FAD'IME (Dangin Jinnu)

08

by @nkds

*FAƊIME..💋🌸💕*

_(Dangin Jinnu)_

©By Nainarh KD & Zahrah Royal Star

08

Dawowarsa ke nan daga masallaci sallahr asuba har ya yi gaba sam bai lura da ita ba ganin haka ya sa ta ce.

“Baba!”

Da sauri ya juya sai kuwa ya yi ido huɗu da Faɗime tana tsaye har ta so ma ta ba shi tsoro, domin sam bai lura da ita ba.

“Fatima me kike yi anan?”

Malam ya tambaya da mamaki.

Faɗime tana shirin magana ta hango fitowar Auta daga banɗaki yana dafe bango cike da gajiya domin kwana ya yi yana zarya zuwa bayi.

Gimtse dariya Faɗime ta yi gudun kar Malam ya ɓaro jikinta shi kuwa Malam ganin inda take kallo ya sa shi mayar da dubansa zuwa wurin.

“Zubair! Lafiya kuwa kake riƙe bango kamar mai naƙuda?”

“Ba..ba bakomai Baba dama gudawa nakeyi tsawon dare shi ya sa duk nabi na galaɓaita”

Auta ya faɗa tamkar ya fashe da kuka.

Juyawa gefe Faɗime ta yi tana sakin dariyar ƙeta tana ji Malam yana yi ma Auta faɗa a kan yawan ciya-ciye daga ƙarshe ya yi masa sannu ya kuma taimaka masa ya koma Ɗakin.

“ƙari so ciki dama ina so nayi magana dake.”

Malam ya faɗa lokacin da ya dawo da kallonsa kan Faɗime.

Ba musu tabi bayansa har zuwa sashensa ta zauna saman tabarma tana jira taji ta yadda sai fara.

“wato Fatima wani babban laifi nayi miki ban kuma san ta yadda zaki karɓa al'amarin ba.”

Faɗime ta ɗa go tana yi ma mahaifin nata kallon ƙasan ido, wato ya ɗauka batasan komai ba ke nan.

“Wani abu ne ya faru Baba?”

Ta faɗa cikin ladabi kamar ba ita ba dan ta ƙosa ya yi ya gama ta fice ta aiwatar da ƙudirinta.

“dama...”

“ai Bama abin da ya faru kawai dai ni ce na yanke shawarar kaiki Birni aikatau ai kina so ko?”

Lami da ta yi wuff ta shigo Ɗakin ta katse Malam da yake shirin magana da faɗin hakan.

Da kallon mamaki Malam ya bita, yayin da Faɗime ta saki murmushi a zuciyarta ta ce.

‘lallai su Inna Lami anji Uwar bari an canza taku.’

A fili kuwa sai cewa ta yi.

“Birni kuma ni ba zan je ba”

Ta faɗa tana miƙe wa tsaye ta fice daga Ɗakin tana sakin dariya domin kuwa ita a nata tunanin faɗuwa ce tazo daidai da zama.

Gidan ta fice gaba ɗaya kai tsaye ta wuce zuwa gidansu Sa'ade, a hanya suka ji karo da Sa'ade dake ta faman sauri tana waige-waige ga tumin kaya a hannunta.

“laa Faɗime ashe kece ni wallahi har kin ban tsoro amma ina naki kayan ne kodai ba zaki tafi da komai ba?”

Sa'ade dake ta faman zuba ta yi shiru ganin Faɗime tana dariya.

“ke ni barni da wannan zancen dan ya zama tsoron labari yanzu dai batun aure babu...”

Sa'ade ta zazzaro ido waje sai kuma cike da zumuɗi ta ce.

“amma naji daɗi sosai hahaha cike su Inna Lami an ji uwar bari ke nan bani labari yadda ta kaya.”

“hmmm ke dai bari kawai domin labarin da tsayi a taƙaice dai yanzu ta ce Aikatau zata kaini Birni....”

“Aikatau kuma?”

Sa'ade ta katse Faɗime tana zazzaro ido.

“matsalata dake Sa'ade bakyajin ribar zan ce ki bari mana na kai aya.”

Cewar Faɗime, sannan ta ci gaba.

“eh kuma da fari zan nuna banaso sai da ƙyar zan amince idan kuma naje ba aikin zan yi ba zai dai kasance na sama hanyar zuwa birni domin cika burina na zama Mawaƙi”

Faɗime ta kai maganar tana lumshe ido cike da zumuɗi bata jira Sa'ade da mamaki ya sa ta kasa magana ba ta ci gaba da faɗin.

“saboda haka yanzu kije tun kafin Laure ta fito ki faɗa ma ta labari ya sauya ba batun guduwa.”

Faɗime tana gama maganar ta juya abin ta zuwa gida domin zumuɗin zuwa birni take.

_____

DA RANA

Inna Lami ce durƙushe gaban Inna Fatuh tana faman yi ma ta magiya a kan ta bari a tafi da Faɗime Birni aikatau a gobe.

Yayin da Faɗime take zaune gefe tana faman kai loma kamar batasan abin da ke wakana ba.

“ke Lami nafa san ba mutunci ne dake ba ki faɗa min abin da kike shiryawa da kike wannan magiyar a kan na bar Faɗime taje Birni aikatau salon ki cutar min da ita ko to kuwa ba zata saɓu ba ehe wato saboda kin ga auren bai yiwu ba shi ne kika ɓullo ta nan.”

