FAD'IME (Dangin Jinnu)

06

by @nkds

*FAƊIME...💋🌸💕*

_(Dangin Jinnu)_

©By Zahrah Royal Star & Nainarh KD

06

Aikuwa mutumin da Zulay ta kira da John gadan-gadan ya nufi FAD'IME yana sakin dariyar ƙeta cike da annashuwa na ganin banza ta faɗi Yarinya kyakkyawa haka a ɓagas.

Sai dai me? Taku ɗaya biyu ya yi a na ukun ƙafarsa ta maƙale ya kasa gaba bare baya duk kuwa da yadda yaso sai dai duk da hakan bai haƙura ba ganin wanda suke tare shi ma ya nufa Faɗimen gadan-gadan yana suɗe baki ya sa ya kai hannu zai fizgota ai kuwa saukar hannunsa saman kafaɗar Faɗime ya yi daidai da wani irin azababen duka da a kai masa a gadon baya Yayin da hannun nasa yaji shi tamkar ya sauka a kan wuta saboda wani raɗaɗin azaba da ya ziyarce shi ai kuwa ba shiri ya durƙushe a wurin tare da fasa ihu jin an ci gaba da zuba masa duka a gadon baya.

Cike da takaici ɗayan yaja wata doguwar tsuka yana kallonsa ya ce. “amma fa gaskiya John ban taɓa sanin haka kake ba ai ka bada maza Bara kaga yadda cikakken Namiji yake ji da Mace irin wannan kucakar ƴar ƙauyen domin ba Dangin Jinnu ba ko ƴar sarkin Jinnun ce da kanta tun da har an biyani ban ga abin da zai sa na kyaleta ba.”

Ya ƙare maganar tare da ƙari sawa wurin Faɗime har da gudunsa yana wani ihu tamkar ɗan kwallon da ya sama nasara.

Baya Faɗime ta yi daidai ya miƙo hannunsa da niyyar fizgota ta yi saurin sa hannunta ta riƙe hannun nasa da kyau tare da murɗewa ji kake Hannun ya bada ƙara alamar an karya shi ai kuwa sai ya zube shima a ƙasa yana zambaɗa ihu tare da magiyar ta saki Hannun.

Sakin hannun nasa Faɗime ta yi tare da nufar Zulay da ta fara ja da baya cike da tsoro baki na rawa ta ce.

“ku...kuyi haƙuri na tuba Wallahi nabi Allah na kuma biku haƙiƙa na yarda Faɗime Dangin ku ne kuma ba wanda ya isa yaja da ita ya zauna lafiya...”

Zulay ta kai maganar wani fitsarin tsoro yana ƙoƙarin kwace ma ta hawaye da macijina sun gama wanke baƙar fuskarta.

Dariya Faɗime take tana dunƙule hannu ta ce. “me ma kika ce yau zaki saka a mayar dani ta yadda ba zan ƙara moruwa ba ko? To kafin ki mayar dani haka ni bara na fara canza miki halitta tukunna.”

Faɗime ta kai maganar tare da saka yatsunta mai cike da ƙumba ta karce gefe da gefe na fuskar Zulay ai kuwa take wurin ya fara fidda jini kaɗan kaɗan Zulay kuwa ta saki ihun azaba tana riƙe fuskarta tare da birgima a wurin faɗi take.

“jama'a ku kawo ɗauki Faɗime ta kasheni zane ta yi min a fuska da zaƙwa-zaƙwan ƙunbarta”

“mun shiga uku Faɗime ki kyalesu haka kizo mu gudu tun kafin kiyi kisan kai.”

Cewar Laure cikin tashin hankali tana janyo Faɗime ai kuwa da gudun bala'i suka bar wurin gudu suke basu dakata ba sai da suka shiga kwanar da zai sadasu da anguwansu Laure sannan ne suka tsaya kowaccensu tana faman sakin numfarfashi na gudun da suka sha.

Laure ta ce.

“faɗime kin faɗar min da gaba wallahi nayi zaton da gaske ba ke ba ce.”

Ita kuwa Sa'ade cewa ta yi.

“wai Allah su Zulay kacao-kacao kuma shikenan an yi ma ta zanen barebari.”

Gaba ɗaya suka kwashe da dariya.

Sa'ade ta ƙara da faɗin. “wai amma Faɗime ba zakiyi wani abu ba haka kina ji kina gani zaki bari gobe a ɗaura miki Aure da wancan Ɗan Abban bayan kin fi kowa sanin halinsa na neman Mata?”

Dariya Faɗime ta ɗan yi sannan ta kallesu gaba ɗaya ta ce.

“a tunaninku zan bari hakan ta faru ne? Ai ba zata taɓa saɓuwa ba Bindiga a ruwa...”

