NUUDARR

9

by @oumameer2671

ChaoNUUDARR 🥀🥀

(A 2025 NOVEL)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

AREWABOOKS@AMINATU IBRAHIM

WATTPAD @UMMU-AMIR

AMEENA IBRAHEEM

(OUM AMEER)

PAGE 9

Assalam Alaykum mutanen arziki mutanen kirki mutanena na jahar Zamfara da ma kewaye ina yi muku fatan alheri, Suna na REEDERT SKIN CARE wadda ke zaune a cikin jahar Zamfara Gusau Nigeria.... Ina mai farin cikin tallata muku kayana cikin aminci da kyakkyawar zuciya.......

Shin en uwa Kun dade kuna neman mayukan da zasu gyara muku jiki Baku samu ba???? 😳ina masu fama da sun burn?? ,knuckles?? ,glass?? ,Rashes?? ,spots?? Da sauran su? 😳ina masu qorafin suna shafa mayuka baya karbarsu,???😎ina wadda tayi bleaching ya bata mata fata tanaso fatarta takoma daidai ???🧚🏻‍♀️🧚🏻‍♀️shin kunada labarin REEDERT ORGANIC SKINCARE,dake jahar zamfara kuwa?? to idan baki taba amfani da products dintaba dan Allah ki jaraba kiga ikon Allah cikin qanqanin lokaci fatarki zatayi kyau ta murje tadinga sheqi kamar autar larabawa 👌❤️❤️ munada kaya kamar haka ➡️➡️

Amarya set

Mai jego set

Knuckles and dark spots removal set

Whitening and glow set

Lightening and glow set Etc........

Haka zalika munada supplements masu kyau da qayatarwa kamar haka ➡️➡️➡️

Weight gain supplements

Weight loss supplements

Anti-aging supplements

Whitening supplements

Breast enhancement and enlargement

Hips enlargement.

Reedert Organic skincare tana nan zaune a Gusau Motorgage Area behind masaqa

***,***

Delivery nationwide 🌍🌍🌍

Muna aikawa a duk inda kike cikin faɗin Nigeria da ma kewaye.

Emraan babu abinda ya ke idan ba raba ido ba, zuciyar sa sai saƙe saƙe ta ke masa domin bai san dalilin wannan zama haka ba ana gobe za'a ɗaura masa aure da masoyiyar sa.

Baba Usman ne ya yi gyaran Murya tare da yin addu'a sannan ya yi musu bayanin tirya tiryan game da al'amarin da matar nan ta xo musu da shi sannan daga baya ya ɗora da kallon Uwai ya ce.

"Baiwar Allah, kinji dai bayanin da na kora da kyau sannan ke ce wuƙa ke ce nama a cikin wannan maganar,sannan sanin kanki ne cewa duk yaran da suka tsotsi Nono ɗaya ko da sau ɗaya ne aure ya haramta a tsakanin su ko? To kinga Emraan da Nuudaraa gobe ne ake shirin ɗaura mu su aure saboda haka miye gaskiyar magana?"

Cikin tsantsar tashin hankali ta fashe da kuka ta na faɗin.

"InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Ni Uwai wani irin kalar rashin hankali ne na aika ta a duniyar nan?? Wallahi tallahi na shayar da su ba ɗaya ba ba biyu ba, har sai da Asabe da Uwar Nura suka yi min magana akan na daina haka..."

"InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un!!"

Gaba ɗaya parlourn suka ɗauki kalma jin wannan irin katoɓara ta Uwai..

Alhaji Mashfiq shima sai sharce zufa ya ke tare da cire hular kansa duk sanyin Acn da ke ɗakin bai hana ma sa sharcewa da gumi ba, ƙara matsowa yayi gaba kaɗan daga kan kujerar yana kallon Uwai cikin ido ya ce.

" Baiwar Allah miye dalilin ki na aikata mana hakan? Tun asali baki san cewa mu maƙota ba ne 'ya' ƴan mu za su iya aurar juna watarana?"

Yanxu kuma kuka ta ke sosai ta girgiza kai tace.

