NUUDARR

3

by @oumameer2671

NUUDARR 🥀🥀

(A 2025 NOVEL)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

AMEENA IBRAHEEM

(OUM AMEER)

Assalam Alaykum mutanen arziki mutanen kirki mutanena na jahar Zamfara da ma kewaye ina yi muku fatan alheri, Suna na REEDERT SKIN CARE wadda ke zaune a cikin jahar Zamfara Gusau Nigeria.... Ina mai farin cikin tallata muku kayana cikin aminci da kyakkyawar zuciya.......

Shin en uwa Kun dade kuna neman mayukan da zasu gyara muku jiki Baku samu ba???? 😳ina masu fama da sun burn?? ,knuckles?? ,glass?? ,Rashes?? ,spots?? Da sauran su? 😳ina masu qorafin suna shafa mayuka baya karbarsu,???😎ina wadda tayi bleaching ya bata mata fata tanaso fatarta takoma daidai ???🧚🏻‍♀️🧚🏻‍♀️shin kunada labarin REEDERT ORGANIC SKINCARE,dake jahar zamfara kuwa?? to idan baki taba amfani da products dintaba dan Allah ki jaraba kiga ikon Allah cikin qanqanin lokaci fatarki zatayi kyau ta murje tadinga sheqi kamar autar larabawa 👌❤️❤️ munada kaya kamar haka ➡️➡️

Amarya set

Mai jego set

Knuckles and dark spots removal set

Whitening and glow set

Lightening and glow set Etc........

Haka zalika munada supplements masu kyau da qayatarwa kamar haka ➡️➡️➡️

Weight gain supplements

Weight loss supplements

Anti-aging supplements

Whitening supplements

Breast enhancement and enlargement

Hips enlargement.

Reedert Organic skincare tana nan zaune a Gusau Motorgage Area behind masaqa

***,***

Delivery nationwide 🌍🌍🌍

Muna aikawa a duk inda kike cikin faɗin Nigeria da ma kewaye.

PAGE3

..... Hararar ta Umma tayi tace.

"Ko bai gaya miki baƙar magana ba Asiyah ina amfanin ya riƙa ɗaga kiran ki matuƙar dai yasan kece kika kira, ko da yake ai yasan kece ɗin tunda ba jahili ba ne yaje makaranta..."

Cikin jin kunya Asiyah ta kwantar da murya tana kallon Umma tace.

"Umma shikenan dai yanxu komai ya wuce kiyi haƙuri"

Sororo Umma tayi sake da baki tana kallon Asiyah tsabar ta raina mata hankali.

Fitowar Alhaji kenan baban su Asiyah shima zai fita wurin aikin sa ya gansu cirko cirko yace.

"Lafiya dai??"

Da sauri Halifah ya durƙusa har ƙasa cikin girmamawa yace.

"Alhaji barka da fitowa"

"Barka Halifah, ya gida ya kuma kasuwa?"

"Alhamdulillah, kasuwa mungode Allah"

Alhaji yace.

"masha Allah. To miye kuke yi a nan? Ke hajiya Murja mi kike yi a nan?"

Ɗan murmusawa tayi tace.

"Haba Alhaji mi kuwa zamuyi, gaisawa muke mana.."

Da sauri Asiyah tace.

"Ahmad ma Umma tunɗaxu yake jiran ki zai fita"

Juyawa tayi ta shige gidan tana faɗin.

"To bari naje daman akwai aiken da zan masa"

Wata irin ɓoyayyiyar ajiya zuciya ta sauke tana mai hamdala ga Allah da ya kawo mata Baba.

Wurin motar sa Alhajin ya nufa yana faɗin Asiyah ta buɗe masa gate daman leƙo yayi ko zai samu yaro waje ya buɗe masa.

Da sauri Halifah ya shiga ya buɗe masa bayan ya wuce sannan ya rufe ya fito ya jingina jikin mashin ɗinsa tare da harɗe hannayensa yana kallon ta kawai.

Tamke fuska tayi ta hau borin kunya tana faɗin.

"Ni wallahi ban san ma wai Umma tazo nan ba..."

With a calm voice yace.

"Baki san taxo ba Asiyah idan baki faɗa mata ba taya zata san wannan abin tunda ba gani take har zuciya ba?"

