KAMPALA ESTATE

Page 18

by @68billygaladanchi

*KAMPALA ESTATE*

                  NA

*BILKISU GALADANCHI*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

Arewabooks@ 
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6790e01cf524f8dc4eabb9dd

   18

Bayan Amrah ta idar da sallan isha a saman sallaya ta zauna tare da tallabe cin ɗinta da hannunta dake nan a dunƙule tana sauke wasu irin zafafan hawaye rayuwar ta gaba ɗaya a rikice take bataji daga sanda aka fara maganar aurenta da Aminullah kawo yanzu akwai ranar data yi kwanan farinciki ko da ko so ɗaya ne, cikin wani irin yanayi me fizga da tsananin damuwa, can ƙasar zuciyarta babbar damuwarta ba Aminullah bane tsananin so da begen Mjay shine biggest fear ɗinta, ba tun yanzu ba ta fahimci bata da wani burin daya wuce kasancewa tare da Mjay sheɗan yana taka rawar gani wurin hura mata wani yanayi game da shi, iyakar ƙoƙarinta kuwa tana yi wurin ganin cewar bata shiga hurumin Allah ba amma sam ta kasa yakice sa a ranta, duk wani abin da zata yi don kaucewa yin wani abu ko kashe tasirantuwar begensa a zuciyarta abun yaci tura, bacci, wanka, girki, office, kotu duk wani abu da zata yi Mjay yana maƙale a zuciyarta ɗoɗar ba wata gazawa, cikin lumshe ido da buɗewa ta furta har muryarta yana rawa "Yaa Rahman ka dubi maraicina, ya wahidul ƙahhar ya zuljalal wal ikram ka cire soyayyar wanin mijina araina, ka ciremun sha'awar sa ya Allah, idan yau na goma gareka ya Rahman bazan iya dubanka ba da wannan ɗinbin mugun aikin, yaa Allah ka ceceni." Kawai sai ta fashe da kuka me sauti a cikin kukan ta ɗaga dukkan hannayenta biyu a sama ta fara gayawa ubanhijin dukkan talikai matsalar ta

"Yaa Allah kaine kake fitar da rayayye acikin matacce ka fitar da matacce a cikin rayayye ya wahidul ƙahhar kai kaɗai kake da ikon cewa abu ya zamo kuma ya zamo anan take, yaa ubangiji wuta da ruwa, ya Ubangijin aljanai da mutane, ya Ubangiji iska da da tsirrai ya ubangiji dukkan komai ya Allah buwayi gagari misali ubangijina me Rahama ya Allah ka sanya hannu acikin sauyawar ƙaddarata daga mummuna zuwa mafi Alkhairi,.Allah ka zaremun soyayyar Majid a raina ya Rahman ka barshi a matsayin yayana da yake ganin kansa ya Allah." Ta shafe addu'ar tana nanata kalmar Allah ka amsa, Allah ka dubeni ka jiɓanci lamarina ya wahidul ƙahhar." Ta daɗe sosai tana kai kukanta a wurinsa kafin wuraren 10:30 ta tashi daga kan sallayar ta ɗauke sallayar ta tana ninkewa ta ajiye hasken wayarta ya tabbatar mata ko kira ko saƙo akwai abin da ya shigo yanzu a wayar tata, hannunta ta miƙa ta ɗauki wayar ta ajiye sallayar hannunta tana shirin duba messages da missed calls da ta gani call ɗin Mjay yana ƙara shigowa lumshe idon ta ta yi ta tsaya kalllon kiran har sai da ya yanke a hankali ta zare hijabin jikinta bayan ta ajiye wayar ta ninke ta ajiye ba tare data cire comfy gown dake jikinta ba ta kwanta tana jan wayarta ta kashe fitilar ɗakin kawai, duba message's ta yi daga wurin Mjay har kusan 13 msd calls 3 message's, messages ɗin ta shiga ta duba na farko

_My little sis inata faman kiran wayar nan ba'a ɗagamun ba na shiga damuwa don Allah kada kiyi mun fushi ƙanwata bazan samu nutsuwa ba kiyi haƙuri ki daga wayata muyi magana._

 wasu hawayen ne suka zubo mata wallahi she is so confuse bata san me zata yi tunani ba kwata kwata saboda arayuwa tunda take da Mjay bayan wannan kulawar ba wani abu daya taɓa nuna mata da zai bata damar fahimtar wani abu game da shi ko bisa suɓutar baki be taɓa yin wata maganar banza gareta ba, hannu ta saka ta ɗauke hawayen idonta ta duba message na biyu

