UMMUL~JAANNAH

01

by @nkds

# Nainarh KD

# Perfectly Pen's

# ***

*UMMUL~JAANNAH..🩸✨🔥*

*Two souls, brought together by fate, navigate love, heartbreak, and self-discovery.*

Copy is not allowed.¡!

Ba kuma zan Lamunci a canzan labari kota wata siga ba.¡!

01.

A mugun razane taja baya hannunta dafe da kumatunta, yayin da fuskarta ke cike da zallar mamaki na marin da Yarinyar ta kwaɗa ma ta domin bata taɓa tsammani ba, kamar a mafarki dai taji saukar marin, baki na rawa na zallar mamaki ta furta.

“Ummul ni kika mara?”

Ta yi maganar cikin nuna zallar mamaki tana kuma kallon Ummul dake tsaye gabanta ta harɗe hannu a ƙirji, Innocent face nata a kame tamkar dai ba ita ta yi marin ba.

“Na mareki Rahina, kuma zan ci gaba marinki muddun baki riƙe girman ki ba, kuma zan ƙara tambayarki a karo na ƙarshe da ki sanar dani inda kuka kai min Mahaifiya tun kafin hukuma ta shiga tsakanina daku.”

Wannan karon tsoro ne ya mamaye fuskar Rahina, sai ta kasa magana sai kallo datake bin Ummul da shi, Yarinyar da aƙalla ta bawa shekaru shida zuwa Bakwai amma yau ta haɗa hannu ta mareta, bama wannan ba ina sanyin hali da tsoron da Yarinyar keda kuma ta taso da shi ne? Domin wannan dake tsaye gabanta batayi kama da Ummul ɗin da ta sa ni ba, Ummul dai Yarinyar da bata ko iya ɗa ga ido ta kallesu duk irin cin kashi da azabtar war da zasuyi ma ta ita da mahaifiyarta, sai taga wannan Ummul ɗin dake gabanta kuma ta haɗa hannu ta sharara ma ta mari ta rikiɗe ta koma wata fusatacciya kuma jaruma da bata nuna rauninta ko kuma barin ko ta kwana.

“ke Ummul dama baki da hankali ban sa ni ba Aunty Rahina ce zaki mara a kan wani dalili?”

Rifaat da sai lokacin ta zama zarafin magana ta kuma dawo daidai daga shocking na mamakin marin da Ummul ta yi ma Rahina da ta shiga, ta yi maganar tana ƙoƙarin marin Ummul ɗin.

Hannu ta sa ta kama hannun Rifaat ɗin sannan ta watsar, ta kalleta tsakar ido cike da rashin tsoro ta ce.

“na maretan kema kuma muddin kika kuskura kika aibata Mahaifiya abin da ya fi mari ma zan yi miki.

Rifaat ta kalla Rahina da tsananin mamaki tana nuna Ummul ta ce.

“ta haukace fa.”

Sai kuma ta juya da sauri ta haye sama tana kwala kiran Mahaifiyarsu. Da sauri ita ma Rahina tabi bayanta dan kuwa Ummul ta bata tsoro yanayin da taga Yarinyar ta koma dan kawai ta aibata Mahaukaciyar Uwarta to ƙarya ta yi ai mahaukaciya ce to mene ne ma na damuwa ko fusata dan Mahaukaciyar ta gudu ai ita Ummul ɗin hutu ne hakan a gare ta.

Hummph!

Ummul ta sauke ajiyar zuciya a hankali tana dafe saitin zuciyarta dake bugu na wuce ƙima, ita kanta mamakin kanta take yi da wannan sabon halin da ta aro ta yafa ma kanta, koda yake hakan shi ne kawai mafita a gare ta dan yanzu Sha Takwas take saboda haka ta wuce matakin da zata tsaya su ci gaba da wulaƙantata da azabtar da ita tamkar wata maras galihu bayan kuma abin da suke taƙama da shi duk nata ne, ba dukiyar ba, ba kuma Mahaifin ba.

