KAMPALA ESTATE

Page 15

by @68billygaladanchi

*KAMPALA ESTATE*

                NA

*BILKISU GALADANCHI*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
   
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6790e01cf524f8dc4eabb9dd

     15.

Tun daga wannan ranar Aminullah ya ɗaura ɗamarar takurawa Amrah ita kuwa bakinta ne baya mutuwa har ta zo ma ta fara shakkar sa tana tunanin ko ya fara shaye shaye? Ga wasu irin maganganun ban mamaki da take samu a bakinsa da suka shafeta da take da tabbacin duk sharrin Raheemah ne, duk kuwa iyakar haƙurinta da kawar da kai sai da ta fahimci wani abu duk da bata kaurara zancenta ba amma tana tsamanin hala Raheemah so take tasan mijinta saboda tace bazata taɓa sanin sa ba ba damuwarta bane duk yanda zata zama close da shi kanta tayiwa. Yau ma kamar kowace Safiya yanda ta ɗaukarwa kanta haka tayi amma amaimakon kofi sai ta ce bara ta masa pepper chicken da party jollof rice se kuma russian salad daya sha pineapple ta haɗa masa Juice ɗin tamarind da yasha haɗin pineapple da ginger da mint da kuma lemon grass da lemon zest kaɗan, ta caramalizing sugar sannan ta saka a ciki, she is doing everything with so much excitement rasa dalilin jin daɗin ta take akan hidimar Mjay, duk da cewar bata wuce 9 bata je office ba amma yanzu se 10 take zuwa saboda aikinsa da bi office ta ajiye masa lunch. Yau koda ta iso office ɗin nasa bata mai waya ba kamar kullum ganin ma'aikatansa na kallonsa duk sanda ta zo da kansa ya ke sakkowa koda ta ce ya turo mata masinjan sa ya sa da kanta ta haura saman don kai masa abinci, a bakin ƙofar office ɗin ta tsaya ta yi knocking sakatariyar ta bata izinin shiga ta turo ƙofar ta shigo sannan ta ɗago kai ta kalli sakatariyar matar me kirki da lulluɓi ma a kanta ta taso tazo tana gayar da ita tare da ƙoƙarin karɓar luxury baskt dake hannunta samun kanta ta yi da kasa bata ta ɗan ja basket ɗin baya tana mata murmushi ta ce

"Noo ki barmun shi kawai Yayana fa?" A hankali ta ce

"Yana ciki ki zauna bara in masa magana." Zama ta yi a kujerun dake nan haɗaɗɗen wurin wato ko Mjay is way too classy and unique office ɗin san nan ya haɗu over, ɗan murmushi ta yi tana ci gaba da samun daman ƙarewa wurin kallo har zuwa sanda matar ta dawo ta mata iso har ciki sannan ta juyo, Mjay yana ganinta kuwa ya miƙe daga zaunen da yake yana mata murmushi

"Our Barrister da kanki? Ya baki kirani nazo na karɓa ba?" Murmushi ta sakar masa

"Ina kwana yayanmu, ya aiki?" Zagowa ya yi ya karɓi basket ɗin ya ɗaura akan table yana mata murmushi 

"Lfy lau ya aiki, Barrister hidimar nan bata yi yawa ba? To nasan ma cewa zakiyi bata yi ba amma to ki bari duk bayan kwana biyu." Ɗan kallonsa ta yi ta ɗauke kanta

"Kayi haƙuri bazan iya ba." Kallon mamaki ya mata sai kuma ya sakar mata murmushi ya zauna da hannu ya nuna mata kujera ta zauna itama kafin a nutse yace 

"Look My little Barrister kinsan ke matar aure ce, kuma zuwanki anan kowane lokaci ze iya kawo maganganu da zai ita taɓa mutuncinki da aurenki koda mu a wurinmu ba haka bane, i understand your pure intention and i truly appreciate your efforts but bana so a sanadina wani mutuncinki ya sosu so try to understand me let it not be always kinji." Rau rau ta yi da ido tana kallonsa sai kuma hawaye shar abin har yaso ya bashi mamaki ya kafe ta da ido, sai kuma cikin sigar rarrashi ya ce

"Look Amrah ba wani abu nike nufi ba, i am so sorry idan na faɗi wata magana mara daɗi ki fahimceni Please." Ya ƙarashe maganar yana miƙa mata tissue daya zara a wurin ta karɓa ta shiga share hawayen idon ta a hankali ta ce

