18
by @oumfatima33
💞💞💞💞💞💞💞💞
AMATURRAHAMAN
*By*
OUM FATIMA
*(Hakimar D. A. W. A)*
💞💞💞💞💞💞💞💞
*DASHEN🌲ALLAH*
*WRITER'S📚ASSOCIATION*
*TEAM*
*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*
BOOK 1
PAGE 18
*بسم الله الر حمن الر حيم*
Sai da suka shiga zauren gidansu sannan Ya Nafi ta saki hannunta tana sauke ajiyar zuciya kafin ta ƙyal-ƙyale da dariya har tana riƙe ciki. "Meye kuma?." Amah ta tambayeta da mamaki.
Sai da tayi dariya sosai kafin ta fara bata labarin yanda Sojoji suka ci uban su Zakiyya da Gaddafin gaba ɗaya, yanda Gaddafin ya buɗe murya ya rinƙa kwarara ihu yana birgima ne ya bata dariya, sai dai bata sami damar yin dariyar ba a lokacin sai yanzu. "Shegen ba mai kama da ƴan daudu, ni na sara abinda kuka gani a jikin wancan busashshen ƙadangaren da har kuke dakuwa a kansa tsabar zubar da aji." Amah ta faɗa cike da takaici.
"Kema kin san ba son sa nake ba, kawai muna ƙaruwa da juna ne, ni muje ki dafa min ruwa in yi wanka muje Asibiti a bani magani." Shigewa suka yi inda suka tarar da mutanen gidan zaune a ƙasan wata ƙatuwar bishiya da suke zama su huta. Habaici ƴammatan suka riƙa jefa masu suna shewa da fadar magana mara daɗi, basu kula kowa ba suka wuce sashensu don yin abinda ke gabansu kafin suyi lokacinsu don sun saba dakuwa musamman Ya Nafi da Salaha.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Doctor Farhan kuwa tunda ya koma Katsina ya kasa cire tunanin yaran daga ransa, yana buƙatar sanin komai game dasu don haka ya kasa samun natsuwa har sai da ya kira Doctor Zubairu ya bashi umarnin bincika masa komai game dasu, bai aje wayar ba sai da masa alƙawarin zuwa gobe zai sanar dashi komai. Gadiya yayi masa ya aje wayar kafin ya samu nutsuwar shiga wankan da tun ɗazu Matarsa ta haɗa masa ruwan amma ya kasa shiga.
******A ɓangaren Zayyad kuwa sai da suka tashi tafiya kafin ya ba Samuel umarnin sallamar su Zakiyya da zuwa lokacin sun yi matuƙar jigata, wucewa sukayi bayan yayi sallama da mutumin da gidan gonar ke hannunsa sun gama duk abinda zasu yi ya bashi komai a rubuce ya kuma sa an cika masa bayan Motocin da naman kaji da zabbi har da cret-cret ɗin ƙwai don kaiwa mutanen gidan kamar yanda ya saba duk lokacin daya ziyarci gidan gonar sai ya taho musu da tsaraba.
Koda yana can wurin aikinsa idan ana buƙatar dabbobi can ake zuwa a ɗauka ayi amfani da su, haka ma duk sallah a cikin dabbobin da ake kiwata masa yake bawa duka jamar gidan suyi layya, wannan halin nasa na kyautatawa yana ɗaya daga cikin abinda ke ƙara masa soyayyar mutane da kuma ƙarin tsana a wurin maƙiyansa, don su so suke a kullum suji ana zagi da kushe shi, so suke suji ana faɗin magan-ganu mara daɗi a kansa musamman Hajiya Ruƙayya da bata ƙi ace yafi kowa lalacewa ba.
Ya tafi da haushin abinda ya gani yanda ƙananan yara suke lalata rayuwarsu akan abin duniya har ake neman illata lafiyar wata sabo da Namijin daba Mijin aurensu ba, tunda suka tafi yake jan tsaki duk bayan wani lokaci. Koda Haneen ta ishe su da maganar wannan fitsararriyar yarinyar a cewarsa tsawa ya daka mata ya kuma ce "Kika ƙara min surutu a hanya zamu ajeki stupid!." Ya ƙare yana jan tsoki.
Tun daga nan tayi ƙus bata ƙara magana ba har suka je gida, sai dai suna zuwa gidan ya tarda wani kayan ɓacin ran, wai Zaheera ce taje ita da ƙawayenta suka yiwa yarinyar data ɗora hotonsa a TikTok da kalaman soyayya dukan mutuwa yanzu haka tana Asibiti su kuma ƴan sanda sun tafi dasu shine aka zo gida aka sanar.
