NUUDARR

13

by @oumameer2671

NUUDARR 🥀🥀

(A 2025 NOVEL)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

AREWABOOKS@AMINATU IBRAHIM

WATTPAD @UMMU-AMIR

AMEENA IBRAHEEM

(OUM AMEER)

PAGE 13

Assalam Alaykum mutanen arziki mutanen kirki mutanena na jahar Zamfara da ma kewaye ina yi muku fatan alheri, Suna na REEDERT SKIN CARE wadda ke zaune a cikin jahar Zamfara Gusau Nigeria.... Ina mai farin cikin tallata muku kayana cikin aminci da kyakkyawar zuciya.......

Shin en uwa Kun dade kuna neman mayukan da zasu gyara muku jiki Baku samu ba???? 😳ina masu fama da sun burn?? ,knuckles?? ,glass?? ,Rashes?? ,spots?? Da sauran su? 😳ina masu qorafin suna shafa mayuka baya karbarsu,???😎ina wadda tayi bleaching ya bata mata fata tanaso fatarta takoma daidai ???🧚🏻‍♀️🧚🏻‍♀️shin kunada labarin REEDERT ORGANIC SKINCARE,dake jahar zamfara kuwa?? to idan baki taba amfani da products dintaba dan Allah ki jaraba kiga ikon Allah cikin qanqanin lokaci fatarki zatayi kyau ta murje tadinga sheqi kamar autar larabawa 👌❤️❤️ munada kaya kamar haka ➡️➡️

Amarya set

Mai jego set

Knuckles and dark spots removal set

Whitening and glow set

Lightening and glow set Etc........

Haka zalika munada supplements masu kyau da qayatarwa kamar haka ➡️➡️➡️

Weight gain supplements

Weight loss supplements

Anti-aging supplements

Whitening supplements

Breast enhancement and enlargement

Hips enlargement.

Reedert Organic skincare tana nan zaune a Gusau Motorgage Area behind masaqa

***,***

Delivery nationwide 🌍🌍🌍

Muna aikawa a duk inda kike cikin faɗin Nigeria da ma kewaye.

Cikin wani irin ƙunar zuciya ya kalli mahaifiyar ta sa ya ce.

"Hajiya ya ki ke so in yi? I can't bear it Wai in ga nuudaar ta shiga duniya ita kaɗai alhali she knows no where to go. Yah Hadiza ce fa ta ke ɗan tafiye tafiye da su da sunan rakiya idan zata wani taron su na manya ko kuma biki, bayan haka babu in da ta sani a duniyar nan ko Saudiyya da suka je tare da Ke ta tafi ita da Fauxa da kuma Halifah kin sani. A nan Gusau aka haife ta a nan ta girma a nan tayi wayo tayi karatun ta bayan haka ba ta san ko ina ba, idan rai ya ɓaci hankali bai kamata ya gushe ba..... "

Cikin gunjin kuka ta katse shi da faɗin.

" Duk na ji Saifuddeen amma dan Allah ka rufa min asiri ka ƙyale yarinyar nan tayi tafiyar ta in sha Allahu za ta dace da hannu na gari. Ga Halifah nan da yake uwa ɗaya uba ɗaya da ita bai tafi ya bi ta ba sai kai Saifuddeen? Haba Saifuddeen......."

Juyawa yayi kawai ya nufi ƙofar shima.

Kallon Mama tayi cikin zafin zuciya tana faɗin.

" Wai Hajiya Sadiya ba ki ga abinda ɗana ya ke shirin aikatawa ba? Ke 'ƴa 'ƴa biyu ki ke da maza ni kuma shi kaɗai ne namiji a gare ni don Allah don girman Allah ki yi min rai ki faɗa masa dan Allah ya dawo"

Ta ƙarashe maganar tana mai harɗe tafukan hannaye ta wuri ɗaya alamar roƙo tare da rausayar da kanta gefe ɗaya tana mai ci gaba da kuka.

