HAIRAN

004

by @takwalam

HAIRAN 馃グ鈾ワ笍馃槶馃挃

No. 4

Ayshatuuu

*Turare_by_ruky* I repeat *turare_by_ruky* are you a fan turaren wuta? Luxurious turare? Ko Kuma irin royalty scent dinnan kike so? Oils ne da khumra kike bukata? Then wannan brand din Kar ya wuce ki, turare ne da duk Wanda ya jishi se ya kalle ki saboda heavenly scent din shi, ga shi pocket friendly, lemme tell you ita kadai ce me turaren da Naga tana koyar da yadda zaki turare a gida, body scrubs and more, abinda muke cewa *DIY* Kuma duka free. Your's is just to follow her on TikTok ku bani labari.

***

Contact her on WhatsApp馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏

***

*ISLAH FOODS!* Har yanzun surfe kike idan zakiyi kunu? Har yanzun wahala kike Sha idan zakiyi kunun Aya! Ya kike Yi idan kina marmarin tuwon dawa Dana alkama  and you have to undergo processes kafin kiyi? Ina masu Yara da zasu fara feeding din su da semi solid, ba dai har yanzun kashe kudi kuke a siyan cereals na gwangwani ba? To kuzo na Baku labarin *ISLAH FOODS* , na maimaita *ISLAH FOODS* wadda ta kawo Mana wannan garin kunun, garin tuwo na dawa da na alkama, garin kunun Aya, pap powder na Koko, ga custard powder processed and fortified cereal na Yara a saukake, daga ziplock se tukunya, a tsaftace Babu ruwanki da surfe da Kuma nika. Contact her 馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏

***

                            ***

Shiru tayi a zaune a wajen har A'isha ta shige dakin su tana zumbura bakin tsawar da ta daka mata, tayi shiru tana Jin wani irin tashin hankali Yana mamaye Mata ilahirin zuciyar ta, har wani sauke numfashi take dai daya saboda firgici, ko Sau daya, ko mafarki Kai ko cikin wildest dream din ta bata taba kawo professor zai iya kallon wata yace Mata Yana son ta ba, balle har ma ya dinga zuwa zance Yana fadawa yaran ta wai aure zaiyi! Balai kenan!! Mikewa kawai tayi da nufin bin shi daki, shi Kuma a wannan lokacin ya fito daga wanka Yana kokarin fitowa Dan daukar wayar shi ya Kuma ci abinci ya kwanta, gaba daya tunanin shi Yana Kai na, musaamman da na dauka tsawon lokaci ban Kira naji yaje lafiya ko kuwa fa, yasan ni din mutum ce me kulawa, saboda alkhairan sa yasa na manta status di na.

Wayar shi Dake Kan handle din armchair da ya bari tun shigowar shi ce ta fara ringing a hankali, kamar ba zata juya ba se Kuma ta juya ta dauki wayar, tana dauka kuwa se gani tayi anyi saving number da cute smile, wani irin Abu ne ya dinga taso Mata tun daga kirjin ta har zuwa bakin ta, ta sake kallon sunan Dake jikin wayar, wai cute smile, wani irin kunci da bakin ciki ne ya turnuke ta, kishi me tsanani ya rufe Mata tunanin ta, a lokaci daya ta daga Kiran tare da fada min dukkan abin da na Baku labari a previous page!

Tun karfin ta take maganar, saboda dama ita Bata kasance mutum me magana a hankali ba, wannan zagin da take ya janyo hankalin Prof da yake kokarin fitowa daga parlon shi zuwa main parlon, mamaki sosae yayi ganin wayar shi a kare a kunnen Ladidi, plus Abubuwan da yaji tana fada yasa ya Isa gare ta Yana fadin

"DiDi me kike Yi? Ke da waye?"

Amma Jin tana ambatar karuwar da take bin mijin ta yayi saurin karasawa ya karbe wayar daga kunnenta Yana fadin

"Meye haka DiDi?"

Ta juyo cikin daga murya tace

" Dole ka tambaye ni meye haka? Kai baka ji kunya ba, Kai..."

Cikin sanyin murya yace tare da ruko hannun ta

" Look DiDi muje daki muyi maganar nan, su Hanifa zasu Jiyo ki"

Hannun ta ta fuzge daga rukon da yayi Mata tace

" Me zaka ce min? Me zaka fada min? Zakace ba Amana ta kake ci ba"

Wani kallon yayi Mata yace

" Wai wacce irin magana kike haka DiDi?"

A ran shi ayyanawa yake wacce irin ruwa DiDi ta ballo Masa a waje na, dama ni da yake lallabawa Kuma ace ta Bari masa wannan aikin, kamar ya daura hannun shi a Kai haka yaji, Amma a wannan lokacin damuwar shi DiDi ce bani ba, tun da DiDi ce a kusa da shi, DiDi zai fara tackling  tukunna, hankalin ta ya sake ja a karo na biyu, wannan lokacin ma ta sake kwace hannun ta yace

" DiDi you should listen to me..."

