AMATURRAHAMAN

20

by @oumfatima33

💞💞💞💞💞💞💞💞

AMATURRAHAMAN

*By*

OUM FATIMA

*(Hakimar D. A. W. A)*

💞💞💞💞💞💞💞💞

*DASHEN🌲ALLAH*

*WRITER'S📚ASSOCIATION*

*TEAM*

*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*

BOOK 1

PAGE 20

*بسم الله الر حمن الر حيم*

"Kina nufin a waccen ranar Gaddafi ne ya aikata maki wannan zaluncin amma shine kika ƙara mallaka masa kanki da yardar ki da amincewarki, me yasa kika yi wannan tuanain Ya Nafi ribar me zakici da kika yi hakan?. Ta ƙarasa hawayen takaici na zubo mata.

"Sabo da shi ya fara kuma shi zai ƙarasa amma ba zai ci banza ba, kamar yanda ya min barazana da rayuwata a wancan lokacin naji ba zan iya sanar da kowa cewar shine ya aikata min ba, duk da dama ko bai min barazanar ba bani da wani gatan da za'a bi min haƙƙi na bani da wanda zai tsaya min, wanda zai tsaya min ɗin baya raye kuma ko yana raye bashi da hujjar da zai yi hakan sabo da abinda yake yiwa ƴa-ƴan wasu ne aka yi tasa ƴar. Alƙawarin Allah ne cewar duk wanda ya taɓa ƴar wani ko Marar wani shima za'a taɓa nasa, Umma ta rasu ta bar mu babu wani mai jin ƙan daya jamu a jiki ya tallafi rayuwarmu, Aunty Rakiya ce kaɗai mai zuciyar tausayi a gidan nan da take iya taimaka mana da lomar abinci, itama a ƙarƙashin wani take wanda Kawune shi a garemu amma ya shata layi tsananin mu yayi rantsuwar bai yafe mata ba idan ta ƙara shiga harkarmu, shin laifin me muka aikata musu? Kawai dan Mahaifinmu ya kasance ɗan Uba a garesu? Ko don ɗabi'unsa da bamu da masaniyar sanda yake aikata abinsa?. Bamu da dangin Uwa, na Uban sun watsar damu basu barmu haka ba sai da suka gama ɓata mana suna a wurin ƴan unguwa har ya zamana bamu isa mun shiga cikin jama'a ba sai zagi, gori akan ƙaddarar da bamu muka zaɓawa kanmuba, bamu isa kuma mun sauyata daga yanda Ubangiji ya tsara mana ba, kar ki manta da irin ƙyamar da ake nuna mana tamkar muna cutar ce a jikinmu, a gidan nan ko kwano muka taɓa basa amfani da shi wai don kar su shafi ciwo. Ya kike so inyi? So kike na zauna bamu da cin yau bare na gobe, bamu da sisin da zamu sayi magani idan bamu da lafiya babu suturar arziƙi, babu sabulun wanka bare na wanki, so kike na zauna har mu mutu mubi Iyayenmu inda suk..."

Kuka ne yaci ƙarfinta ta kasa ƙarasa maganar sai da tayi mai isarta sannan taci gaba da cewa "Bani da wani zaɓi ne Amaturrahaman dole na karɓi sana'ar da Babanmu ya bar mana gadonta ko don mu samu muci gaba da rayuwa, wannan dalilin ne yasa na koma ma wanda ya fara domin ya ƙarasa, amma kuma ba zan bar shi ba har sai na tabbatar dana saka shi a ukkun da bazai taɓa fita ba, ina roƙon ki da kada ki shiga rigimar da zata ɓalle tsakani na da Gaddafi domin a halin yanzu na riga dana ƙuna ba abinda ya isa ya min domin ina da makamin yaƙarsa a hannu na." Ta ƙarasa maganar tana nuna mata wani memory card dake cikin kwamson sa."