"Wallahi Alhaji ba ni da wani dalili bani da wani nufi na cutarwa a gare ku. Kawai a wannan lokacin ya kasance su ana kawo min su rai no idan iyayen su za su fita aiki, to shi Emraana kuka ne da shi, idan ya fara sai ya yi tamkar zai suƙe in yi rarrashin duniya kuma ba ya yin shiru, ni kuma sai ya bani tausayi sai na ɗauke sa na bashi Nono ita kuma Nuudaara a tausayin da take bani shine ga shi tasha ciki kuma idan uwar zata fita sai ta barta tare da mu ta tafi da Nuru sai idan ta dawo ake zuwa a ɗauke ta wani lokacin ma ko ta dawo ana kai magariba sannan idan Halifah ya dawo yake zuwa ya ɗauke ta shiyasa take bani tausayi saboda sai inga Nonon da uwar ke bata baya isar ta shine na riƙa shayar da ita. To sai wata rana Asabe ta fita karɓo sabulu gidan Alhaji Gaju domin ta yi musu wankin su da suka kawo shine ta tarar da Nuudaara a wannan cinyar tana shan Nono Emraana ma a ɗayar cinyar, sai ta tsaya ta kalle ni tace"

"Uwaiii! Kina fa aikata kuskure, wallahi laifi ne ki ke aikatawa domin ba da izinin iyayen su ki ke shayar da su ba, ka da su zo watarana su ji labari a samu matsala, ni dai ina baki shawara ki daina"

Itama sai ga Uwar Nura ta fito daga ɗakin ta tana faɗin.

"Duk ina jiyo abinda ku ke tattaunawa a kai, wannan maganar gaskiya ce Uwai ake faɗa miki, domin shayarwa tana da iyakoki kada ki ƙetare iyaka idan iyayen yaran nan suka sa ni akwai matsala musamman idan ba ma su fahimta ba ne"

Mayafinta ta saka ta share fuskar ta da ta yi jage jage da hawaye cikin magiya ta ce.

"Wallahi tallahi tun daga wannan ranar ban sake kuma shayar da su ba.."

Wani irin harbi Emraan ya kai mata da ƙafa zuciyar sa na masa wani irin tururi tamkar ana yi mai feshin wuta tsabar baƙin ciki. Cikin zafin nama Halifah ya riƙe shi da dukkan ƙarfin sa yana faɗin.

" Haba Emraan!.... "

" Wallahi sai ta ci kutumar ubanta matar nan, tsohuwar banza kawai jahila..."

"InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Emraan! Kana da hankali kuwa? Dattijuwa kamar wannan ka ke wa irin wannan zagin Emraan?"

Duk irin girma, izza da mazantakar da ya ke ji da ita bai san lokacin da Hawaye suka ɓalle daga idanuwansa ba, wani abu ya ke ji mai matuƙar ɗaci da gauni ya tsaya masa a maƙogwaron sa, cikin wata irin azaba ya buɗe bakin sa daƙyar ya ce.

"Halifah kasan irin girman illar da matar nan tayi min? Ta zalunce mu taci amanar mu ta ruguza mana duk farin cikin mu, a yau tayi min shamaki na har abada da farin ciki wanda har na koma ga Allah ba zan sake farin ciki ba, domin Nuudaa ita ce rayuwa ta... "sai kuma ya juya ga Asabe ya ce.

" Sannan ke kuma algunguma munahika er wuta da ta ƙi barin bo ne yayi kwana yanxu ina so dan Allah dan girman Allah ki faɗamin miye ribar ki? Miye ribar ki na ce? Da baki zo ba da yanxu muna nan a farin ciki kamar yadda muke a baya, amma don kina munahika annamimiya kika wanko ƙafa kika zo wurin haɗa fitina, to wallahi ke ma Allah ba zai bar ki ba, dukkan ku yadda kuka raba mu da farin cikin mu kuka saka mu zubar da hawaye daga yau kuma kun fara kuka kenan har ranar Juma'ar da ba ta da Asabar..... "

Hawaye Hajiya Akki ta share itama ta kalli Uwai ta ce.