"Kai zaka saurare ni bani ba.."

Tana fadar haka ya juya ya nufi dakin shi zuciyar shi har wani irin zafi take Yi masa saboda bacin rai, a duniyar shi ya tsana yana magana aki sauraren shi, ita Kuma halin ta ne, ita sede ka saurare ta ba dai ita ba. Yana shiga dakin ya tuna ya bar wayar shi hannun ta bai karba ba, komawa yayi da niyyar shiga Amma kafin ma ya fita sukai kicibis da shi, bahaushe yace mugun gamo kenan!  Hannun shi ya Mika Mata yace

" Bani waya ta!"

Ko kallon shi batayi ba tace

" Sede ka saya wata amma wannan Kam kunyi sallama da ita"

Da mamaki yake kallon ta, ran shi ban da tafarfasa babu abin da yake, zuciyar shi har wuyan shi amma beneath his breath addua yake wadda yasan zatayi calming din shu, baya son yin abun da zai zo Yana Bata hakuri ko Kuma Dana sani Amma a wannan lokacin zuciyar shi fada masa take ya kwada Mata mari, Amma se ya kyale ta ya koma ciki, tare da kwanciya Saman gado yayi rub da ciki, trying hard to suppress his anger.

A bangare na , na Jima kwance ba tare da ko kwakwaran motsi nayi ba, illa muryar wadda nake da tabbacin matar shi ce take min amsa kuwwa cikin kunnuwa na, what did I do to deserve wadannan insult din? Kawai saboda na kula shi shi ne ya bata damar Kira na karuwa? Astagfurillah amma matar nan ta gama da ni, se Kuma na fara tunanin to me nayi Mata da zafi haka, se ma na fara bashi laifin Bata damar daukar wayar shi har ma ta min irin wannan zagin. Ko kadan banyi kuka ba, kamar yadda Abu kadan yake saka ni kuka, amma wannan karon se naji my tears are too precious na zabar dasu akan ta. Amma fa kada ku tona zuciya ta kuji irin kuncin da take ciki, na kasa ma tunanin abin da zanyi, ni data hakura ma ba auren shi zanyi ba balle wani Abu...

Washegari da asuba na duba waya ta, a tunani na ya Kira ni ya bani hakuri abin da matar shi tayi min, Amma se Naga Babu message haka zalika Kuma Babu Kira, Rai na ya sake baci na ayyana wato ya zaba matar shi akai na, ni da aka kuntatawa ni bazai Kira ya bani hakuri ba tun da ni ba matar shi bace ba, one reason for me to abandon him kenan!

Sukuku haka nayi ta shiryawa Dan tafiya class saboda inada 8am lecture, na gama wanka na dawo daki na shirya cikin mix and match na atamfa da lace Wanda shi ne kyautar farko da ya Fara min, yace wajen Omni360collection ya saya, in dai kayan sawa kuke so da mutum zaiyi standing out of crowd, to gaskiya omni360collection shi ne kat, haka handle din su yake a IG, Ina Baku shawarar checking din su ku bawa idon ku abinci.

Nuriyya na kalla ganin har lokacin Bata tashi ba daga bacci, nasan Bata da lecture kenan, garin danwake na dakko daga locker Wanda muka siya daga wajen Islah foods, na kwana cikin sauki ba tare da Ina ta neman kuka ko kanwa ba, na wuce kitchen na jefa sannan nazo naci kadan na aje ma Nuriyya sauran, Rai na a bace na fita ba tare da na tuna ya kamata na Sha magani ba, gaba daya it slipped my mind, bansan hakan ma wata matsalar nake jawa Kai na ba. Har karfe. Shida Muna lecture dukda intervals din biyu ne kawai Amma still na gaji, ga zulumi, ga bacin Rai, na duba wayata for only God knows how much, Amma Babu Kiran shi Babu dalili, kenan hakan Yana nufin shikenan, dama yadda yake ce min dole ma ya aure ni Ashe matar shi zata iya raba mu. Waya ta na janyo na shiga contact di na, na tsurawa contact din shi idanu, Prof kamar yadda nayi saving na yi deleting, tunani na idan nayi hakan zanji sauki cikin zuciya ta, Amma maimakon hakan se naji zuciya ta tayi kunci, naji kamar na nesanta Kai na ne daga gare shi.

