Page 20
3*KAMPALA ESTATE*
NA
*BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
Arewabooks
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6790e01cf524f8dc4eabb9dd
*Hello fan's ina muku fatan alkhairi, this is to let you know that anan zamu kammala da free pages in shaa Allah, nasan kuma kuna so kuji yanda zata kaya to kawai ku antayo kuɗinku a wannan asusu ajiyar.
Regular 500
Vip 1k
8039424298
Opay
Balkisu Musa
Zakuma ku iya samunsa a Arewa a link na sama Please patronise me. ***.
20
Wani kalan masifaffen tashin hankaline ya ziyarci Mjay da tunda uwarsa ta haifesa be taɓa jin kwatankwacin sa ba, zuciyarsa banda harbawa ba abin da take ya sani cewar be riski Raheenah a cikakkiyar mace ba amma be ɗauki hakan damuwa ba a ganinsa wannan lokacine da ya wuce ba yanzu ba, kuma idan da ace yau yasan cewa Raheemah bazata tsayar da ƙafarta ba da a satin auren nan bazai gushe ba sai ya saketa, kowane lokaci bata bashi haƙƙinsa a zuwan bata son takura to idan bata son takura meye haɗinta da maza? Kai anya ma Raheemah ce kuwa ko dai an haɗa mata munafurci ne to ko da saka hannun Amrah saboda tana sonsa? Kai bazata aikata haka ba Barrister nagartacciya ce ya sani ba sai an gaya masa ba, a wannan daren kam da ƙyar yaga gari ya waye masa lafiya don ya kira wayar Raheemah ya kai so hamsin bata shiga, washe gari kuwa daga tashinsa ya fara fafutukar neman visa zuwa dubai ba zai iya haƙura ba, da cuwa cuwa da komai kuwa ya samu visa ɗin ko bi ta kan Amrah beyi ba a duk wunin visa sai dai ta umara ya samu daga can ya wuce dubai haka ya hakura ya zauna zaman jiran nan da 3 days ayi tafiyar.
Amrah kuwa ta gama tafasa zama mu iya cewa ta ƙone ƙurmus don sassafe ranar 7 ba agidan ya mata ba, wani abincin ta ko na Mjay duk ba ta kansa take ba, gani take idan gaske ne ƙarshen cin amana cin zarafi da tozarci Aminullah ya mata, a ganinta ya nemi koma wacece, ya tafi duk dare ya kwanta da mace dubu ba damuwarta bane dama dai ta taɓa gaya masa duk abin da zaiyi ya yi using protections don ba za ta iya da cuwuka ba tana zaman zamanta, bayan haka ita Raheemah me kenan ta yi mata to? Zalunci? Cin amana? Cin fuska ko rashin mutunci? Duk waɗannan abubuwan bashi ta ci muddin suka tabbata wallahi Raheemah taci bashin da kaf duniya ba abin da zai iya biya mata shi har abada!
Sanda ta isa office ɗinma sai da ta sha wahalar lalubo nunber Detective tukur don shine gurunta saboda ta tarwatsa waccen wayar tata don haka dole ta nemi number sa a office kafin ta kirasa da ɗayan wayar da ko Mjay baida number saboda ta family ce kawai. Sanda aka masa iso a office ɗin tana zaune yana shigowa ta miƙe suka gaisa a mutunce kamar ko yaushe sannan a hankai ta ce
"Aiki zan sakaka Detective tukur and i am paying 3.M for the job but akwai sharuɗa dole sai ka rubuta ko ince mun rubuta undertaking cewar we bury wannan maganar da duk wata maganar da zata biyo wannan wannan da bincken da zamu yi har abada else i will makesure i skin and burn you alive ai ka san dai abin da zan iya ko?" Detecttive murmushi ya yi sannan ya ce
"Barrister is this a threath?" Murmushi ita ma ta yi se yanzu ta zauna sannan ta ce masa
"Not at all it's just a warning just so you know how bad i want to keep it a secret." Yana numfasawa ya ce
"Koda ba xa mu rubuta undertaking ba you can count on me bazan taɓa gayawa kowa ba and for the money banson sisin kwabo indai aikin naki ne, sai kuma we should write and sign the undertaking it's very important." Ba musu ta bashi takardar da ta rigada ta rubuta, ya karɓa ya karance sannan ya saka hannu ita ma ta saka suka raba copies ta ajiye original sannan ta mayarda hankalinta a kansa ta ce