Hawaye ne suka wanke mata fuska tace.

"Daman ai na san Laifi na zaka gani, kai ne da yimin laifi kuma kai ne ka ke ganin nike da laifi..."

"Look Asiyah, ba wai naga laifin ki ba ne, a'a ke kullum baki da uxuri baki yiwa mutum uxuri da zaran abu ya faru ba zaki tsaya ki ji miye dalili ba kawai zaki yanke hukunci ki kama fushi, kuma rayuwa ba zata je mana a haka ba Asiyah"

"To idan ba shi ba miye kaga wannan uban hadari na jiya yadda ya haɗe ko ina kace zaka zo ɗauka ta amma ka ƙi zuwa sai da ruwa ya min duka, sannan babban abinda ya ƙara ɓata min rai shi ne wai na daɗe ina kira baka ɗaga ba ƙarshe ka ɗaga kuma ka kashe wayar baki ɗaya...."

"Wallahi har na kamo hanya idan kin yarda har na iso round-about ɗin gidan ruwa sai ga kiran Nadeeyah wani issue ya taso na gaggawa dole ban da yadda zanyi na juya na koma, kuma ganin ruwan yasa na cire wayata daga Aljihu na sanya cikin mashin ɗin kada tasha ruwa, bayan kuma na je gidan still mantawa nayi da ita sai da Nurudden ya kawo "

Cikin takaici tace.

" To yanxu har ka iso gidan Ruwa wane kalar uxuri ne zai sa ka ƙi ƙarasawa in da nike Halifah?"

" it's my personal issue Asiyah, ni dai ina baki haƙuri... "

Wayar sa dake gaban aljihun rigar sa ce ta hau vibrating alamar kira ya shigo.

Ciro wayar yayi yana murmushi ganin sunan mai kiran ya kara a masarrafar sauraron sa.

" Yah Halifah ko da na fito daga bacci har ka fice kasuwa"

Murmusawa yayi yana faɗin.

"Na tambayi Nadee tace kina bacci"

"wallahi yau nayi bacci sosai, dan Allah Yah Halifah ka bani 10k cream ɗina ya ƙare, na tambayi Yah Saifu yace min wai shi ba shi da kuɗi amma in faɗa masa sunan cream ɗin zai siyomin"

"To ki faɗa masa mana ai sai ya karɓo miki kawai idan ya samu kuɗin.."

Girgixa kaina nayi kamar ina a gaban sa nace.

"Hmm! Ya Saif ɗin ne ba shi da 10k?kawai dai ba zai bayar ba ne. Don Allah kai ka bani kaji Yayana"

Girgixa kai yayi yace.

"Nuudaa...."

"Haba Yah Halifah na Aunty Asiyah! Yah Halifahn Mama Ruke, Yayan Hannah da Nuudaar, wallahi idan baku bani ba zan yi muku abinda bakwa so in tambayi Emraan...."

Dariya yake sosai yana girgiza kai yace.

"Nuudaar shugaban en Fada, kada fa kije ki na yiwa Emraan wannan abin girma ya faɗi..."

Dariyar nayi nima nace.

"In dai zan samu abinda nike so miye a ciki"

"To miyasa ba zaki yiwa Saif ba.."

Mere Baki nayi nace.

"Ina mutum yaga fuska, kullum fuska ba annuri, ai wallahi matar Yah Saif ta shiga uku Yah Halifah..."

"Kai Malam ni fa ina da abinyi idan har ku baku da shi, aikin banza kawai mtsww!"

Cewar Asiyah tare da ɗaga ido tana hankaɗarsa tun daga sama har ƙasa.

Tsinke wayar yayi yana faɗin.

"Ba damuwa Nuudaa zan tura miki idan na isa shagon"

"Shekaranjiya nan na tambaye ka 20k kace min baka da ita amma yanxu kai tsaye zaka ba wata 10k..."

Cike da Mamaki yace.

"Wata?? Nuudaar ce fa Asiyah"

"To ina ruwana! wallahi Nima sai ka bani 20k ɗin da na tambaye ka..."

Girgixa kansa yayi yace.

