17
by @oumfatima33
💞💞💞💞💞💞💞💞
*AMATURRAHAMAN*
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
💞💞💞💞💞💞💞💞
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*BOOK 1*
*PAGE 17*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
Yana zuwa ya samu Samuel ya fito da motocin da zasu tafi don haka shiga kawai yayi ya zauna ya ciro IPad ɗinsa ya shiga duba tarin sakonnin da aka turo masa ta email ɗinsa. Kusan tare Muzaffar da Haneen suka ƙaraso suka shiga Motar da yake ciki Muzaffar ya zauna kusa da shi Haneen ta shiga gaba Samuel ya tada motar sauran yaransa suka shiga ɗayar motar suka fice a gidan yayinda Salim da shigowarsa kenan yabi Motar da wani mugun kallo yana jan tsaki tamkar zai tsinke harshe ya nufi sassan mahaifiyarsa Hajiya Ruƙayya.
"Allah Momy na tsani in buɗe ido inga wancan gayen yana abinda yaga dama a cikin gidannan, ki duba da irin Motocin da yake fita Sojojinsa na take masa baya tamkar wani president!." Salim ya faɗa muryarsa da amon ɓacin rai lokacin daya shiga falon Mahaifiyarsa ba tare da yayi ko sallama ba ya fara ƙorafi.
"Na fika tsanar in buɗe ido in ganshi yana rayuwa a duniyar ma gaba ɗaya salim, wai ka ma san cewa Alhaji Baba ya mallaka masa ƙaton filin nan nasa dake Kano kyauta wai zai gina Companyn sarrafa abinci!." Hajiya Ruƙayya ta faɗa tana jin kamar ta mutum tsabar Hassada.
"Momy da gaske ne wannan maganar?." Salim ya faɗa yana zaro ido. "Ƙarya nake don Ubanka, dama ai na saba maka ita!." Ta faɗa ranta na ƙara ɓaci.
"I'm sorry Mom, maganar ce ta dake ni." Ƙwaffa tayi bata sake cewa komai ba sai shine yaci gaba da cewa "Wai me tsohon can yake nufi damu ne komai Zayyad, Zayyad sai kace shi kaɗai ne jikansa mu kuma ga agololi, kai ina da sake wallahi." Ya ƙare maganar a fusace kamar Zayyad ɗin ne a gabansa.
"Me ka isa kayi? Ai ko Ubanka bai isa yasa shi fasa abinda yayi niya ba, shima farin ciki yake da hakan. Na rasa wace irin masifa ce wannan gaba ɗaya matar nan ta shige min hanci tayi kane-kane, amma ta kiyayi ranar da zan fyato ta ita da ɗan da take gadara dashi!" Ta faɗa tana jin ɗacin yanda Hajiya Busaina tazo ta aure mata Miji ta kuma haifi ɗan so wanda kowa ya ɗauki son duniya ya ɗora masa daga Mijin nasu har iyayen mijin ta mamaye kowa.
"Ah to gara dai ki san abin yi tun wuri." Salim ya faɗa yana miƙewa ya fice daga falon. Kallon takaici ta bishi da shi tana jin haushin yanda yaƙi tsayawa ya maida hankalinsa ya zama mutum kamar kowa, ba abinda ya iya sai shegen yawo da kashewa ƴammata kuɗi, yaƙi ya maida hankali ya gama karatunsa ya kama aiki sai faman mai-maita shekara yake ga Muzaffar nan tuni ya kammala nashi karatun ya kama aikinsa aiki mai tsada kuwa, shi yasa a kullum ƴaƴan Hajiya Busaina sune na kirki a idon Mijinsu da Mahaifinsa. "Dole ka dawo cikin hayyacinka Salim ba zan taɓa zuba idanu in zama ƴar kallo ba." Ta faɗa tana cin alwashi.
Matazu.....
Kasancewar yau weekend ne ba Makaranta yasa bata tashi da wuri ba kamar yanda ta saba, dogon bacci tayi tana warware gajiyar zirga-zirgar da tayi a satin. Ganin tana jin daɗin baccin yasa Ya Nafi data gama shirin fitar ta don zuwa haɗuwa da Gaddafi kamar yanda suka yi alƙawari, bata tashe ta ba kawai ta tafiyarta bayan ta tabbatar data aje mata abin ƙarin data haɗa musu.
