Page 17
*KAMPALA ESTATE*
NA
*BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6790e01cf524f8dc4eabb9dd
17.
Mjay tunda yabar Amrah zuciyarsa take a cunkushe tunani yake hala wannan wane irin ƙazamin halacci ne da har ba'a iya ganin matsalar dake tattare da halaccin da kawar da kan? Yarinyar can is hurting so badly, shi kuma a ɓangarensa tausayinta ya ninku a ƙirjinsa yana ji kamar ya je ya shaƙe Aminullah ya fahimci cewar shi dabba ne, idan shi bazai tattali that rare gems da Allah ya bashi ba he will help him that very good care of her kai indai abune wanda bai saɓawa addini ba he promise to takecare of her akan wannan abin in shaa Allah, he will make her feel like she is also a woman.
After Isha Amrah tana zaune a parlor sama tana faman aikin da ta saba a system ɗinta wayarta ya yi ƙara, jan wayarta ta yi ganin Momy ya sa murmushi ya ɗan suɓuce mata saboda koma yayane ita tana so mahaifiyarta sosai, ɗaga kiran tayi ta kara a kunne haɗe da yin sallama, mahaifiyar tata ta amsa sallamarta da fara'a ɗauke a fuskarta ta gayar da ita ta amsa sannan a nutse Momy ta fara magana
"Amratu na kiraki ne kamar ko yaushe in ƙara baki haƙuri in miki nasiha akan rayuwar aure ki sani a duk duniya banida wadda nike so sama da ke, a duk cikin yaran da Allah ya bani kece mafi soyuwa agareni don haka wannan kaɗai ya isa ya gaya miki cewar baxan taɓa yi ko aikata wani abun da zai cutar dake ba, aurenki da Aminullah ƙaddara ce kuma na amince da haka ne saboda yanayin rashin lafiyar uwata Umma, kinsan umma tana faman da hawan jini me tsanani ga kuma ance zuciyarta ya kumbura, kin sani na baki labari game da rayuwarta tun tana da shekaru sha bakwai take fuskantar ƙalubale iri iri, ga na rashin aure da wuri surutun mutane kawai ya isheta tunda a yanzu masu 30yrs ma saisu kai ba auren ba komai ada ai abin magana ne, na biyu tazo tayi auren nan fitinar kishiyoyi da 'ya'yansu ga rashin haihuwa, na uku ta haifi yazo ya zama me kuɗi amma shaƙiyin yaro baya ji Aminullah sam, uwarsa batada wadda take ganin zata rufa mata asiri sama da ke, ki daure ina yawan miki addu'a kuma in shaa Allah ko don sanadin tsantsar biyayya da haƙurinki zaki ga riba Amratu, nasan wani zubin zaki ce Momy bata duba halin da nike ciki ba haka bane My Baby wallahi wallahi na fiki shiga damuwar yanayinki, na fiki shiga tashin hankali nafiso ko yaushe inji labarin kun fara samun fahimtar juna ke da Aminullah Amratu." Jin mahaifiyar ta yi shiru yasa a hankali ta ce
"In shaa Allah Momy zan iya ubangiji Allah ya amsa addu'ar ki nasan jinkirin Alkhairi ne don nasan addu'ar uwa akan yaranta batada hijabi, ki kwantar da hankalinki Momy koda ace yau Aminullah naman jikina yake ɗeba yana miya agidansa akan ki raina fansa ne zan zauna dashi in shaa Allah." Addu'a sosai mahaifiyarta ta tama sannan ta ce
"Yayunki sun baki kyauta me girman gaske Amratu, dukkansu kadarorine masu muhimmanci,.Daddynku kuma ya siya wasu shares a kampanin cement ɗinsu ki kwantar da hankalinki my Angel in shaa Allah zaki haifi yaran da zasuci rigar dukiyarki." Godiya sosai ta ke cewa zata kirasu ta musu godiya sannan ta zauna zaman kukan tausayin rayuwar ta ita kam.
**************
Kai tsaye sheraton hotel ya musu booking wani danƙareren ɗaki na alfarma, Raheeman sai rawar kai take kamar jikar ƙadangaru, nan da nan ta faɗa wanka duk wani turaren data karɓo a wurin uwar daba da kuma na wurin malam ismu sai da aka dangwala shi, mafi akasari kuwa na mallaka ne ance zata mallake zuciyar sa ya zamana baya ganin kowa sai ita, dukiyarsa take hari duk da acan ƙasan zuciyarta tana jin ai tama fi sonsa akan mijinta Majid! Yana zaune da laptop a gabansa akan wani table shi yana kujera ta iso kusa dashi tana wani rausayar da kai, ɗagowa ya yi ya kalle dressing ɗinta ba komai a jikinta sai wani abu fari sol very transparent ta masa wani ɗan iskan ɗauri ta tsakiya inbtwn breast ɗinta ilahirin jikinta a bayyane yake, tsayayyun dukiyar fulaninta dake shan gyara suna nan a tsaye ƙyam da ubansun niple da black areola daya zagaye su, lip's ɗin sa ya lasa yana mata wani shaƙiyin kallo, jan kujerarsa baya ya yi sannan ya rungumeta yana daga zaunen ya daura hannayensa akan mazaunanta yana matse su sai wani lumshe ido take tana jin daɗi shima haka.....