Yana gama jin labarin a bakin Mukarram yaron Uncle Yusuf gaba yayi kawai yana mamakin yaushe yaran nan suka raina shi da har Zaheera take iƙirarin sonsa, har ta samu ƙwarin gwiwar dukan wata, kai bama wannan ba uban waye ya basu ƙwarin gwiwar ɗora hotonsa a social media da sunan wai suna sonsa duk kuma bai taɓa sanin hakan na faruwa ba 'Zan yiwa tufkar hanci'. Ya raya a ransa. Ɓangaren
Ammah ya fara zuwa ya mata sannu da gida ya wuce sashensa ko wurin Baba Alhaji bai jeba so yake yayi wanka tukun, kayan da suka zo dasu Samuel yasa duka aka kwashe su aka kai sashen Ammah kamar yanda aka saba ita zata raba ta bayar akai ko wani sashe dake cikin Mansion ɗin.
Sai da yayi wanka ya huta kafin ya nufi wurin Baba Alhaji don Abba baya nan yayi tafiya zuwa Kuwait akan harkokinsa, koda ya isa ya samu Baba Alhaji a faolonsa yana kallon labaran da ake haskawa tashar BBC. Zama yayi ya gaishe shi kafin suka shiga taɓa hira anan yake shaida masa cewar hutunsa ya ƙare wani satin zai koma bakin aikinsa. "Bazaka bari ka ƙara hutawa ba Zayyad kafa daɗe baka zo gida ba."
"Akwai tarin ayyuka dake jirana ne Bana." Ya bashi amsa a taƙaice. Kallon shi Baba Alhaji yake sosai yana nazarinsa, kamar akwai abinda ya ɓata masa rai amma da yake yasan halinsa na shanye ɓacin rai da damuwa yasa bai tambaye shi ba, yasan ba zai wuce akan abinda ƴar'uwarsa Zaheera tayi bane. Shi kansa abin ya fara isar sa don ba'a fi sati ba da Hajiya Sha'awanatu tazo ta same shi da maganar Anisa wai itama shi take so har tayi rantsuwar in ba'a aura mata shiba zata sha guba, tayiwa Uncle Maina maganar amma yace kar ta sake tada maganar Zayyad ba yaro bane da za'a masa auren dole ba, shi bazai sa shi yayi abinda baya so ba, idan har shi da kan shi yace yana sonta to zai yi farin ciki da hakan domin yaron nagartaccen yaro ne.
Gani halin da Anisa ke ciki ne yasa yazo ta samu Baba Alhaji da maganar don ta san idan ya yake hukunci ya zauna a gidan baki ɗaya. Ajiyar zuciya Baba Alhaji ya sauke yana duban Zayyad yace "Amma Zayyad baka ganin zuwa yanzu ya kamata ace ka aje Iyali, yanzu da ka riga ka fitar da matar kayi airenka yaranan dole su haƙura su daina wannan shirmen da suke yi, yanzu ina amfanin abinda yarinyar nan Zaheera taje ta aikata tsabar sha-shanci?, ga mutane daga waje ma sai tuntuɓar mu suke akan kaje kaga yaransu ko jikokinsu sun ku dai-daita sun baka amma na hana Mahaifinka takura maka sabo da a baka damar zaɓar abokiyar rayuwarka da kanka."
An zo wurin, dama abinda ya ɓata masa rai kenan yau ɗin, zai so ace ya ɓallawa yarinyar can ƙafa ɗaya ko zata dawo hayyacinta. Hajiya Iya da shigowarta kenan ta samu ana magana akan gaɓar da take so don haka ta ɗora daga inda Baba Alhaji ya tsaya "Ni kam ina ganin anya ba aljana bace ta aure min jika tasa kwata-kwata baya ƙaunar a masa maganar aure zabgegen ƙato da shi. Ɗagowa yayi ya jefa mata wani kallo mai kama da harara yana cewa "Ni ba wata aljanar data aure ni lokaci ne kawai bai yi ba har yanzu."
