin gidan saboda ya kasa bacci kawai da ace ze ga ko giccin ta ne da bazai damu kansa akan komai ba.


Zarah duk da gida ɗaya sukutum Bukar ta kama mata haya but bata jin daɗin zaman gidan kwata kwata ita kaɗai, ga iyayen dokoki da sharuɗa tsaurara, yana zuwa dama kai tsaye enrolling nata ya fara yi awurin koyon mota after that kuma ya tabbatar cewar ya mata license da komai kafin ya nemo mata mace househelp ta hannun matar wani abokin sa a tsaurare ya tabbatar mata cewar karta kuskura ta fara magana da maza kai ko kecturer ne kuwa, abubuwa da yawa ciki hadda saka hijab da niƙab ko nan da can zata je, motoci biyu ya ajiye agidan yace yau idan ta hau wannan gobe ga hau waccen koda an samu akasin wata daga ciki ba lafiya, data roƙeshi ya dawo mata da mahaifiyarta a kanon sai yace se ya yi shawara don bega dalilin yin hakan ba, daga bisani ya nemo mata mass communication ya tattara xuwa dubai abinsa wurin watsewarsa.


Amrah tana zaune a kichen ɗinta a saman plastic chair tana jiran miyan da take na eforiro ya gama dahuwa ta juye ta saka a freezer saboda ya fiye mata sauƙi, zata yi girki me yawa duka wani stew da soup's da kanta zata giggirka ta saka a freezer, wayarta ta fara ringing ta janyo wayar tana murmushi ganin Mjay ne duk da faɗuwar gaban data samu, ɗaga kiran ta yi tana masa murmushi still cikin sanyin murya ta yi masa sallama ya amsa sannan ta ce "Ina wuni ya aiki Yaa Mjay?." Yana faɗaɗa fara'arsa ya ce


"Lafiya lau Alhamdulillah ɗazu na ganki a kasuwa ai inata gaisuwa baki ji ba." Cikin jimami ta ce


"Ayyah ban kula ba ban ganka ba wallahi, dama maza suna kasuwa irin ku?" Ɗan dariya ya yi me sauti kafin ya ce


"A mana suna zuwa idan suna da abin da zasuyi, nima akwai abin da naje yi ne, a bayan kasuwar akwai wasu da suke karɓar kaya daga Company kuma sun dulmiyar da kuɗi kusan 180.M to naje da kaina ne inyi addressing na issue ɗin kuma sai suka baƙanta raina, shine naje neman wani kifi da nike so bayan na kammala shi ɗinma ban samu ba na dawo." Resting bayanta ta fara yi jikin kujerar kafin ta ce


"Ayyah people can be so mean wallahi yaya zasuna yiwa mutum wasa da dukiya, ai da ka barni dashi ba zai wuce 10 days ba he will provide your money haka muke fama da case ɗinsu idan na shigar da case nashi har tara se ya biya haba." Murmushi ya yi kafin ya ce


"Noo Madam baza'ayi haka ba, ki rabu dashi ai kansa ya yi wa gobe ai be isa yazo ya ce mun in bashi wani abu ba kuma ko?" Cikin ɗan rigima tace


"Allah Yaya wallahi sai ya dawo da kuɗin nan ko ƙwandalarka bazai yi ciwon kai ba, ba yanda za'a riƙa ƙyalesu duk ma wani case da ka share a tattaro a bani address da details irin wannan fa karyaka zasuyi." Mjay shiru ya ɗanyi kafin ya ce


"Kuma mutane da yawa suna mun hakaz yanzu haka treasury manager na an nemi over 650.m a hannunsa an rasa na rasa me zan yi wallahi, su basa tunanin ba bishiya muke jijjigawa suna zubowa ba na daɗe ina shan wahala kafin kampunan nan su kafu." Cikin masifa ta ce


"Shi ɗinma fitowa dasu i hope an dakatar da shi daga aiki?"


"Calm down mana Barrister yana on suspension muna kan bincike."