Kai tsaye guest house ɗin Mahaifinsa dake bayan gari ta nufa gidan dake da tarihin da bazata taɓa mantawa ba a rayuwarta, gidan da nanne inda aka ƙwace mata mutuncinta ta ƙarfin tsiya, gidan da shine silar rushewar rayuwarta, shine mafarkin komai, amma yanzu shine take kai kanta da kanta don cimma wani buri nata. Kuɗaɗe take son amsa a wurin Gaddafi manyan kuɗaɗe kuwa don haka kanta tsaye ta sanar masa yace tazo su haɗu a inda suka saba haɗuwa.
Ba tare da wata shakka ko tsoron kar wani ya ganta ba ta tunkari gidan dake can bayan gari kanta tsaye, so take a yau ta amso kuɗaɗen da zasu isa ta haɗa ta biya kuɗin gidan da tayi cinikinsa zata saya musu don ta rantse baza su ci gaba da zama a nan ba bare har Kawu Isa ya samu damar da zai aura wa Doctor Farhan Amah ba.
Bayan taje sun gama uzurin daya kaisu ta fito ƙofar gidan zata tafi kawai taji an shaƙi kwalar rigarta. "Ina zaki je baƙar munafuka? Wato baki ji duk irin gargaɗin da na maki akan Gaddafi ba shine kika sake zuwa inda yake ko? To yau sai naga uban da zai zama gatanki a wurin nan." Tana gama faɗa suka shiga jibgarta tako ina ita da ƙawayenta ba tare da jiran komai ba. Da yake itama bata tsoron rigimar haka ta shiga ramawa da iya ƙarfinta sai dai ance Sarkin yawa yafi Sarkin ƙarfi dan da nan suka jij mata ciwo amma hakan bai sa ta karaya ba.
Gaddafi dake cikin gidan yana kwasar bacci hayaniyarsu ta tashe shi ya fito daga shi sai guntun wando yana yiwa su Zakiyya ihun su rabu da ita. Nan da nan jama'ar dake wucewa suka fara taruwa duk da cewar bayan gari ne.
Tun daga nesa Muzaffar ya hango taron jama'a an zagaye wani abu "Da alama akwai abinda ke faruwa a wurin nan." Ya faɗa yana kallon Yayansa da kansa ke ƙasa yana ta famar daƙilar wayarsa. Ɗagowa yayi a ɗan fisge ya kalli wurin ya maida kansa kan abinda yake yi.
Tsabar yanda wurin ya hargitse da rigima sun zagaye ta suna mata dukan tsiya suna ƙoƙarin halaka ta yasa basu ji uban horn ɗin da ake musu ba, jin sun tsaya ba'a ci gaba da tafiya ba yasa shi ɗago kansa a karo na biyu. Ganin taron mutane sai hayaniya ake yasa shi bawa Samuel umarnin zuwa ya duba.
Buɗe Motar Samuel yayi ya fita wanda hakan ya bawa sauran Sojojin dake dayar motar damar fitowa suma, ganin sojoji a wurin yasa nan da nan mutane suka fara watsewa suna gudu kar a haɗa dasu. Tsawa ɗaya tak Samuel ya buga da ƙatuwar muryarsa su Zakiyya suka tashi a firgice daga kan Ya Nafi da suka danne suna jibga tamkar sun samu jaka. Ƙoƙarin tserewa suke Samuel ya bada umarnin a kama su duka har saurayin a kaisu gidan gonar dake gaba kaɗan kafin su iso.
Nan da nan kuwa aka cika umarnin daya bayar, har Yaya Nafi dake takawa da ƙyar aka haɗa aka yi gaba dasu, jama'ar dake wurin kowa ya kama gabansa ana tattauna maganar.