"Meye wannan ɗin? Meye a ciki? Kada fa kice zaki saka rayuwarki a cikin haɗari Ya Nafi, ina jiran lokaci ne wanda zan yiwa duk wanda keda hannu a cikin ƙuntata rayuwarmu hukunci amma ba yanzu ba da bani da wani karfin yin hakan ba, ki rufa min Asiri ke kaɗai gareni,." Amah ta faɗa.

"Ki maida hankali kiyi karatunki na maki alƙawarin biya maki kiyi duk irin karatun da kike son yi ko me zan sadaukar a kanki zan yi hakan matuƙar burinki zai cika rayuwarki tayi kyau don kece dalilin ci gaba da rayuwata, a wancan lokacin dana rasa Abba da Umma da kuma mutuncin da.Umma ke fargabar kar na rasa shi ako da yaushe, a ace babu ke to dana kashe kaina na huta da ƙuncin dana shanye a cikin zuciyata, abu ɗaya nake neman alfarmar kiyi min shi."

"Menene shi?!." Ta tambayeta muryarta na rawa alamun kukan dake shirin ƙwace mata.

"So nake duk rintsi duk wuya, duk inda rayuwa zata kai ki ki kula da kanki ki riƙe mutuncinki, kada ki bari wani yanayin rayuwa yasa kibi layin da muka bi nida Babanmu, yafiye maki ki rasa ranki wurin kare mutuncinki ko hakan zai sa Ummanmu ta ɗanji sauƙin zuciyarta!."

Rungume ta Amaturrahaman tayi suka shiga rusa kuka irin wanda suka daɗe basu yi ba, har suka yi kukansu suka gaji babu wanda ya leƙo ya duba me ya same su. Wanna ita ce irin rayuwar da suke yi a cikin gidan babu wanda ya damu da su, su mutu ko suyi rai amma shine Kawu Isa yake da ƙwarin gwiwar aurar da Amaturrahaman ga wanda bata so sabo da biyan buƙatar kansa.

Wuri ta samu mai kyau ta ɓoye memory card ɗin da kuma kuɗaɗen, wayarta ta zaro ta kira wanda zata sayi gida a wurinsa ya faɗa mata inda zasu haɗu.

Bayan fitar Ya Nafi Amaturrahaman ta daɗe a kwance tana saƙa da war-wara kafin ta tashi ta kunna ƙaramin gas cooker ɗin da Ya Nafi ta saya musu ta ɗaura musu girkin rana, sai da ta kammala tayi wanka ta zauna tana duba littattafan ta na makaranta. Haka kawai yau Ƙaton Sojan nan ɗaya taɗeta ta faɗi yake faɗo mata a rai, tsoki tayi a fili tace "Baƙin mugu idona idonka sai na rama don baka ci bulus ba." Tashi tayi ta zuba abincinta taci ganin shiru Ya Nafi bata dawo ba.

Hijabinta ta saka ta fito ta kulle ɗakin ta tafi gidan su ƙawarta Salma zata amso littafin ta data ara mata zata kwafi note, a hanyarta ta zuwa gidanne ta haɗu da Gaddafi ya taho a fusace har ya kusa takata da mota sai da tayi saurin kaucewa ya taka wani mugun birki ya fito. Wani irin zalamammen kallo yake binta da shi yana cije baki ganin irin hallitar da Allah ya aje, fusatattun idanunta ta watsa masa ganin rashin mutuncin daya mata na ƙoƙarin takata da Mota sannan ya tsaya yana ƙare mata kallo na rashin ɗa'a. Ji yayi zuciyarsa ta motsa da kallon data masan kwarjininta na mamaye sa, jarumtarsa ya aro ya ɗora saman fuskarsa sabo da abinda ke gabansa bashi da lokacin wasa matuƙar ba gani yayi ya amshi memory card ɗin dake hannun yarinyar can ba.

Ta matuƙar shammatarsa ba kaɗan ba, koda ta zo ta kawo masa kanta bai yi zaton da wata manufar tazo ba, wai ma tayaya, yaushe hakan ya faru bai sani ba.