"Kagani ko Alhaji gaskiya da buƙatar a bincike shi, yo wane irin lokaci ne bai yi ba, sai yaushe kenan lokacin zai yi?, gaskiya dole a san abin yi tunda ita Babar taka ta zuba maka ido ta kasa maka magana." Ganin zancen bana ƙare bane ya miƙe yayi musu sallama ya tafi yana jin Hajiya Iya na mitar"Yo ba kaji ba, ace yaro da an fara maganar aure sai ya bar wurin, to ko dai bashi da lafiya ne?." Da sauri ya ƙarasa ficewa jin tana ƙoƙarin liƙa masa rashin lafiya kuma bayan shi kaɗai yasan yanayinsa. A ɓangaren halittarsa da lafiyar jikinsa shi kan shi ya san yana buƙatar abokiyar rayuwa, amma maganar auren ce kwata-kwata baya so don jinta yake tamkar wani ƙaton zunubi, kai shifa Matan ma gaba ɗaya basa gabansa bare aje ga maganar soyayya da aure.
Lokuta da dama idan ana masa maganar auren yana tsayawa yayi tunanin menene matsalarsa? Wannan amsar ita ce ya gaza ganowa har yanzu. Sai dai da yake bai wani sa abin a ransa ba yasa bai wani maida hankali wurin binciken abinda ke faruwa ba...
✨✨✨✨✨✨✨✨
Sati ɗaya Yaya Nafi na jinya a gida bata zuwa ko ina Amah na bata kulawa yanda ya dace, sunje Asibiti an ƙara dubata an bata magani sabo da tsamin jiki a hankali take ƙara samun sauƙi. Tun daga wannan ranar idan ta kira wayar Gaddafi bata samu saboda blocking ɗinta yayi yace sai ya huce tunda a kanta ne aka masa dukan ɓarawo.
Su Zakiyya kuwa sai da aka basu gado a Asibiti tsabar yanda suka jigata, tsinuwa da Allah ya isa sun iya ba iyaka, zagi kuwa ba irin wanda basu yiwa Ya Nafi ba don har Kakanta Mahaifin Mukhtar sai da aka kira aka ɗora masa zagi. Oho a banza don ita bata ma san suna yi ba tana can itama tana jinyar kanta.
******Kamar yanda Doctor Zubairu yayi wa Doctor Farhan alƙawari a washe gari ya bashi bayanin komai dangane da rayuwar su Amah, labarin su daya ji baisa yaji sonta ya ragu a zuciyarsa bare yaji ya daina sonta gaba ɗaya ba, sai ma ƙwarin gwiwar samuntan da yayi don yanda yaga Kawunta mayen kuɗi yasan duk abinda za'a yi sai ya aura masa ita.
Sai dai shi a nasa bangaren so na gaskiya yake mata don haka yake son samun soyayyarta da yardar ta ba wai a mata dole ba sabo da haka ya shirya yaƙin nemanta zai kuma fara daga yanzu.
Shirya wa yayi tsaf cikin kyakykyawar shiga kasancewar sa ɗan gayu dama sai yayi ɗas abinsa, Matazu ya nufa kansa tsaye duk da ba ranar zuwansa bace amma zaije domin ta. Zai je ya sanar da Kawunta cewar ya amince zai aureta amma ba yanzu ba, zai bata lokaci har ta gama karatunta zuwa lokacin zai yi ƙoƙarin ganin ya shawo kanta sun fahimci juna.
Da farin cikinsa yake tuƙin har ya isa ƙofar gidansu, yana ƙoƙarin neman yaron da zai aika sai ga Kawu Isa ya fito kamar ya san da zuwansa, yana ganinsa ya hau washe baki da rawar jiki ya iso inda yake. "Ranka ya daɗe barka da zuwa, ai har na fara tunanin ko ka canza ra'ayi ne dana jika shiru." Kawu Isa ya faɗa yana washe masa baki.
"Ina yini Baba, na same ku lafiya?." Ya tambaya cike da girmamawa yana sunkui da kai irin na gaban surukin nan.
"Lafiya lau alhamdulillah, bari na turo maka ita yanzun nan." Ya kuma faɗa yana ƙoƙarin juyawa Doctor Farhan yace "a'a dama ina son yin magana da kai ne Baba."
"To... To ba matsala, Bismillah." Ya faɗa da saurin baki yana nuna masa hanyar shiga zaure.
"A'a nan ma ya isa ba wani abu." Doctor Farhan ya faɗa yana mamakin yanda yake ta wani rawar jiki.
Bayanin abinda ya yanke ya masa na cewar yana sonta zai aureta amma a barta har ta gama Makaranta tukun. Ɓata rai Kawu Isa yayi don ba haka yaso ba, so yayi ya fito yanzu ya aura masa ita su tattara su bar musu gida don har ita ƴar'uwarta ta ma korarta zai yi da sunan tana ɗauko musu magana, shike nan sai Sule ya gyara wurin ya saka Matarsa idan anyi auren (sabo da son zuciya). Kuma sannan ga alkairin da zai samu a hannun Doctor ɗin.