Zuwa dare Ina kwance akan gado da katon bruner Ina karatu a midst karatun se kawai nayi drifting zuwa tunanin shi, yau dukka banji muryar shi ba, wani irin rashin Dadi nake ji cikin zuciya ta, na dakko wayar tawa tare da rufe katon bruner, na saka digit din shi cikin wayata, Wanda Bata lokaci ne ma deleting din da nayi ma tunda na Riga da na haddace su a kaina, ba Bata lokaci ko wani Abu kawai na fara Kiran shi, cikin zuciya ta Ina ayyana irin complain din da zanyi masa, Amma har ta katse baa dauka ba, na aje wayar Ina tura baki cike da rashin Jin dadin na Kira shi bai dauka ba Kuma ba yadda zaayi na goge Kiran, zai ga kamar ma ni na damu da shi bashi ba. Na sake yin juyi Ina babbata Rai ni daya. Ashe ban sani ba wayar Bata gurin shi, bansan wanne irin audacity wasu Matan suke da shi ba, lokacin da yace ta bashi wayar shi Taki bashi, se bai kulata ba se yayi kwanciyar shi, Amma a zuciyar shi Allah kadai yasan irin bacin ran da yake ciki, har safe wayar na hannun ta, ya shirya Dan fita office ya same ta a daki Dan ko fitowa batai ba, ya zauna Saman bedside table yace

" DiDi!"

Ko kallon shi batai ba ya cigaba da danna wayar ta da take hannun ta, ya ji wani irin bacin rai ya sake taho masa Dan shakka babu Ladidi Bata ganin mutuncin shi, kilan sakar Mata da yayi Dan ya kyautata Mata ita Kuma tayi amfani da hakan tana ganin ya gaza

"I'm talking to you, Ladidi"

Ta dago tana kallon shi, da idanun ta masu laifi tace

" Me ya faru?"

Kai! Ya furta ba tare da yasan yayi hakan ba, ta dauke Kai tana cigaba da abin da takeyi, yace

" Bani wayata Zan fita"

Wani kallon ta Kara Yi Masa tace

" Wayar ka Kuma? Ai wannan wayar se de Kasai wata Amma wallahi ba zaka Kara amfani da ita ba"

Yayi shiru Yana mamakin halin Ladidi da ko bai sani bane ba, se yau take fito da shi ko ko Yaya? Yace

" Wai DiDi ni kike ma magana irin haka? Are you sane? Ki bani wayata my friend!"

Ya fada Yana dan daga murya, ta sake cewa

" Ni kake dagawa murya Abu Hanifa? Saboda kawai na nuna bacin rai na akan yarinyar da kake cin amanata..."

Cikin sauri ya katse ta da fadin

" Look DiDi! Ba amanar ki nake ci ba, just listen to me nayi Miki bayani, auren ta nake son..."

"Kayi?"

Ta fada idanun ta suna cikowa da kwalla,

"Amma ka manta alkawarin da Kai min ba zaka min kishiya ba"

Se ya sake Baki galala Yana kallon ta, wanne alkawarin a Kuma yaushe

"Wallahi indai Ina Raye ba zaka Kara aure ba, wallahi ni kadai ce matar ka.."

Girgiza Kai yayi kamar Wanda yake ganin kanta ya tabu yace

"Just give me my phone DiDi!"

Ko kula shi Bata sake Yi ba har ya karaci zaman shi ya juya ya fita, a zuciye yake saboda ran shi ba karamin Baci yayi ba, kawai Ladidi tana cin darajar mahaifin ta da mahaifiyar ta, idan ba haka da tuntuni yayi maganin ta, he can't just sit ta dinga dealing din shi kamar ita ce mijin shi ne matar. Haka ya fita ko breakfast Bai Yi ba, dukka tunanin shi suna guri na, tunanin halin da nake ciki kawai yake, plus Bai San ta inda zai iya contacting di na ba, Kan shi yaji ya Fara ciwo a haka ya karasa office ya tura a sama Masa sabiwar waya, daga can wajen azuhar yake yayi blocking wancan sim din yayi swapping wani, wayar ya ruke a hannun shi Yana adduar google ta dawo Masa da dukkan contact din shi. Cikin nasara se gasu dukka sun dawo Amma Babu nawa a ciki!

HAIRAN is not free, contact me via WhatsApp 馃憞馃憞馃憞

***

Wanne labarun kike so? Aure ne bakiyi da wuri ba kike ganin kamar ba zakiyi ba? Karanta *FARA YAR SHEHU* Abu Kika rasa kike ganin kamar ba Zaki samu madadin shi ba, then ki nema *UNAISA* Soyayya ce tayi Miki kamu Kuma wani tsaikon ya Hana kiyi aure? To *ZUMA* ya kamata ki nema, A cikin *BANI DA LAIFI* Zaki gane cuta ba mutuwa bace ba, Kuma rabon kwadon ko ya hau sama se ya sakko, kiba ce da ke ko ke siririya ce da mutane suke shaming din ki har Kika fara samun mental break down ki sani *BINTUN BATUUL* Na jiran ki. Auren dole akai Miki, ko Kuma kina fama da maraici ne? Kuma Baki karanta *AFIYYA* ba jiran me kike Baki karanta *TSINTUWA* , *HIKMA* , *ME RABO KA DAUKA* , *UWARGIDAN BAHAUSHE* ba?

漏Oum A'eesh