A wannan lokacin bayan komai ya kafa ba kalan alƙawarin jin daɗin duka duniya da bai mata ba ita kuwa acikin kissa take ƙara cusa masa tsanar matarsa a fakaice har tayi nasarar ƙara ingizashi akan barin yi wa Amrah kowace irin ɗawainiya tace da shi ai Amran tana da dukiya kyau ace yana karɓar kuɗi ma a hannunta tunda ita macece, shikuwa sakarai yace ba abin da zeyi da kuɗinta shi yanada kuɗi ko yanzu ya tafi ya kwanta har nan da shekaru ɗari bazai taɓa cinye abin da ya tara ba na dukiya nan dai suka lalace da aikata masha'a yana mata ɓarin kuɗi tana masa barin jikinta tunda ma ta iso Dubai ko so ɗaya bata buɗe wayarta ba ita kam, Mjay ya kikkirata baya samu don haka ya haƙura ya kira hotel da suke sauka idan sun tafi dubai suka ce basa bayarda information na customers ɗinsu don haka ya yi haƙuri a dole ya share don yasan daba lafiya ba da tuni yaji wani abu. Ita kuma Amrah kodama ta san idan ta kirasan a waya ba ɗagawa zeyi ba don haka ko a jikinta fatan alkhairi kawai ta yi masa don kuwa ta ɗaukarwa kanta alƙawarin cewar har abada ita da saka damuwar mutumin da bai damu da ita ma ba bare damuwarta a tata rayuwar abu na biyu kuma ba zai ƙara dukanta ba tana kallonsa, muddin yazo zai daketa zata nemi hanyar guduwa dama ba wurin da yake take kai ƙafarta ba don haka kowama ya ji da matsalar sa amma maganar haihuwa kam ta bashi shekaru 2 idan sunada rai muddin yaci gaba da maganar be shirya ba ita kam ko da sama da ƙasa zasu haɗe zata nemawa kanta mafita faƙat!
**************
*ZARAH*
*BAYAN WATA UKU*
Tun sasaafe dama ta shirya kanta sosai acikin shigar kamala da hijabinta har ƙasa da niƙabi sannan ta nemi barin gidanta zuwa makarantar da tun last 3MONTH ta fara zuwa, batada sukuni sam bata jin daɗin rayuwarta, ta sani wata rahamar Allah ce rabata da ganin Habib amma kuma mahaifiyarta fa da ta yi mata nisan kiwo? Kowane lokaci da wannan damuwar take kwana take tashi. Tayi nisa sosai a tunanin daya addabi zuciyarta, wani irin ƙarar dataji da dukan da aka yiwa gaban motarta shiya dawo da ita duniyar tunanin data lula ganin yanda wata motar ta daki motarta ita kuma gadan gadan ta nufi wata daf yasa kawai ta ɗaura hannu a kanta ta ƙwalla ƙara tare da ambaton Allah daga nan kuma ɗif! Bata ƙara sanin inda kanta yake ba, cincirindon al'umma suka taru akansu gaba motarta banda tashin hayaƙi ba abin da yake tako ina hayaƙi ke tashi abin ba kyawun gani, da ƙyar da rigima mutane suka raba jikin motarta da jikin daf data daka , Babban mutum me kamalar da agaban idon sa aka yi komai shida ɗansa ya janyo wayarsa a aljihu kai tsaye ya kira police mafi kusa dasu tare da kiran hukumar kula da tsaron tituna, anata diramar ciro yarinyar da duk hijabi da niƙabin jikinta ya nannaɗe ta amma an kasa sunyi cirko cirko a tsaye suna kallon ikon Allah ga alama kuma ba numfashi a tattare da ita sam! Isowan road safety da ƙasa da 15mns aka gama fito da ita wanda gaba ɗaya ta sandare bata numfashi duk da ba wani rauni a jikinta amma kamar ta yi jaraya a hannu da ƙafa, neman wayarta aka shiga yi amma tas ɓarayin wurin sun sace dole wannan bawan Allah ne ya ja ragamar kaita asibiti tare da police officers guda biyu don bayar da report!