Girgiza kai Mama ta ke ta yi tun ɗazu tana darzar kuka tsabar abin da ya ke ciciyar zuciyar ta yafi ƙarfin magana, daga ƙarshe ta buɗe bakin ta cikin kuka tace.

"Saifuddeen! Dan Allah idan har na isa da kai to ka ƙyale Nuudaa tayi tafiyar ta, duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ke yiwa duka..."

Juyawa ya yi ya kalli Mama da kyau sannan ya girgiza kai ya nuna Baba da yatsa ya ce.

"Ku faɗawa mijin ku ya dakatar da Nuudaar da fita daga cikin gidan nan idan ba haka ba babu abinda zai sa na bar er uwata ta tafi ba tare da ta san ina ta nufa ba"

Kowa kallon sa ya mayar gun Baba suna jira su ji kalmar yafiya a gare shi, sai dai inaaa! Bakin alƙalami ya riga ya bushe domin Baba ko alamar motsa bakin sa bai yi ba balle har su ji kalmar haƙuri daga bakin sa.

Daga haka Yah Saif ya fito cikin tsantsar baƙin ciki da takaici, fuskar nan tasa tamkar an yi masa wahayin mutuwa, ni kaina da na kalli yanayin fuskar sa sai da ya sa hantar cikina kaɗawa ganin irin yanda idanuwansa suka kaɗa suka ri ne tamkar jan gauta jijiyon gaban kansa duk sun hihhirɗo tsabar tashin hankali.

Hannu na ya damƙa da ƙarfin tsiya ya soma Ja na tamkar dabba mai taurin kai da uban gidan ta.

"InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Kai Emraan ka riga ka haɗa mu da carɓin ƙwai mai wuyar ja a gare mu. Allah mun tuba! Allah ka dube mu da idon rahama ka tausaya mana ka yi mana mafita ta alheri a cikin wannan al'amari Yah Allah...."

Cewar Yah Hadiza tana mai zubewa a ƙasa rai na yi mata wata irin tafarfasa da ƙuna akan wannan al'amari.

Itama Mama Ruke faɗuwa tayi ƙasa taci gaba da kuka tamkar ranta zai fita daga ruhin jikin ta.

Wucewa kawai Baba ya yi ya shige ɗakin sa, ganin haka yasa kowa ya sulale ya fice suna masu alhini da matuƙar jimami a wannan al'amari.

Mama Ruke ma bata haƙura ba ganin da gaske Saif ɗin ya tafi bai dawo ba yasa tayi waje ko takalmi babu a ƙafar ta tana dube dube ko Allah zai sa ta gansa.

********

Emraan

Tunda ya yi receiving kiran Nadeeyah ya ƙara shiga tashin hankali musamman da ta yanke wayar ba tare da ta gama jin zantukan sa ba.

Ganin ya yi ta kiran wayar ta bata ɗauka ba yasa shi ƙara haukacewa ya yo waje yana kiran Sunan Daddy da Mommy.

Daman su ma ba su shiga baccin ba suna nan sunyi cirko cirko suna tattaunawa domin ganin yanda Emraan ya birkice ba ƙaramin ɗaga musu hankali yayi ba musamman hajiya Akki.

"Daddy Mu koma gidan su Nuudaar pls akwai abinda ni ke so kowa ya sani mai matuƙar muhimmanci"

Kallon agogon wayarsa daddyn yayi yaga ƙarfe ɗaya na dare hakan yasa ya girgiza kai ya ce.

"Emraan dare yayi ka bari sai gobe idan Allah ya kai muna rai..."

Hannun sa ya riƙe cikin nasa yana masa magiya yana faɗin.

"Abin is urgent pls, ba zan iya bari gari ya waye ba, dan Allah kuxo mu tafi akwai matsala..."

Hawaye Hajiya Akki ta share ta ce.

"Haba Emraan! Kayi haƙuri mana, yanxu ina zamu nufa cikin daren nan uhm? Ka yi haƙuri ko ma miye shi ka bar shi sai gobe da safe..."

"Hajiya za su cutar da Nuudaa idan ban je ba,..."

