HAIRAN

005

by @takwalam

HAIRAN πŸ₯°β™₯οΈπŸ˜­πŸ’”

No. 5

Ayshatuuu

*ISLAH FOODS!* Har yanzun surfe kike idan zakiyi kunu? Har yanzun wahala kike Sha idan zakiyi kunun Aya! Ya kike Yi idan kina marmarin tuwon dawa Dana alkama  and you have to undergo processes kafin kiyi? Ina masu Yara da zasu fara feeding din su da semi solid, ba dai har yanzun kashe kudi kuke a siyan cereals na gwangwani ba? To kuzo na Baku labarin *ISLAH FOODS* , na maimaita *ISLAH FOODS* wadda ta kawo Mana wannan garin kunun, garin tuwo na dawa da na alkama, garin kunun Aya, pap powder na Koko, ga custard powder processed and fortified cereal na Yara a saukake, daga ziplock se tukunya, a tsaftace Babu ruwanki da surfe da Kuma nika. Contact her πŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌ

***

*Turare_by_ruky* I repeat *turare_by_ruky* are you a fan turaren wuta? Luxurious turare? Ko Kuma irin royalty scent dinnan kike so? Oils ne da khumra kike bukata? Then wannan brand din Kar ya wuce ki, turare ne da duk Wanda ya jishi se ya kalle ki saboda heavenly scent din shi, ga shi pocket friendly, lemme tell you ita kadai ce me turaren da Naga tana koyar da yadda zaki turare a gida, body scrubs and more, abinda muke cewa *DIY* Kuma duka free. Your's is just to follow her on TikTok ku bani labari.

***

Contact her on WhatsAppπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌ

***

"Duk ranar da kuka gan shi yaje makarantar Ina so ku kamo min shi na gani"

Dattijon malamin ya fadawa daliban shi bayan sun zo sun fada Masa daya daga cikin su Yana zuwa makarantar Boko, a wancan lokacin dattijon malamin Yana ganin hakan matsayin kafirci da Kuma yahudanci. Dan haka ya Basu damar duk lokacin da suka ga yaron ya dawo ko zai tafi makarantar to su kamo shi su kawo Masa, shi daya se mahillicin shi yasan me zai yiwa yaron. A cikin aji da ko kadan basu da yawa, gaba daya basufi su goma ba cikin ajin, saboda yadda iyaye suka ki bada hadin Kai wajen ganin yaron su sun shiga makarantar ta zamani wato Boko. Baturiyar malamar Dake tsaye Gabon black board tana koya musu darasi ta dubi daya daga cikin students din ta Dake gyangyadi, cikin harshen turanci tace

"Ibrahim bacci kake yau ma?"

Yayi firgigit ya tashi Yana mutsuka idanun shi, ba tare da ta sake ce Masa komai ba ta cigaba da darasin ta, bayan ta Kamalla tace masa ya biyo ta zuwa office din su, haka yabi bayan ta suka Isa office din, kusan dukkan su turawa ne se kabilu uku se wani bahaushe a zaune, ta karasa wajen bahaushen ta fara fada Masa cikin turanci

"Wannan yaron, kamar Yana da damuwa, Ina so ka taimaka kayi magana da shi, idan ma zuwa ne mu samu iyayen shi duk se muyi!"

Malam Idi ya dubi Ibrahim yace

" Ibrahim ya akai kake bacci a aji?"

Ibrahim yayi shiru ba tare da yasan abin da zai fada ba, se ya danyi masa fada daga karshe yace ya tafi aji. Ko da aka tashi banda sauri Babu abin da yake yi saboda lokacin karatu ya kusa Kuma yasan idan yayi fashi ko latti Malam zai saka garada su Dake shi, Yana ta sauri Dan ya samu ya Isa akan lokaci kawai se ji yayi an cafke shi, kafin yayi yunkurin guduwa Yara sa'oin shi su kusan biyar sukai Masa kofar rago suka kama shi, Yana ta bubbuge amma Ina sarkin yawa yafi sarkin karfi, su kuwa murna suke kamar Wanda suka kamo kifin da yafi kowanne girma a gasar Arugungu fishing festival! Haka suka Isa makarantar, duk yawanci almajiran sun taru wasu ma har suna kokarin fara rubutu, aka dire shi a gaban malam, ko kafin ma malam yace Masa komai se da ya saka aka lallasa Masa jikin sa kafin yayi Masa gargadi akan idan ya sake zuwa wannan makarantar ta kafirai zai ga abin da zaiyi masa. Kwana biyu Ibrahim ya dauke kada daga zuwa makaranta, da yaga kurar ta lafa se ya cigaba da zuwa abun shi a boye kamar yadda ya saba, seda aka kusan shafe watanni kafin yaran suka Kara ganin shi a assembly sun zo wucewar, Suka Kara komawa suka sanar da malam, a wannan karon kuwa Malam kawai se ya kori Ibrahim daga makarantar shi.

