KAMPALA ESTATE

Page 16

by @68billygaladanchi

*KAMPALA ESTATE*

               NA

*BILKISU GALADANCHI*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

 
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6790e01cf524f8dc4eabb9dd

    16

Mjay hannayensa ya mayar a bayansa ya soma zagayen office ɗinsa cikeda dumuwa, yana nazarin ta ina zai ɓullowa wannan gagarumar matsalar dake tinkarar sa, yana ɗaukar abin da sauƙine ganin kamar kome yake ji game da Amrah zai iya haɗiyewa har abada bazata taba ganewa ba, ko da wasa beyi tunanin shaƙuwar da suka yi ze kaita ga fara nuna masa zallan so haka ba, ya sani she is a very calm woman don ya san da hakan ya kula da kamewarta se dai mata ababene masu rauni sosai tunda shi yakan ɓoye abin da ya je ji akanta amma natan yana nunawa har yana fargabar ita ko wani su fahimta don idan ta fahimci inda zuciyarta ke janta akwai damuwa, hanyar da zai ɓullowa hana afkuwar mummunan al'amari ya fara tunani don shikam komai lalacewar sa bazai taɓa neman matar aure ba koda kuwa ace sa soyayyar fatar baki ne ya san is not good... Ganin 12:pm ɗin ta riske sa ya tilasta masa barin wannan tunanin ya bar kampanin shi da driver sa suka nufi Chamber ɗin ta.

  Har office ɗinta sakatariyar ta ta raka sa sannan ta basu anan suka ɗan gaisa cikin damuwa ya ce

"Rigimar ya ƙare tunda na zo ko? Gaskiya Barrister ni da ke bazamu shirya ba idan kika ce haka zaki ta yi." Sauke kanta ta yi a kasa tana fidgeting yatsun hannunta a hankali ta ce

"I just need someone to talk to kuma kaine nake da a kusa, kayi haƙuri ina damunka." Madubin idon sa ya zare yana sauke mumfashi me huci a hankali ya ce

"Menene matsalar ki? Wani abu yana damunki ne?" Tana kallonsa cikin ido ta ce

"Yaa Mjay i want to leave lagos, i want to go back to kano duk sanda shi Aminullah yake so ya gaisa da iyalinsa ya nemeni ya ganni na gayawa mamana ta rufeni da faɗa na gayawa mahaifiyarshi tunda yayar mamana ce itama ta kasa fahimtata tace zan bar mata yaro anan ba mata, na gayawa Daddy ya ce ba ruwanshi bashida iko akaina, zama zanyi anan Aminullah ya kasheni wallahi wallahi na gaji, ni bance zan kashe auren ba don nasan se dai a fitar da gawata agidan muddin mahafiyarsa da tawa suna raye, a kanon ma zan iya aiki ai ko ko anan ɗinma zaman kaina nike niba lauyar gwamnati bace." Duk maganar da take kallon ta kawai yake har takai aya wani irin tausayinta ya mamaye sa musamman ganin yanda take ta ƙoƙarin hanawa kanta amma muryarta se rawa yake, a hankali ya ce

"Shawarata kike nema Amrah?" Cikin sanyi ta gyaɗa masa kanta ya ce

"To ki zauna a kusa da mijinki, baki da wata hujjar barinsa shi kaɗai kome ya aikata a dalilin hakan laifi dai yana wurinki har a wurin Allah." Tana ta ƙokarin danne kukan ta ce

"Ni ban taɓa zama mace ba a wurin Aminullah, baya kwanciya wuri ɗaya dani, baya cin abincina, baya zama inda nike, baya hira dani, baya ciyar dani, baya tufatar dani, baya mun sutura, bakuma ya damuwa da shige da fice na to me zan hanashi idan ma na zauna? Jiya da mace ya kwana a gidan kenan zamana a lagos bazai hanashi aikata komai ba har abada saboda haka da in zauna zuciyata ta farke ƙirjina ta fito gwara in tafi kanon kawai." Rasa ya yi abinda zai ce mata kawia ya kafeta da ido na wuccin gadi a hankali kuma sai ya fara magana