"D tukur ga list na contact da nike so ayi mun hacking sirrin wayarsu a Nigeria suke waɗannan gaba ɗayansu banson a rage komai, idan ta kama ayi amfani da jiga jigan yahoo voice ɗin garinnan amma ina so duk wani social media handle ɗinsu insan me suke aciki duk wata wayar da zasuyi insan da ita duk abin da zasu ƙulla ina so in san dashi bayan wannan sai mutane biyu which happened to be my husband and my so called friend, suna Dubai ga contact ɗinsu ina son sanin location ɗinsu a dubai ko nawa ne zan biya, sannan idan sun shigo Nigeria ma ina son duk abin da suke ciki da wayoyinsu in sani, duk abin da suke a tare ina so shima in sani." Tk ya ɗanyi shiru na wasu seconds sannan a nutse ya ce
"Barrister wannan abu ne me sauƙi ni bana buƙatar ko sisinki da ba don ke da taimakonki da tuni na rasa aikina amma mutanen dubai dole zasu caji kuɗi sosai wanda ni nasan zasufi ƙarfina." Tana gyara zaman sustem dake gabanta ta ce
"Ba damuwa bane wannan fa i can takecare of the bill's just help me insan me suke ciki." Karbar paper ya yi yana mamakin wayon Barrister da hikimarta saboda lfy lau ta tsara komai daga google account ɗin ta ta cire duka contact ɗin da take buƙata, sallama suka yi ta bashi 100k ya sha mai da ƙyar ya karɓa sannan ya fita.
**************
Washe gari sassafe ta tafi office da tsananin mamakinta akan bayanan tukur akan komai daya shafesu a dubai tare suke yawo tare suke zama a hotel ɗaya kai har new pictures an turo mata nasu a tare da video suna shiga hotel su fito a tare kamar wasu couple. Wuraren 11 zuciyarta a zafafe ta bar Chamber ta zuwa office ɗin Mjay inda kai tsaye akai mata iso ciki, ta shiga da sallamarta akan coach ta same shi a zaune yana dafe da goshinsa, be ko ɗago ta kalleta ba har ta zauna, a hankali ta ce
"Good morning sir." Sai a sannan ya janye hannunsa akan goshinsa ya zube masa mayun jajayen ƙananun idanuwansa kamar baya son maganar a cikin wani ruguɓaɓɓen yanayi ya ce
"Barrister kina lafiya." Ƙura masa idon ta tayi ta gaza ce masa komai shikuma ya sake lumshe idon sa yana nazarin yanayin ta dauriyarta tana bashi mamaki don shi ko magana wahala take masa tsabar baƙin kishi da azabar so da yake yiwa Raheemah ya rasa wane irin hukunci zai mata inhar ya je dubai ya ganta da wani wallahi ze iya kashe wannan ya kashe ta duk a huta, cikin sassauta murya da lallami ta ce
"Yayana don Allah ka ɗauki abin nan da sauƙi kaga duk yanda ka rame a kwana biyu? Nasan akwai zafi nasan zaka fini jin ciwo saboda men normally flirt ba sabon abu bane a wurin su but for women abun ya girmama gaskiya, amma dukkanmu muyi haƙuri I'm worried da wannan shirun naka don Allah na dauremun." Se yanzu ya tashi zaune jijiyoyin kansa har yana wani irin harbawa ya kalleta da kyau sannan ya ce
"Zanje dubai gobe wallahi tallahi na gansu a tare sai na kashe ta na kashe sa duk abin da za'amun ma an daɗe ba'a munba." Cikin tashin hankali ta ce
"Subhanallahi Mjay wai kana tunani straight kuwa? Kishi hauka ne da zaka jawa kanka masifa akan mace? Macen ma wacce batasan daraja da ƙimar aurenta ba tsinanniya tambaɗaɗɗiya, ka samawa kanka salama and let's settle this a nutse." Kallonta kawai yake ta ƙara tausasa harshe tace