Juyawa ta yi ta buɗe ƙaramin fridge dake gefe ta ciro ruwa mai sanyi bata kai ga sha ba kunnuwanta suka jiyo ma ta sautin takun takalmin mai tsini ana tunkaro inda take hakan ya sa ta juya su kayi ido huɗu da Mommy Reyhana dake saukowa daga matattakalan cikin izza.

Da kallon ƙasa da sama Mommy Reyhana take bin Ummul tana ɓoye mamakin abin da su Rahina suka sanar da ita a kan Yarinyar wai ta mare Rahina.

“Me ya sama kayanki?.”

Mommy Reyhana ta faɗa tana ƙoƙarin ɓoye ɓacin ranta na marin da Ummul ɗin ta yi ma Ƴarta Rahina yayin da gefe guda take ƙoƙarin nuna damuwa da kulawa a kan Ummul ɗin kamar yadda ta saba.

Kallon jikinta Ummul ta yi sai lokacin ta tuna danbarwar da ta sha gaba ɗaya uniform ɗin jikinta ya canza kala sakamakon ruwan makoki iri-iri dake jiki ta wani wurin ma an yaga ba iya kayan jikinta Bama har fuskarta Akwai ɗigo ɗigon maka da fenti.

“Yau muka yi Candy, celebration muka yi a School shi ya sa kayan suka koma haka.”

Ta faɗa kanta tsaye tana mayar da dubanta kan Mommy Reyhana da ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba, ta ƙari sa ta zauna saman ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun palon.

“mene ne Rahina ta yi miki da kika mareta matsayinta na Yayarki?”

“Ai bata Mahaifiyata ta yi.”

Ummul ta bata amsa.

Shiru Mommy Reyhana ta yi tana ɗan mamakin yadda Yarinyar take bata amsa kanta tsaye, da gaske Yarinyar ta canza kuma canjin nata a yau ne, daga tafiyarta school zana jarabawar ƙarshe zuwa wannan lokacin ne ta koma haka.

“Mommy Reyhana yanzu bata waɗan tambayoyin naki nake ba Dan Allah ki sanar dani inda kuka kaimin Mahaifiyata domin na dawo ban ganta ba kuma kafin na fita na barta cikin ƙoshin lafiya a ɗakinta”

Ummul ta faɗa murya a raunace domin cikin tashin hankali take bata fata a ce wani abu ne mummuna ya sama mahaifiyar nata ita ɗaya tilo gareta da take gani taji daɗi.

Wani irin bugu ƙirjin Mommy Reyhana ya yi ta zazzaro ido cike da tashin hankali da yafi na Ummul ta miƙe tsaye tana faɗin.

“Mahaifiyarki baki ganta ba a cikin gidan nan ina ke nan ta shiga?”

Ta faɗa cikin rawar murya sai kuma da sauri ba tare da ta jira amsar da Ummul zata bata ba, ta nufa Up da sauri tamkar ba ita ce mai taku ɗaiɗai ba a ƴan sakannin da suka gabata.

“Ke Rahina dama baki da hankali so kike ki kasheni da sauran raina, faɗa min ina ne kika kai Mahaifiyar wancan Figaggiyar?”

Mommy Reyhana ta faɗa a fusace lokacin da ta ƙari sa Palon sama ta sama Rahina da Rifaat zaune.

Miƙe wa tsaye su duka suka yi Rahina ta turo baki cikin halin ko'in kula ta ce.

“ah to inda ya dace da ita na kaita dama ba neman hanyar rabuwa da su kike ba shi ne kawai nayi abin da nake ga ya kamata...”

Bata ƙari sa ba Mommy Reyhana ta kwasheta da mari a matuƙar fusace ta shaƙo wuyanta tana faɗin.

“yau na tabbatar baki da hankali Rahina ba zakiyimin bayanin inda kika kaita ba saina hallakaki?”

Cikin mamaki da tsoro Rifaat ta kira sunan Mahaifiyar tasu tana zaro ido ganin kamar ta fita daga hayyacinta tana ƙoƙarin yin kisa.

“Mommy, could you please stop?”

