AMATURRAHAMAN

19

by @oumfatima33

💞💞💞💞💞💞💞💞

AMATURRAHAMAN

*By*

OUM FATIMA

*(Hakimar D. A. W. A)*

💞💞💞💞💞💞💞💞

*DASHEN🌲ALLAH*

*WRITER'S📚ASSOCIATION*

*TEAM*

*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*

BOOK 1

PAGE 19

*بسم الله الر حمن الر حيم*

A matuƙar fusace Amaturrahaman ta shiga ɗakinsu ta nemi wuri ta zauna ko ta kan abincin da take ci bata ƙara biba sai faman sauke numfashi take. "Meya faru?." Ya Nafi ta tambaye ta.

"Nayi masa gargaɗi ne idan har ƙwaƙwalwarsa na aiki yanda ya kamata bana jin zai ƙara zuwa inda nake."

"Kina bani tsoro wasu lokutan Amah." Ya Nafi ta faɗa tana kallon ta ganin yanda gaba ɗaya ta sauya.

"In daina baki tsoro Ya Nafi, Amaturrahaman ɗinki ce dai ƙanwarki da kika raina da hannunki."

"Na sani Amah, kawai yanayin fusatarki da kalamanki a wasu lokutan suke ɗaure min kai, don rasa inda suka dosa nake, gani nake kamar sun girmi shekarunki."

"Ba wani abu bane, kin san kowa da yanda Allah yake halittarsa da yanayin da yake gudanar da rayuwarsa."

"Haka ne kuma." Ya Nafi ta faɗa, daga haka suka shiga taɓa hira na tunawa da Iyayensu. "Wai shikenan dangin Baban su Umma sun manta da ita, tunda ya rasu suka zo suka raba gadonsa suka tafi ba ɗaya daga cikinsu da ya wai-wayi ƴarsa ƙwaya ɗaya daya bari!." Ya Nafi ce mai maganar cikin jimami.

"Ki manta da duk wasu dangin Umma ya Nafi, ki saka a ranta baki da wasu dangi sai ni kaɗai mun ishi kanmu zamu rayu ko ba su." Amaturrahaman ta faɗa da wani irin emotions a cikin muryarta.

"Amma Amah abin da ciwo ace muna da dangi na Uwa da Uba amma muke irin wannan rayuwar marar ma'ana, ki dubi irin halin da nake ciki ki duba abinda Kawu Isa ke shirin aikatawa taki rayuwar k...".

"Dan Allah ki manta da abinda ya faru, kamata yayi mu fuskanci rayuwar da zata riske mu a gaba." Amaturrahaman ta faɗa fuskarta ba walwala ko kaɗan sai tarin damuwar data bayyana a samanta. Shiru Ya Nafi tayi tana kallon yanayin Amaturrahaman tana karantarta. Abinda Umma ta taɓa faɗa mata ke dawo mata cikin zuciyata.

"Ƙarama ce amma tana da zurfin tunani, tana da haƙuri sosai akan al'amura ba komai take maida hankali a kansa ba amma tana da zafin zuciya idan ta fusata, kece babba a kanta shekara shida ke tsakanin ku amma tunaninta ya zarta naki, ki kula da ita sosai ki kuma karɓi gyara ko shawara idan ta baki ko bana raye zaki ga amfanin hakan, sannan ki kula da abinda zai tado zafin zuciyarta don in ta fusata ba lallai bane abinda zata yi ya iya zama mai sauƙi ba."

Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da tazo nan a tunaninta, sai a yanzu take ƙara tabbatar da kalaman Mahaifiyarsu akan ƙanwarta, musamman yanzu da take girma tana ƙara hankali da kuma irin ƙaddarorin dake fuskantar rayuwarsu a kullum suna ƙara bada gudummawa wurin ƙara dakewar da zuciyarta keyi.

Firgita tayi lokacin da Amaturrahaman ta kaɗa yaysunta biyu a saman fuskarta. "Lafiya Ya Nafi kike kallona haka kina tunanani tamkar an sauya maki ni?."