_Amma ƙanwata ai nace kiyimun haƙuri saboda banzo da ke ba kike fushi? Ki daure kiyi haƙuri i promise to make it up to you in shaa Allah don Allah ki ɗaga wayarki._ 

Murmushi ta ɗanyi a duniya dama akwai wanda zai shiga damuwa idan yaga tana fushi is she that important?? Sai message na uku

_Idan kikaci gaba da share kira na bazan iya bacci ba don Allah ki ɗauki waya kiji._  

Kuka me sauti ta fashe dashi don wallahi banda wutar son sa babu wani abu dake ruruwa a cikin jikinta a yanzu, tana cikin tsantsar azabar so me zafi da shirin cutar da ita, gefe guda tsananin tsanar Aminullah da halin daya jefata a ciki, wataƙil da ace ranar da motarta ta tsaya ya bata kulawa da daga wurin Mjay bazai ƙara sakata a ido ba sai daga nesa da tuni tana kame a cikin rufin asirinta, wani haske wayar ya ɗauka ta sake fahimtar kira yake a ƙasan pillow kawai ta tura wayar ta shiga rera kuka, ita ba fushi take da shi ba kawai so take ta nesanta kanta dashi su rage shaƙuwar ko dama halan hakan zai saka ta samu sassaucin azababben son sa day a dafe mata numfashi! Bacci ne ɓarawo ya saceta wuraren 2:30 kuma asuba ta farka yanda ta saba tana idar da salla ta zauna sa wayarta a hannu tana azkhar a wayar kiransa ya fara shigowa, bata ɗaga ba har ya yanke kira kusan biyar ya mata bata ɗaga ba, har ta kammala ta shirya a ranar tun 8:am ta fita ta shirya zuwa office saboda tana tunanin aikin zai rage mata damuwar da take ciki, se dai me tunda Amrah ta shiga office ta kashe wayarta take kuka, tayi tayi ta raba kanta da tunanin Mjay ta kasa so take ta daina sonsa amma kamar abin ƙaruwa yake ta ko ina a jikinta, huda jijiyoyin jikinta yake yana shiga kafin ƙarfe biyu zazzafan zazzaɓi ya rufe ta da ƙyar ta daddafa tayi azahar anan ta kwanta akan doguwar sofa dake gefe guda acikin office ɗin jikinta banda rawa ba abin da yake wani zazzafan hucin zafi ke fita a jikinta me kashe jiki da ƙasƙantar da tsirin gaboɓi, sakatariyar ta ce ta shigo akan ta yi baƙi ganin halin da take ciki ya sanya ta ce

"Ranki ya daɗe ko asibiti zamu je ne naga kinsha paracetamol abin ba sauƙi." Ɗan yamutsa fuska ta yi jikinta ba ƙwari ta kalleta ta ce

"Noo ba sai kunje ba ze sauka da kanshi, help me to the room please." Da sauri ta tayata tashi zaune ta ɗan dafata zuwa cikin wani madaidaicin ɗaki dake ɗauke da gado da komai har da ƙaramin wardrobe da Ac, a kan gadon ta kwanta taja mata bargo ta fita nan da nan jikintan ya ƙara rufewa da zafi ita sanyi take ji amma jikinta zafi yake ɗauke baya buƙatar abubuwa masu nauyi a yanzu, ficewa sakatariyar ta yi kawai taje ta bawa baƙon haƙuri wanda Samuel ne direban Mjay take gaya mishi madam is seriously sick bazata iya fitowa ba ko a shiga wurinta ya yi haƙuri." Nan ya kira ogansa yake gaya masa aka bawa sakatariyar wayar anan yakejin tun safe yau ta fito ma amma batada lafiya, ai kwaia manager ya baro a Abuja shi ya nemi available flights bama business classs ya shigo na kowa da kowa wuraren 5:15 suka iso ya nemo uba ta ɗakkoshi zuwa office ɗin nata don har lokaci Samuel ya gaya masa tana cikin office don ba ind ayaje.

