10
NUUDARR 🥀🥀
(A 2025 NOVEL)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
AREWABOOKS@AMINATU IBRAHIM
WATTPAD @UMMU-AMIR
AMEENA IBRAHEEM
(OUM AMEER)
PAGE 10
Assalam Alaykum mutanen arziki mutanen kirki mutanena na jahar Zamfara da ma kewaye ina yi muku fatan alheri, Suna na REEDERT SKIN CARE wadda ke zaune a cikin jahar Zamfara Gusau Nigeria.... Ina mai farin cikin tallata muku kayana cikin aminci da kyakkyawar zuciya.......
Shin en uwa Kun dade kuna neman mayukan da zasu gyara muku jiki Baku samu ba???? 😳ina masu fama da sun burn?? ,knuckles?? ,glass?? ,Rashes?? ,spots?? Da sauran su? 😳ina masu qorafin suna shafa mayuka baya karbarsu,???😎ina wadda tayi bleaching ya bata mata fata tanaso fatarta takoma daidai ???🧚🏻♀️🧚🏻♀️shin kunada labarin REEDERT ORGANIC SKINCARE,dake jahar zamfara kuwa?? to idan baki taba amfani da products dintaba dan Allah ki jaraba kiga ikon Allah cikin qanqanin lokaci fatarki zatayi kyau ta murje tadinga sheqi kamar autar larabawa 👌❤️❤️ munada kaya kamar haka ➡️➡️
Amarya set
Mai jego set
Knuckles and dark spots removal set
Whitening and glow set
Lightening and glow set Etc........
Haka zalika munada supplements masu kyau da qayatarwa kamar haka ➡️➡️➡️
Weight gain supplements
Weight loss supplements
Anti-aging supplements
Whitening supplements
Breast enhancement and enlargement
Hips enlargement.
Reedert Organic skincare tana nan zaune a Gusau Motorgage Area behind masaqa
***,***
Delivery nationwide 🌍🌍🌍
Muna aikawa a duk inda kike cikin faɗin Nigeria da ma kewaye.
Dukkan su sun ɗauka zafin raba mu ne ya sa ni wannan katoɓarar may be hakan yasa su ji tausayi na su yarda su amince muyi auren.
Shiyasa Yah Hadiza ba tare da kawo komai a ranta ba ta riƙo shoulders ɗi na tare da kafe ni da idanawanta ta ce.
"Ke ki nutsu kinji ko ba na son hauka. Soyayya hauka ce hala da zaki zauna ki na kirawa kanki mugun abu. Gwanda ma ki daina wannan haukar domin yanda ki ka san wanda ya mutu har abada ba zai dawo ba to haka ma yanxu tsakanin ki da Emraan ke da shi har abadan abidina..."
Ƙara damƙar hannun ta nayi still ina mai ƙara ba ta tabbacin magana ta na ce.
" Wallahi da gaske na ke miki Yah Hadiza ku yarda da ni, wallahi ciki ne da ni.. "
Wani mugun mari Yah Hadiza ta kifamin tare da turani baya cikin ɓacin rai ta ce.
"Yes! Mari ne na ba ki ko Allah zai sa ki dawo cikin hayyacinki don naga kin haukace"
Ganin ba ta yarda da magana ta ba yasa na juya gun Aunty Nadee tare da kama ƙafar ta na ɗora kai na akan ƙafar ta ta still ina kuka na ce.
"Aunty Nadee Yah Hadiza ta kasa fahimta ta kuma ta ƙi ta yarda da magana ta. Wallahi tallahi ina ɗauke da cikin Emraan wanda babu wani mahaluƙinda ya sani daga ni sai shi sai Allahn da ya halicce mu muka sani,kuma wallahi ni cikin hayyaci na da gaske ni ke gaya muku bari na je na kawo muku scanning ɗin da muka yo last week ago..... "
Ba Mama ka ɗai ba, duk wanda ke wurin sai da yaji hantar cikin sa ta kaɗa musamman Baba da ya bi ni da wani irin kallo wanda ni kaina ban san fassarar sa ba.
