NUUDARR

2

by @oumameer2671

NUUDARR 🥀🥀

(A 2025 NOVEL)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

          AMEENA IBRAHEEM

              (OUM AMEER)

            PAGE 2

........ Na miƙa hannu na kenan da nufin buɗe ƙofa mukayi ido biyu da Aunty Nadee, cikin faɗuwar gaba na saki jakar kaya na tare da sakin kuka a hankali murya ta a ƙasa in a pleading tone nace.

"Aunty Nadee pls Allowed me kada kice zaki hanani, Mama tace ba zan auri Emraan ba, ni kuma na gwammace da in shiga duniya wallahi da a hanani auren Emraan Aunty Nadee domin shine duniya ta...."

In a very low tone naji muryar Nurudden a bayana tare da damƙar hannu na yace.

"Nuudaar you are mad! What do you think are you doing huhh? Akan Emraan? Emraan É—in banza Emraan É—in wofi kike nema ki kassara rayuwar ki, to ki tafi kije ina??"

Cikin matsanancin ɓacin rai na fisge hannu na ina kallon sa nace.

"Nurudden kada ka sake kiran Emraan da banza..."

Hannuna Aunty Nadee ta damƙa da gudu ta Jani ta shige dani cikin kitchen ganin kamar mama ce zata fito.

Nurudden shima cikin zafin nama ya wawuri jakata ya wulla bayan motar Baba sannan ya buɗe ƙofar gate ya fice daga gidan zuciyar sa na yi masa wani iri akan abinda Nuudaa ke neman aikatawa.

Hawaye na gani kwance a cikin idanuwan Aunty Nadee, cikin karyewar zuciya ta kalle ni tace tace.

"Nuudaa miye yayi zafi haka? Kin san girman abinda kike neman aikatawa kuwa? Idan kika yi hakan kina ganin kin yi mana adalci kenan musamman Mama, yanxu da ace Allah bai sa na zo kitchen ɗin nan na ganki ba da shike nan sai ki sanya ƙafar ki ki fice daga gidan nan?"

Ina tsiyayar hawaye nace.

"To Aunty Nadee what should I do? Wallahi tallahi ina matuƙar so da ƙaunar Emraan, I can't live without him Wallahi, Mama Kuma tace ta kai ƙarshen maganar ta cewa ba zan aure shi ba to ya zanyi da raina..."

"Haba Nuudaar! ko mai fa yayi zafi maganin shi Allah, abinda kike neman aikatawa kuskure ne, idan kika fita cikin daren nan ina zaki nufa? Ga gari da mutanen cikin sa babu kyau, sannan shi wanda zaki aikata wannan katoɓarar domin sa shi ya shirya barin nasa iyayen? ko kuma ya tanadar miki masauki a cikin gidan su da zaki zauna? Nuudaa ƙimar ki da ta iyayen ki taɓuwa zatayi har abada a idon duniya, Mama da ta haife ki ta raineki tun kina zanin goyo har kika kawo yanxu baki yi mata adalci ba,Baba da yayi ta miki ɗawainiya tun haihuwar ki zuwa yanzu shima baki masa adalci ba, kuma duk abinda kika ga Mama ta yi saboda ke take yin sa ba don kanta ba,sannan idan kinyi don ki burgesa wallahi iyayen sa da dangin sa ba zaki burge ki su ba, kinga kin ɓata goma kuma biyar bata gyaru ba. Kiyi haƙuri ki barwa Allah zaɓi shi ne yasan abinda yafi da cewa da rayuwar ki duk ba wannan shirmen ba. Sannan kin san halin Saif sarai kamar yunwar cikin ki even Yah Halifah ban san yadda zai yi ya tsaya miki ba a kan wannan lamarin.... "

Faɗawa nayi jikinta tare da rushewa da kuka ba tare da na furta komai ba domin jiki na ba ƙaramin sanyi yayi ba, duk abinda ta faɗa babu ƙarya a ciki kawai dai tsabar son zuciya ne irin nawa da kuma tsananin soyayyar da nike yiwa Emraan......