A rikice ya ƙaraso office ɗin nata inda ya tsaya a wurin sakatariyar ta ita ta shiga masa akan a masa iso sai dai a firgice ta dawo gana gaya mata cewar madam tana jijjiga a tare har Samuel ɗin suka rufa a ɗakin, Mjay kusan fitane kawai ransa beyi ba ganin tana datse harshenta yanda take jijjjga gadon ma abin tsoro ne, batare da ya tsaya wani tunani ba ya shiga ƙoƙarin buɗe bakinta yana cewa su kawo masa ruwan sanyi, Samuel ne ya cikin office ya buɗe fridge ya dakko taki ta buɗe bakin wanka mata ruwan kawai yayi ta ƙara zabura ta kuma buɗe baki ta so rufewa tana ƙara jijjjiga ya kama ya tura mata yatsarsa a baki ta taune yatsar da haƙoranta, nan da nan suka yita watsa mata ruwan sanyi har abin ya lafa kaɗan sannan ya cirata sama kawai sai mota, ma'aikatan wurin sai addu'ar samun sauƙi suke mata shi kuwa yatsarsa data tauna sai jini yake ita ma duk ta daddaste harshenta, haka suka isa asibitin wani abokinsa babba sosai aka karɓeta a cikin gaggawa.

Mjay banza zarya ba abin da yake har sai wuraren 10 na dare sannan ya samu ganin likita, anan suka zauna likitan ya ce

"Sannu sir i hope sunyi treating na wound din ka?" A hankali ya ce

"Yea ai bashida wani girma." Jinjija kai likitan ya yi sannan ya ce

"Zata ɗan kwana biyu anan, ta saka damuwar wani abu a rants shike damunta sosai ga kuma fever duk ta datse harshe saboda yanayin jijjiga data samu, zamu ɗan dubata yanzu dai she is conscious amma bacci take." Majya cikin damuw ya ce 

"Ba wata damuwar high bp dai ko zuciya ko?" Likitan yace

"Noo ba ko ɗaya 'yar damuwace ta haifar da ciwon kai me tsanani sai fever ya shiga ciki to matsalar zafin jiki ne ya mafa yawa da ace ta sha magunguna kafin zafin jikin bama zata yi jijjjiga ba, amma da zaran ta samu sauƙi lallai a bincika aji matslaar ta ta meye ce." Jinjina kansa ya yi alamar gamsuwa kafin ya masa godiya ya fita zuwa gidansa acan ya yi wanka ya fara tunanin neman hanyar da zaibi ya gayawa me aikinta don ba wayarta a hannunta ya zama rikice hakan ya sa kawai ya fito ya koma asibitin a ɗakin ya zauna bayan ya kwaso fresh milk da Youghurt ko da zata nemi abinci, akan chair sake ɗakin ya zauna yana kallonta yanda take sauke numfashi a wahale haka ya zauna anan bacci ya kwashe sa sai wuraren 3 kukanta ya tashe sa tana kiran Momy, da sauri yaje gareta yana mata sannu, ɗago jajayen idonta ta yi ta kallesa tana ganinsa wani sabon shagwaɓa ya taso mata ta ƙarawa kukanta sauti 

"Menene Amrah me yake damunki? Wani abu yana miki ciwo ne a kira Dr.." da hannu ta nuna masa bakinta 

"Yaya harshena ne yake mun zafi ina ji ya ƙara girma, don Allah me muke a nan? Ka kiramun Momy." Wayarsa ya duba sannan ya kalleta

"Calm down mana Amrah kinga bakida lafiya and nan ɗin asibiti ne ba gida ba, wayarki yana office bansan ya zanyi in kira momy ba, Please ki kwantar da hankalinki zuwa safiya zanje in ɗakko wayarki sai a kirata." Shiru ta yi tana ƙoƙarin tunano me ma ya faru amma ta kasa tunano sanda yazo tana so ta tambayesa yaushe ya dawo amma ta kasa babu bakin hakan.

Bayan kwana biyu a asibitin aka sallameta me aikinta ne da Mjay suke ɗawainiya da ita sosai har ta warke, Momy ma ba lafiya don haka bata samu zuwa ba sai kiran wayar Amrah da take tana jin ya jikinta kullum. Bayan an sallameta da kwana ɗaya ta fita office duk ta rame sosai, tana zaune a office Mjay ya shigo tayi mamakin ganinsa da kuma mamakin rashin shigowar sakatariyarta kafin shi, zama ya yi ta gayar dashi ya amsa sannan a nutse ya ce

"Me yasa baki bari kin ƙarasa warwarewa ba tukunna ki fito aikin?" Kallonsa ta yi ta kafe idonnta akan sa kafin ta ce

"Menene amfanin zaman to? Damuwa kawai zemun yawa gwara nan ɗin." Shiru ya ɗanyi yana kallonta sannan ya ce

"Meyasa da naje Abuja nayita kiranki baki ɗauka?" Sauke idon ta ƙasa ta yi tana wasa da 'yan yatsunta a hankali ta ce

