Page 19
*KAMPALA ESTATE*
NA
*BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
Arewabooks@
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6790e01cf524f8dc4eabb9dd
19
Mjay a mota daya zauna ya shafe 40mns ya kasa cewa Samuel ga inda zasu je, daga bisani kawai ya ce "Ka kaini gida." Zuwansa gidan ma ya kasa sukuni babbar damuwarsa ita ce shin wane hali Amrahnsa zata shiga? Yaya xata ɗauki wannan al'amarin anya xata iya daurewa kuwa kamar shi? Tunani sosai ya rufe masa kai har ma yazo ya rasa takameme me zeyi tunani akai shikam, daga bisani da taimakon maganin bacci ya samu ya yi baccin.
**************
Tunda ya shigo ɗakin yake kallonta amma ya kasa gaskata me idon sa yake gaya masa, kai ina ba ita ɗin bace ma saboda to me zai kawo Zarah a kano har da tuƙi har taje ta yi wancen accident? Kai kamanni ne kawai ya ayyana hakan a ransa, a kanta suka tsaya banda kuka ba abinda take cikin azaba da rashin sanin inda kanta yake kwata kwata, Leo cikin damuwa ya kalli Sule ya ce
"Dr. I suggest you do your work first ƙafarnan yana damunta gaskiya, kai kuma dole se an aske yankan yanada tsayi idan taci gaba da loosing blood akwai matsala." Mutumin da aka kira da Dr. Sule ya ce
"Sir ƙafar zata iya jira jinin be jira ba bari kawai na aske wurin ayi saurin bata agajin gaggawa inaga zai fi." Juyawa yana nazarinta kai kodama ba'a gaya masa ba yasan wannan zarah ce a sautin kukan ta ma akwai sautin muryarta to me take a kano idan ma ita ɗince? Ya nemeta sama da ƙasa amma be sameta ba ya nemi bukar ɗinma baya kasar aka tabbatar masa ya zata ko sunyi tafiya tare ya nemi wanda ma suka san bukar ɗin duk be samu kowa ba Lauya daya bawa bukar hayar gidan yace number da yake da na bukar baya tafiya shiyasa ya haƙura da neman zarah don a watannin baya yasha alwashin nemanta amma duk iya kar ƙoƙarin sa abin yaci tura.
Mahaifinsa ne ya taho da zarah asibitin don haka da plate number motar ta yasa aka shiga faɗa a gidajen radio na kano cewar mota iri kaza me lamba kaza 'yarsu ta yi accident tana unconscious a asibiti kaza amma shiru shiru har aka kwana biyar ko kiyashi be zo ba nemanta ba, a ɓangaren me aikinta kuwa bata san miyar da ake sha ba batada number ogansu kuma ta kira wacce ta kawo ta aikin tace ita ma fa kawai waya ya kira Agency aka ce ta kawota batada nunber sa , a Agency ɗin ma sun kira layin bukar basu samu ba akan wannan kawai me aikin ta ƙara xama na sati ɗaya ko zata dawo aji lafiya tunda wayarta a kashe.
**********
Amrah a cikin kwana biyu gaba ɗaya ta yi wata mahaukaciyar rama, ita dai tunda Mjay yabar office ɗin ta bata ƙara yin yunƙurin kiransa a waya ba, bata masa saƙo ba kamar yanda be mata ba amma shaƙuwar dake tsakaninsu ya sanya kwata kwata bata da sukuni, takan girka abincin da shi kuma kullum Samuel zezo ya karɓa a hannun sakatariyar ta ya dawo da kwanukan jiya amma bata taɓa zuwa ko wurin samuel ɗin ba, shi kuwa hidimar ma dayake sai ya ja baya ya rage a ransa kuwa tsoro yakeji kar ya jefata a cikin tsananin wuya kasancewarsa namiji ita mace, duk wani da zai aikata zai iya zame masa ado amma ita fa? Abincin ma don baya so ta yi tunanin cewar she lost it all shiyasa yake karɓowa don kwata kwata bashi wata nutsuwa ko sukunin cin abincin, da ƙyar yake turawa shima saboda yana sakashi jin wani nishaɗi da sukuni a jikinsa duk sanda gaci. Bayan barinta office kasuwa ta wuce saboda kifin da yafi so ya ƙare yauma sai talafia ta masa gashi ba tarwaɗa, don haka ta shiga kasuwa ta saya kwalin kifin da