Kafin na iyar da ƙarasa miƙewa tsaye ban yi aune ba Yah Halifah ya sake kifamin wani sabon marin da yayi sanadiyyar wuntsilawa na faɗa ƙasa wurin ƙafar Mama tare da ganin wasu taurari na yawo a cikin idanuwana tsabar yanda marin ya shige ni da kyau. Wani irin iska mai zafi ya furzar daga bakin sa sannan ya nuna ni da yatsa ya ce.
"Kin san da wannan har kika bari suka fita suka bar gidan ba kiyi magana ba?..."
Aunty Nadee itama cikin fushi ta ce.
"Yah Halifah idan ma da gaske ta ke miye amfanin maganar ko da ba su tafi ba? tunda ba auren ne a tsakanin su ba miye daɗin wannan magana? sannan ko da ace da auren miye amfanin hakan?? Dan Allah Nuudaa miye haka kika aikata mana kika aikatawa kan ki??"
A hankali Baba ya miƙe ya kalli Yah Huzaifa calmly ya ce.
" Huzaifa gobe kai zaka tsaya tare da ni a nan, Saifuddeen kuma su tafi tare da Baban ku da Alhaji Amadu gidan Alhaji Ma'aji"
"Alƙali wai ba ka ji miye ya ke faruwa ba ka ke wani zance na daban??"
Cewar Baba Usman yana kallon Baba cike da mamakin sa.
Master bedroom ɗinsa ya nufa ya ɗauki kayan buƙatar sa ya wuce ya ɗauki motar sa ya nufi gidan Mama Ruke.
Ganin haka shima Baba Usman ya miƙe yana faɗin.
" To, yanxu abinda za'a yi mu bar wannan zancen xuwa jibi mu gani a samu a gama da al'amarin ɗaurin auren gobe, idan aka sallami komawa zuwa Monday sai a sake zama a tattauna domin a san mafita"
A hankali suka shiga tsiyayewa daga parlourn kowa rai babu daɗi, cikin mintina ƙalilan kowa ya watse ya rage parlourn daga ni sai Mama sai Yah Hadiza.
Itama ganin yanda duk na birkice na gigice ina ta wasu sabbatu kamar mai taɓin ƙwaƙwalwa ina kuka yasa ta kasa jurewa kawai ta miƙe tabi bayan su Aunty Nadee tana kuka ta fice.
Matsawa na ƙara yi wurin ƙafafuwan Mama wanda a yanxu na kasa fahimtar a wanne yana yi ta ke, ita dai ba kuka ta ke ba, kawai dai tayi zurum tana kallon wuri ɗaya tamkar mai cutar mantau.
"Maa.aaammaahhh! Dan Allah Mama ta kiyi haƙuri ki yafe min, wallahi sharrin shaiɗan ne Mama, mun haƙa mun binne mun ɗauka muna da wayo ashe ba mu san cewa akwai ranar tonan asiri irin wannan ba...."
Sai yanxu ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi tashiga girgiza kan ta tana faɗin.
" Nuudaa miyasa? Miyasa kika min haka? Yanxu tukuicin da zaki baku kenan ni da Mahaifin ki da sauran en uwan ki na tsawon shekaru da mukayi muna wahala da ke? "
Miƙewa nayi na sauka akan guiwoyina na tsaya a gabanta da kyau ina sheshsheka na ce.
"Mama ko a mafarkin mu bamu taɓa sa ran cewa ba zamu yi aure ba Mama, mun ɗauka cewa shikenan mun zama abu ɗaya babu wani abu a duniyar nan da ya isa ya farraqa tsakanin mu... Sai ga shi ƙaddara... Ƙaddara ta yi mana abinda bamu zata ba Maaamaahh!"