"You don't need to go Mjay suna tare i paid alot of money na samu duk wani information akansu,me faruwa ya rigada ya faru so muyi haƙuri don Allah" cikin fusata yace
"Akan me zanyi haƙuri? I settle her bill's all of them, not a single abu Rahee ke saya da kanta daidai da sanitary pad ni ke sayawa Raheemah, Toothbrush, toothpaste, panties, bras, recharge card, Data, Fuel every single thing da Raheema ke buƙata ina mata, akan zamantakewa idan ban zama acikin jerin maza sahun farko ba bazan wuce na biyu ba, i am also sexually fit and very ok lfy ta ƙalau i can stay fit all night long ita take guduna kowane lokaci duk da zamana me dukiya da tarin ayyuka ban taɓa kwana a waje ba a gidana nake kwana, kowace rana kuwa 5 a gida take mun muddin ina gari sai dai da wani babban uzurin ko da zan sake fita sai na kai after isha tukunna, menene na mata dana cancanci wannan cin amanar.?" Amrah cikin sigar rarrashi ta ce
"Na sani Yaya Mjay, mutanen da suka raɓeka ma suna cin arzikin ka bare kuma iyalanka duk da haka you have to calm down don Allah." Shiru yaƙi cewa komai ta ci gaba
"Please ka nutsu ka saurareni." Nan ma shiru ya gaxa cewa komai ta ce
"Yaya ka rabu da su suyita yi amma karka ce musu komai dukkansu don Allah, ita ɗinma idan ta dawo karka nuna mata komai akwai babban shirin da nike yi a kansu dukkansu sai naga bayansu wallahi." Shiru ya na kallonta sai can ya ce
"Wane irin shiri ne wannan?" Ɗan murmushi ta yi sannan ta ce
"We both don't deserve them as life partners, basa ƙaunarmu suna zaune ne damu akan wata manufar so why not we play along??." Da mamaki kawai yake kallonka nan da nan ta shiga masa fashin baƙi akan kuɗirinta akan dukkansu, a lokaci guda yaji sanyi ya mamaye duniyarsa ya tabbatar tarayyarsa da Amrah Alkhairi ce.....
**************
Yau bukar ya diro garin kano don kuwa kwana da kwanaki baya samun wayar Zarah tun dirowarsa Niger daga tafiya, ya yi rashin sa'a kuwa be tarar da kowa a gidanba, hankalinsa a matuƙar tashe ya shiga nemanta ya bincika Agency ɗin da suka kawo masa househelp suke gaya masa tun sanda abin ya faru suke nemansa basu same sa ba anan yakejin a gidajen rediyo ma anyi sanarwar mota kaza da kaza tayi hatsari tana asibiti kaza amma suma fa jiya suka jin hakan, Bukar ransa ya ɓaci ga wani ubansun fargaba daya masa dirar mikiya, meya samu matar sa'ar sa? Ina zai fara nemanta yanzu don shi bemasna asibitin ba, da ƙyar ya saisaita kansa ya shiga neme nemen hanya a gidajen radio bashi ya isa asibitin ba a wannan wunin sai after magrib, da ƙyar da misalai aka barshi zuwa ɗakin da Zarah ke jinya a wannan lokacin.
Zaune take an jingina bayanta da jikin gadon an saka mata pillow tana jingine ƙafarta a wurin cinya ɗaure da da ubansun bandage da hannun ta ɗaya, fruits salad ne a bowl an ɗaura mata a serving tray na patient dake tsakiyar gadon, gefe guda wani nurse ne namiji da kuma Leo dake ƙoƙarin kai spoon bakinta ita kuma sai kuka take tana cewa su bata waya ta kira mananta don duk wannan kwanakin yau ta farfaɗo ta fara magana. Bukar sake bakinsa ya yi yana kallonta kafin daga bisani a sarari cikin masifa ya ce
"Yau ga sabon iskanci kai wane irin tsohon ɗan iska ne da zaka saka mun mata a gaba kana bata abinci a baki?" Baba daya suka juyo euna kallonsa, Zahrah kuwa nan da nan jikinta ya ɗauki rawa ta fara ƙoƙarin ja baya amma ba hali tunda ba ƙafa, Leo cikin jin zafinsa ya ce
"Kai wane irin wawan mutum ne wai? Yaya zaka faɗowa mutane cikin ɗakin marasa lafiya kana mana hargowa? Kasan darajar matar taka baka neme ta ba sai yau duk tsawon lokacin data ɗauka anan?" Bukar kamar wani ɗan tasha ya kwaɓe hular kansa ya na nuna Leo dashi