Ƙara kwantar da murya tayi taci gaba da faɗin.

" Yanxu dan Allah É—iyar gidan AlÆ™ali guda! AlÆ™alin ma Musayyib wanda ya ke tsayawa a shari'ar iyayen da suka kawo Æ™arar saurayi ya gudar musu da 'Æ´a yau shi ne za'a wayi gari ace  'Æ´arsa ta gudu tabar gida ta shiga duniya akan saurayin ta mi kike tunanin zai faru?Nuudaar kiji tsoron Allah ki tuna haƙƙin iyayenki, kina da ilmi ta ko wane fanni bai kamata ki É—auki turbar marasa lissafi da duhun jahilci da rashin wayewa ba, komai cikin hikima da ilmi ya kamata mu riÆ™a yin abubuwan mu. HaÉ—a auren mu lokaci É—aya babu matsalar da zai baki Nuudaa ki kwantar hankalin ki, Yah Halifah namiji ne ni kuma ba auren farko ba ne, babu abinda zanyi daga zaran an É—aura aure shikenan, ko Yah Hadiza kaÉ—ai zata saya miki duk abinda kike so ga Mama ga Alhaji, ga Yah Halifah ga yah Saifu, shin duk waÉ—an nan ba su isa su saya miki duk abinda kike so ba? Ni na riga na sayi gadaje na guda biyu tun tuni su Baba suka bani kuÉ—i na haÉ—a da nawa na sayi har kujeru abinda ya rage min kaÉ—an ne, saboda haka ki daina neman tsaurara abubuwan nan komai zaki yi sa yadda kike so. Auren Hudah É—in Yah Hadiza iyaka 10month yanxu shin idan kika ce sai sun zo sun  koma kuma su sake dawowa dan Allah baki basu aiki ba? Saboda haka kiyi haÆ™uri ku tsara duk abinda kuke so ke da Emraan É—in babu wanda zai hana ku"

Ajiyar zuciya na sauke cike da gamsuwa da Kalaman ta na buÉ—e idanuwa da kyau na kalle ta waÉ—anda sukayi luhu luhu tsabar kuka nace.

"Shikenan Aunty Nadee na amince, Allah yasa shi ne mafi alheri, na gode sosai da tunatarwa"

Murmushin nasara Aunty Nadee ta saki sannan tace.

"Yawwa Nuudaa É—in Yah Halifah da Mama"

Turo baki nayi gaba ina gunguni nace.

"Ni wallahi ba ta Mama ba ce tunda bata son wanda nike so..."

Juyawa tayi ta janyo fillet guda É—aya tana FaÉ—in.

"Naji dai shi kenan to, bari na sanya miki abinci da kaina saboda na san tun break fast É—in safe ne a cikin ki kuma kada ki yarda kice ba zaki ci ba..."

"Aunty Nadee Mama fa nike tunani kin san halin ta, kada ta ƙi janye maganar ta"

Juyowa tayi ta kalle ni tana mai bani assurance tace.

"In sha Allah zata amince ba matsala kada ki damu"

GyaÉ—a kaina nayi nace.

"Tau shi kenan. Kuma dan Allah Aunty Nadee ina neman alfarma da ki kira Emraan ki bashi haƙuri akan wannan maganar..."

Cike da Mamaki tace.

"In kira Emraan na basa haƙuri? Akan wane laifi to?"

Hannunta na damƙe ina mai magiya nace.

"Dan Allah Aunty Nadee pls! Kada yaga cewa an masa ba daidai ba"

Ita dai Aunty Nadee bi na kawai tayi da ido tsabar yanda gaskiya tayi mata yawa, to kawai tace min don ta huta da ni.

********

ASIYAH

  Tunda ta koma gidan Aunty Zainab take banbami tamkar zata tada gidan tsabar masifa. Ita dai Auntyn ta ta sai faman bata haÆ™uri take tana faÉ—in.

"Haba Asiyah kiyi haƙuri mana, it may be akwai uzurin da ya gifta masa tunda bai sa ba yi miki haka ba..."