********Sai ƙarfe 10:00am ta tashi daga baccin data koma wanka ta fara yi ta wanke bakinta kafin tayi zaman karyawa tana tunanin inda Ya Nafi ta shiga, har zuciyarta bata ƙaunar yawon nan da take amma ba yanda zata yi da ita don har kuka ta mata amma ko tayi alƙawarin ta daina ba inda alƙawarin yake zuwa, shi yasa bata da wani zaɓin daya wuce tayi mata addu'a, don haka kullum tayi sallah sai ta roƙi Allah ya shiryar mata da ƴar'uwarta wacce take a matsayin Uwa da Ubanta.
Tana cikin cin abincin tana duba wayarta Sultan yaron Aunty Rakiya ya shigo da gudu yake faɗa mata Wasu na can a bayan gari sun kusa kashe Ya Nafi, kuma Sojoji sun tafi dasu dukansu. Kasa haɗiye laumar data kai bakinta tayi ta midota ta miƙe a tsorace tana tambayar yaron "Kace an kusa kasheta kuma Sojoji sun tafi da ita? To ina suka kaita!." Ta masa tambayar lokaci ɗaya tsoro na kamata da tunanin kar fa a kashe mata ƴar'uwarta.
"Ance wai wannan gidan gonar na can bayan gari suka shiga." Ai bata tsaya ɓata lokaci ba ta kunce ƙaramin mayafin data ɗaura saman doguwar rigar atamfar dake jikinta ta yafa shi ta zura takalmi tayi waje zuciyarta na tsits-tsinkewa.
Gidan gonar ta nufa kanta tsaye sabo data san shi don har shiga sun taɓa yi ita da ƙawarta Samra da daɗewa suka amsowa Babansu ƙwan zabbi da ake fitarwa a wurin, ba kalar dabbar da ba'a kiwatawa a gidan gonar tun daga kan tsuntsaye har manyan dabbobi. Don haka bata sha wahala ba ta isa gidan, bugawa tayi mai gadin wurin yazo ya buɗe yana ƙoƙarin tambayar ta mai take nema ta raɓa ta gefensa ta shige ba tare da ta saurari kiran da yake ƙwala mata ba.
Ƙarƙashin wata rumfar da aka ƙawata ta da kujeru da tables don hutawa ta hango Ya Nafi a zaune saman ɗaya daga cikin kujerun wata kyakykyawar budurwa na mata dressing ɗin ciwukan da taji cikin kulawa sai faman sannu take mata. Sauri ta ƙara ta nufi wurin tana zuwa ta fara magana ba tare data lura da mutanen dake zaune a ɗayar rumfar dake gefe ba. "Kai! Ya Nafi wasu tsinannun ne suka maki wannan dukan tamkar sun samu jaka!." Ta faɗa da tsananin bacin rai tana taɓa gefen bakinta inda aka rufe ciwon da bandage. Haneen dake kula da ciwukan da aka jima Ya Nafi tsayuwa kawai tayi tana kallon kyakykyawar matashiyar yarinyar da akalla zata bata shekaru huɗu tana faman masifa da ɗan ƙaramin bakinta mai matuƙar kyau.
Alamar kiyi shiru Ya Nafi ta mata amma taƙi shirun taci gaba da cewa "Faɗa min su Uban waye nace?!."
"Ke Amah dan Ubanki ki iya bakinki, baki san a inda kike ba ko?." Sai a lokacin ta ɗago idanunta ta shiga kallon mutanen dake wurin wanda bata kula dasu ba lokacin data shigo sabo da hankalinta na kan ƴar'uwarta. Da Haneen ta fara haɗa ido wacce ke kallonta tana mata murmushi sabo da haka kawai yarinyar ta birgeta ta shiga ranta.
A hankali ta ɗauke idon ta kalli gefen damarta inda suke zaune shida Muzaffar sai Samuel dake tsaye daga gefensa yana nuna masa abu a Tab ɗin dake hannunsa. A wani irin slow ya ɗago ya zuba mata idanunsa masu tsananin kwarjinin dake karya lagon duk wanda ya tsare dasu.