Rifaat ta faɗa tana fashewa da kuka dan farar kura ce ga tsoro ga ban tsoro akwai iya zallar mugunta sai dai ko kaɗan bata son tashin hankali.

Mommy Reyhana bata saurareta ba ta kuma tambayar Rahina da ina ta kai Mahaifiyar Ummul cikin ɗaga murya.

Cikin fitar hayyaci Rahina ta ce.

“Fita da ita nayi daga gidan, gani nayi tanason fita ni kuma na taimaka ma ta.”

Cak! Mommy Reyhana ta dakata tana kuma kallon Rahina cikin ɗacin rai ta ja da baya sai kuma ta ɗaura hannu a ka tana faɗin.

“shi ke nan Rahina kin gama dani kin kasheni Rahina tun da har kika fitar da Asma'u daga wannan gidan shi ke nan asirina ya tonu”

Kallon juna Rifaat da Rahina suka yi sai kuma suka mayar da dubansu ga mahaifiyar tasu cikin rashin fahimta suka haɗa baki wurin faɗin.

“Mommy me kike nufi da asirinki ya tonu?”

Rahina ta ƙara da faɗin.

“ni dai iya sanina tun da na taso baki da wacce kika tsana irin Asma'u da Ƴarta Ummul, kuma baki da wani buri da ya wuce a wayi gari basa cikin gidan nan kuma naga Daddy ma kanshi bai damu da su ba shi ya sa yau kawai da naga dama ta samu na buɗe ma ta ƙofa ta bar gidan kuma ai naga Mahaukaciya ce cikin hauka take saboda haka wannan ai ba abin damuwa ba ne ko...”

“Rahina kika kuma magana zaki ga abin da zai biyo baya shashsaha kawai.”

Mommy Reyhana ta faɗa a fusace tana ta miƙe wa tsaye cikin neman mafita domin zama bai ganta ba dole ta kira Aminiyarta domin su san abin yi lamari dai ya riga ya ɓaci tun da har Asma'u ta sa ƙafa ta bar gidan da hakan na nufin watan tonuwar gaba ɗaya asiranta ne ya yi.

Wani irin bugu ƙirjinta ya yi Mommy Reyhana ta tsaya cak lokacin da ta juya su kayi ido huɗu da Ummul dake tsaye hawaye nayi ma ta sintiri tana kuma bin su da wani irin tsanannen kallo.

“ah..ah dama ke Ummul tun yaushe kika shigo Palon?”

Mommy Reyhana ta faɗa cikin rabewar murya.

Hakan ya sa Rahina da Rifaat suka mayar da dubansu kanta.

Ummul batace komai ba ta fara taku har ta isa gaban Rahina cikin wata kalar murya ta furta.

“ina kika kaimin Mahaifiyata?”

Shiru Rahina ta yi hakan ya sa Ummul ta kuma daka ma ta tsawa da faɗin.

“tambayarki nake Mahaifiyata tana ina?!”

“Na rantse da Allah ban sa ni ba abin da na sa ni kawai shi ne na buɗe ma ta ƙofar Gate ta fice”

Ja da baya Ummul ta fara tana bin Rahina da kallon tsana sannan ta juya ga Mommy Reyhana dake sandare ta kasa motsi ta ce.

“daga ke har ƴaƴanki ku kuka da kanku domin wani abu ya sama Mahaifiyata hukuma ce zata rabani daku!”

Tana gama faɗar hakan cikin sauri haɗe da gudu-gudu ta nufa stairs ta fara taka wa da sauri-sauri ta nufa ƙasa.

Yayin da kalaman Ummul suka dawo da Mommy Reyhana daidai daga Duniyar tunani da ta lula da mugun sauri ta shige bedroom ɗin ta dake nan Up ɗin yayin da Rahina tabi bayanta ita kuwa Rifaat ta zauna ɗabas cikin rashin abin yi dan kanta ya kulle ta rasa wani tunani ma zatayi.

“Aminiya ba lafiya fa!”

Mommy Reyhana ta faɗa lokacin da ta shige can ƙuryar Bedroom ta lalubo lambar Aminiyarta Hajiya Sara.