"Ina matsiyaciyar Yayarki take?." Gaddafi ya faɗa yana zaro mata ido wai ko zata daina masa wannan kallon da waɗannan idanun nata masu shegen kyau da kwarjinin tsiya.

"A kwai matsiyacin daya wuceka sha-sha-sha ɗannakuya mara mutunci." Ta faɗa masa a matuƙar harzuƙe tana jin tamkar ta shaƙe wuyansa har sai ya daina numfashi tsabar yanda take jin tsanarsa.

"Kan uban can, ke ni keke zagi?." Ya faɗa da tsananin mamaki.

Wani shegen kallo ta jefa masa mai nufin baka isa na baka amsa ba, hannu ya ɗaga zai mareta aka riƙe hannun. A fusace ya juyo don ganin wanda ya riƙe masa hannu. Doctor Farhan ne ya riƙe hannun yana masa kallon gargaɗi.

"Sakar min hannu!." Ya faɗa yana huci. Yarfar masa da hannun yayi ya fuskance shi da kyau yace "Kada ka kuskura kace zaka zaka taɓata ko a mafarkin ka domin ita ɗin mallakina ce."

Rikici yaso ɓallewa a tsakaninsu tuni Gaddafi ya fara ɗaga murya yana faɗin "Kai ka san ko ni waye da zaka shiga harkata? Ni zaka takala da rigima?, zan maka rashin mutuncin da zaka yi nadamar shiga harkata da kayi.

"Who are you?." Doctor Farhan ya faɗa yana cin kwalar Gaddafi. Ƙoƙarin kai masa duka Gaddafi yayi ganin hakan da Doctor Farhan yayi ya masa duka ɗaya ƙwaƙwƙwara wanda ya zube ƙasa ba tare daya shirya ba. Ganin mutane sun fara taruwa yasa Doctor Farhan shiga Motarsa ya tafi bayan ya duba bai ga ko me kama da Amaturrahaman a wurin ba.

Amaturrahaman kuwa tun da suka fara rigimarsu ta bar wajen zuciyarta cike da takaicin abinda wan can sakaran yayi mata. Ta tsane su gaba ɗayansu shida Doctor Farhan ɗin don kome ya samu Yayarta sune sila, da ace Doctor Farhan ya taimaka mata sabo da Allah da bata kai kanta gidan su wancan ƙazamin ba har ya samu damar yi mata abinda yayi mata.

Fasa zuwa inda tayi biyar zuwan tayi ta nufi gida mutane sai kallonta suke suna ƙus-ƙus ɗin gulmar abin da ya faru, bata bi ta kan kowa ba ta shige gida ta nemi wuri ta kwanta.

Ya Nafi bata dawo gidan ba sai da dare tana jin sanda ta shigo Sule ya tareta da gadara yana faɗa mata cewar idan ta ƙara dawo musu gida a irin wannan lokacin sai dai ta kwana a waje, sai kace shi ɗin ba dawowar tasa kenan ba. Biye masa tayi suka fara ɗaga murya har Kawu Isa ya fito yaci mata mutunci yayi rantsuwar korarta a gidan idan bata yi wasa ba.

"Babu wanda ya isa ya koreni a gidan nan sabo da Ubana yana da gado a cikinsa, na rantse da Allah idan aka takura min zan maka mutum kotu a ƙwatar mana haƙƙinmu." Ya Nafi ta faɗa cike da rashin kunya tana jin abin nasu yayi yawa turar ta kai bangon daya kamata ta fara maida martani.

"Mu zaki kai kotu Nafisa? Eh lallai abin naki gaba yake ƙara yi na lura, to ko Mukhtar ya dawo duniya bai isa ya hana ni tattaka ki ba yau a gidan nan." Yana rufe baki ya warci icce ya shiga dukanta. Ganin bazata iya bari ya daketa ya daki banza ba don haka ta murɗe hannunsa ta ƙwace iccen har yana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa Sule ya tare shi da sauri.