"But he should be behind bar's by now what if he flee? Please gobe i will cancel all my meetings all of it zan zo ka bani address i will have to investigate my self ai ba'a haka ai, zanzo da detective Data." Mjay dariya ya yi me sauti


"Barrister haka kika iya rigima? Kinga abi komai a hankali inaga zaifi." Cikin rigima tace


"Noo ni fa gobe gobe zanzo, dama ina less busy gaskiya duka wani case a tattaro su zamuyi bincike a kansu, ba'a wasa da dukiya na gani a wurin mahaifina kowa tsoron taɓa masa yake saboda yana ɗaukar mataki da zaran anga baka yafewa azzalumai kowa ze shiga taitayinsa ne." Dariya ya ƙara yi


"To na gode Barrister se kin shigo goben what time zaki zo?" A hankali tace


"11: am in shaa Allah nayi restocking na kayan abinci ina rage soup's ɗina saboda in saka a freezer so idan na tashi i will cook 2 different soups kafin na fito." Yana jinjina kansa ya ce


"Ohh Barrister so you cook?" Dariya ta yi


"A mana banson girkin masu aiki shigasa nake yi da kaina.".


"Bakiso ko oga baya so?" Tana dariya kamar bazata yi magana ba sai kuma ta ce


"Baya cin abinci a gida ai, i made meals for my self and the house help." Jinjina kansa ya yi kamar tana gabansa


"To Barrister i will like to taste your cookings so pack some for me while coming tomorrow." Dariya ita ma ta ƙara yi


"What do you like most to?" Se da ya ɗanja fasali kafin yace


"I like swallow da any soup but i prefer anything vegetable with fish in it." Ɗan dariya ta yi har ya tambayeta dalilin dariyar ta dan tsagaita kafin tace


"It's funny how we actually like the same thing wannan ne favourite ɗina swallow, vegetables and fish, shiyasa indai gashin kifi ne da peppersoup abarmun abuna kawai." Cikin sigar wasa ya ce


"Banda yabon kai fa kar ki bari muci muzo muna amai." Tana ɗan ɓata fuska ta ce


"Allah i'm not only Barrister I'm a Barrister and more, the great chef barrister Amratu." Dariya ya yi don ta bashi dariyar da gaske ya ce


"Fine then we shall see." Hira sosai suka yi akan issues ɗinsan na Company kafin suka yi sallama.


A wannan daren kuwa Raheemah yanda suka tsara da Aminullah haka suka yi, tun da suka watse daga majalisarsu ta munafurci sai ta shigo gidanta ta gama shirinta tsaf na banza ta bulala Jilbab har ƙasa tabi ta baya ta shiga gidan Amrah kamar yanda suka tsara da Aminullah acan kuwa basu sararawa juna ba sai 12:30 na dare Aminullah a karon farko sheɗan ya daɗaɗa masa matar wani a ransa yaji a duk duniya bai taɓa saduwa da wata mace me kwatankwacin daɗin Raheeman ba a ɓangarenta kuwa taji daɗin kasancewa tare da shi duk da kuwa baifi mijinta da komai sai uwar jarabar data fahimci yafi Mjay da yawan surutu he is the lousy type amma koma menene she will definitely dig his money za taita haƙa ko nawa ne zata kashe don ta ƙara ɗanɗano a wurin uwar daba saboda Aminullah!


Mjay ya nemi matarsan yayta knocking bata buɗe ba haka ya haƙura saboda ta saba yin hakan tsammaninsa tana ɗakinta ta kwanta.


