Page 14
*KAMPALA ESTATE*
NA
*BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6790e01cf524f8dc4eabb9dd
14.
A hankali ta janyo wayarta dake ringing akan bed side cike da kasala saboda baccin daya fara fuzgarta, shirin saka wayar silent take amma ganin Mjay ne ya sa ta fara kallon time taga 8:45 pm wayar ta ɗaga ta kara a kunne haɗe da yin sallama acikin muryarta na bacci, amsa sallamarta ya yi kafin ya ce
"Subhanallahi Barrister har kin kwanta afuwan don Allah." A hankali tace
"Noo ba komai Barka da wannan lokaci."
"Yauwa ya yau, dama nace zan kira in miki godiya ne Allah ya saka da alkhairi."
"Ameen." Ta bashi amsa a takaice, ganin ya yi shiru ya sanya ta ce
"Amm kayi haƙuri Please Yaya Mjay is not right kana kirana at this time of the night i am a married woman remember, idan abu me muhimmanci ne just send a text i will call back if it's ok with me a lokacin ko na maka reply na message naka." Kunya ce ta wani irin lulluɓeshi cikin jin haushin kansa ya fara bata haƙuri
"Don Allah kiyi haƙuri Barrister na gode da kika fahimtar dani in shaa Allah zan kiyaye." Ɗan murmusawa ta yi kafin ta ce
"Ba komai fa kawai na maka tuni ne kasan ku maza yanda kuke, am gobe kifin gasawa zanyi ko pepper soup?" Cikin sanyin jiki ya ce
"Anya ban baki wahala ba Barrister ai inaga kawai ki bari wani lokaci." A hankali tace
"Noo Please ba haka zamuyi ba, kaga kullum inada abinci a freezer basa komai musamman stews da soup's so da ace kana siya ai ko driver ne zai iya zuwa ɗaukar maka ko a gida ko a office please Yayana don't say no kaji." Ta ƙarashe maganar da shagwabar da bata ma san tana yi ba nan da nan kuwa ya shiga wani yanayin a take ya soma ƙoƙarin yi mata sallama yana godiya kamar daga sama yaji an daki wani abu a cikin wayar ƙara matsa wayar ya yi a kunnensa
"Lafiya kuwa? Hello? Amrah , ita kuwa a gefebta tsabar firgice ta cillar da wayarta a gefe ta mike zaune tana ma Aminullah wani kallo na tuhuma,
"Ke wai me kike tunani ne? Ajiyeni kika yi da zaki riƙa fita sanda kika ga dama ki dawo sanda kika ga dama?" Dama amra ba dai rashin haƙuri ba cikin jin zafin sa tace
"Aminullah wai nikam kanada wani damuwa da ni ne? Ina ruwanka da rayuwata these days da kake ta takuramin? Ban fahimci ina fita in dawo sanda naga dama ba na taba wuce 6 ban dawo ba komai tulin aikin dake kaina?." Saukar wani lafiyayyen mari taji daya saka ta ƙwalla ƙara ta dafe wurin fashewa ta yi da kuka me ciwo
"Me na maka ne kake so kaga bayana Aminullah? Bayan baka sona ba ka ƙaunata baka son zuwa inda nike yanzu kuma hatta kwanciyar hankalina baka so? Me na maka a rayuwa ni Amratu?" Cikin hasala ya sake kai mata duka a baya yana haurawa akan gadon da kyau ya shaƙo mata wuya
"Don ubanki bokaye kike bi ko? Kin gado uwarki data asircemun mahaifiyata sai yanda ta yi da ita kina bibiyar bokaye ko? Nasan komai kuma wallahi ba zakici riba ba akan haka zan hallakar da ke da tasirin samuwarki." Cikin jin azabar ya mata yawa ta ce
"Aminullah you are hurting me let go of me." Tureta ya yi kanta yaje ya daki kan gadon ta dan ƙwalla siririyar ƙara ya miƙe yana mata mugun kallo
"Na riga naji abubhwan da kike gayawa mutane cewar ke bakya tsoro na, wallahi Amrah sai na yi sanadin da duniyar nan zata dawo miki baka ƙirin ba dai bakida aiki se zuwa kina cewar kinfi ƙarfin abin hannuna ba bakya relying da abina kar in rainaki har kina zuwa kina fallasa cewar bana miki cefane in miki cefane ni na auroki ina cewa mahaifiyar tawa data auroki tana miki cefanen 'yar iskar banza sakarya." Cikin jin zafin wannan cin kashi Amrah ta miƙe tsaye