"Wallahi Aunty Zainab wulaƙanci ne kawai irin na Halifah daman ba yau ya saba yi min irin haka ba, Yanxu duk irin uzurin da zai bani ba zai wuce na yace min lalurar ƙannen sa ce ta gifto ta danne tawa lalurar ba shiyasa na tsane su a rayuwa ta musamman wannan shegiyar Nuudaar ɗin er bura'uba...."

Baki sake Aunty Zainab ta shiga kallon ta tsabar mamakin ta da ya kashe ta. Sai da ta dasa aya sannan Aunty Zainab É—in tace.

" Asiyah kin fara shaye shaye ko? Ki samu mutum da en uwansa sannan kice wai kin tsane su tun baki ma kai ga shiga gidan ba..."

Miƙewa tayi tsaye jin wani ƙarin ɓacin ran da Aunty Zainab ta da ɗa sanya mata tace.

"Aunty Zainab daman na san ba zaki fahimce ni ba shiyasa ban taɓa yi miki ƙorafi ba, kuma ke don mijin ki yana shi kaɗai ga iyayen sa shiyasa ba zaki gane matsalar ƙannen da yayyun miji ba. Yanzu Aunty Zainab ki duba ki gani kullum idan zance yayi min wani abu sai ya ce min wai ba shine a gaban sa ba haɗin lefe yake gini yake miye miye duk sai ya kawo ƙauli da ba'a ɗi ya rattaba min, amma a gabana wallhy da zaran wani daga cikin su ya kira shi ya tambaye shi wani abu jiki na ɓari zai tura, to ni zaunawa zanyi ne kai na yayi murfi? Wallahi ba zai yi yu ba...."

GyaÉ—a kanta Aunty Zainab tayi tace.

"Lallai ba shakka! Ke yanxu er jaririyar yarinya da ke haihuwar jiya har kin san matsalar dangin miji tun ma baki shiga ba? Duk da cewa dangin miji suna da tasu matsalar a mafi yawan Lokuta amma mu muke fara sayawa kan mu matsala da kuɗin mu,idan ba neman rashin zaman lafiya ba miye naki don ya yi musu lalura? Dolen sa ne su ke kuma ba dolen sa ba ce a halin yanxu sai ma idan anyi auren, sannan ko anyi auren baki isa ki hana sa hidimtawa en uwan sa ba matuƙar kina neman zaman lafiya a gidan auren ki...."

"Aunty Zainab dududu nawa ne samun sa baki ɗaya da har zai iya ɗauke lalura ta sannan ya ɗauki ta su? Iyayen su na da kuɗi fa tsabar baƙin ciki ne kawai Aunty Zainab"

"Asiyah! Dan Allah ki rufawa kan ki asiri ki kuma rufa mana muma da ƙurciyarki kada ki ɗorawa kan ki wahala..."

Jakar ta ta figa daga kan cushion É—in Aunty zainab É—in ta wuce É—akin yaran ta ta kwanta akan gado saboda bata so ma tana sauraren ta, shi kenan shi kullum kwanan duniya bai da wani zance sai na Nuudaa, Nurudden, Saif, Yah Hadiza, Nadee, Fauxa, Hanna... Mtsw! Aikin banza kawai wallahi tallahi dani suke zancen"

Nan tayi zamanta sai da mijin Aunty Zainab É—in ya dawo Yayah Sufyan bayan an É—auke ruwa sannan ya É—auke ta ya kai ta gida wanda har ta bar gidan bata sake yiwa Aunty zainab magana ba.

Tana shiga gida ta faÉ—a jikin Umma ta fara kuka tana faÉ—in.

"Umma nifa na gaji da wulaƙancin da Halifah ke min wallahi"

Cikin rashin jin daÉ—i Umma tace.

"Miye kuma yau ya faru?"