Nauyi idanun nasa suka mata wanda yasa taji yana shirin ruɗewa hakan yasa ta buɗe masa duka girman nata idanun itama tana zaro masa su wai ko zai ji tsoro ya ɗauke nasa. Akan idonun Haneen, Muzaffar da Samuel hakan ya faru don basu taɓa ganin wanda ya jure kallon tsakiyar idon Ya Zayyad ba, ko su da suke ƙannensa kuwa. Amma a mamakinsu wanna ƙaramar yarinyar da bata ida cika budurwar kirki ba ta tsare shi da kallo har tana zaro masa ido don haka suka zaro idon suma suna rufe baki da jiran ganin hukuncin da zai mata amma sai suka ga ya ɗauke ido ya mayar kan abinda Samuel ke nuna masa yana basarwa tamkar ba abinda ya faru.
Ajiyar zuciya ce ta ƙwace mata lokacin daya ɗauke idonsa wanda Ya Nafi data mutu da mamakin tsaurin idon ƙanwarta ce kawai taji, dariya taso ƙwace mata ganin yanda tayi wuri-wuri ta tabbata tsoro ne fal cikinta. Tama yi ƙoƙari wannan gabjejen mutumin data kasa kallon idonsa ko sau ɗaya sai satar kallo shine Amah take zarewa ido.
A hankali ta cewa wa Ya Nafi "Ke wai me kike a nan? Ina shegun da suka dake ki suke?." Da ido Ya Nafi ta nuna mata inda su Zakiyya suke kamun kunne bayan dukan da suka ci a hannun Sojoji. Wani irin daɗi ya ziyarci zuciyarta har bata san lokacin data sake murmushi ba tace "Dai-dai kenan saura haɗiwarku da Amah don na rantse ba wanda zan ƙyale cikinku har wancan matsiyacin da aka jibge ki a kansa, sjege mai kama da ƴan daudu!." Ta faɗa hankalinta kwance ba tare da damuwa da inda take ba.
"Dan Ubanki tashi mu tafi gida kar ki jawo a ƙaramin wani dukan bayan wanda waɗancan ƴan hauɗin suka min." Haneen data kasa riƙe dariyarta na abinda Ya da ƙanwar keyi ta matso ta zauna kusa da Amah tace tana mue"Yaya sunanki?." Ɗagowa tayi ta kalleta kafin tace "Amaturrahaman." A hankali.
"Nice name, ni kuma sunana Haneen daga yau mun zama ƙawaye." Kallonta ta kuma yi kafin ta kama hannun Ya Nafi tana cewa "Muje gida." Miƙewa tayi ba musu don itama ta matsu su bar wurin suka ji muryar Haneen tana cewa "Kuje Asibiti a kara dubata."
"Mun gode ta faɗa tana ci gaba da jan hannun Ya Nafi tamkar itace babbar, sai da suka zo dai-dai saitinsa yasa mata ƙafa bata sani ba sai gata a ƙasa ta bige gwuiwowinta. "Next time ki fara duba inda kike kafin ki buɗe wannan bakin naki mai kama da gidan tsutsa ki fara magana." A hankali yayi maganar wanda iya ita kaɗai taji mai ya faɗa.
Hawayen daya cika idanunta na raɗaɗin da gwiwarta ke mata suka zubo mata ga haushin maganar daya faɗa mata suka haɗu suka tsaye mata a rai. Kallon gargaɗi ya sakarwa Muzaffar daya taso da sauri zai kama mata ta tashi, ba shiri ya koma wurin zamansa. Saman fuskar Ya Nafi data kamata ya mayar da kallonsa yace "Idan na ƙara ganinki a wannan gidan sai na ƙarya ƙafafunki sakarai kawai, ku ɓace min daga nan!." Ya ƙarasa a tsawace.
Ai tuni Ya Nafi ta manta da ciwon da take ji ta warci hannun Amah dake tirjewa suka yi waje tana faɗin "Ke wai me ya shiga kanki ne?."
"Kina gani wancan mugun ya taɗe ni na faɗi, ƙilama na karya ƙafa."
"Da kin karye zaki iya takawa ne, ni muje tun kan ya canza shawara yasa waɗancan garadan su koya mana hankali." Wucewa tayi suka nufi gida tana ta ƙunkuni a ranta na abinda ya mata....
*Oum Fatima*