Inna Fatuh ta ƙare maganar tana bin Inna Lami da kallon banza.

Wani takaici ya cike Lami amma ta daure domin ita kaɗai ta san abin da take shiryawa a kan zuwan Faɗime Birnin, hakan ya sa ta ce.

“wallahi Inna Fatuh ba abin da nake shiryawa kawai dai nayi nadama ne da irin abubuwan da nake yi ma Faɗime a da.... ouch”

Ta kai maganar tare da sakin ƙara na azaba sakamakon wani tsunƙuli da a ka yi ma ta a baya.

Faɗime ta saki dariyar mugunta a fili da hakan ya sa duk suka dubeta sai ta ma ze da faɗin.

“Inna Fatuh kawai ki yarda kika sani ma ko na samo zuƙeƙen miji a can Birnin”

Washe bari Inna Fatuh ta yi jin kalaman Faɗime sai kawai ta duba Lami dake sakar ma ta harara a fakaice.

“to ai sai ki tashi ki bani wuri tun da ta amince kuma kada ki kuskura na gano kina shirya wani abin ne dan ba zan kyaleki ba.”

“ai Inna Fatuh ba ma abin da nake shiryawa.”

Cewar Lami sannan ta bar wurin cike da farin ciki ta lalubo ƙaramar nokiya ɗin wayarta ta kira Dillaliya ta sanar da ita halin da a ke ciki.

_____

“wai Faɗime shikenan yanzu tafiya Birnin zakiyi?”

Laure ta tambaya lokacin da su ukun suka haɗu a wurin da suka saba haɗu wa.

Sai da Faɗime ta gwagwiyi goribar hannunta sannan ta ce.

“da gudu ma, ke Laure ko dai baƙin ciki kike min ban sani ba?”

Da sauri Laure ta ce.

“Ni a wa Allah baki haƙuri kawai ina jajatawa ne zamuyi kewarki”

Sai Faɗime ta yi dariya tana faɗin.

“mu je nayi ɓarna na ƙarshe kafin na tafi birni domin ban san ranar dawowata ba.”

Ɗunguma suka yi suka nufa hanyar fadamar mai gari da suka ɗibo rake jiya.

____________

Hajiya Saleema uwar gidan Alhaji Sa'id Ahmad Lamiɗo tana da yara huɗu sun haɗa da Alhaji Ahmad da shi ne Babba sai kuma mai bi masa Eng. Khamis sannan sai Alhaji Tasi'u da kuma Prof. Ridwan sai kuma Auta wato Hajiya Saratu...

Sannan sai Hajiya Haleema yaranta biyu, Alhaji Dauda sai kuma Hajiya Laraba.

Duka suna zaune ne a SAL Estate tare da iyalansu baki ɗaya.

Hajiya Saratu wato mahaifiyar Fidaus ta kasance mace ce da bata yarda wani yafita da komai ba zata iya aikata komai muddun wani muradi nata da ta saka a gaba na son duniya zai cika sam bata yarda da faɗuwa ba al'amarin ta shi ya sa sam basa shiri da Mommy Matar Alhaji Dauda kasancewar Mommy ita ma halinta kusan ɗaya ne dana Hajiya Saratu na son abin duniya sai dai ta wani ɓangaren sun sha bamban. Kowacce tana Burin ganin tafi ɗaya a komai shi ya sa har yaransu sun taso a haka sam basa wani ga maciji tsakaninsu kuma hakan ya samo asali ne daga iyayen nasu mata, domin su iyayen maza kullum burinsu bai wuce ganin kan yaran nasu ya haɗu ba.

Alhaji Ahmad SAL yana da mata biyu Hajiya Zakiya da ake kira da Mamy sai kuma Hajiya Lubabatu da a ke kira da Nur.

Mamy yaranta huɗu curr, Salim, Maryam, sai kuma Muhammad da Saddika, yayin da Hajiya Lubabatu take da yara Biyar duk da kasancewarta mace ta biyu a gidan Alhaji Ahmad SAL sai dai ita ce macen da ya fara so tun ƙuruciya yayin da Hajiya Zakiya ta kasance auren haɗi a ka yi musu sai daga baya ne ya Aura Hajiya Lubabatu wato Nur, kuma ita ce mahaifiyar Safiuddin, Safiya ita ce ƴarta ta fari sai kuma Safiuddin mai bi ma ta sannan sai Jalil da Jalila twins sai kuma Auta Shaheeda.

Prof Ridwan Matarsa ɗaya yaransu biyu rak, mace da namiji kuma suna zaune a ƙasar Faransa har wa yau kasancewarsa Ambassador.

Haka ma Eng. Khamis da Alhaji Tasi'u duk matansu ɗaiɗai kuma kowannensu Allah ya azurtashi da yara.

Sai kuma Alhaji Dauda Mijin Mommy matansa biyu Mommy ce ta biyu yayin da Hajiya Saima da ake kira da Ammiey ta kasance ta farko, Mommy yaranta biyu Asma da Fahat, sai kuma Junaidiya da Sudais da kuma Firdaus su kuma yaran Ammiey wato Hajiya Saratu.

Tsayawa ƙiyasa adadin familyn SAL ba abu ne mai sauƙi ba mu dai afka gadan-gadan cikin labarin a hankali za'a san kowa kuma halin kowa ya bayyana mu dai ci gaba da gashi kawai...