"Wallahi kayi kaɗan kazo nan ka riƙa dukana a banza tunda ba jakar gidan ku bace ni, me na maka? Haka kawai cin zali? Na sha gaya maka wallahi kotu zan maka ka." Wata iriyar mahauciyar dariya ta kwashe da ita irin ta rainin hankalinnan sannan ya ce
"Kije ki kaini kotun mana kiga next idan zaki ƙara auruwa ko moruwa a wurin wani kuma wallahi da idan a shirya miki wani gagarumin makircin se kin firgice, sai na sa duka duniya ta tsaneki mark my words." Fashewa ta yi da kuka
"Aminullah don girman zatin Allah ka fita a harkata, ka daina shigamun rayuwa zaman da muke ada yafiyemun kwanciyar hankali, menene tsakaninka da Raheemah da zata rika zama tana shirya maka karya akaina kana ɗauka? Wallahi ni duk abin da take gaya maka karya take mun amma kome zance nasan ba zaka yadda ba, ni ban taba gayawa kowa cewra baka ɗaukar nauyina ko so ɗaya ba kawai nasan nacene bana kwanto da abinka shikenan." Tsaki yaja
"Can kyaji dashi 'yar wahala a wahale zaki kare in gaya miki wallahi i will makesure i make life miserable hell for you idiot." Cikin rashin kunya
"Kaje Allah ya fika mugu azzalumi." Ko kallonta be ƙara yi ba ya wuce abinsa anan ta duƙa taci gaba da rera kuka tana neman mafita a wurin Allah with a sad tune. Majid da mamaki ya zare wayar a kunnensa bakinsa a sake sai ƙoƙarin yake ya yi assimilating dukkan maganganun da yaji suna faɗa a kunnensa! Cikin lumshe ido da buɗewa ya ce "Haxbunallah wa ni'imal wakeel." Kasa aikata komai ya yi yaci gaba da mata addu'a don ya ma kasa tunani straight shikam.
**************
Washe gari da fuska a kumbure ta farka but hakan be hanata yin hidiman gabanta ba ko da yashigo kitchen ma ta gaidashi be amsa mata ba yau ya dafa Indomie abinsa ya fice ya barta tana faman yin pepper fish ɗinta da sea food fried rice da kunun aya, ta haɗa a kwando biyu nata da nashi saboda yau bata so ma su haɗu bataji zata iya amsa masa tambayoyin da take da tabbacin yaji komai, can ƙasan zuciyarta kuwa wani irin raɗaɗi da zugi yake da sababbin halayen da Aminullah ya ƙirƙiro yake nuna mata wanda ada ita dashi sai su shafe watanni uku idan ba ta gayar dashi ya amsa ba ba ruwanta da shigarsa da fitarsa shima kuma haka. A farfajiyar ma'aikatarsa ta yi parking ta shiga kiran wayarsa ringing biyu ya ɗaga suka gaisa ta ce ya aiko masinjansa ya karɓa masa lunch ɗin zata wuce office yau akwai abin da zatayi after 2days dai zata shigo suci gaba da bincike, to ya ce ya ajiye wayar, da kansa ya taho ya zago wurin me zaman banza ya buɗe ya zauna ta ɗauke kanta daga dubansa gana jan mayafin abayarta duk da ta ɗaura face mask a wurin bakinta har hanci, ɗan ƙureta da ido ya yi na few seconds kafin ya sauke wani nannauyan ajiyan zuciya ya ce
"Barrister?" Ba tare da ta juyo ba ta ce
"Sir barka da wannan lokacin, ina sauri ne sir shiyasa ban shigo ba zuwa jibi zan zo." Girgiza kansa ya yi cike da tausayinta duk gefen idonta ya yi ja ya kuma kumbura a hankali ya ce
"Barrister are you really going to hide it away from me bayan kinsan cewar naji komai? I have alot of questions to ask and kinsa i most be very curious about it shine zaki ɓullo ta wannan hanyar, i heard him hitting you, he hit you more than 3times and i don't understand yanda maganar ki ke haɗashi da Raheemah why is she doing that to you ke kuma meye na gayawa ƙawaye duka maganganun da naji?" Shiru ta ɗanyi a wani lokaci kafin cikin jan numfashi da saukewa ta ce
"Yaya Majid kayi haƙuri but i really don't want to talk about it gaskiya." Sauke nannauyar ajiyar zuciya ya yi cikin sigar rarrashi ya ce
"You just have to trust me on this coz i cant have him beating you always kamar wata jaka da iliminki da komai sai kace ya auro akuya ? No matter what kome kika masa hakan kuskurene and ke kinfini sanin wannan domestic violence haramun a addinnance da kuma tsarin ƙasa." Hawayen da suka zubo mata ta saka hanky ta ɗauke cikin son ta nuna dakewa ta kalle sa ido cikin ido kafin a hankali ta ce