" Uwai baki kyau ta mana ba sam, kin riga da kin cuce mu kin ci amanar mu Uwai... "

Sai yanxu Baba ya saukar da numfashi mai sauti sannan ya ce.

" Kuskure ne ya riga ya faru, sai dai mu ce Allah ya kyauta. Baiwar Allah Haƙiƙa kin aikata kuskure mai girman gaske, shayar da yara abu ne mai riski wanda shari'ar musulunci ma bata amince da shi kai tsaye ba sai ya cika wasu ƙa'idoji da sharuɗa kafin a aiwatar don gudun irin haka. Allah ya sa haka shi ne mafi alheri, Allah kuma ya haɗa kowa da rabon sa... "

Wani irin kallon ban gane mi ka ke nufi ba Emraan ya yi wa Baba sannan cikin tsabar kaɗuwa da gigita ya ce.

"Haba Baba Alƙali! Dan Allah kar ku biye ta wallahi mahaukaciya ce, da ganin wannan mahaukaciya ce wallahi. Sannan koma ace ya kasance haka ne ni dai ina son kayata don Allah kar ku raba ni da Nuudaar wallahi ita ce rayuwata idan kuka rabamu ban san ta ya ya zan rayu ba "

Girgiza kai Saif ya yi yayinda Nuudaa ke masa gizau da irin haukar da zatayi idan ta tabbatar lallai dimun dimun ba zata auri Emraan ɗin ba, gaskiya akwai tausayi a cikin wannan al'amari.

Alhaji Mashfiq a hankali ya miƙe yaxo ya kama hannun Emraan cikin kalamai masu kwantar da hankali ya ce.

"Emraan! Kayi haƙuri, ka ce InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Allahumma ajirni fi musibatina wa akhlufni hairan minha! Kayi wannan addu'ar in sha Allahu zaka samu sassauci daga yanda ka ke ji a zuciyar ka. Kayi haƙuri ko wane irin bawa da irin tasa kalar ƙaddarar da ubangiji ya rubuto masa zata same shi... "

Yah Hadiza kallon Uwai tayi ita da Asabe rai babu daɗi ta ce.

" Pls zaku iya tafiya ku bamu wuri... "

Jiki na rawa suka miƙe da nufin tafiya, Caraf! Emraan ya sake damƙar mayafin Uwai kamar wani sabon mahaukaci ya ce.

" Kashe ki zan yi ko zan samu sukuni, la'ananniyar Allah ta'ala...."

"InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Emraan! Emraan!

Da ƙyar Saif ya ƙwaci Uwai a hannun Emraan wanda ya koma tamkar wani mayunwacin zakin da ya fito farauta.

Durƙushew yayi kan ƙafafunsa tare da fashewa da wani marayan kuka yana girgiza kai ya ce.

" Kai co! Kai co na ni Saif, yau ni naga baƙar rana, dama ace banzo wannan duniyar nan, dama ace mutuwa ta ce ta riskeni ba wannan mummunan abun ba,oh Allah irin kalar jarabawar da zaka yimin ke nan???....."

Sai yanxu Mama ta ɗago idanuwanta da suke ri ne tsabar kuka ta kalli Emraan ɗin ta ce.

"Yah Allah! Emraan dan Allah ka yi haƙuri... Ka da ka ƙetare iyakar ubangiji ka sanyawa rayuwar ka salama da haƙuri, idan kayi haƙuri haƙuri mai kyau in sha Allahu za ka ga sakamako mafi alherin da ba ka zata ba..."

Girgiza kansa kawai ya ke yana faɗin.

" Ba zaku gane ba, ba zaku taɓa ganewa ba Mama, ni ka ɗai nasan irin tashin hankali da baƙin cikin da ni ke ji a yanxu, ni wallahi dama a ce mutuwa ce ta riskeni wallahi da ta fiye min wannan baƙar ranar a rayuwata..."