wasu abubuwan buƙata sannan ta fito tabi super market saboda taga kayan shayin gidan yaja baya koma ince ya ƙare saboda ita da mayyar shayince ta hugawa a jarida sam bata wasa da shayi komai yawan damuwa zata sha shayi me kauri kuwa, don haka ta je ta kwashi kayan shayin da kuma mayukanta na jiki da turaruka ta turo cart ɗinta zuwa canter don yin payment tabar wurin, wani irin mummunan faɗuwa gabanta ya yi yin ido biyu da Mjay da har hakan ya kasa ɓoyuwa har ya nuna cewar tabbas ta razana da ganinsa haɗe da ɗimaucewa, kame kame ta fara amma ta kasa gayar dashi kamar yanda ta kasa nutsuwa sai shine ya ce
"Ahhh Barrister da kanki, me kika zo yi a nan a wannan lokacin." Kallonsa kawai take ta gaza cewa komai, matsowa ya yi yana kallonta yanda daga ganinsa ta rikice masa kuma ta sako ruwa a idonta cikin taushin murya ya ce
"Amratu menene kuma?" Sauke idon ta kawai ta yi ƙasa gaba ɗaya ta kasa cewa komai saboda gani take hala da zaran ta yi magana kuka ne zai ƙwace mata ba ƙaramin shiga rububi tayi ba ganinsa kawai da tayi, kamar ya fama mata wani abu ne daya ɗan kwanta mata kwana biyu tana ƙoƙarin dannewa, a hankali ya kuma cewa
"Not here not now please Barrister." Bata dai ɗagoba ya karɓe cart ya fara turawa yana cewa
"Muje." Ba musu tabi bayansa har duk ya gama bidirinsa wurin motarta suka tsaya yaron super market din ya jere kayan data saya a bayan mota sannan ya tafi, zagawa ta yi ta zauna shima ya zauna a gefen me zaman banza shiru duk suka yi tsawon lokaci se can yace
"Amrah ya naga duk kin rame ne? Akwai wani abu dake damunki ne ko mecece matsalarki?" Cikin ƙokarin danne damuwarta ta ce "Ba wani abu yanayin aikine kawai amma banda hakan banida wata damuwa in Shaa Allah." Kallonta kawia yake sai can yace..
"To amma laifin me na miki kika gagara gayar da ni?" Wasa ta shigayi da 'yanyatsunta
Kafin tace
"To kayi haƙuri mamakin ganinka nayi ban zata zan ganka ba anan na zata bazan ƙara ganinka ba arayuwata na shiga ruɗu ne zuciyata tana shakku ko hala ka fara mun gizo ba kai ɗin ba ne ba." Ta ƙarashe maganar muryarta a karye sosai, cikin damuwa ya ce
"Hana Barrister wannan wace irin magana ce? Yaya za kice bazaki ƙara ganina ba akan wane dalilin?" Tana daɗa sauke kanta a ƙasa ta ce
"Gani nayi kwata kwata bakada ban maka komai ba kaima ka tsaneni ne ai, nagane yanda kowa ke guduna kaima guduna kake bayan kaine ƙwarin gwiwata, kaine kake kulawa dani, kai kaɗai ne ka fahimci irin matsalar rayuwar da nike ciki, akan ka na haƙura da zaman garin nan amma shine yaya kaima ban maka laifin komai ba zaka gujeni, a duk mutanen dake guduna ba wanda ya gujeni nakejin ɗacin hakan a raina sama da kai, zuciyata tana ƙuna idan na tuna cewar a duk cikin mutane mutumin daya fi kowa fahimtar yanayin da nike ciki kuma shine ya tsaneni, so laifi ne? Ko kuma nina sakawa kaina son naka, kafin ka sanni ma yaya nasan cewar ni matar aure ce wallahi bazan taɓa aikata abinda zanciwa addinina da al'adata mutunci ba amma shine ka gujeni har kana kafamun sharaɗi inane tudun dafawata yanzu? Ina zanbi inga haske ni Amrahtu?" Ta ƙarashe maganar tana share hawayen idonta dake sintiri mata a kumatu. A cikin tsantsar mutuwar jiki da tausayin kansu ya ce
"Amrah ya kikeso nayi? Ni ban gujeki ba duk wani motsinki yana kan ido na amma Amrah ki sani fa dole ce ta haddasamun haƙura da kusanci da ke saboda shifa kiɗa muddin ya canja to fa ko ana so ko ba'a so rawa ma canjawa take, ban gujeki da wata manufa ba Allah ya sani kawai ina bin hanyar da anawa ɓangaren ina ganin zata wadatar damu wurin kare kanmu amma ni bazan taɓa gudunki ba amma ya kike so ayi?" Ya ƙarashe maganar da sigar tambaya yana me kakkafeta da ƙananun shanyayyun idanuwansa, ɗagowa ta yi suka kalli juna ido cikin ido sannan a hankali tace