Bata tsaya jiran komai ba ta ruga sashensu ta kulle ƙofar tana haki, a zaune ta samu Amaturrahaman ta haɗa kai da gwuiwa tana kukan baƙin ciki da takaici. "Kiyi haƙuri Amah." Ya Nafi ta faɗa.

"Wace irin rayuwace wannan Ya Nafi? Shike nan mu haka zamu ci gaba da rayuwar da bata da wata ma'ana tamkar wasu dabbobi kowa ya ɗebo bolarsa a kanmu zai juye, ke kaɗai nake dake a yanzu a matsayin komai na amma kin kasa nutsuwa kiyi abinda ya dace bare ni ki ɗora ni kan hanyar data dace, ki taimake ni ki daina waɗannan yawace-yawacen ki tsayar da miji kiyi aure ko yaya mun samu mutuntawa daga al'umma Ya Nafi na roƙe ki, na maki alƙawarin neman aiki ko wane irine don mu rufawa kanmu asiri."

"Kiyi haƙuri Amah komai zai wuce in sha Allah."

"Sai yaushe zai wuce? Kullum haka kike faɗa, sabo da abinda Abbanmu yayi da abinda kike yi a yanzu yasa wanda ya isa da wanda bai isa ba suke takamu su mana abinda suka ga dama." Ta faɗa cikin zafin zuciya.

"Waye zai aureni Amah? Waye zai aureni a halin da muke ciki, duk fa wanda kika ga yazo wurina ba maganar aure ke kawo shi ba face biyan buƙatar kansa, kema kin san bani da wani gatan da za'a aureni a killace ni sabo da bamu da wanda ya tsaya mana mu muke ikon kanmu sannan sunanmu dana Iyayenmu yayi ƙaurin da ake ƙyamar haɗa zuri'a da mu, bani da wani zaɓin ne akan rayuwar da nake!." Ta ƙare maganar kuka na cin ƙarfinta.

"Ya Nafi bakya ganin ya kamata mu nemi inda Aunty Halima take na san ko me muka zama ita zata amshe mu bazata ta gujemu ba, sabo da ita kaɗai ce wacce suke ciki ɗaya da Abbanmu."

"Ta ina zamu fara neman nata? Kin san dai tun Abbanmu nada rai tazo ta musu sallama akan zasu tafi ƙasar waje ita da mijinta ya samu aiki a can bamu ƙara jin labarin ta ba har Allah ya yiwa Abba da Umma rasuwa, sannan bamu taɓa zuwa gidansu na Katsina ko gidan Iyayen mijinta bare muje mu nemi ko lambar wayar ta ba, to ta ina zamu neme tan?."

"Hakane ne Ya Nafi kuma ma wa ya sani ko tana raye ko ta rasu itama, zaman gidan nan da garin ma gaba ɗaya ya fita a kaina Ya Nafi komai baya min daɗi a nan, ina kammala Makarantar nan zamu bar garin nan muje koma ina ne in da ba'a san asalinmu ba bare a tsangwame mu, Kinga zan yi karatuna cikin kwanciyar hankali kema ki samu Miji kiyi aure ko ki koma Makarantar, amma ko mun tafi sai na dawo domin karɓar haƙkinmu idan lokaci yayi." Amaturrahaman ce mai wannan maganar.

Murmushi kawai ya Nafi tayi tace "Allah ya cika maki burikanki na rayuwa Amah."

"Ameen Ya Nafi kema Allah ya cika maki naki burikan."

"Ni bani da wani buri Amah duka burikana akan ki suke, burina shine rayuwarki ta inganta ki samu kulawa kiyi ingantaccen ilimin da zai zama haske a gareki ko bana raye."

"Kina ma raye ya Nafi, in sha Allah kina raye zaki ga na zama duk abinda kike son na zama, Allah zai dube mu ya kawo mana ɗauki.".....

Manage please