"Umma shi ne fa da kansa ya kirani ni ya tambaye ni cewa yaga hadari duk ya game gari ina gidan Aunty Zainab É—in ya zo ya kawo ni gida, nace masa eh ina nan sai ya ce to in jira sa, ganin hadari ya taso sosai yasa na fito ina tsumayin ganin sa amma har ruwan nan ya sauko Halifah bai zo ba kuma idan na kira sa baya É—aga Kirana har yanxu"

Cikin zafin rai Umma tace.

"Ke nifa idan Halifah yasan zaman ƙunta ta miki zaiyi idan kunyi aure gwara tun yanxu ya rabu da ke zai fi mini kwanciyar hankali, don ba zan sai da a Kuya ta dawo tana gogar mini danga ba, bari Alhaji ya dawo gidan"

"Wai Umma Aunty zainab sai wani ganin laifina ta ke wai na dai na ganin laifin sa miye miye..?"

Mere Baki Umma tayi sannan tace.

"ƙyale shegiya er baƙin ciki tunda ita ta samu nata mijin a ɓagas ta samu gindin zama ai sai ta miki baƙin ciki. Ni wallahi abin nan yana bani mamaki wai ciki ɗaya amma mutum yana yiwa ɗan uwansa hassada"

Miƙewa Asiyah tayi tare da ɗaukar Jakarta ta wuce ɗaki tana mai ƙara kiran wayar Halifah cikin sa'a kuwa sai taji an yi picking.

"Aunty Asiyah kiyi haƙuri zan kai masa wayar yanxu"

Jin Muryar Nurudden yasa tayi saurin jan mugun tsaki ta kashe wayar kai tsaye tana mai gunduma mai zagi a ranta tana fadin ko me ya kai wayar Halifahn hannun sa Oho!

Bayan kusan 10mnt ta sake kiran sa a lokacin da yake gaban Mama zaune ta fara mai tijara shine fa ya kashe wayar tare da sanya ta a fly mood.

Daman ta kawo iya wuya akan takaici sai kuma gashi ya kashe wayar. Kuka ta fasa tare da wurgar da wayar a gefe tana faÉ—in.

"Na shiga uku ni kam Asiyah, ni tawa jarabawar tun a waje nike ta ƙunsar baƙin cikin ɗa namiji da dangin sa, idan ba shi ba miye ruwan Nurudden da kiran da nike yiwa Halifah ko kuma baya son Magana da ni ne?"

Xumbur ta miƙe zaune tare da janyo wayar ta shiga gidan text message ta rubuta masa.

" Halifah Musayyib Alƙali ni Asiyah Ma'aji na fasa aurenka ka aiko gobe a karɓa maka sadakin ka da kayan auren ka na fasa tun da ba kai kaɗai ba ne autan maxa.. "

*******

HALIFAH

Yana baro gaban Mama ya cire wayar a flymood ya kamo numbern Asiyah jiki ba ƙwari ya dailing numbern. Allah ya shine shaidar sa har ya kama hanyar zuwa ya ɗauko ta kamar yadda yayi alƙawari sai ga kiran Nadee ya shigo tana sanar mai ga abinda yake faruwa shiyasa ba shiri ya juyo kan Mashin ɗin nasa ya nufo gida, ganin an fara ruwa sosai yasa shi ciro wayar sa ya buɗe seat ɗin Mashin ɗin ƴa saka wayar a ciki gudun kar ta jiƙe, to shi tun a time ɗin ma ya manta da wayar a wurin,to amma yanxu duk abinda zai faɗa mata yasan ba yarda zatayi ba complain kawai zata cika shi da shi har da kuka. Kira kusan uku yayi amma ana ce masa wayar a kashe take, yana nan yana nazari sai ga text ɗin da ta tura masa ya shigo.

Yana gama karantawa yayi murmushi tare da girgiza kan sa kawai yana mamakin rayuwa irin ta Asiyah. Kwata kwata ba ta da uxuri ko kaÉ—an.

"I'm Sorry Love!, Allah ya huci zuciyar ki"

Abinda ya rubutu mata kenan ya tura mata ya share da zancen ta.

Washe gari bayan ya gama shirin sa na fita kasuwa yazo É—akin Mama ya zauna ya kira Nadeeyah akan ta kawo masa break fast É—insa.