Asalin Ibrahim Dan garin kiyawa ne Dake karkashin jahar jigawa tamu tarin Allah kenan, Kuma abar alafaharin mu. Mahaifin shi malam Muntari, malamin makarantar allo ne, a wannan tsangayar yayi fice sosae Kuma ba karamin dalibai yake da su ba, ya yaye ya Kuma dauka. Yana da Mata uku, ta farko ita ce Biba wannan Mata zaka Dade baka ga hatsabibiya irin ta ba, ta biyu Huwaila ita Kuma se abin da Biba ta fada take Yi, dukkan su Basu taba haihuwa ba, se da malam ya tsufa sannan ya auro musu Halima wadda idan da sun haihu to da matsayin ya ce gare su, ko wata Bata tsallake ba ta samu ciki, duk wani Abu da Biba zatai Babu abinda batai ba Dan ganin cikin ya lalalce amma Dake Allah shi ne Allah se da aka Haifa Ibrahim, malam Yana son Ibrahim yadda ba ma Zan iya kwatanta muku ba, tun Yana jariri yake fita da shi kofar gida, hakan ba karamin bakanta ran su Biba yake ba...

***

Se nayi kamar Zan Kira Hanifa se na fada, saboda itama bata Kira ni ba which is odd, plus ni tunda na hadu da Prof I.Mukhtar ban taba cikakiyar away ashirin da hudu bai Kira kamar Sau hudu ba, irin mutanen nan ne masu fada maka dukkan abun da ke gudana cikin rayuwar su, bini bini se ya Kira not minding ko Ina lecture, se ya Kira yaga ban dauka ba se yace mun nayi hakuri shi din Yana son yaji yadda Rana ta ta kasance me, a hankali Kuma ya Fara haddace yadda timetable di na take, he make sure bai Kira a wannan lokacin ba. Na sauke ajiyar zuciya Ina Jin Babu dadi Wanda ko ban fada ba kowa ma yasan Babu dadi, na Saba da shi Kuma lokaci daya se ya dauke wuta. Na girgiza kai na cikin rashin kuzari na cigaba da jotting main point da zasu taimaka min. Bayan an gama class din Baki daya na mike Dan tafiya, waya ta dake rike hannu na ta fara vibration Wanda yasa nayi saurin dubawa, duk tunani na shi ne, Amma se Naga Nuriyya ce, haka dai jiki a sanyaye na dauka nace

" Gani nan fitowa!"

Ba tare da na jira amsar ta ba kawai na katse Kiran na nufin hanyar fita daga lecture hall din, can na hango ta tana tsaye ita da wani yaro da take kulawa, Murad, ni Kuma har zuciya ta bana kaunar yaron saboda nasan playing din Nuriyya kawai yake, duk da ban kasance me saka idanu ba a al'amuran mutane ba Amma nasan Yan Matan shi sunyi biyar a cikin ajin mu, Shima Kuma ya tsargu ko suna tare Ina zuwa wajen zai tafi, ita Kuma tayi ta cewa wai saboda Ina daure fuska ne.

Kamar kullum Ina karasawa kuwa ya bar wajen, na dan ja karamin tsaki Ina ayyana munafuki kawai, ta harde hannayen ta a kirji tana kallon na, na saurin sunkuyar da Kai saboda bana son tace zata fara tambaya ta abin da yake faruwa da ni. Aikuwa banci nasara ba, ta dube ni bayan mun fara tafiya a hankali Dan zuwa cefane tace

" Hairan me yake damun ki ne Dan Allah? Kinga yadda Kika koma kuwa, duk Jin rame ke dama ba jikin kirki ba!"

Nayi shiru kamar banji me tace ba, cikin kwantar da murya tace

" Hairan magana nake Miki, me yake damun ki Dan Allah? Wallahi bana Jin dadin ganin ki a haka. Amma ki sani wannan will be the last time da Zan tambaye ki, Allah ma ya sani!"

Kunsan no matter how introverted you're, akwai wani lokacin da kake Jin kawai kana son ka fadawa wani damuwar ka, damuwar tayi min yawa, tun daga lokacin da nayi deciding quiting relationship di na da Prof nake cikin tashin hankali, nake cikin damuwa da tsoron, ni na sani Ina son shi, ban taba son wani halitta yadda nake son shi ba, Dan ni marainiya ce, ba uwa balle uba, gwara uban Ina iya tuna wasu Abubuwan nashi Amma uwata ba Zan iya tuna komai akan ta ba. Ban sani ba ta mutu ko tana da Rai Allahu masani.

"Zan fada Miki mana, Nuriyya ni da Prof ne"

Ta kalle ni da sauri ganin har idanu na sun cika da kwalla, na danyi sniffing dan kada na barsu su zubo, tace

" Subhannallah! Wani abun ya faru ne?"

Na gyada Kai na nace

" Ni nace Masa mu rabu..."

"Saboda me?"