"Babu abinda zai faru da ita in sha Allahu, zata kasance cikin aminci. Oh ni Jamila na shiga uku in dai ƙwaƙwalwar Yaron nan ba taɓuwa da tayi ba"

Girgixa kai Daddy yayi cikin alhini ya ce.

"In sha Allah babu abinda zai same sa da an kwana biyu komai zai daidai ta da yardar ubangiji"

Da ƙyar suka samu suka lallaɓashi ya bar zancen har gari ya waye.

Da safe ma tun asuba ya so su tafi Alhaji Mashfiq ya ce ya dai bari gari ya iyarda wayewa tukun.

Wuraren 7am Alhaji Mashfiq ƴa kira Baba Usman ya ce masa Emraan ta ce yana da magana da su dan Allah su haɗu gidan Alƙali Musayyib zuwa ƙarfe takwas.

Shi kuma Baba Usman jin wannan maganar yasa shi farin ciki a tunanin sa Emraan ya amince ya auri ɗaya daga cikin en uwan Nuudaara ɗin, shi yasa sai da ya gama shirin sa tsab na zuwa ɗaurin auren sannan ya fito daga gida ya kira wayar Alhaji Mashfiq wuraren tara da rabi na safen.

Kusan lokaci ɗaya suka isa gidan domin Emraan ba ƙaramin uzzurawa rayuwar su ya yi ba.

Suna shiga suka tarar da Baba zaune a parlour shi kaɗai ya jingina bayan sa da jikin kujerar da ya ke zaune yayin da idanuwansa suke a rufe kamar mai bacci.

"Alhaji Lafiya kuwa? Ko kai ma abin ne har yanxu bai sake ka ba ko? Dole a ɗau haƙuri domin komai na Allah ne,Allah dai yasa hakan shi ne mafi alheri"

A hankali ya buɗe idon sa yana mai ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya. Hannu alhaji Mashfiq ya ba shi ba musu ya karɓa suka gai sa.

"Wallahi Emraan ne tun jiya ya birkice mana wai dole sai munxo gaba ɗayan mu akwai abinda ya ke son sanar ma baki ɗaya"

In ban da ido babu abinda Baba ya ke bin sa da su. Wayar Mama Baba Usman ya kira ganin Baba bai da niyyar ta shi ko kuma ya ɗaukar waya da sunan kira, wanda duk yana ganin hakan akan damuwar Nuudaar ce ta ke bugun sa.

Daman babu mai kuzarin ɓarka ta wani abin arziki a wannan lokacin tunda suka bar parlourn a ɗazu kowa na can ya samu wuri ya nutsu yana jimami, shiyasa ko yanxu ba'a ɗauki lokaci ba sai ga su sun bayyana kowa da addu'ar Allah yasa Baba ne ya yafe Nuudaar ta dawo gida.

Ganin Emraan yasa su ka ji wani irin abu a zuciyar su tamkar su shaƙe sa ya mutu ba ma kamar Halifah da Yah Hadiza.

Mama a irin kallon da ya ga tana yi masa yasan cewa ba zata taɓa yafe masa ba amma shi duk hakan bai dame sa ba matuƙar za su haƙura su aura masa masoyiyar a haka sun biya sa...

"Miye ka xo ka faɗa mana Emraan???"

Tambayar da Mama ta jefa masa kenan tare da kafe sa da idanuwanta tana jira taji da wace rashin kunyar yaxo.

Cike da karyewar zuciya ya ce.

"Cikin da ke Jikin Nuudaar na wa ne Mama, ciki na ne na san da shi, kuma duk da hakan ban yi nufin juya mata baya ba wallahi ina ta sonta ina tsananin ƙaunarta ita da abinda ke cikin ta, dan Allah ko don wannan ku tausaya mana ku bar mu muyi aure dan Allah... "

Alhaji Mashfiq, Hajiya Akki da Baba Usman rige-rigen miƙewa tsaye suka yi jin wani zance mai hautsina ƙwaƙwalwa da lalata ma ta sai ti......

OUM AMEER