Ruwan Tea daban ta kawo masa da bread sannan filet É—in jollop É—in spaghetti daban.

Kallonta yayi yana murmushi yace.

"Nadee Yanxu 11am zaki kawo min Tea? You are not serious! Bani filet É—in Sai ki É—auke wannan"

Itama dariyar tayi tace.

"Yah Halifah kai ne dai baka shan Tea yanxu, bari kaga Yah Saif Idan yaxo yanxu muddin bai yo breakfast daga gida ba Tea É—in zai ce a basa"

"To Saif in dai gidan abinci ne ai kamar mace haka ya ke. Ina Hajiya ne wai?

" Mama fa ta fita tun 10am tacemin idan suka tashi daga school É—in zata wuce gidan Baba Usman"

" Ok to ina Mutuniyata na leƙa ta lokacin da na dawo daga masallacin subhi na ganta akan sallayah zaune"

Girgiza kai kawai Nadeeyah tayi tace.

"Hmm! Ai wallahi Yah Halifah arziki mukayi daren jiya"

Spoon É—in hannun sa ya ajiye yana faÉ—in.

"Subhanallah! Miye ya faru?"

Ƙara yin ƙasa da muryar ta tayi ta bashi labarin duk yadda sukayi da Nuudaar a daren jiya har yanda tayi ta samo kanta.

Cikin tashin hankali yace.

"InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Har abin nata ya kai haka ashe? In sha Allah ba za'a fasa auren ba, ai gwanda ma ayi a gaggauta kowa ya huta"

"Wallahi Nima dai abinda nace kenan, to É—axu na kira Yah Hadiza tunda assusuba na faÉ—a mata abinda ake ciki tace min in bar mata zancen a hannun ta ko kai kada kayiwa Mama da Baba magana"

GyaÉ—a kansa yayi yace.

"To shi kenan, Allah yasa ayi wannan auren lafiya a ƙare sa Lafiya ko zamu samu kwanciyar hankali. Wallahi Nadee tunda Emraan ya shigo rayuwar Nuudaa shi kenan ta sauya daga yanda ta ke"

"Ni ma dai shi na gani Yah Halifah, gwanda kawai ayi auren shikenan an kai ƙarshen komai"

Haka dai suka yi ta tattaunawa har ya kambala sannan ya É—auki kayansa ya fice zuwa kasuwa.

Gidan su Asiyah ya nufa direct ya ajiye mashin É—insa a gefe ya aika yaro akan cewa yana mata sallama.

Bayan Yaron ya dawo yace masa ance tana zuwa sai ya samu wuri ya tsaya a gefen gate É—in nasu yana dakon zuwan ta.

"Ina Halifahn yake?"

Zaro ido yayi tare da yin ƙasa ya duƙa yace.

"Umma ina kwana..."

Hannunta ta É—aga masa tace.

"Da ban kwana ba zaka ganni ne? Kai ni fa Halifah tsakani da Allah ka fito fili ka faÉ—a min idan baka son 'Æ´a ta ba abin dole ba ne..."

Cikin rashin fahimta yace.

"Umma ita Asiyar tace an yi mata wani abun ne?"

"Oh! Abinda zaka ce kenan ma wato, Yanxu ka bawa ƙanin ka waya ya ɗauka yana gaggaya mata baƙaƙen maganganu sannan yanxu ka tsaya a gabana kana tambayata wai anyi mata wani abun ne ko? To don Allah da ka sanya mata hawan jini da kai da dangin naka tun yanxu da ƙurciyarta gwanda kowa ya haƙura kawai..... "

Da sauri Asiyah ta fito hankali tashe saboda bata san cewa Ummar ta fito wai da sunan magana da Halifah ba. Ita yau wannan abun kunyar ina zata je da shi ace wai Umma ta fito tana faɗa da saurayin Haba! Cikin takaici ta zumɓuro baki gaba tace.

" Umma ni fa ban ce miki Nurudden ya faɗamin baƙaƙen maganganu ba.......

OUM AMEER