HAIRAN

001

by @takwalam

HAIRAN 馃グ鈾ワ笍馃槶馃挃

No.1

Ayshatuuu

*ISLAH FOODS!* Har yanzun surfe kike idan zakiyi kunu? Har yanzun wahala kike Sha idan zakiyi kunun Aya! Ya kike Yi idan kina marmarin tuwon dawa Dana alkama and you have to undergo processes kafin kiyi? Ina masu Yara da zasu fara feeding din su da semi solid, ba dai har yanzun kashe kudi kuke a siyan cereals na gwangwani ba? To kuzo na Baku labarin *ISLAH FOODS* , na maimaita *ISLAH FOODS* wadda ta kawo Mana wannan garin kunun, garin tuwo na dawa da na alkama, garin kunun Aya, pap powder na Koko, ga custard powder processed and fortified cereal na Yara a saukake, daga ziplock se tukunya, a tsaftace Babu ruwanki da surfe da Kuma nika. Contact her 馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏

***

*Turare_by_ruky* I repeat *turare_by_ruky* are you a fan turaren wuta? Luxurious turare? Ko Kuma irin royalty scent dinnan kike so? Oils ne da khumra kike bukata? Then wannan brand din Kar ya wuce ki, turare ne da duk Wanda ya jishi se ya kalle ki saboda heavenly scent din shi, ga shi pocket friendly, lemme tell you ita kadai ce me turaren da Naga tana koyar da yadda zaki turare a gida, body scrubs and more, abinda muke cewa *DIY* Kuma duka free. Your's is just to follow her on TikTok ku bani labari.

***

Contact her on WhatsApp馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏

***

***

Cikin jirgin da ya taho daga Saudi Arabia wadda muka fi Kira da Makkah ya tsaya ya yada zango a adis Ababa dake ethopia. Passengers ne da zaka kalla ka fahimci ba wai Yan Nigeria ne kawai ba, akwai wasu Yan kasashen a ciki, kilan zasu zo Nigeria yin wani abun ne da ya shafa kasuwanci ko aiki. Karar da wata karamar yarinyar da dukka shekarun ta ba zasu wuce bakwai ba ta kwala a cikin jirgin da yasa kusan kowa Dake kusa da Dan nesa dasu se da suka ji, yasa hankulan air hostess din komawa kanta. Tuni balarabiyar hostess din ta nufe ta cikin yaren larabci take tambayar ta menene? Tana kuka tana girgiza mutumin da ke gefen ta tana Kiran

" Abiey! Abiey!!"

Cikin raunanniyar muryar ta, wadda zata saka dole ma kaji tausayin ta ya shiga zuciyar ka. Air hostess din ta fara Kiran sunan mutumin da Sir! Amma baiyi motsi ba, hakan yasa passengers Dake kusa suka Bata shawarar neman taimako, tuni jirgin ya Fara hargitsewa da maganganu iri irin, wasu na fadin dama tun da sukai boarding flight din daga adis Ababa to mutumin wasn't in a good condition ko kadan. Yarinyar ke ta faman daiwaniya da shi, zuwan likita da nurse din ya Dan kwantar da hankulan mutanen, ga Kuma volunteer har biyu da aka samu cikin passengers, Wanda suke doctors ne. Daya ya manyanta sosae Kuma kana kallon shi kasan ya hada iri da larabawa yayin da dayan yake matsayin matashi Wanda shekarun sa ba zasu wuce ashirin da bakwai ba, Kuma shi din Dan asalin Nigeria ne. A tare suka dukufa bawa mahaifin wannan yarinya taimako, Amma dukda haka Basu samu damar fito da shi daga coma din da suke tunanin ya shiga ba.

Yarinyar na ta kuka ta kankame hannun shi cikin nata, se shesheka take, idan ka kalle su dole se kaji tausayin su ya tsirga maka. A wannan halin jirgin ya sauka a airport Dake birnin Lagos! Tun kafin a sauka aka sanar da hukumar jirgin akan patient da suke da shi, Kuma already har an turo ambulance da premedics suna jira, so ko da suka sauka aka shigo da stretcher aka dauke shi, yarinyar Bata bar hannun ta daga nashi ba, Kuma babu gajiyawa kuka kawai take. Mutane na tayi Masa addua, har motar da take ta blaring siren ta wuce. Suna asibitin koyarwa na LUTH aka shiga bashi taimakon gaggawa Amma ko kafin wani lokaci bawan Allah nan ya cika!

                           ***

Cikin nutsuwa take takowa zuwa inda ta hangi motar shi yayi parking, ko daga baya idan ta hange shi, Bata tunanin akwai ranar da ba zata gane shi ba ko da kuwa nan gaba ne! Ta saki ajiyar zuciya tana furzar da iska daga bakin ta, haka kurum Kuma gaban ta yake faduwa, take Jin kamar kafafun ta zasu harde ta Fadi ko Kuma ta kasa karasawa in da yake, Amma dai fa dole tayi wannan namijin kokarin ta karasa abin da tayi niyya!