"Amratu i believe you so much have trust in me, kin aminta dani kin kuma ɗaukeni a matsayin yayanki idan haka ne tambaya uku nake so na miki kuma ki bani amsa kai tsaye." Jinjina masa kai tayi yanzu kam tana ɗauke hawayen idon ta da yatar hannunta kamar baya son magana ya ce

"Is he starving sensually?" Ɗago ido ta yi suka kalli juna sai kuma ta kawar da kai a nutse ta ce "A." Shiru ya ɗanyi kafin ya kuma cewa

"Are You sure you want to continue with this thing call marriage?" Bayan hannunta ta sanya ta sake share hawayen idon ta kafin a hankali ta ce

"No matter how i hated this marriage there is nothing i can do about it saboda mahaifiyata, amma wallahi wallahi da za'a bani dama da kuma ace mace na saki da da kaina zan saki Aminullah." Jinjina kansa ya yi ya sake cewa

"Tambayana na ƙarshe, ya akayi kuka yi aure?" Hannunta ta miƙa ta zari tissue ta share fuskarta sannan a hankali ta ce

"Mahaifiyata da mahaifiyar Aminulla su biyo rak iyayensu suka haifa, kuma sai ya zamana iyayen nasu en boko ne sosai tun a wancen lokaci, mahaifiyar Aminullah ta sshafe shekarun haihuwa 14 kafin aka haifi mahaifiyata wacce tamada shekaru 3 a duniya mahafansu suka yi accident suka rasu atake. Hakan ne ya yi sanadiyar lalacewar komai kasamcewar ɗan abin da mahaifinsu ya bari dangi sun masa caaa a wancen lokacin kuma ita Umma wato mahaifiyar Aminullah tana da shekaru 17 a duniya, a lokacin take aji na biyar a secondry. Saboda yanda ƙanwarta wato Momyna take ƙarama kuma aka rasa me ɗaukar su ya riƙe sai ya zamana karatun da take a makarantar kwana ya tsaya daga SS2 ɗin ta zauna zaman reno a cikin gidan mahaifinsu da shi kaɗai aka barsu da shi, duk da haka kawunsu a wancen lokacin kawu bala ya ɗakko matarsa ɗaya ta dawo gidan da zama amma fir taƙi ta kula da Momyna kuma kawun yana kallo bece komai ba, sai ya zamana Umma tana shan wahalar renon Momyna ga ƙuruciya samari sun taso mata da xancen aure amma se kawu ya ce reno take don haka sai tazonta rasa mashinshini har takai shekaru 22 a duniya a lokacin Momyna tana da shekaru 8, wanki da guga Umma keyi saboda makaranta da kulawa da komai da Momyna, har wata rana Allah ya kawo mahaifin Aminullah yazo ɗaukan gugan matarsa ya ce yaji ya gani kuma ze Momyna haka kawu na takaici ya aurar da Umma batare da ko tabarma ba sai abin da ta saya da kuɗin wahalarta, acikin kishiyoyi biyu taje auren don haka zaman gidan ma ba daɗi bane sai di yanda Alhaji Audi gero ke sonta ya sa dole suka sarara mata da kuma Momy data zamto mata 'ya, ta sha wahala kafin ta samu cikin Aminullah don har ta cire rai a lokacin ta cika burinta ta yi karatu har ta zama lauya babba itama Momyna ta zama budurwa, se a wannan lokacin ta samu cikin ban mamaki don kuwa kishyoyin can sunji haushi abin be ƙara basu haushi ba sai da ya zamto su duka yaransu mata ne ita namiji ta samu. Mahaifina kuwa yaron Alhaji audi gero ne mijin Umma, don zamu iya cewa matan Alhaji audi sun sha haushi da mijinsu be haɗa auren yaronsan da 'ya'yansu ba sai Momy na don haka tasha gori ita dai bata damu ba kuma tabi zaɓinsu ne saboda bata iya cewa Umma no don ita bata taɓa mata kallon yayarta ba kallon uwa take mata haka akayi auren har aka samu ƙaruwa ina da yayu maza biyu nice ta ukunsu, mahaifina yana da kuɗi sosai na gani na faɗa ma kuwa don ya samu sa'a a rayuwarsa shikam don haka koda aka haifeni ya daɗe da barin matsayin yaron wani.