"Bana kusa ne." Kafeta da mayun idonsa ya yi cikin rasa sanin mema zai ce can dai yace

"Amratu meya sa ina ta kiranki bakya ɗaukar waya na, kuma meke damunki likita yace kina cikin damuwa? Kinsan dai bama ɓoyewa juna komai we are the best of friends don Allah ki gayamun mecece matsalarki." Shiru ne ya ratsa wurin na kusan 2mns shi yana kallon ta ita kuma ta noce kanta a ƙasa ta gaza cewa komai sai ƙoƙarin danne kukanta take tana daɗa ƙoƙarin danne abubuwan da bakinta ke so ta furta masa amma ga alama zasufi ƙarfinta ne tabbas! 

"Amrah." Ya kira sunanta, yanzu kam ɗagowa ta yi suka kalli juna a hankali ta ce

"Yaya kayi haƙuri bazan iya gaya maka ba." 

"Me yasa? Bazaki iya gayamun cewar kina fama da soyayya ta ba acikin zuciyarki kin rasa yanda zakiyi da ita? Ko bazaki iya gayamun cewar abin yana damunki ba saboda bamuda hope?." Da sauri ta miƙe tsaye tana kallonsa har lokacin cikin sakewa ya ce

"Sit." Ba musu ta zauna lip's ɗin ta har yana rawa ta fara magana

"Yaya ba kaifina banez bansan me yake damuna ba bansan yaushe na fara sonka ba, na sani ba daidai bane ba kuma nasan haramunne ina matar wani ina kuma son waninsa na san banyiwa addinina da al'adata adalci ba idan na aikata hakan, amma ba son raina ba ne na rasa yanda zanyi in cire, ina tunanin idan na nesanta kaina da kai zan samu sassauci, jikina yana bani cewar na haukacene akan sonka Mjay wallahi banida hankali, tayaya ni Amratu da aurena da komai inzo ina son wani, na tabbatar wannan idan itace ƙaddarata haƙiƙa na haɗu da mafi munin ƙaddara don bansan inda zan fara bama ma, ka fahimceni wallahi ni banida wani mummunan nufi akanka amma laifin zuciyata ne." Mjay cikin sauke numfashi ya ce

"Dukkan wani abu da yake damunki Amrah ina jin irinsa game da ke tun kafin ke kisan cewar kina jin wannan abin akaina, ki sani sai dole mun kawar da kai dabin umarnin zuciya mun kama na mind ɗinmu saboda a wurinta ne kawai zamu samu sassauci da tunani me kyau, shi son zuciya ɓacinta yake zama, ke matar aurece banida dalilin shiga gonarki, our relationship should strictly be na brother and sister kamar da can, no string attached, muyita addu'a even though we are hopeless, don Allah ki sassautawa kanki muci gaba da addu'a." Kukan datake tarewa ne ya zo mata ta rufe bakinta da hannayenta bayan ta tsagaita ta ce

"Yaya zuciyata gayamun take idan babu kai bazan rayuba, i want to be with you, inaso kullum ace ina tare da kai, ina so ace yau kaine mijina, ina so ace bana ji bana ganin kowa sai kai, idan zanyi wanka kaine a raina, bacci kaine a raina, girki kaine a raina duk abin sa zanyi a duniya kaine a raina yaya tayaya zan iya haƙura and kai kana gayamun cewar we are hopeless." A hankali ya ce

"We keep praying for the best, zamuyita gayawa Allah Amrah duk wani abu da zai aiwatar haka zamu rungumi ƙaddara ba yanda muka iya." Shiru kawai ta yi tana saurarensa har ya idar ya miƙe tsaye yana gyara zaman suit ɗinsa.

"Kiyi Haƙuri daga yau bazan kara kiranki a waya ba, bazan ƙara tura miki saƙon waya ba sai after sati ɗaya duk bayan sati ɗaya na miki alƙawarin zan kiraki mu gaisa, duk wani abu da kike buƙata na san dashi i will keep on yin abin da nike kiyi haƙuri wannan ita kaɗai ce hanyar tsare mutuncinki a gareni." Yana kaiwa nan ya nufi hanyar waje, kasa cewa komai ta yi kawai ta zauna akan kujerar ta a wannan yanayin kuka ma kasa yinshi tayi.

*KAMPALA ESTATE 2025*
*BILKISU GALADANCHI*
VIP 1K 
REGULAR 500
8039424298
OPAY
BALKISU MUSA 
***.