"Asiyah ki daina yi min haka, kece mutum ta farko da ya kamata ace yanxu kinfi kowa sanin waye ni bayan en uwa na, tun asali kin san ni ko waye kin san abinda nake iya yi miki iya ƙarfina da wanda bana iyawa, kuma ba zan taɓa ɗaukar abinda ba zan iya ba, ki duba girman lalurar da ke gabana mana, Saif shi ne yayi mana wearing ɗin gaba ɗaya gidajen kinga ba zan zauna in bar sa da aiki ba,na faɗa masa ni ne zan yi fenti duk da yace bai yarda ba"

Taɓe baki tayi tace.

"Uhm! To miye a ciki don yayi komai, ai daman hanyar samun sa tafi taka yawa tunda shi yana aiki kuma ga albashinsa Na shago kai kuma fa? Shagon ne kawai ba aikin, to miye Allah ya hutar da kai zaka ce sai kayi don ɗai nemarwa kai wahala..."

"That's not how I'm Asiyah, ni na san in da kaina ya ke min ciwo idan har ke baki sani ba..."

"WaLlahi ni dai ba ruwa na muddin ka tura mata 10k wallahi sai ka bani 20k.."

Mashin ɗinsa ya haye kawai ya kama hanya yayi tafiyar sa ya barta a tsaye.

Tana shiga zata fara kuka ta tuna irin abinda tayiwa Umma dole taja bakinta tayi shiru ranta babu daɗi.

Tana shiga Umma dake kitchen ta fito tana Hararar ta tace.

"Don ubanki Ina Ahmad ɗin mai jira na? Kan ki kikayiwa bani ba kuma tunda har baki so a ja masa kunne shi kenan sai kiyi ta ƙunsar baƙin ciki wani abin ma sai kinje gidan zaki gane alli ne gawayi. Wuce kuma ga Hidaya can ta tashi bacci ki yi mata wanka ki bata abinci Ahmad ya wuce da ita gida bani iyawa da rigimarta, Zainabu bata da kirki ko kaɗan sai tayi turomin yarinyar nan kuma tasan halin ta ba ta da daɗin sha'ani"

Ahmad da Fitowar sa kenan da toothbrush a hannunsa yace.

"Ummah miye rashin kirkin Aunty Zainab ɗin? Ni wallahi bana ganin matsalar Hidayah, asali ma Ruma ta fita matsala ita da a kullum dunkum dunkum kamar wata kaza mai ƙwai a ciki"

Umma tace.

"To duk waye ya sakankanta su idan ba ita ba?"

Girgixa kansa yayi yace.

"Hmm! Haka dai kuke gani Umma amma wallahi Aunty Zainab tana ƙoƙari akan yaran nan..."

"Kai ni dai dan Allah naji bana son fa munafurci Ahmad, tau yayi! Kayi maxa ka gama in aike ka, mutum sai ya kwanta tun baccin daren jiya sai ya kai sha biyu na rana sannan ya tashi saboda kawai komawa baya"

Shiru yayi mata tare da ɗaukar bucket ɗinsa ya wuce toilet ya share da ita.

Itama Asiyah wucewa kawai tayi saboda bata jin ma zata iya yin magana akan abinda yake damun zuciyar ta.

*********

Mama

Tana fitowa daga makarantar da take koyarwa wato GGSS Samaru Gusau ta kira wayar Saif tace yazo ya kai ta gidan Baba Usman Alƙali wato ƙanin mijinta Alhaji Musayyib Alƙali.

Tun a mota take ta bala'i akan Nuudaa har suka isa gidan Baba Usman ɗin da ke Rijiyar gabas. Shi dai Saif bai ce mata komai ba domin shima al'amarin Nuudaar na ci masa tuwo a ƙwarya.

Suna shiga ta wuce ɗakin matar sa wato Hajiya Bilkisu, bayan sun gama gaisuwa ta tashi ta wuce parlourn Baba Usman ɗin.

Saif yana zaune a parlourn Mama Balki yana latsa wayar sa sai ga Nusaiba ta fito daga ɗaki cikin shirinta na fita zuwa lectures ta kalle shi tace.

"Yah Saif Ina wuni?"

Kallonta yayi sama da ƙasa sannan yace.

"And where are you going like this?"

Kallon kanta Nusaiba tayi sama da ƙasa sannan tace.

"Yah Saif what's wrong with my dress? Abaya ce nayi rolling Kuma na saka kaya a ciki, Kaga ni ko.."