A tsakanin wannan lokacin kuwa a abubuwan ban al'ajabi da dama sun faru, musamman wata irin shaƙuwa me ban tsoro dake shiga tsakanin Mjay da Amrah har ya kai matakin duk wani abu da zata yi sai ta gaya masa haka shima duk abin da zai yi sai ya gayawa Amrah, dukkansu suna mantawa sam da al'amarin mutanen dake aurensu don kuwa harga Allah kaso 80 na damuwar da Amrah ke ciki ya rasu akan Aminullah saboda batada wani tunani yanzu dukkan damuwarta Mjay ta yaye mata ita, hidima kuwa da biyama mata dukkanin buƙatu sai abin da yaci gaba, daidai da Man mota Mjay yake tura kuɗin saya duk sati tun tana ƙorafi har ma ta haƙura. Mjay ma baya damuwa sam da Raheemah yanzu hankalinsa kacokam yana kan Amrah yayinda Raheemah da kuma Aminullah suna can sun shagala da bautawa jikin juna har kamar abin ya zame musu addiction ta yanda basa ganewa komai sai junansu, wannan ya sanya bayan sun dawo daga waccen tafiyar yanzu ma basa nan satinsu 6 a ƙasar suka sake zuwa suka bar garin ita Raheemah har faɗa abin ya so ya zame musu da Mjay akan ya yada tayi business trip ne so 2 a shekara amma tana neman maidashi sakarai ta nuna masa cewar ba wanda ya isa ƴa hanata rawar gaban hantsi ya kira mahaifiyarta amma tabi bayan 'yarta shiyasa ya tattarata ya watsar can mata ita ta sani. Yauma dai kamar kullum Amrah tana tattara kayanta tana shirin barin office wayartá ya shiga ruri murmushi ta yi ta kalli agogon bangon dake manne acikin makeken office ɗin sannan ta kalli wayar don ta tabbatar Mjay ne, cikin zaƙuwa taja wayar ta ɗaga sannan ta kara a kunnenta ya mata sallama ta amsa mai ta gayar dashi sannan ya ce
"Amrah zanyi tafiya and it's an emergency I'm going to Abuja this evening zan kwana biyu kafin in dawo." Wani irin mutuwa jikinta ya yi da har sai da hakan ya nuna a yanayinta cikin rashin kuzari ta ce
"Yaya har kwana nawa zaka yi?" Yana ɗan murmushi ya ce
"Sati ɗaya zanyi Amrah it's very urgent abinda zanje nayi ɗin kuma bansan zasu nemeni a matsatsen lokaci haka ba da na gaya miki maganar tafiyar tun tuni ai." Kamar zata mai kuka tace
"Sati ɗaya Yaya, wallahi ya yi yawa don Allah ma rage yawan kwanakin to.' Dariya ya yi me sauti
"Kinganki ko Momy ta shagwaɓaki da yawa Amrah, banda haka yanzu don zan yi tafiya xakiyi kuka?" Kukan ta dan sake masa me sauti sannan cikin shagwaɓar dai tace
"To don Allah ni zan bika sai in sauka gidan ƙanwar Babana dama na kwana biyu banje mata ba kuma banida wasu ayyuka a nan, yayanmu don Allah karkace mun A a bafa yanda zan zauna a garinnan ni kaɗai." Shiru ya ɗan ratsa wayar yana sauraren surutun ta da mitar ta cikin shagwaɓa da saiɓi tare da sakalci, a zuciyarsa yana tunanin yanda hakan zata yiyu ko da ba komai a ransa ba shida nufin aikata mummunan abu da ita amma a kafice ma dai ba a musulunce ba tayaya shi zai yi tafiya da matar mutane? Kai ko da ma ace yau Amrah batada aure yaya zai ɗauketa su yi tafiya a tare? Yana tsakiyar wannan tunanin ta ce
"Yaya kayi shiru Allah nace fa." Yana sauke ajiyar zuciya ya ce
"Look Amrah abin da bazai yiyu ba kenan gaskiya saboda tayaya zan ɗauki matar wani haka kawai in bar gari da ita ke kinga hakan a al'adance ya miki? Bare aje ga maganra addininmu? Ehm ki sani zanso ace nayi tafiyar dake amma kada mu cika biyewa zuciyarmu saboda zuciya mugun nama ce muddin mutum ze biyewa zuciyarsa to babu shakka wata rana zata kai mutum ta barosa ne, think twice my sister yaya zamu aikata hakan? Nasan tunaninki yana baki zaki sauka agidan wata yar uwarki but still ba daidai bane Amrah nasan kinada ilimin addini daidai gwargwado Please Amrah be using and following your mind not your heart." A hankali ta ce
"To yaya amma ya zanyi?" Yana ɗan murmushi ya ce
"Zan dawo nan da 3days for you my sister, kiyi haƙuri zan riƙa kiranki kullum safe da yamma kuma da dare zan baki labari har sai kinyi bacci shikenan?" Kamar yana wurin ta gyaɗa masa kai ya sake yin murmushi
"Bazaki mun magana ba kuma." Tana turo baki ta ce
"Naji Allah ya kiyaye." Dariya me sauti ya yi
"Alright zanje gida na kintsa sai munyi magana." A haka suka yi sallama ta zauna a office ɗin jikinta a mace kasa zuwa gidan ta yi sai after an hour kafin ta bar office ɗin.
*KAMPALA ESTATE 2025*
*BILKISU GALADANCHI*
8039424298
OPAY
BALKISU MUSA
VIP 1K
REGULAR 500
***