"We can stop seeing eachother but still keep in touch koda a wayane Yaya Mjay, we both are matured enough to handle the situation, let's make a promise cewar maganar soyayya har abada ni da kai bazamu ƙara kawoshi a zuciyarmu ba, since we are not meant for eachother to mu cire wannan shirmen tunanin a ranmu, mu tabbbata a matsayin farko and takecare of eachother dearly." Yanata kallonta har ta kai aya cikin mutuwar jiki ya sauke wata iriyar kasalalliyar ajiyar zuciya me tatare da huci me zafi sannan ya ce
"Idan har kinsan zaki cire abin da kikeji a rainki game da ni shikenan ni na daɗe da cireki a raina don nasan ke matar wani ce, bazan so inga matata da wanina ba saboda haka baxna taba wuce gona da iri ba wurin aikata hakan, zamu ci gaba da waya, zamuci gaba da kulawa da juna kamar brother and sister kamar tun farko but we have limit visiting eachother saboda tsaro." Tana ɗauke hawayen idonta ta ce
"Na gode sosai." Kafin wani a cikinsu ya yi magana wayarsa ta yi ƙara yana janyowa taga sunan Meena raɗam, ɗauke kanta ta yi shi kuwa ya ɗaga kiran da sallamarsa suka gaisa sannan ta ce
"Alhaji Majid check your WhatsApp na tura maka wani saƙo da zaran ka duba sauran bayani zasu biyo baya." Kafin ya yi wata maganar ta katse kiran jikinsa har rawa yake ya shiga whatsapp ya lalubo sunanta kawai yana shiga yaga ta turo masa irin picture ɗinnan da ake viewing so ɗaya tak, buɗe hoton ya yi harga Allah shi ya manta da inda yake zaune ma tsabar tun dazu ta gama gaggaya masa maganganu akan Raheemah da suka gama gigita masa tunani dannewa kawai yake, yana buɗe hoton screen na hasko masa Raheemansa sanye da wani arnen tafi tsiraran bikini a bakin beach kwance shaɓe shaɓe a ƙirjin Aminullah a saman wannan gadon katakon me 'yar runfar kare rana a bakin beach, wani irin faɗuwa gabansa ya yi da saida wayar ta nemi suɓuce masa ya tarota, hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ya ƙara zumin hoton jikinsa yana wani irin rawa wallahi Raheemah ce da Aminullah mijin Amrah, Amrah hannunta ta ɗaura akan bakinta tana so ta kakkamta kanta amma ta kasa jikinta banda wani uban rawa ba abin da yake ta san mijinta ba nutsatse bane amma Raheemah fa? Mjay ƙoƙarin screenshot yake amma sai anan nuna masa due to security reasons bazai iya screanshoting na hoton ba, ɗagowa ya yi suka kalli juna shida Amrah da ta fishi shiga tashin hankali da wani irin kishin abu biyu na farko bata gane alaƙar dake tsakanin Mjay da Meenah ba na biyu kuma Raheemah fa da Aminullah! "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati." Ta furta a sarari, wayarsa ta fara ringing a karo na biyu Meenah ya fito ɓaro ɓaro da sauri ta karɓe wayar a hannunsa ta ɗaga kiran tare da buɗe speaker ta saka a hands free, Meenah ta kwashe da dariya