“to yanzu mene ne abin yi?”

Laure ta faɗa cike da damuwa.

“ai tuni na samo mana mafita, ku matso kuji.”

Cewar Faɗime tana sakin dariya ba musu suka ƙari sa ƙasa-ƙasa ta sanar da su shirin da ta ratsa ai kuwa a tare suka saki murmushi cike da farin ciki Faɗime ta ce.

“kun ga dama yazo mana a daidai ke nan ko?”

Gaba ɗaya suka ce E, Laure ta ƙara da faɗin. “lallai Faɗime ƙwaƙwalwarki na ja.”

“hhhh to an faɗa miki ni ɗin jahila ce, ku ƙara matsowa ma kuji wani abu...”

Faɗime ta faɗa cike da fariya sannan ta ci gaba da sanar da su yadda shirin nasu zai wakana basu suka rabu ba sai da suka gama tsara komai da zasuyi sannan suka rabu bayan Faɗime ta gama jaddada musu a kan gobe su shirya da wuri sannan ne kowacce ta wuce gida.

______

Ba sallama ta faɗa gidan abin ta tana ƴar waƙarta cike da nishaɗi tana lura da irin kallon da matan gidan ke yi ma ta suna gulma ƙasa-ƙasa amma ta yi kamar bata gani ba sai ma dariya da take yi ta shige Ɗakin Inna Fatuh sai dai bata tarar da ita ba da alama bata dawo ba daga Anguwan da ta tafi hakan ya sa Faɗime ta yi kwanciyarta ba abin da ya dameta ba'a jima ba kuwa bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita duk da lokacin yammaci ne kuma ko can anjima da Inna Fatuh ta dawo ta tarar da ita bata yi yunƙurin tashin ta ba domin a Ganinta hakan babu amfani sai ma tashin hankali da zai biyo baya dan kuwa fitan da ta yi ta sama labarin da ya girgizata a kan batun Auren Faɗime da Ɗan Abba ta kuma fusata da yadda labarin ya zagaye ƙauyen amma ita bata da labari yanzun ma ta dawo ne tana jiran Malam Yahaya ya dawo daga kasuwa ta turkeshi sai ya sanar da ita dalilinsa na ɓoye ma ta batun auren Faɗime da ya yi.

Ai kuwa an yi sallar isha'i ba jimawa Malam ya shigo gidan kuma har lokacin Faɗime bata tashi ba dan so take ta yi bacci ta darje dan akwai abin da ta shirya zata yi a daren yau shi ya sa ta nutsu tana bacci cikin kwanciyar hankali domin ta rantse yau babu mai rintsawa a gidan tun da har a ka munafurceta yau ba zata kyale kowa ba kowa sai yaji a jikinsa tun da har ita za'a ɓoye ma ta magana a kan aurenta ke nan da sai dai taji labarin an ɗaura aure...

Kai tsaye Ɗakin mahaifiyarsa Inna Fatuh Malam Yahaya ya wuce a nutse ya Gaishe ta tare da fara kama kame a kan ta yadda zai sanar da ita maganar dake tafe da shi dan ya yanke shawarar sanar da ita maganar auren in yaso ya lallaɓata ta yarda ita kuma Faɗime zuwa da asuba zai zaunar da ita ya yi ma ta nasiha mai ratsa jiki sannan ya sanar da ita maganar auren.

Da ƙyar ya samu ya iya zayyanewa Inna Fatuh kalaman dake bakinsa.

Tun da ya fara maganar har ya kai aya Inna Fatuh ta zuba uban ta gumi hannu bibbiyu tana saurarensa ba tare da ta katse shi ba har sai da taji ya kai aya sannan a fusace ta ce.

“ka gama? Nace ka gama surutun banza da wofin e mana banza da wofi mana domin ba zan lamunce ba, amma yahayah ka bani mamaki har lalacewar taka ta kai haka ban sani ba?”

Sai kawai Inna Fatuh ta saka kuka tana ci gaba da faɗin.

“shikenan zama bai sameni ba, Lami ta gama dani Lami ta mallakemun ɗa wayyo ni Fattuh.”

Shi dai Malam Yahaya yana zaune gefe abin duniya ya haɗe masa goma da ashirin domin ji yake muddun bai aurar da Faɗime ba a gobe to fa Akwai matsala, da ƙyar ya iya furta.

“dan Allah Inna kiyi shiru ba fa abin da kike tunani ba ne kawai dai ni ne naga hakan ya dace shi ya sa na yanke aurawa Faɗime wannan yaro amma idan na ɓata miki rai bisa ɓoye lamarin da nayi a gareki kiyi haƙuri....”

“Yahaya ka tashi ta fitarmin daga ɗaki tun muna mumu biyu.”