"Ni ba komai kawai ni to idan ban kawo maka abincin ba se dai ka ta siyen unhygienic food da bakada tabbacin tsaftar sa, ni to bana son haka suyita maganar amma bazan daina kawo abincinba ai idan kana bin ta mutane ba abin da zaka yi ko da ma bakayi ba zasu yi ta yi da kai." Sauke wani gauron numfashi me tafe da hucin zafi ya yi yana son yarinyar nan ta fahimceshi is for her own good shi ya sani

"Look Barrister na san da hakan but kinsan ba kyau ka bawa mutane daman kafa wata hujjar akan ka? Idan ma zasuyi surutun to ka tabbatar duk wanda aka tustiye acikin mutanen bashida hujja kin gane? Naji zaki dafamun abinci kuma ai bazan iya rayuwa banci abincin ki ba amma ki daina zuwa da kanki." Da sauri ta kalleshi ya sakar mata murmushi

"Yea ki daina zuwa da zaran kin isa office naki i will send Samuel ya karɓo senya tafi miki da kayan da kika taho dashi yau is that ok?" Wani uncontrolled hawaye ta sake sharewa tana turo masa baki 

"To idan banzo ba that means bazan ƙara ganinka ba?" Shiru duk suka yi ya kafeta da ido baya ko ƙiftawa kafin a hankali ya ce

"Amratu ki yi haƙuri, zaki ganni mana, duk bayan kwana biyu i will visit your work place mu gaisa, na san dai kin saba ganin client ko yaushe wani client ɗin ma se ki shafe shekara kullum yana hanyar office ɗin kinga ba wanda ze mana mummunan fahimta after all we have business to takecare of together please ki fahimceni." A hankali ta gyaɗa masa kai cikin sigar wasa ya janyo basket ɗin yana dubawa

"My Barrister, a Chef and more me kika kawomun yau." Murmushi ta sakar mai tana goge fuskarta ya buɗe warmers ɗin yana dubawa yana murmushi godiya ya mata bayan ya rufe komai sannan ya ce

"And zan bada tukuicin wannan girkin." Girgiza masa kanta ta yi 

"Ni bana son komai just promise me cewar zaka zo office ɗin after 2days as promise" yana jinjina mata kai ya ce "Sure no matter how tight my schedules are zan zo." Miƙewa ta yi tana cewa 

"To na gode ni zan tafi." Cikin sigar rarrashi da kamewa ya ce

"Barrister please do me a favour by sending your account details." Wani ware idon ta tayi da mamakinsa

"Akan me to?" Gyaran murya ya yi yana lumshe mata ƙananun idon baccinsa "Ba komai ba wnai na raina iyawarki bane but time ya yi da zamuyi restocking food stuffs mu yi fueling motoci and mu saka kati a waya." Murmushi ta yi har sai da duka side of her chicks suka lotse sannan ta ce

"Ka huta kawai yayanmu but i can takecare of duk abubuwan daka lissafa, i have been doing it alone fa shekara da shekaru." Ɗan bata fuska ya yi

"Me kike nufi to? Ko da ace tun da kika zo duniya kike ɗawainiya da kanki ni a matsayina na yayanki i will take care of you and settle your bill's so my sister bana son musu send your aza asap" ya ƙarashe maganar ba wasa a fuskarsa, murmushin dai ta yi tace

"To in shaa Allah." Yana shirin masa sallama wayarsa ta shiga ruri ya janyo wayar yana kallon screen mamaki ya isheshi yanda wannan matar ta addabeshi da kira, ɗaga wayar ya yi ya kara a kunnensa bayan ya yi sallam, aka gayar dashi ya amsa sannan ta ce

"Mjay ni ɗince dai daka yi blocking da wancen layin don Allah ka tsaya ka saurareni." Shiru ya yi yana jinta ganin be kashe ba ya sanya ta ce

"Don Allah ka taimakeni yanda Allah ya taimakeka ka bani lokaci mu fahimci juna ni da kai, ni sonka kawai nike ka agajeni ko da so ɗaya ne ka ragemun raɗaɗin da nike ji." Cikin jan gajeran tsaki ya ce