Ta iyarda maganar ta tare da ɗaga Abayar ta nuna mai jeans da t-shirt ɗin da ke jikinta.

Share ta yayi tare da mayar da kallon sa akan screen ɗin wayar sa kamar ba shi ne yayi mata magana ba.

Ƙara matsawa tayi kusa da shi tace.

" Yah Saif dan Allah ka bani 2k mana"

"Kiyi uban me da su??"

Ƙara marairaice murya tayi tana mai karyar da wuya gefe tace.

"Wallahi duk na kashe kuɗin sati na kuma daman kuɗin ba isar mu suke ba munyiwa Daddy complain yace ba ruwan shi..."

"Ai ni daman na gaya musu a daina baku kuɗin satin nan ba'a ji shawara ta ba ne, Ina saudah?"

"Saudah morning lectures take da yau ta tafi tun 8am"

5k ya ciro ya jefa mata sannan yace.

"Ki ɗauki 2k,Saudah 2k sai ki bawa Hannah 1k"

Ɗaukar kuɗin tayi tace.

"Thank you, Allah ya biya"

Sai da ta fita taja tsaki a ranta tace. 'Yah Saif ka shiga uku wallahi, baƙin ƙwanƙiro kawai, duk matar da zaka aura ta shiga uku da baƙaiƙan ƙa' idoji da muguwar rowa mtsw!'

Mama kuwa bayan sun gama gaisawa da Baba Usman tace.

"Abinda yasa nace kada Kazo Alhaji Usman sauri nike yi a daxu da ka kirani shiyasa"

Cikin mutuntawa yace.

"Ba komai Hajiya Sadiya, daman Hadiza ce ta kirani da zancen Nuudaa, to ban ma fara yiwa Alƙali magana ba nace sai na fara yi miki..."

Girgixa kai Mama tayi tace.

"Wato Alhaji Usman wallahi al'amarin Nuudaa yana bani takaici ta ɗauki Emraan tamkar wani ubanta"

"Duk da haka Hajiya haƙuri zakiyi, tunda har an zo ƙarshe miye abin ɗaga hankali a ciki, ai ita Hadizar ta gayamin cewa yanxu ta yarda a haɗe auren lokaci ɗaya, kinga yanxu idan aka fasa auren nan ba tare da wani genuine reason ba za'a tuhume mu da rashin dattako, kuma ko don zaman tare da akayi da iyayen sa kinga abin a duba ne, sai dai idan kinga wani abinda bai kamata ba ki yi mata faɗa ki kuma ja mata kunne"

"Nima wani lokacin ai don Hajiya Akki ita mahaifiyar Emraan ɗin kawai nike duba wani abin"

"To ai shi ne, kuma kinga duk wannan lamarin ƙuruciya ne daga zaran an gama zai zama sai labari, ayi haƙuri da sha'anin yaran duk haka suke. Ina ce Halifah ya gaya miki yadda akayi da Saudah itama?"

Girgixa tayi tace.

"Banji ba kuwa ina ga duk mantawa sukayi"

"Wani yaro ne fa wai course mate ɗinta ne, to Yaron ɗan Katsina ne babu wanda yasan asalin sa karatu ne kawai ya kawo sa Gusau ɗin yanxu ta kafe kai da fata tace shi take so, har Alƙali ya kira ta yayi mata magana amma duk a banza"

Cikin jimami Mama tace.

"Subhanallah! Kai waɗannan yaran zamani Allah ka shiryar mana da su ka rabamu da su lafiya"

"To amin! Shi ka ɗai za'a cewa"

Daga nan suka ƙara tattaunawa ta fito tayi Sallama da Hajiya Balki Saif ya ajiye ta a gida shi kuma ya wuce shagon sa da ke kasuwa Sabuwa.

Yana shiga ya taradda Halifah zaune yana jiran sa.

Kallon sa yayi yace.

"Ɗan Uwa Lafiya dai na ganka haka?"

Ajiyar zuciya ya saukar sannan yace.

"mtsw! Na yanke shawarar rabuwa da Asiya Saif, yarinyar nan dai tsari na da nata bai zo ɗaya ba.."

Da sauri Saif ya girgiza kansa yace.