Ta tambaya ba tare da ta jira na karasa magana ta ba, na dan samu guri na zauna saboda da gaske yau so nake na gwada fada mata damuwa ta naji yadda ake ji

"I've my reason Nuriyya, Ina son shi Amma akwai wani abu da zai Hana na aure shi, Kuma yace min ba zai bar hannu na ba, yau kwana shi biyu Bai Kira ni ba, zuciya ta zafi take yimin!"

Ina gama fada na saki kuka a hankali, Nuriyya ta saka hannun ta a bayan na ta cigaba da Dan bubbugawa tana lallashin na akan nayi hakuri, Amma tamkar tunzura ni take kukan se karuwa yake. Se da ta Bari na gama Dan Kai na tace

" To ke Hairan kinsan kina son shi haka, why will you defy yourself happiness Hairan?"

"To ai nace Miki ni da shi ba zamu iya aure ba, I've my own reason fa"

Tayi shiru Dan tasan I've opened up enough, ko da tace na fada reason din to tasan bazan fada ba

"To Hairan ke Kira shi Mana, yanzun fa an daina wannan soyayyar wallahi da zaa jira se namiji ya Kira, you can call him fa!"

Cikin kosawa nace

" Na Kira shi fa, matar shi ta daga ta zazzage ni Kuma Bai Kara Kira ya bani hakuri ba fa!"

Tace

"Ta zage ki? Kin rama? Karki ce min shiru kikai Mata taci bulus. Ban wayar ki karya take wallahi"

Na girgiza Kai na nace

"A'a ki barta kawai kanta tayiwa bani ba, ita ce mahaukaciya bani ba, ba Zan taba kula ta ba, Kuma tasan naji bana son auren shi ..."

"Saboda kina Jin tsoron ko? To in shaaa Allah se ki aure shi, tashi mu tafi kafin nan nayi tunanin way out, Amma bana son cigaba da zaman ki cikin wannan kuncin!"

Da haka ta Jani muka tafi, a cikin sati daya kuwa yau ne kawai naji dadi cikin zuciya ta, se naji kamar rabin damuwa ta ya kau, naji Dan karfin gwiwa. A haka muka je mukai cefane muka dawo. A hanya bayan mun dawo Muna tafiya hostel har lokacin Nuriyya balai take akan kyale matar Prof da nayi tayi, ai Fadi take inama ita ce da wallahi daga kanta ba zata sake Kiran wata 'ya mace ba. Ni dai murmushi kawai nake, wayata tayi vib nayi hanzarin cirowa Dan dubawa, Ina dubawa kuwa se naji jiki na yayi sanyi, ba wadanda nake expecting din bane ba. Na Kara kunne na Ina fadin

" Anty Ina wuni?'

Da murmushi da Ina Iya jiyowa tace

"Hairan Dear, ya school?"

Nace

"Alhamdulillah Anty! Ina kowa da kowa?"

Tace

"Dukka suna lafiya Hairan Dear, yaushe ne exams din Kuma?"

Nace

" Nan da 3 weeks Anty, akwai wani abun ne?"

Tace

"Eh, daga facility din da kike karban therapy Suka Kira wai kije biometric cikin satin nan, Zaki iya zuwa?"

Nayi shiru Ina kallon Nuriyya da take ce min zata shiga ciki na gaida Anty, na gyada Mata Kai nace

"To Anty Zan fadawa level coord din mu, zanzo ko Thursday in shaaa Allah!'

Tace

" Allah ya kaimu, hope dai Babu damuwa kuma kina Shan magani"

Na zaro idanu na tare da rufe Baki Dan wallahi Nafi kwana goma rabon da na sha magani, ni n Isa na fadawa Anty haka se nace

"Anty Ina Sha, Kuma Babu matsala!"

Se tayi min fatan alkhairi sannan mukai sallama akan zata Aiko min kudin motar da Zan dawo. Washgari Ina shirin fita class, na shirya cikin wata blue din chiganvy me gold embellished itama daya daga cikin collection din Omni360 collection kenan...

HAIRAN is not free, contact me via WhatsApp πŸ‘‡πŸ‘‡ πŸ‘‡

***

Wanne labarun kike so? Aure ne bakiyi da wuri ba kike ganin kamar ba zakiyi ba? Karanta *FARA YAR SHEHU* Abu Kika rasa kike ganin kamar ba Zaki samu madadin shi ba, then ki nema *UNAISA* Soyayya ce tayi Miki kamu Kuma wani tsaikon ya Hana kiyi aure? To *ZUMA* ya kamata ki nema, A cikin *BANI DA LAIFI* Zaki gane cuta ba mutuwa bace ba, Kuma rabon kwadon ko ya hau sama se ya sakko, kiba ce da ke ko ke siririya ce da mutane suke shaming din ki har Kika fara samun mental break down ki sani *BINTUN BATUUL* Na jiran ki. Auren dole akai Miki, ko Kuma kina fama da maraici ne? Kuma Baki karanta *AFIYYA* ba jiran me kike Baki karanta *TSINTUWA* , *HIKMA* , *ME RABO KA DAUKA* , *UWARGIDAN BAHAUSHE* ba?

Β©Oum A'eesh