Sosai Hajiya Akki ta ke rera kuka ganin irin yanayin da ɗanta tilo ya shiga lokaci guda, wannan irin al'amari da mi ya yi kama? Kai duniya! Idan dai baka mutu ba komai ma zaka ji shi kuma zaka gani wanda ya girmi tunanin ka...

Miƙewa Alhaji Mashfiq yayi yana kallon Hajiya Akki ya ce.

"To! Sai mu tafi ko? Allah yasa hakan shi ne mafi alheri..."

Baba Usman ne ya kalli Alhaji Mashfiq ya ce.

"Wai Alhaji ni cewa nayi tunda har hakan ta ri ga da ta kasance mi zai hana a ɗaura da Fauxiya ko kuma Hannatu tunda an riga da an gama komai ɗaura aure ne ya rage...."

"Bana so! Wallahi ban son ko wace mace idan ba Nuudaar ba, dan Allah ku tausayamin ku ceci rayuwata ku aura min Nuudaa, wallahi da ita kawai zan iya yin rayuwa"

Da ƙyar Alhaji ya samu damar ɗaga Emraan ya ja shi zuwa mota wanda Huzaifa har bakin motar ya bishi yana ƙara ba shi hak'uri yace kuma ya ƙara nazari kafin gobe da ace ya rasa baki ɗaya gwanda ya auri cikin en uwanta ko zai rage radaɗi.

Nurudden Baba ya aika ya ce ya kirani.

Daman kwance ni ke kawai tamkar mutum mutumi hawaye na ta zuba daga idanuwana suna yin in da suke so, kawai na kasa kunne ne ina jira in ji ina aka kwana da zance, jin kiran Baba yasa na miƙe zumbur kamar an tsikare ni da Allura na zunduma hijabi na na tafi.

Bugun zuciyata ne ya ƙaru ganin yanda duk su kayi cirko cirko kowa fuska babu walwala.

Rakubewa nayi gefen da Yah Hadiza ta ke zaune tare da sadda kai na a ƙasa ina sauraren mi za'a furta a gare ni.

"Nuudaar!"

A hankali na ɗago idanuna na kalli baba Usman da naji ya kira sunana.

"Kash! Ai ma kamata ya yi ace anyi maganar nan ga Emraan ɗin ga ki kema ko kuwa jama'a?"

Gyaɗa kai Baba ya yi sannan ya ce.

"Haka ne ya kamata, amma kuma ko yanxu ai an riga an warware komai yanda aka sanar mai haka za'a sanar mata"

Hamdala nayi tare da yin tasbihi ga ubangiji domin rai na ya bani an riga da an kai ƙarshe wannan matsalar.....

"NUUDARR, kamar dai yanda ki ka ji maganar nan haka take, ya tabbata ita wannan matar ta shayar da ku Nononta saboda haka babu aure a tsakanin ku da Emraan har abada...."

Hannu na ɗora a kai tare da kurma wani sabon ihun na faɗi ƙasa kamar wata mai cutar farfaɗiya na dinga murje murje ina faɗin.

" A'a! Wallahi tallahi ƙarya ne wannan maganar, wallahi ƙarya matar nan take mu ku kada ku yarda da ita,... "

" Ke wai miye haka ne dan Allah! Haba Nuudaa!"

Cewar Yah Hadiza tare da miƙewa tsaye ta saka hannayenta ta ɗago ni tsaye tana fadin.

"Kamar ba musulma ba, kiyi tawakkali mana..."

Cikin tsananin ruɗewa har ban san loakcinda na fallasa sirrin mu ni da Emraan wanda babu wanda yasan da shi daga ni sai shi sai kuma Allah da ya haliccemu na ce.

"Yah Hadiza kada mu rabamu dan Allah dan girman Allah kada ku rabamu.."

"Nuudaa mi zai sa a rabaku ban da wannan ƙaddarar"

Kallon nayi ido cikin ido with so much heart broken murya na rawa ina kuka ina girgiza kai na nace.

"Yah Hadiza wallahi ciki ne da ni! Cikin Emraan........."

OUM AMEER