Daga can ɓangaren Hajiya Sara dake kishingiɗe ta tashi zaune tana tambayar meke faruwa.

“kedai bari wancan shashashan mana Rahina taje ta buɗe wa Asma'u ƙofa ta fita daga gida ban sani ba”

Mommy Reyhana ta faɗa cike da takaici tana wurgama Rahina da ta biyo ta harara.

“Oh My! amma garin ya ya hakan ta kasance?”

Cewar Hajiya Sara cike da mamaki tana komawa ta zauna domin zancen ya rikitata, bata jira Mommy Reyhana ta amsa ba ta ƙara da faɗin.

“bari ina nan zuwa Gidan sai mu tattauna da kyau.”

“tohm shi ke nan Aminiya sai kin zo”

Cewar Mommy Reyhana sannan ta katse wayar tana bin Rahina da kallo mai kama da harara.

“Am so sorry Mommy ban yi hakan dan na ɓata miki ba, hasali ma nayi ne domin na faranta miki”

Rahina ta faɗa cikin sanyin murya kamar mai shirin fashewa da kuka.

Ajiyar zuciya Mommy Reyhana ta sauke ta ce.

“It's Okay, karki damu komai ya wuce amma gaskiya kin ɓata min rai”

“Sorry, Mom. I promise I won't do that again.”

Rahina ta yi saurin faɗa.

Ba yadda Mommy Reyhana ta iya domin bayan Aminiyarta Hajiya Sara, Rahina ita ce Abokiyar kashewa da binnewanta na wasu abubuwan sai dai matsalar Rahina ɗaya muguwar shashasha ce bata abu da tunani wannan shi ne yake haɗa ta da Mommy Reyhana.

UMMUL POV.

Tafiya kawai take yi tun da ta fito daga gidansu ta bar Anguwansu ba tare da ta san inda take jefa ƙafafunta ba.

Haƙiƙa tana cikin tashin hankali ba kaɗan ba domin batasan ta ina zata fara neman inda Mahaifiyar nata take ba daɗi da ƙari ga lalurar hauka dake damun Mahaifiyar nata, fatan ta ɗaya shi ne ta kasance tana cikin ƙoshin lafiya kuma ta faɗa hannu na gari.

Tun wuraren uku na rana take abu ɗaya ta shiga nan ta fita can har yanzu wuraren magrib gaba ɗaya ta galaɓaita yunwa da ƙishirwa sun fara addabarta ƴan hanjinta ji take kamar za su fito amma haka ta daure tana ci gaba da neman ta, inda take tunanin ko Allah zai sa ta yi dace ta gata Mahafiyar nata.

A gajiye ta hayo saman ginin Babban Asibitin da yawon neman Mahaifiyar nata ya kawota domin a tunaninta wata ƙila ta shiga ciki sai dai ba inda bata duba ba amma bata ga koda mai kama da ita ba, dabara ce ta faɗo ma ta kasancewar asibitin Babba ne na gaske hakan ya sa ta yanke shawarar hawa ta can sama ko zata iya hango ta cikin rububin mutane kasancewar idan a ka hau saman ba iya harabar asibitin ba, har cikin gari ma ana hangowa shi ne fa yanzu ta hawo saman a galaɓaice da ƙyar ma take iya buɗe idonta saboda yunwa da gajiya, hakan ya sa ta zube a wurin dan ta huta ba tare da lura da shi ba, shi kuwa tsaye yake a wurin idanunsa a lumshe yaji lokacin da a ka buɗe ƙofar exit ɗin ta shigo ciki har zubewan da ta yi, mayar da dubansa zuwa zurfin ƙasa ya yi yana nazari sannan ya sake kallon inda yake tsaye ƙafafunsa saman ginin ƙarshe na wurin da yana ƙara motsi kaɗan ƙasa zai yi, murmushi ya yi domin yanason kasada irin haka yana burgeshi.