"Kaga wawan yaro ɗan iska tsinanne, Billahillazi akan yarinyar nan zan iya ɓatar da kai a doron ƙasa." Leo murmushi kawai ya yi don kallon mahaukaci tubutan ya ke wa Bukar ya isa kusa da Zarah ya tuge ƙarin ruwan da ake mata ya rikito da duka serving table ɗin har sauran fruits ɗin suka watsu a jikinta ya sanya hannunsa ya ɗauketa da mari ya tureta daga kan gadon sai da Leo ya tareta ta ƙwalla wata uwar ƙara daga nan baji ba gani Bukar ya shiga kai kata duka kamar wanda Allah ya aikoshi Leo sai tattarewa yake dukan yana sauka a jikinsa sai da wannan yaron ya fita neman mutane aka shigo aka rirriƙe Bukar
"Dama nasan tunda kikayi arba da kyakyawan yaron nan kike bibiyarshi tsinanne me siffar aljanu, yanda na ɗauke ido akanki kika je kina bin wani ƙato kika bashi kanki ko wallahi tallahi sai dai wani ba shi ba sai na ɓatar da ruɓaɓiyar uwarki da ke da shi kansa yaron da kuke karuwanci, ni zan kawo ki karatu in ajiye miki komai na jin daɗin rayuwa ki taho ki mayar dani dan iska wato nan Kano ne ko ba idona, an ɓuge da ciwo ana tambaɗewa." Banda sururai ba abin da yake Leo ransa ya bala'in ɓaci ita kuwa Zahrah banda firgita ba abin da take daga bisani a hannu ta some masa wasa wasa fa da ƙyar aka fitar da Bukar a asibitin nan, Aliyu ya tafi har gate ya yi warning securities akan kar su ƙara bari ya shigo asibitin bayan haka sai da visiting card dole kowane visitor zai shigo, ya koma suka rufar mata da ƙyar aka samu kanta tana farkawa kuwa ta fara kuka,.leo ya shiga rarrashinta amma ina tsananin azaba ya tayar mata da ciwon hannunta da ƙafa ga ciwon kai tana cikin azabar ta ce
"Don Allah my pilot ka taimakeni ka sa a ɗauke mun mamana daga gidanta a Lagos wallahi wallahi Bukar ze iya kasheta sabida ya fusata da ganina anan, banida kowa se ita banida gata nasan tunda yake tunanin na aikata wani abu akanta zai huce haushi, ku nemomin shi in bashi Haƙuri don Allah." Leo cikin rarrashi ya ce
"Calm down mana Zarah yanzu bar batun wancen Bukar ɗin da hanzari bani address na mamanki a Lagos in shaa Allah zan saka a ɗauketa daga can kwata kwata." Tana runtse idon azaba ta fara gaya masa nan da nan ya shiga kiran waya da address din da komai ya bayar sanann ya ce nan da 2 hours in shaa Allah zata bar gidan ita dai banda kuka ba abin da take, kafin wani a cikinsu ya yi wani yunƙurin sai ga police a ɗakin su kusan goma tare da Bukar, Baki a sake Leo ya tsaya kallonsa ita kuwa kawai ta fashe da kuka cikin tashin hankali tana nanata kalmar "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Bukar da hannu ya nuna Leo yace
"Gashinan yallaɓai tun a lagos yake bibiyar matata, har gidansa take kwana, yanzu kuma na kawo ta karatu a kano ya biyota yau datinta ɗaya bata gida ashe tana nan wurinsa suna ƙaryar jinya nazo tafiya da matata na tarar yana rungume da ita yana bata abinci a baki, na yi magana ya saka an ɗagani sama an fitar a asibitin." Leo kawai girgiza kansa ya yi ya miƙe tsaye yana kallon Bukar sannan a hankali ya ce
"Wai kai kanada hankali kuwa? Ko sai na maka hankali zaka shiga hankalin naka?" Cikeda jin haushi Bukar ya ce
"Da hankalin ubanka nake aiki jaki kawai." Nan dai police suka tasa Leo a gaba sai mahaifinsa aka kira a waya shi kuma aka wuce dashi police station.
*KAMPALA ESTATE 2025*
BILKISU GALADANCHI*
8039424298
OPAY
Regular 500
Vip 1k.
End of free pages.