Tun baifi meter dari biyu ba, ya juyo Dan ganin ko ta taho, cikin sa'a kuwa ya hango ta tana tahowa, a take ya maida dukkan hankalin shi Kan ta, tafiyar ta, shigar ta ba karamin daukar hankalin shi suke ba, shi mutum ne da yake son gayu, Yana son yaga mace ta iya kwalliya Amma ba wai kwalliyar fuska ba, a takaice ma dai shi baya son yaga an caba powder, an saka gashin idanu da sauran su. A kullum idan ya kalle ta ji yake tana Kara burge shi saboda yadda take shigar ta cikin burgewa da Kuma iyawa!

A yau din ma wata atamfa ce a jikin ta, Cotonou chiganvy wadda tayi Mata kyau da ta siya daga Omni360_collection, rigar kusan har kaurin ta, an Kuma tsaga gefe da gefen ta, ga straight skirt a kasan rigar, tayi daurin turban wrap akan ta sannan ta saka mayafin da ya shiga da kayan da ke jikin ta, sede fuskar ta Babu walwala ko kadan wanda ya saka gaban shi ya fadi, kamar yadda nata gaban yake faduwa. Kamar hadin baki kofar motar ta baya dukka biyun aka bude su, na farko yarinya ce me kimanin shekara biyar tana sanye da English gown me hannun shimi, kanta Babu Dan kwali, wanda ko cirewa yayi ko Kuma baki daya ma baa saka Mata ba, se Yar budurwa itama da shekarun ta zasu Kai Sha uku zuwa biyar sanye da Riga da skirt na atamfa vlisco da ta siya daga Omni360_collection, da Kuma mayafin da ta yafa ya shiga sosae da atamfar Jikin ta. Kana kallon yaran kasan uwar su Yar gayu ce.

Lokaci guda suka nufi wannan budurwa da take tahowa, da murnar su da komai suka fada jikin ta lokacin da suka karasa in da take, itama murmushin da ke fuskar ta ne ya fadada, ta bude hannayen ta, Babu musu suka fada jikin ta tare da fadin

" Oyoyo!"

Ta rike hannun su tare da cupping fuskar Hanifa wato babbar tace

" My girl! Ashe tare kuke da shi?"

Ta fada tana murmushi tare da Kuma kallon Ogan da ya kasa dauke idanun shi daga kanta, Yar karamar me suna A'isha ta zumbura Baki tana bubbuga kaga tace

"Kin fi son Ya Hanifa!"

Cikin sauri ta saki fuskar Hanifa ta kama ta A'isha tace

" My jealous baby! Ina school?"

Ta bangale bakin ta Wanda yayi exposing hakoran ta da suka Fadi alamar famfara take yi wasu suna neman dawowa.

"Abbu yace wai muzo mu ganki, mu baki hakuri, Abbu yayi miki laifi ne?!'

Tayi dariya tana sakin ajiyar zuciya me nauyi tare da girgiza kai  sannan ta ja hannun su zuwa inda yake tsaye da lallausan yafi kalar sararin samaniya, plain dinki me da babu adon zare Amma dukda haka ya fitar da kamanin shi, Kan shi sanye da hula wadda ta kara Masa cikar haiba da Kuma kima. Ya lumshe idanun shi lokacin da ta karasa gaban shi, ji yake kamar ya zuke ta da idanun shi kowa ya huta, ko Kuma ya maida ita matar shi cikin kankanin lokaci. Maganar da tayi Masa yasa ya dube ta da faraa a fuskar shi yace

" Kinyi kyau!"

Murmushi ta saki tana ayyana ai kullum ni a idanun ka kyau nake, a hankali ya fara tafiya Wanda ya tilasta Mata mara Masa baya a hankali, yaran komawa cikin mota sukai suna kallon uban nasu.

"Hairan!"

Ya fada a hankali, saboda shi ya kasance mutum ne me sanyi, ta dube shi idanun ta na haskawa tace

" Naam!"

Se da ya zauna cikin daya daga kujerun da suka zagaye wooden table din Dake cikin famous luxurious eatery din dake cikin makarantar ta ABU, Wanda yasa dole itama ta zauna tana kallon shi Yana going through menu din, a lokacin waitress din Dake sanye da black and white uniform ta karaso Dan karbar order, se da ya fada mata mocktail daya da Kuma bottled water daya sannan yace ayi packaging abincin in three places kafin ya maida hankalin shi akan Hairan da take ta battling da zuciyar ta, kokonto ne fal cikin zuciyar ta rasa yadda zata fara Masa maganar

" Naga kamar gwara ace nazo munyi maganar one and one, saboda a wayar nan bana gane abin da kike nufi ko kadan!"

Tayi shiru ta rasa me zata ce, yace

" Hairan!"

Ta dago idanun ta da suka fara kadawa zuwa ja, fuskar ta damuwa ce kwance fal a cikin ta, ta kasa amsawa hakan yasa yace

" Akwai dalili ko? Nasan kina da dalilin cewa mu rabu, just tell me kinji?"