"Wai ke wace irin cheap prostitute ce! Ban gaya miki ki daina damuna, i am not like any other men da kika sani, i have my wife and she is enough for me i don't need to mingle with cheap en iska irin ki, duniya ta lalace mata ba kamun kai wallahi kika bari na kama ki sai na kaiki police station for disturbing my life." Magiya ta hau yi ya katse wayar yanata masifa Amrah dai ta tsaya tana kallonsa sai can da taga ya fusata sai hawa yake ta ce

"Yaya ka yi haƙuri wacece kuma menene matsalar?" Cikin faɗan ya ce

"Can you imagine yanzu mata akan kuɗi kome zasu iya yi koda yake ni wannan ban ganewa kanta bama ba kudin take so ba shaƙiyanci ne kawai da izgilanci, in banda samun wurin kin samu number na kina mun magiya in sameki a hotel i blocked her 3 different numbers she still manages to change number ta kirani." Sauke nannauyan ajiyan zuciya ta yi sannan ta ce "To kar ka sakawa kanka damuwa fa azo kanka yana ciwo bani number i will makesure bazata ƙara kiranka ba " fara karanta mata number ya yi amma tun first 6 digit jikinsa ya bala'in sanyi ta tsaya mamakance tana kallonsa da ƙyar ta gama zube numbers ɗin ta dialling number suna yana fitowa, da sauri ta ce "Subhanallahi ta shige ɓoye wayarta binta da kallo ya yi don yaga sunan MEENAH KAMPALA MINI GATE, cikin mamaki ya ce

"Is that number not save on your phone already? I can see it's saved lemme see." Ɓoye wayar ta ƙarayi hakan ya jefa zuciyarsa a cikin shakku cikin dakiya ya ce

"Barrister mana ina magana sunan waye." Tana ɓoye kanta tace

"Its Amina from our estate mamaki kawai nake shiyasa." Taɓe baki ya yi sannan ya zauna akan kujerar sa

"Allah ya kyauta." Kawai ya faɗa ita kuma ta juya ta fita jikinta ba ƙwari.

**************
 *Bayan kwana uku*

Ƙaramar zarewa Amrah ta yi acikin kwanakin nan uku na rashin ganin Mjay be zo ba bashida lokacin kiran waya ita kuma se dai message ta kara kiransa yakanyi reply ma messages ɗin ta but be taɓa kiranta ba, abubuwan daya hango game dashi a tattare da ita suna da yawa gwara shi namiji ne ita kuma fa mace? Rauni ne da ita duk da taƙi tura masa acc details ya bata driver sa kuɗin ranar aka kai mata har 500k kuwa kuma ta karɓa ta masa godiya. Yanata duba lamarin maganarta shin meyasa take roƙon ganinsa? Gwara kawai kada ta gansan yafiye masa Alkhairi. Yau cikin kasa haƙuri Amina ta kirasa yana zaune a office shi kaɗai yana wasu ayyukan jan wayar ya yi ya daga kiran da sallama suka gaisa kowa ya yi shiru, se can ta ce

"Yaya You broke your promise." Kawia sai ta fashe masa da kuka, a cikin kukan take cewa 

"I want to see you yaya mjay i am missing you wallahi, Please idan bazaka zo ba ni zanzo." Da sauri ya ce

"Noo Please ba sai kinzo ba zanzo yanzu kuma meye na kuka?." Tana daɗa jan shesheka ta ce

"Ai kaine ka hanani zuwa maka kuma kaƙi kazo ka ganni." Da sauri ya ce

"To ya isa by 12 zan shigo Shikenan?" Kamar yana wurin ta gyaɗa masa kanta, tana cewa "To." Ya shiga ban baki har ta haƙura ta sakko suka yi sallama hular kansa ya cire ya ajiye cikeda mamaki, hankalin sa ya masifar tashi anan da yake cikin damuwa ya cura kansa a ɗan sumar kansa kaɗan kafin a sarari ya futa

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un me yake damun mu? Me yake shirin faruwa da mu ne? Kaddai duk abin da nake ji yarinyar nan haka take jinsa wanann wane irin mummunan ƙaddara ce ke bibiyar mu?" Ya ƙarashe maganar yana ambatar "astagfirullah wa atubu ilah...

*KAMPALA ESTATE 2025
*BILKISU GALADANCHI*
***
REGULAR 500
VIP 1K
VIA 8039424298
OPAY BALKISU MUSA.