"I know you most be shocked! Kaga holy husband da evil wife, wato na gaya maka ka saki jikinki mu mori juna Mjay you are a hot guy and i am not after your money i am after your body! I like your sexy body i want to have you all amma kai kana jamin ayoyi kana rantsuwar matarka tayi asarar ƙawa ita bazata yi haka ba to in gaya maka tare tayi tafiya ko wancen karon da Aminullah wannan karon ma suna tare, idan zaka saki jikinka zan ci gaba da baka information back to back in return mai kuma submit your whole self to me inji daɗinka because I want you i want all of you." Mjay zeyi magana kawai Amrah ga katse kiran tare da manna Meenah blacklist kai tsaye ajiye wayar tayi a gefe ta fuskanci gabanta tare da ɗaura hannunta asaman staring motar kusan mintuna 5 motar ta ɗauki shiru ba wanda yake magana kowa jikinsa ya mutu sai kawia Amrah ta kaiwa staring wani irin mugun duka da duka hannyneta biyu kawia ta fashe da wnai tsumammen kuka me razanarwa da firgitarwa, kuka kawai ta shiga rerawa kamar wata zautacciya shikuwa ya tsaya kawai yana kallonta don zuciyar sa ta kasa gaskata abin da ya gani kuma a kwanakinnan fa Amrah ta daina tambayarsa kuɗi kuma bata son ɗaga kiransa ada duk tsiya duk inda take sai ta kirasa sunyi waya, wani irin zufa ce ta keto masa tana tsiyayya har cikin jikinsa da ko inansa, ita kam Amrah banda surutai tana ihun ina zata tsoma kanta Aminullah fa da Raheemah wata wutar kishice da bata taɓa ji akan Aminullah ba yake ɗebarta batare da ta shirya ba ma ta shiga buga kanta ajikin sitarin motar tana daɗa ƙarawa kukanta da surutanta sauti, Mjay ganin zata illara kanta ya sanya ya riƙota gaba ɗaya ya shiga bata baki yana ƙara riƙeta haɗe da bawa kansa baki don yaga so take ta hallakar da kanta a banza, da ƙyar ya shawo kanta tayi shiru daga bisani ma sai ta dawo masa kurma banda ajiyar zuciya ba abin da take saukewa masu fita da ƙyar da wahalar nunfashi, Mjay ya kasa cewa komai duk wannan rarrashin bada baki yayi sa ba sai dai ya jijjigata harya samu ta yi shiru, da ƙyar ya ce
"Barrister ki dawo nan lemme drive you home nasan bazaki iya tafiya ba." Ba musu ta sauka a fusace ta zago sukayi musaya ya tashi motar ya balbala, ikon Allah ne kawai ya kaisu gida lafiya har wurin da take parking ya kaita ya tsaye be bata izinin fita ba don beyi unlocking motar ba, fitilar motar ya kunna saboda dare ya rigada ya yi suka kalli juna idon nan nata sunyi jajir kamar zata tashi sama haka take ji, da ƙyar ya iya yace
"Don't tell anyone kiyi shiru da bakinki kina jina ko? Kar ki musu magana suma, karki cewa Aminullah komai nima bazanwa Raheemah magana ba, bari mu samu proof har yanzu bamuda tabbas saboda ana photo shop kuma kin sani ke Barrister ce zanyi bincike me tsanani akai." Cikin dakewa ta ce
"Ope the door for me." Ba musu ya yi unlocking da sauri ta kwashi jakarta ko key bata tsaya karɓa ba ta wuce ciki a parlour ta tarar da me aikinta tace taje mota ta kwaso kaya ita kuma ta haura sama, har ta me aikin ta fito yana mota sai da ya ganta sannan ya sauka ya bata key ya nufi gidansa ransa a jagule..
Amrah tana zuwa ta saka hannunta gaba ɗaya ta sauke abubuwan dake kan madubinta, ta wurga wayarta a jikin bango gaba ɗaya saida ta hargitsa ɗakinta wallahi tunda take bata taɓa jin kishi me kaifi da ɗaci irin na yau,duk abin da Aminullah ke yi be taɓa baƙanta mata rai ba kamar yau data gansa da Raheemah ta tabbatar wallahi su ɗinne kuma tasha alwashin ɗaukar kwaƙwaran mataki wallahi sai ta ɗauki fansa sai ta saka Raheemah zubda hawaye da bazasu taɓa yankewa ba zasu bita har kabarinta in shaa Allah!! Gefe guda tana tsananin jin takaicin Mjay ina ruwansa da Meenah? Shi wane irin mutum ne wai da har zeyi saving number wayarta suna waya ita kanta meenar wallahi sai ta shaida cewar ita ɗin lauya su gwada buga game ɗin dukkansu aga wa iliminta zai amfaneta a cikinsu duka!!
*KAMPALA ESTATE 2025*
*BILKISU GALADANCHI*
VIP 1K
REGULAR 500
8039424298
OPAY
BALKISU MUSA
***