Ajiyar zuciya ta kuma saukewa tace "Tunanin rayuwa nake Amah, Bari kiga in tashi in shirya da inda zanje." Ta ƙarasa tana miƙewa. Wari irin kallon tuhuma Amaturrahaman tabi Yayarta da shi amma tayi kamar bata gani ba tayi gaba abinta ba tare da ta yarda sun haɗa ido ba don ta san data tsareta da waɗannan idanun nata zata karya mata zuciya ta fasa fitar bayan kuma fitar nada muhimmanci don zuwa zata yi suyi wacce zasu yi da Gaddafi akan kuɗinta da su Zakiyya suka kwashe lokacin da suka dake ta, tayi rantsuwar ko biyar bazata yi asara ba sai ya biyata don mutumin da suka yi maganar cikin gida da shi yace idan bata shirya ba zai sayar da gidansa.

Shirya wa tayi ta fice abinta Amaturrahaman na kallonta har ta ɓacewa ganinta, zamewa tayi ta kwanta ta faɗa tunanin rayuwa da tarin abubuwa data shirya aikatawa. Hutun nan da za'a yi musu a Makaranta suna komawa zasu shiga aji shida wanda shekara ɗaya kenan ya rage mata ta kammala ta shiga jami'a ta fara karatunta wanda ta ɗora ko wane hope ɗinta a kansa.

Da farko so take tayi karatu mai zurfi ta tsaya da ƙafafunta wanda hakan zai bata damar gudanar da duk wani plans ɗin da take da shi, wannan dalilin ne yasa ko kaɗan bata wasa da karatunta. Da waɗannan tarin tunanukan bacci yayi awon gaba da ita wanda bata tashi farkawaba har sai da Ya Nafi ta dawo ta zube iyayen kuɗi a ƙasa ta tashe ta...

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

Doctor Farhan kuwa tunda ya koma gida magan-ganun data faɗa masa suke tsaye a ransa yana ƙoƙarin warware ma'anarsu amma ya kasa, me take nufi da sunansa ya shiga cikin baƙin littafinta? Dama tana da wani baƙin littafi data ware take rubuta sunan wasu mutane don ta musu hukunci? To ma wane irin hukunci, kuma sannan su waye suka cutar da su? Wace irin cutarwa aka yi musu kuma?, shifa gaba ɗaya yarinyar mamaki take bashi maganganunta nada matuƙar ɗaure kai. Shi dai a iya bayanan daya samu a game dasu ya san cewar marayune Mahaifinsu ya rasu sakamakon cuta ƙanjamau haka Mahaifiyarsu ma, sannan suna fuskantar tsangwamar mutane tun Mahaifiyarsu nada rai.

Basu da kowa a halin yanzu sai ƴan'uwan Mahaifinsu da suka kasa riƙe su sai kuma Yayarta da aka ce karuwanci ta maida sana'ar yinta wanda hakan ba ƙaramin mamaki ya bashi ba sabo da abinda ya faru a tsakaninsu lokacin daya buƙaci hakan daga gare ta. Kiran daya shigo wayarsa ne yasa shi dawowa daga nisan da yayi a tunani. "Barka da yamma Dady." Ya faɗa cikin girmamawa, shiru yayi yana sauraren abinda ake faɗa masa daga ɗayan ɓangaren kafin yace "Ok ganin nan zuwa."

Yana aje wayar ya shige bathroom ɗinsa ya sakar ma kansa ruwa, wanka yayi ya fito yana shirya wa a gaggauce sabo da kiran da Dady ya masa. Yana ƙoƙarin fita ne Matarsa Suhaima ta shigo tana cewa. "Abban Jalila yaushe ka shigo ban sani ba kuma har zaka fita?." Ta masa tambayar xuskarta da damuwa.

"Bana jin daɗi ne lokacin dana shigo yanzu kuma zan amsa kiran Dady ne." Ya faɗa yana ƙoƙarin wucewa.

"Baka yi lunch ɗinka ba fa."

"Zan yi a wurin Hajiya, sauri nake Please." Yana gama faɗa yayi wucewarsa ba tare daya ƙara bata wata damar ba. Zama tayi daɓas a saman gadonsa tana jin kamar ta fashe da kuka, ta rasa sai yaushe ne Farhan zai juyo ya fuskance ta? Ta rasa yaushe ne zai amsheta a matsayin cikakkiyar Matarsa? Har yanzu da suke da yara biyu ya kasa bata cikakkiyar damar da zasu sake da juna suyi rayuwa tamkar ko wane ma'aurata.