Babban dalilin daya sanya aka auramun Aminullah saboda an gano yana soyayya da wata kuma ance shaye shayensu suke a tare, bayan wannan kuma mahaifiyarsa irin mutanen nan ce masu masifaf son 'ya'yansu ita kuma mahaifiyata aduk duniya gani take idan ta saɓawa Umma wuta zata shiga saboda kallon uwa take mata komu daga baya mukasan cewa yayarta ce ba uwarta ba, to a hakan dai a bana so bana so mahaifiyata bazata iya musu ba haka mahaifina shima ba zai iya musu ba don haka mu kuma bamu isa muce komai ba don dukkanin iyayen namu mata masu tsauri ne, bayan an ɗaura mana aure atare suka gaya mana tsinuwa zata tabbata agaremu idan muka warware wannan auren, duk da nasan cewar ni nake biyayya amma ko Aminullah biyayar yake don yasan halin mahaifiyarsa, ita ta san ɗanta shaye shaye yake, mazinaciine amma kullum gayamun take ni zan iya rufa masa asiri, ita tasan ɗanta baya sona amma ta dage akan in zauna, ita take turomin kuɗin cefane duk wta don tasan baya yi." Shiru ta ɗanyi sai kuma a hankali ta e

"Idan nayi magana mahaifiyata zata ce halaccin da umma ta mata arayuwa take ramawa, koda kasheni Aminullah ze yi lallai dole zan zauna inso duk wani abin da ya fito daga tsaston Umma, bana so inyi sanadiyar lalacewar zumuncinsu sam sam, atare na zo na gansu kuma nima nasan cewar Umma tayiwa Momyna halacci amma shin nice xan sadaukar da farin cikina inyi auren biyan bashin sakayya? Aminullah baya bani haƙƙina na aure, Aminullah ya nani haihuwa nayi nayi na gayawa Momy cewa take ze sakko ne daga baya Umma kuma taƙi yadda tace ƙafarta ya ɗakko ze sakko ne daga baya, se ya shafe shekara be nemeni ba idan na kai kaina ya zazzageni ya kushe halitta na, ya gayamun duk abin da ransa ya masa yaci mutuncina ya wulaƙantani, idan nayi magana ya dakeni, idan be kawo mace yau ba gobe xe kawo ko ya zauna yin video call na banza da 'yan mata, idan ma duk wannn be masa ba ze bar gidan ya kwana baya nan, shin haka ni rayuwata zata kare a tozarce ? Bazan ga ɗana ba kenan saboda Aminullah baya sona bazai iya haihuwa da ni ba ya kuke so nayi? Ya zan yi?.... Ta fashe da kuka har tana ɗaura kanta a saman desk ɗin taci kukanta yakai na 15mns don kanta ta yi shiru don bece mata komai ba, sai da ta yi shiru sannan ya ce

"Kiyi haƙuri Amrah in shaa Allah duk wannan ze zo ya wuce, abu ɗaya zan gaya miki fight for your right ko da Umman ce ta haifeta we do what's best for us abin da bazai cutar da mu ba, zaki iya faɗawa halaka with this sesual starvation alone, kada ki kuskura biyan bashin halacci ya sa ki manta cewar ke macece me rauni nan da nan zaki iya aikata abin da zaki dawo kina dana sani kuma bazai taɓa gyararuwa ba saboda haka ki ƙwaci 'yancin ki,ina tausaya miki saboda kindhearted heart da kike da please Amrah do something for your life, akwai hanyoyi da yawa na ƙwatar kanki a hannunsa bawai se ta fitina ba , you are well educated saboda haka ki san me zakiyi kinji." Gyaɗa masa kanta tayi ya zauna ya shafe 2hours yana aikin rarrashin ta kafin ya samu kanta gaba ɗaya....

**************

   Kamar yanda aka tsara tafiya haka Raheemah da Aminullah suka cira zuwa Dubai, shi Mjay yana kallon matarsa ta tafi business ita ma Amrah dataji labarin tafiyarsa a wurin mahaifiyarsa tana kallon cewar her husband is going for a business trip ta masa addu'a duk da be gaya mata ba sam don haka sun tafi yawon duniya abinsu.

*KAMPALA ESTATE*
*BILKISU GALADANCHI*
8039424298
OPAY
BALKISU MUSA 
REGULAR 500
VIP 1K.