Ban sa mi Mama ta tuna ba da ya saka ta sa ke fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya tare da girgiza kai tana faɗin.
"InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Kaico na ni Sadiya! Wannan yarinya wannan yarinya baki yi min adalci ba, kin yi min abinda na tabbata shi ne zai zama ajali na. Haba NUUDARR! Ciki! Saboda kawai an sa muku rana shi ne yasa kika je kika sakarwa namiji jiki Nuudaa? Wato iyakar Ubangiji kuka tsallaka hankalin ku kwance kuna tunanin shikenan kunci ɓulus babu wanda ya sani kuma babu wanda zai sa ni har abada kenan? Kun manta cewa ba'a yi wa Allah wayau domin babu wani abinda ya fi ƙarfin mulkin sa, shine mai yadda ya so kuma a lokacin da ya so... "
Hankali na ne ya ƙara tashi jin irin Kalaman da Mama ke furtawa masu matuƙar tasiri da hankaltar da ɓatacce iri na.
" Nuudaa! Haƙiƙa ki sani kin yi min illah kuma kin ci da haƙƙina amma kema ki kwana da sanin cewa ke da farin ciki kun yi hannun riga har abada, idan dai don soyayyar namiji kika yiwa kan ki wannan illar kin aikata kuskure wanda har abada ba zaki taɓa iya mayar da hannun agogo baya ba"
Daga haka ta miƙe ta wuce kawai ta barni nan durƙushe akan ƙafafu na.
*********
Nadeeyah
Tunda ta bar ɗakin ta fita waje babu abinda ta ke idan ba kuka ba, kanta ya yi zafi da cunkushewar da ta ma rasa wane kalar tunanin zata yi. Maza! Hmmm! Haƙiƙa kaso saba'in cikin mata da tanbon namiji za su mutu a rayuwar su, domin ko ita har yau har gobe tana jin ciwo sosai a zuciyarta idan ta tuna da Sabeer, soyayya suka shimfiɗa abinda ake kira soyayya, ita ma da bata bayar da jikinta a waje ba haka ta ƙare cikin baƙin ciki da tarin damuwa da nadama wanda har ila yau tana jin ciwon hakan, ballantana ita da ke waje ta rasa wane kalar rashin hankali ne da rashin wayau har yasa Nuudaa ta yarda ta bawa Emraan jikinta....
Juyawa tayi daga safa da marwar da take ta nufi ɗaki ta ɗauki wayarta ta kamo numbern Emraan ba tare da wani tunani ba ta kira. Kunsan 10miss calls tayi masa amma bai ɗauki kiran ba.
Yah Hadiza da ke ta neman Nadeeyar tun ɗazu sai yanxu ta hango ta jikin window tana ta pressing wayarta tana ƙara neman layin Emraan ɗin.
Ƙarasowa Yah Hadizar tayi ta kalle ta murya a dusashe tsabar tasha kuka tace.
"Nadeeyah wai kina ganin maganar nan da Nuudaa ta faɗa mana anya da gaske ta ke? Ni fa gani nike har yanxu kamar dai tana saka rai ne da auren Emraan ɗin yasa tayi kanta wannan sharrin"
Wasu hawayen Aunty Nadee ta share sannan ta ce.
"Ina fatan haka Yah Hadiza, amma kuma bana tunanin Nuudaa zatayi ƙarya a wannan maganar...."
Ganin sunan Emraan ya bayyana a gaban screen ɗin wayar ta yasa tayi saurin yin picking tare da kai wayar kunnenta ta ce.
"Emraan!"
Da Muryar sa kamar wani ɗan maye ya buɗe baki da ƙyar ya ce.
"Nadee mi ya faru?"
Kai tsaye ta ce.
"Emraan shin kana sa ne da cewa Nuudaa tana ɗauke da cikin ka??"
Daga can ɓangaren Emraan ɗin ya ce.
"Ciki!!???......
OUM AMEER