Ta dago ta kalle shi Amma me zata ce Masa? No ba zata iya fadar masa asalin dalilin ta ba, to ita tun farko me yasa ta fara kula shi bayan tasan akwai wannan ranar dole zata zo. Ta Kara sauke ajiyar zuciya me nauyi tace

" I'm sorry!"

Cikin kosawa yace

"Look Hairan ki fada min dalilin ki na rabuwa da ni. Ko dai baki hakura ba akan abin da Na'ima tayi Miki?"

Tayi saurin girgiza Kai tace

" Ai mun gama maganar wannan! Kawai dai..."

"Kawai dai me? Hairan. Kinsan yadda nake son ki ko? Even the kids wants to be with you, ya Zaki Mana haka?"

A hankali siraran hawaye Suka fara sauka daga idanun ta Wanda tun zamansu take kokarin ganin wannan hawayen basu sauka ba, saboda tasan idan tayi kuka yasan akwai abin da yake damun ta kenan! Inama ita din lafiyayya ce kamar kowa, inama ita din zata iya auren shi tabbas da se ta aure shi, Amma ba zata kasance azzaluma ba marar tausayi, saboda a wajen ta shi din bai cancanci ta ha'ince shi ba saboda shi din son ta kawai yake da dukkan zuciyar shi...

"Kuka kike? Subhannallah! Wait to shikenan mu bar maganar. Dan Allah ki daina kukan kinji?"

Duk se yabi ya sake rikicewa ganin hawayen na sauka akan tafukan hannayen ta da sukai jawur alamar nervousness. Maimakon ta daina kukan se ya Zama kamar ya sake zugata ne, ta dinga kuka a hankali Wanda gaba daya ya hargitsa Masa lissafi, shi ya kasance cikin mazan da basu son kukan mace, wannan weakness din shi ne me girman gaske da yake da shi. Ya rasa Ina zai saka Kan shi yaji Dadi, gashi ita Kuma taki ta daina kuka, gashi bashi da damar lallashin ta, tunda shari'a bata bashi wannan damar ba. Ya tashi ya koma kujerar da take kusa da ita ya zauna tare da yago tissue Dake aje tsakiyar table din ya Mika Mata Yana fadin

" Kiyi hakuri na saka ki kuka!"

Ta amsa ta goge fuskar ta, sannan ta dago ta kalle shi, idanun ta sunyi jawur, Bai ce komai ba se mikewa yayi yaje yayi settling bills din kafin Kuma ya dawo yace

" Mu tafi na maida ki hostel!"

Ta mike a hankali kamar wadda kawai ya fashewa a cikin ta, tabi bayan shi, suna tafe Babu me yin magana har Suka karasa motar, kowanne zuciyar shi babu dadi, ko da suka shiga motar A'isha tayi bacci Hanifa ce kawai, itama Kuma da ta ga atmosphere din ta Zama dull yasa ba tace komai ba, ya tada motar suka fara tafiya, har se da ya Kai gaban hostel din su kafin yayi parking yace

" Se munyi waya?"

A hankali ya gyada kanta, fitowa yayi itama haka bayan sunyi sallama da Hanifa, tana tsaye tana Wasa da edge din mayafin jikin ta yace

" Idan Baki saki ranki ba, I'll be thinking about you har bansan yaushe ba"

Ta dago ta kalle shi, se Kuma ta Dan Yi murmushi kadan tace

" Nagode sosae Allah ya kaiku lafiya"

Yayi murmushin Jin Dadi yace

"Ko kefa! Koma menene yake faruwa know that you're for me and I'm for you kinji. I can't let you easily kinji?"

Tayi shiru ba tace komai ba, Amma itama cikin zuciyar ta hakan take tana Jin ba zata iya rabuwa da shi ba haka da sauki, to Amma idan Bata rabu da shi ba ya zatayi? Babu yadda zatayi fa rabuwar ce maslaha!

Assalamualaikum beautiful souls! Allahu ya amince Hairan is here, but Hairan is not free, contact me馃憞馃憞馃憞

***

Wanne labarun kike so? Aure ne bakiyi da wuri ba kike ganin kamar ba zakiyi ba? Karanta *FARA YAR SHEHU* Abu Kika rasa kike ganin kamar ba Zaki samu madadin shi ba, then ki nema *UNAISA* Soyayya ce tayi Miki kamu Kuma wani tsaikon ya Hana kiyi aure? To *ZUMA* ya kamata ki nema, A cikin *BANI DA LAIFI* Zaki gane cuta ba mutuwa bace ba, Kuma rabon kwadon ko ya hau sama se ya sakko, kiba ce da ke ko ke siririya ce da mutane suke shaming din ki har Kika fara samun mental break down ki sani *BINTUN BATUUL* Na jiran ki. Auren dole akai Miki, ko Kuma kina fama da maraici ne? Kuma Baki karanta *AFIYYA* ba jiran me kike Baki karanta *TSINTUWA* , *HIKMA* , *ME RABO KA DAUKA* , *UWARGIDAN BAHAUSHE* ba?

漏Oum A'eesh