*********


Washe gari kuwa sassafe Amrah na tashi ta fara hada hadan girkin nan tsabar yanda take so ta faranta masa rai fasa yin sauran stew tayi kawai ta warming masa Eforiro data girka ta masa tuwon masa me shegen laushi da kyau sannan ta masa gashin kifi da irish a gefe ta masa fresh Apple and pineapple juice ta jere komai a wnai basket me kyau sannan ta shirya kanta a cikin wata jallabiya Emerald green ta kampanin Arham hussain da wani karamin hijab shima na kampanin Arham hussain daya matuƙar karbeta banda lipbalm da kwalli ba komai a fuskarta, a ƙafarta kuwa wani ubansun wage hill's ne black da jaka black dukkansu na kampanin Milano, she looks so beautiful and in a modest and decent way, me aikinta me suna Biba ita ce ta tayata da basket ɗin har zuwa mota, kasancewar tayi late don sai after 10 ta fito ya sanya ba motar kowa a cikin matayen Estate ɗin duk sun fita, da Google map ta yi using ta ƙarasa katafaren company Mjay da ganinsa ya sa sai da ta raina kanta don zata iya cewa ko mahaifinta babu ɗaya daga cikin kampunnansa da ya kai wannan girma it's far daga cikin gari but an narka kuɗi kam. Da kanshi ya sakko taryanta suka gaisa a mutunce sannan yaronsanya ɗaukar mata basket suka wuce har VIP Guest house dake cikin kampanin inda baya ganawa da kowa sai manya manyan baƙinsa, tana gabatar masa da abincin ba ɓata lokaci ya fara dubawa sanda ya buɗe grilled fish ɗin kallonta ya yi suka haɗe iso ya saka mata wani murmushi ba tare da ɓata lokaci ya saka fusk ya ɗan gutsira ya kai bakinsa da mamaki ya kalleta sai kuma bece komai ba ya ɗauke idon sa ya shiga cin abinsa duk suka yi shiru sai da ya cinye ɗaya tas har irish dake kai dake dama duk ɗaya yana naɗe ne a foil da dankalinsa a gefe sannan ya ɗago ya kalleta yaga ita wayarta ma take dannawa cikin tsokana ya ce


"Barrister a ina siyo wannan kifin sun iya gashi sosai i can't get enough of it nima zan fara saya a wurinsu." Dariya yayi da be taɓa ganin tayi irinsa ba har fararen haƙoranta ras suka bayyana gefen kumatunta duka biyu suka loɓa sannan tace


"Yaya kace mun thank you kawai yayi daɗi wannan kifin kasna indai ba chefs na gida ba bazaka samu masu sayarwa da me daɗinsa ba, da Youghurt na gasa fa da kuma spices na indiyawa." Dariya ya ƙarayi shima sannan ya na saisaiga nutsuwarsa ya ce


"Na yadda wallahi ya yi daɗi i hope sauran ma mani kika yiwa?" Gyaɗa masa kanta ta yi ya ce


"To na gode zan bada tukuici amma fa kin shigo hannuna kenan mayen kifi neni don haka kullum ma ki shirya gasamun ko a yimun peppersoup ko a soya na bar miki kayanki naki ne." Murmushi ta yi sannan tace


"Ba matsala anything for my brother." Shiru ne ya ɗan ratsa wurin na wani lokaci kafin ya shiga fito da matsalolin kampaninsa musamman wannan babban da baya samun isashen lokacin kulawa da shi, nan tayi going through lot of file's musamman gefen treasury nan aka fi samun matsala daga nan ta kira Detective Umar yazo suka zauna aka duba abubuwa har wuraren 4 na yamma sannan suka samu kansu shiyasa bata dawo gidan ba sai 6:18 inda ta tarar matan yau ba kowa sun watse ta wuce cikin gidanta kai tsaye. Turus tayi acikin parlour tana ƙarewa Aminullah da Rahima kallo da suke baje a cikin parlor suna shan lemo suna hira, mamaki ya kamata amma sai ta haɗiye ta ce


"Raheemah yaya dai?" Raheema na wani gyarawa 12 inches wig ɗinta zama a gefen kunne ta kalleta taba murmushi kafin tace


"Hajjaju sai yanxu tun ɗazu nazo nemanki tunda ranar daga faɗar gaskiya kika kujemu a teburin uwar daba na biyo sahu in bada haƙuri na tarar bakya nan na kuma taho ne takanas in gaya miki yaron nan fa an kama shi." With so much excitement ta zago ta zauna tana kallonta


"Kai Alhamdulillah and where is he now?"


"Yana station ai ɗan banzan yaro." Amrah ta ce


"Ba damuwa gwara da kika gayamun duk da ina da new cases i will make sure zan je station ɗin gobe.," nan suka tattauna kafin suka yi sallama ta wuce sama tana mamakin yanda Raheema tayi kane kane taƙi barin wurin amma ba komai a ranta ta wuce abinta ta kimtsa kanta a sama ta shirya kwanciya.


****

*Kampala Estate 2025*

*Bilkisu Galadanchi*

*****