Auren zumunci akayi musu ita da shi da Mamanta da Babansu Doctor Farhan Uwa ɗaya Uba ɗaya suke, halinsa na shegen neman mata yasa Iyayensa suka yanke hukuncin yi masa aure tun bai kammala karatunsa ba. An bashi dama ya fitar da wacce yake so a aura masa amma yaƙiya shine suka yanke hukuncin haɗa shi da Suhaima dake tsananin sonsa.

Koda aka faɗa masa za'a haɗa su ya nuna bai shirya ba Babansu yace bai isa ba, dole ya amince aka sa musu rana. Suhaima tayi matuƙar farin ciki da wannan haɗin don haka take ta rawar kai don ma bata samun fuska sosai a wurin angon.

Bayan bikinsu ma bata canza zani ba don haka suke rayuwwar ba wata ma'ana don duk yanda taso ta samun kusanci dashi baya bata damar hakan dole take haƙuri dashi a yanda yake so. Rayuwa suke baya nuna mata wata soyayya ko kulawa sai dai idan buƙatarsa ta taso masa yazo ya sauke babu wata kulawa. Maganar mu'amalarsa da ƴammata ba abinda ya fasa har Allah ya basu rabon ɗansu na farko mai suna Suhaib.

Bayan haihuwar Suhaib ne zaman nasu ya ɗan sauya salo suka fara mua'amalantar juna ya ɗan fara sake mata fuska sabo da yana matuƙar son yaron. Wannan damar data samu ita ta riƙe gam take amfani da ita wurin ganin sun ɗan samu shaƙuwa da juna, ba laifi abubuwa sun yi sauƙi a tsakaninsu har ta haifi ƴarta ta biyu Manal rayuwar dai tsakaninsu kada ran kada han ce, in yaso yazo mata da fuskar sauƙi in yaso ko fara'arsa bayta gani.

Ajiyar zuciya ta sauke ta tashi ta fice daga ɗakin ta nufi kiching don duba aikin data ba mai aikinta.

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

Zaune yake gaban Mahaifiyarsa tana masa addu'a yana amsa wa, ya gama shirinsa tsaf zai koma bakin aikinsa don haka ya shigo yi mata sallama, doguwar addu'a tayi masa kamar yanda ta saba duk sanda zai koma bakin aikinsa. Sai da ta gama tsaf ya miƙe yana godiya kafin yace "Zan wuce Ammah ki kula da kanki."

"Allah ya tsare ya bada Sa'a, ya kare ka a duk inda kake, ka kula sosai da addu'a da yin azkar Yayansu in sha Allah ba abinda zai sameka sai abinda Allah ya ƙaddara maka."

"In sha Allah." Ya bata amsa suka fice shida Muzaffar da Haneen da zasu masa rakiya inda Motocinsa suke. Har yanzu Abba bai dawo ba don haka ɓangaren Baba Alhaji kaɗai ya shiga ya musu sallama suka wuce cike da kewar juna, Uncle Maina da sauran Uncles ɗinsa duk ya musu sallama da suka haɗu a masallaci da Asuba.

Motocinsa da aka fitar aka wanke ƙal sai sheƙi suke Samuel ya buɗe masa ya shiga ya zauna, ɗago kansa yayi zai yiwa Haneen magana ya hangota a laɓe tana leƙensa tana share hawaye. Tana ƙara leƙowa suka haɗa ido da sauri ta koma inda ta fito tana jin tamkar zuciyarta ce zata tafi ta barta. Anisa ce wacce tunda taji labarin komawarsa a bakin Haneen take cikin damuwa, Momynta tace ta kwantar da hankalinta ta gama saita komai amma har gashi zai koma bata ji wata magana daga wurin iyayensu ba.

Baki ya taɓe yana mamakin yaran a ransa, sallama ya ƙara yi da ƙannensa ya ƙara ja musu kunne akan su kula kafin aka ja Motocin suka fara tafiya saman kwaltar da zata kaisu ƙofa.

"Allah yasa kayi hatsari ka mutu a hanya kowa a ya huta, aikin banza shine har zaka saka a yiwa abokanaina dukan tsiya dan sun shana abinsu, ance maka kowa irinka ne marar shauƙi saƙagon banza!." Salim dake kallon fitowarsa har shigarsa Mota ne ya furta hakan yana zaro karan Cigarette ya kunna mata wuta ya fara zuƙa.