"Baka ce komai ba Baba?." Doctor Farhan ya tambaye shi.
"Yo to ranka ya daɗe ai ka riga ka yanke hukunci, amma Allah na tuba bokon me za'a tsaya jira, ai ni a ganina gara a ɗaura kawai sabo da yaran nan ba abin yarda bane ba."
"Ba abinda zai faru Baba a dai bari zuwa lokacin, ga wannan ina son ganinta kafin in wuce in ba damuwa." Doctor Farhan ya faɗa haɗi da miƙa masa ɗaurin kuɗi.
A zalame ya miƙa hannu ya wafce yana faɗin "Wata irin damuwa kuma? Ai yanzun nan zata zo." Yana gama faɗin haka ya shige zauren gidan inda suka ci karo da Kawu Isma'il yana kallon sa, da sauri ya ƙara cusa kuɗin aljihunsa don kar ya gani bai san ya riga daya gani ba don akan idonsa aka bashi. Yana muzurai ya shige ciki yayin da Kawu Isma'il ya gyaɗa kai ya ida ficewa.
Tsayawa yayi suka gaisa da Doctor Farhan shima ya bashi nasa hassafin yayi gaba zuwa uzurinsa da tunanin sai ya wa Kawu Isa magana akan wanda aka bashi dan yaga masu yawa ne kuma ya san ba yau aka fara bashi ba.
Suna zaune suna cin abinci ita da ya Nafi da bata daɗe da shigowa gidan ba ta shigo musu da soyayyen kifi wanda suka zuba shi saman shinkafa da miyar da Amaturrahaman ta girka musu. "Ke Amatu maza ɗauko gyalenki kije waje kina da baƙo." Kawu Isa daya shigo musu ko sallama babu ya faɗa.
"Kamar ya tana da baƙo Kawu? Amaturrahaman ɗin da ko hira bata fara ba." Ya Nafi ta faɗa tana ɓata rai.
"Eh yanzu zata fara ai, ke ai abin da yafi hira ma kin fara shi, ke zoki wuce ko in tattaka ki a wurin nan!." Ya ƙare yana zaro mata ido.
"Gaskiya Kawu sai dai kayi haƙuri amma ba inda zataje." Ya Nafi ta faɗa tana riƙe hannun Amah. Fita yayi ya wawuri tabarya ya shigo ɗakin ai ba shiri suka yi waje da gudu don ba ƙaunarsu yake ba tsaf zai lahanta su. Sai daya tabbatar ya kai Amaturrahaman har gaban Doctor Farhan kafin ya juya ciki yana sauke numfashi.
"Barka da fitowa." Ya faɗa yana kallonta, wani sanyi yake ji a ransa na ganinta kawai da yayi don ba ƙaramar jarabawar soyayya ya faɗa ba. Ɗagowa tayi ta watsa masa mugun kallo da kyawawan idanunta wanda hakan ya kusa gigita nutsuwarsaya bita da mayen kallo yana jin tamkar ya rungumeta a jikinsa ko zai samu sauƙin abinda ke masa yawo cikin jnin jikinsa.
"Ina mai gargaɗinka da kada kayi ƙoƙarin cusa kanka inda zaka sha baƙar azaba, har abada AMATURRAHAMAN MUKHTAR JIƘAMSHI baza ta taɓa mallakinka ba, idan baka sani ba to ka sani na tsaneka tsana mafi muni tunda na fahimci mummunan halinka ka shiga cikin baƙin littafi na da nake rubuta sunan duk wani wanda hukuncina zai riska. Ina mai baka shawara daka nesanta kanka dani kila ka tsallake hukuncina a nan gaba, idan kuma ka ƙi aikata hakan kaci gaba da matsar rayuwata abin ba zai maka kyau ba."
Tana gama faɗin haka ta juya ta shige ciki ta barshi da tsananin mamakin kalamanta, gaba ɗaya ya kasa fassara abinda magan-ganunta ke nufi a ƙwaƙwalwarsa don haka jiki a sanyaye ya kira yaro ya bashi tarin sayayyar da yayo mata ya shiga dasu shi kuma ya shige mota jiki a sanyaye ya ɗauki hanyar Katsina ba tare daya bi takan yarinyar daya aje a masaukinsa na nan ba zai ɗan rage zafi, sai text ya tura mata akan ta tafi kawai....
Oum Fatima