"Ban goyi baya ba Halifah, ku dai sake shiri tun da wuri, I meant ku zauna ku ƙara fahimtar juna, kai kasan halin Baba Usman dai musamman akan Alhaji Ma'aji ba zai ɗaga maka ƙafa ba"

"To Saif ya zanyi da rai na, Asiyah kwata kwata bata da hankali tamkar wadda bata da ƙwaƙwalwa haka ta ke. Ga shegen kishin bala'i da fushi nan take"

"Duk naji Halifah wannan duk zaka iya daidaitawa da ita batare da zancen wata rabuwa ba, miye wani rabuwa wai kamar wasu en yara? Dan Allah ka daina wannan zancen"

"Hmmm! Kai Mahaifiyarta fa ta fito ta turke ni..."

Nan ya labarta mai duk abinda ya faru, bayan ya gama gaya masa sai kuma yace.

"Wallahi Saif Allah ne ya kawo Mahaifinta wurin, da tana ci gaba da turkeni zance mata na haƙura da 'ƴar ta ta taje ta bawa duk wanda zata ba..."

Saif Sai dariya yake kamar zai suƙe yana ƙara mamakin wannan ƙarfin hali irin na mahaifiyar Asiyah....

Cikin ƙufula Halifah ya kalle sa yace.

" Wato kai abun dariya ma ya baka kenan ko? "

Dakatawa yayi da dariyar sannan yace.

" To ni wallahi na daɗe banji labari irin wannan ba, to ita yanxu da ace wani abu ya haɗa ku da Asiyar ka daddalla mata mari fa??"

"Cab! Da ranar nasan a station zan kwana..."

"Halifah ka zauna da Asiyah, tana sonka sosai saboda haka ku fahimci juna zai fi, ka kuma gaya mata ta daina saka iyayenta da en uwanta a sha'aninku muddin bai kama dole ba..."

"Asiyah fa ta raina wayo na Saif, ba'a fi sati biyu ba tace sai na bata 30k na bata shekaranjiya tace na bata 20k na ce babu shine yau don Nuudaa ta tambaye ni 10k ina gabanta wai itama dole sai na bata 20k tunda har zan bawa Nuudaa.."

"Wannan kuma zancen banza kenan, kada ka ɗaukar mata wannan zaka sha wahala watarana. Allah ya kyauta ya bada haƙuri.. Ango kasha Mai.."

Tsaki Halifah yaja tare da ɗaukar wayar sa ya zura aljihu ya miƙe yana faɗin.

"Sai anjima Malam"

"Allah ya tsare mana kai angon Asiyah, ango kasha ƙamshi"

Banza yayi masa ya buga mashin ɗinsa ya tafiyar sa.

********

Nuudaar

Sai kusan 12pm na farka tsabar baccin da ya addabeni a daren jiya domin ban kwanta ba sai kusan 2am bayan mun ɗau lokaci muna waya da Emraan sannan daga ƙarshe muka rabu da ƙyar kamar kar mu rabu a wayar ma.

Bayan na tashi da sauri na fara aikin share sharen gida, daman nike shara da wanke da wanke wani lokacin kuma Nurudden, sai Aunty Nadee ke mana girki.

Bayan na kambala ina cikin cin abinci sai ga Nurudden ya shigo, haɗe fuska nayi tare da yin kamar ban san ya shigo ba...

"Nuudaa! What you did yesterday was wrong, very very wrong. wallhy kin bani kunya, pls don't even try it again..."

Still banza nayi masa kamar ba da ni yake ba.

"Twin sis!"

Ya kira ni kamar yadda yake kirana wani lokaci, daman shekara ɗaya ce tsakanina da shi tare muka taso kamar twins domin shi da yake baya na har yafi ni jiki ma ko a wannan time ɗin.

"Dan Allah kada ki sake irin haka pls, saura kaɗan zuciyata ta buga da naga irin abinda kika so aikatawa. Tashi muje na ajiyeki nima ina da lectures yau"

Kai tsaye nace.

"I'm free today"

Miƙewa yayi ya ɗauki kayansa ya fice ya ƙyale ni, ni kuma bai fahimci cewa tun jiya da ya kira Emraan da Banza ya gama ɓata min rai na ba.

Ina gamawa na yi wanka shap shap na shirya na cewa Aunty Nadee na fita kasuwa yanxu zan dawo.....

OUM AMEER