"My mother chooses this path for me and i believe its the best, i trust her and i believe in her, if this is the leaving hell she chooses for me so be it amma nasan idan har watarana Aminullah be kasheni da duka ba baƙin cikinsa ne zai yi ajalina, hala da badan ta hanani kai shi ƙara kotu ba ya isa ya kai wannan lokacin yana cin dunduniyata?, duk wannan wahalar da nike sha ina shansa ne akan biyan bashin halacci! Shin halaccinne ni ya zame mini cuta??? Kokuma mu bamuda wani haƙƙinda ya kamata iyaye su duba kafin su yi biyan bashin halacci da mu wallahi wallahi na gaji duniyar ta isheni so nike in mutu ma in huta." Ta ƙarashe maganar cikin tsananin gunjin kuka me tsananin tsuma zuciyar me saurarenta, ta kai hannunta ta janye face mask ɗin fuskarta ta ce "This is not the first time but the second da Aminullah yake duka na, ina masa shiru ne saboda mahaifiyata, ban damu da yanda yake wofintar da haƙƙoƙin aurensa a kaina ba, ban damu da rashin ciyar dani dayake ba ban damu da rashin suturtani da yake ba, ban damu da rashin sauke dukkan nauyi dake kansa da yake ba ban kuma damu ba da yake shafe wata uku banda gaisuwa ta ba abin da yake amasawa ba shima da ƙyar ban kuma damu ba da baya cin abincina ban taɓa damuwa ba don yana kallon tsakiyar ido na yana gayamun cewar he hates me ba yace i am not his type ya ce na masa gajarta ban taɓa damuwa ba, the only thing da ya dameni shine duka na da yake zuciyata tana gayamun akan wannan dukan zan iya saɓawa umarnin mahaifiyata wanda dama shi nike tattali." Majid duk ya rasa me ma zai ce daga nan ya shiga ban baki da nasiha da wa'azi tare da janyo ayoyin da ga sani har ya samu hankalinta ya ɗan dawo jikinta suka haura saman a tare ya kira clinic suka zo aka duba idon ta da azabar mari ya sanya jini ya kwanta aka kuma duba mata bakinta da ya fashe kaɗan suka bata magunguna tunba na wurin wuyanta da shatin hannunsa da shaƙar daya mata ya nuna ɓaro baro sannan aka bata magunguna suka sake tattauna akan matsaloli daban daban in no time wata irin muguwar shaƙuwa ya shiga tsakaninsu me ban mamaki.
Yau bayan an watse a majalisa Meenah ta kimtsa sosai tabi bayan Raheemah ta shigo gidan tana wani rangwaɗa ta ɗauke kanta daga duban mijinta tana yauƙi ta wuce ɗakinta a zuwan zata je wanka, shi dai bece mata komai ba saboda inda sabo ai ya sana da wannan halayyar nata na banza, tana haura da mintuna kaɗan Meenah ta yi knocking house help ɗin gidance ta buɗe ta gaishe ta take gaya mata cewar ai anty ata ta shiga wanka a sama., tana wani ɗan iskan lanƙwasa ta kutso kai a cikin gidan tana cewa zata jirata me aikin tayi ƙokarin janta zuwa ƙaramin parlour ganin ogan a zaune amma kuma sai ta ki bin bayan me aikin taci gaba da abin da take a tsaye dole ta haura ta barta a wurin, cikin kisisina da yaudara ta ce
"Ina wuni Mjay." Mjay da se yanxu ma ya kalleta ya amsa da "Yauwa sannu." Tana wani karairaya ta ce
"Don Allah yallaɓai ko zaka taimaka ka bani aron wayarka zan kira megidana ya tahomun da saƙo da nawa wayar na kasa samunsa." Ba tare da ya kalleta ba ya nuna table inda wayarsa ke kai ta matsa ta ɗauka tana wani shu'umin murmushi kafin tace
"Na gode." Anan ta zuba number wayarta ta kira kanta yana shigowa ta kashe ta ajiye masa wayarsa tana cewa "Gashi ma yana kirana na gode." Bece komai ba ta juya ya taɓe baki a duk cikin kwashe kwashen Raheemh shi yafi tsanar wannan abar me kamada agwagi se rawar kan masifa... A ɓangarenta kuwa ranta fess tayi number Mjay tasha alwashin samun sa ko ta halin yaya....
*KAMAPLA ESTATE 2025*
*BILKISU GALADANCHI*
***