A hankali ta buɗe dara-daran idanunta farare da tsabar gajiya da wuya yasa suka fara sauyawa zuwa ja-ja-ja aikuwa ta ware su a kan sa, sai ta miƙe tsaye zumbur cike da mamaki tana ɗan mirza ido dan in ba gizo ba gani take kamar ƙoƙarin kashe kansa yake yi, ai da sauri ba tare da ta tsaya tunanin komai ba ko kuma shawara ba ta nufa wurin da ƙari sawarta tasa hannu ta riƙo rigarsa ta baya ta dage iya ƙarfinta ta janyo shi yayo taga-taga kaɗan ya rage ya faɗa kanta ya yi saurin tsaita tsayuwarsa yana kallonta da mamakin abin da ta yi.

Ita kuwa Ummul idonta ya rufe da masifa bata jira abin da zai ce ba ko kuma ta saurari uzurinsa ta fara balbaleshi da bala'i ta inda take shiga ba ta nan take fita ba ta ci gaba da faɗin.

“yanzu fisabilillah mene ne ribarka idan ka kashe kanka uhum? Ko kuwa kawai dan Duniyar ta yi maka zafi sai a ka ce kashe kanka shi ne mafita? Waya faɗa maka kashe kai shi ne mafita, ai ba mafita bane a komai fa ce janyo wa kai asara na har abada domin in ka kashe kanka ai ka mutu kafiri daga nan kuma kai tsaye sai jahannama. Kaganni nan inda a ce biyewa matsalolin da nake ciki zan yi to da tabbas har abin da yafi kashe kai ma zan yi, amma bana buƙatar duk waɗan nan..”

Ummul ta dafa kafaɗarsa ba tare da damuwa da tsayin da ya ɗan fita ba a ƙoƙarinta na ganin ya fahimci abin da takeson nusar da shi ta ci gaba da faɗin.

“saboda haka Yallaɓai baka buƙatar ka kashe kanka saboda matsaloli sun yi maka yawa tsayawa zakayi ka fuskancesu kaji ba?”

Sai ta ɗan kalleshi ta ɗan yi murmushi sannan ta ci gaba da. “gaka ɗan kyakkyawa wannan ai mutane da yawa zakayima asara inka kashe kanka ba iya kai kaɗai ba?”

Mayar da kallon ta ga ƙasan wurin ta yi sai kuma ta dubeshi a iya ƙiyasinta inma wata gagarumar matsala ce gare shi to ba zai wuce na kuɗi ba dan a yadda ta ganshi sanye da kayan asibiti ta yiwu wata lalurar ke damunsa ko kuma za'ayi masa aiki bashi da kuɗi wata ƙila shi ya sa ya nemi kashe kansa, a iya nata tunanin ke nan, hakan ya sa jikinta ya yi sanyi ta dubeshi da ya kafeta da ido da mamaki tsakani da Allah dariya ma ta bashi.

Ita kuwa Ummul hannu tasa a aljihun wandon makarantar dake jikinta ta ciro ATM card sannan ta riƙo hannunsa ta damƙa masa ta ce.

“ga wannan zai isheka kayi maganin matsalar ka amma kada ka sake ƙoƙarin kashe kanka kaji ko memakon kayi wannan kayi amfani da hakan wurin roƙon Allah shi kuma koma mene ne zai kawo maka mafita cikin sauƙi sannan ka tayani da addu'a da fatan naga Mahafiyata da ta bar gida cikin lalurar hauka.”

Tana gama faɗar hakan ta sakar masa murmushi sannan taja ƙafarta ta bar wurin fitowa ta yi daga asibitin gaba ɗaya wurin da batayi tunanin zuwa ba da farko nan ta nufa wato Police Station.

Ƙarar da wayarsa ta yi ne ya sa Aliyu dawowa nutsuwarsa sai yabi ATM ɗin da ta bashi da ido ya sakin ɗan murmushi sannan ya ciro wayar tare da ɗa ga kiran ya kara a kunne bai jira ance komai ba ya furta.

“Ka sameni a asibiti yanzu”

Sannan ya katse kiran ya mayar da wayar aljihu ya koma Ɗakin da yake a can VIP na asibitin..

# Ummul

# Aliyu

# Two souls brought together 🍂

# UMMUL-JAANNAH 🔥✨

# Nainarh KD ✍️