Inna Fatuh ta faɗa a fusace tana nuna masa hanya ba musu Malam ya tashi cikin sanyin jiki ya fice.

Sai Inna Fatuh ta mayar da dubanta wurin da Faɗime ke kwance kamar mai bacci sai dai tun shigowar Mahaifin nata ɗakin ta farka sai dai bata yi motsi ba.

“Allah sarki Baiwar Allah marainiyar Allah ta'ala muddun ina raye ban ga meyi miki Auren dole ba.”

Inna Fatuh ta kai maganar tana ƙara fyace majiya wai duk cikin tausayin Faɗime sannan ta miƙe tsaye tunawa da ta yi bata yi sallahr isha'i ba ta fita domin ɗauro al'wala.

Hakan kuma ya bawa Faɗime damar sakkowa daga gadon na Inna Fatuh da ake kira da mambari ta tsaya tsakiyar Ɗakin tana tunanin ta inda zata fara, murmushi ta saki dan bataso duk abin da zai faru a daren yau Inna Fatuh ta sani tun da ita tana goyon bayanta.

Aljihun doguwar rigar jikinta ta saka hannu ta ciro abin da ta siyo ɗazu kafin ta shigo gidan ta yi saurin barbaɗawa cikin miyar tuwon dare a ka kawo ma Inna Fatuh bataci ba, sai da ta juye duka sannan ta yi ma za ta fito daga Ɗakin ai kuwa suka buga karo da Inna Fatuh da gata ɗauro al'wala tana shirin shiga Ɗakin.

Washe baki Inna Fatuh ta yi tana faɗin. “ƴar albarka Faɗime na kin tashi ke nan? To ma za kiyo al'wala kiyi sallah sannan kizo mu ci abinci kinji?”

Inna Fatuh ta faɗa tana kamo Hannun Faɗime domin tayar da ta yi komai amma ban da abubuwa guda biyu su ne; ƙin yin sallah da kuma zama da yunwa.

Turo baki Faɗime ta yi cike da shagwaɓa ta ce.

“Ni Inna Fatuh bana jin yunwa kuma zan yi sallahr amma sai anjima yanzu zan je wurin ƙawata Sa'ade ne akwai abuna dana manta ban karɓa ba a wurinta.”

“amma kuma ba zaki bari sai zuwa da safe fa Faɗime gani nayi dare ya ɗan yi...”

“karki damu Inna ai zan iya kare kaina kuma ba zan daɗe ba yanzu zan je na dawo.”

Faɗime ta faɗa tana yin gaba Inna Fatuh ta jijjiga kai sannan ta shige Ɗakin ta gabatar da sallahr taso ta jira Faɗime ta dawo su ci tuwon tare amma ƙamshin miyar kukan dake dakar hancinta ya sa ta gaza haƙura ta buɗe kwanon tuwon ta loda abin ta har da tanɗe hannu a fili ta ce.

“yau kuma su Salaha an yi abin kai kome ta sakama miyar nan ta yi wannan maganaɗisun daɗi ohoo.”

Inna Fatuh bata yi minti biyar da gama cin tuwon ba bacci mai nauyi ya ɗibeta ai kuwa ta jingine a Wurin tana kwasar bacci.

Ita kuwa Faɗime kai tsaye sashen Inna Lami ta nufa ta kuwa yi Sa'a ƙofar a buɗe da sauri ta ƙari sa ciki ta jiyo motsin Lami a bayi, hakan ya sa ta yi wuff ta shige Ɗakin Auta domin muguntar ta kansa za'a fara kwanon tuwonsa ta gani a gefe da alama bai ci ba, murmushin ƙeta ta yi dan kuwa ta san yadda Auta ke muguwar son tuwo ba abin da zai hana shi cin tuwon nan ɗayan maganin dake aljihun ta ta ciro tare da barbaɗewa gaba ɗaya a cikin miyar tuwon Auta ta saka hannu ta juya cike da mugunta tana shirin miƙe wa taji alamun za'a shigo Ɗakin ai da mugun sauri ta ƙari sa bayan ƙofa tare da ɓuya, Auta ne ya shigo yana danna waya da alama chatting yake sai faman sakin murmushi yake yi, da sauri ganin ya juya baya Faɗime ta yi wuff ta fice daga Ɗakin, shi kuwa Auta zama ya yi tare da buɗe kwanon tuwonsa ya naga abin sa yana ci gaba da chatting ɗin sa hankali kwance.

Faɗime fitowa ta yi daga ɓangaren Inna Lami duk da bata gama da su ba amma zata fara komawa shashen sauran mutan gidan Matan yayyi da ƙannin mahaifinta duk ta yi musu abin da ta shirya dan ta rantse yau dai babu mai yin Bacci a gidan....