Sai da ya shanye ta ya take guntun kafin ya nufi sashsen Mahaifiyarsa.

*****Dawowarta kenan daga Makaranta ta samu labarin tafiyarsa a bakin Fatima, ji tayi kamar tayi ta zabga ihu don yau a shirye tsaf ta dawo da shirin tunkararsa duk ma wacce za'a yi ayi, don haƙurinta ya gama ƙarewa shi kuma taga bashi da alamar rusuna.

Waya ta ɗauka ta kira ƙawarta tana kuka tace "Huda komai fa ya ɓaci, gaba ɗaya shirin mu ya lalace don Ya Zayyad ya koma!." Ta faɗa cikin kuka da takaicin asarar wannan damar da tayi.

"Kina jina ko? ki kwantar da hankalinki in kin rasa wannan damar zaki samu wata, kuma zaki yi nasara." Huda ta faɗa cikin sigar kwantar mata da hankali.

"Shike nan, sai mun haɗu gobe."

"Ok kar fa ki damu." Ta kuma faɗa mata kafin suka kashe wayar.

"Allah ya fitar dake daga wannan kogin wahalar da kika faɗa." Fatima ce da taji komai da suka tattauna ta faɗa tana juyawa ta fice daga ɗakin.

🪸🪸🪸🪸🪸🪸🪸🪸

"Ke tashi ki tayani lissafi." Ya Nafi ta faɗa tana bubbuga ƙafar Amaturrahaman dake baccinta hankali kwance "Wane irin lissafi kuma Ya Naf..." Kasa ƙarasa tambayar tayi ganin uban kuɗi zube a ƙasa tamkar takarda.

"Wannan kuɗin fa, a ina kika samo su?." Amaturrahaman ta tambaya tana zaro ido.

"Cewa nayi ki taya ni lissafi zan yi maki bayani daga baya." Ba don taso ba tayi shiru suka fara girga kuɗin bandir ɗin dubu ɗari-ɗari ne miliyan ɗaya da dubu dari biyar."

"Kuɗin waye kika ɗauko Ya Nafi?" Amaturrahaman ta kuma tambayarta a dake tamkar ita ce Yayar.

"Na wan can sakaran ne kuma na rantse da Allah sun shigo kenan ba zasu fita ba." Ya Nafi ta faɗa tana haɗe kan kuɗin a wata ƴar jaka data zubo kuɗin a ciki.

"Kina nufin Gaddafi?, wai miye tsakanin ki da guy ɗin can?." Ta kuma ƙara jefo mata tambayar a karo na biyu.

"Ki manta kawai Amah alaƙa ce ta son zuciya, kowa biyan buƙatarsa yake samu."

"Ki tattara kuɗinsa ki mayar masa dan ba za'a zo a ɗaga mana hankali ba muna zaman lafiyarmu ba." Rikici ne yaso ɓallewa a tsakaninsu Amaturrahaman ta kafe akan sai Ya Nafi ta mayar da kuɗin nan itama ta kafe akan ba zata mayar ba. Ganin Amaturrahaman ta warci jakar zata fice yasa Ya Nafi riƙo hannunta tace "Kar ki mayar masa Amah har yanzu banji na karɓi kuɗi adadin mutunci da kimata wanda Gaddafi ya ƙwace su da ƙarfin tsiya ba. Alƙawari na ɗauka akan sai na karar da duk wani abu da Gaddafi yake gadara dasu, so nake in tsiyata su daga shi har Uban nasa daya ɗaure masa ƙugun yin rashin mutunci da aikata zalinci ga na ƙasa dasu."

"Me kike son cewa." Amaturrahaman ta mata tambayar murnarta da wani irin ɓacin rai. Sanar da ita tayi duk abinda ya faru ranar da suka kai Ummansu Asibiti da dalilin da yasa taje neman taimako wurin Mahaifiyarsa wanda a can ne suka sace ta suka mata fyaɗe ta ƙarfin tsiya ya kuma yi mata barazana akan kar ta tona masa asiri bayan ya jefeta da kuɗin da ta yini neman taimako.....

Kuyi following ɗin account ɗina a Arewa Books@ Oumfatim33 don samun sabbin pages