UMMUL~JAANNAH

02

by @nkds

***

02

A jere motocin guda uku suka faka a harabar asibitin, securityn da ya fito daga motar farko ya ƙari sa tare da buɗe ta tsakiyar, tsawon sakanni sannan wata Kyakkyawar Mata ta fito da aƙalla a shekaru zata kai Hamsin da ɗauriya, sai dai yanayin kyau da shigar alfarma dake jikinta ya sa ba ma za'a gane takai waɗan nan shekarun ba, cikin takun ƙasaita da izza ta fara tafiya zuwa ciki, yayin da Securities ɗin ke take ma ta baya.

Yana zaune saman tsakiyar gadon Ɗakin ya tankwashe ƙafa yana waya a ka turo ƙofar, ba tare da sallama ba ta shigo har sai da ta kusa ƙari sawa dab da shi sannan ta furta.

“Hey, Son.”

Ɗago lumtsatstsu kuma nutsatstsun kyawawan idanunsa ya yi tare da sauke su saman fuskarta, a take kaso mai yawa na fara'ar dake tare da shi ta gushe.

Ta san za'ayi hakan duba da yadda yanayinsa ya canza da ganinta sai dai bata damu ba ta ƙari sa tare da zama gefensa tana ƙoƙarin kamo hannunsa tare da faɗin.

“Son Why? so kake zuciyata ta buga uhump? Ace anharbeka a wurin aiki, harka dawo garin kayi jinya duka ba tare dana sa ni ba, an ya kuwa ka ɗaukeni matsayin Mahaifiya a gare ka?”

Janye hannunsa ya yi a nutse ya dubeta jikinsa ya ɗan yi sanyi da kalamanta, dan ya san bai kyauta ba amma ya ya iya koma mene ne ya yi ai ita ce sila.

Yana shirin magana a ka turo ƙofar Room ɗin duk suka mayar da dubansu wurin yayin da Assistant ɗin sa John ya bayyana yana sauke kai ƙasa dan yasan ya yima Boss ɗin nasa laifi na sanar da Mahaifiyarsa da ya yi.

“ai ka kyauta kaji ko na nema da kazo kai ɗaya shi ne kayo gayya”

Aliyu ya faɗa yana mayar da kallonsa gefe.

Assistant John yana shirin magana Professor Zulfa ta riga shi da faɗin.

“Son! Yanzu ni ce gayya ɗin ko?”

Ta faɗa tana ƙoƙarin su haɗa ido. Sai dai Aliyu yaƙi bata dama, murmushi ya ɗan yi ya ce.

“E mana tun da ban so kin sama labari ba saboda nasan zaki shiga damuwa kuma fa na warke don harsashin bai shiga sosai ba”

Ya faɗa yana ɗan ya ye rigarsa ta baya saitin wurin da a ka harbeshi sai dai bai bari ta gani da kyau ba ya yi saurin rufe wa.

Ajiyar zuciya ta sauke kamar bata lura da abin da ya yi ba ta ce.

“amma dai wannan karon kazo ke nan ba inda zaka koma sai ka huta da kyau ba?”

Kallonta ya yi suka haɗa ido ya ce. “ke mijinki kuna buƙatar na zauna ne?”

“sosai ma kuwa Son. Please ka manta da abubuwan da suka faru a baya mu fuskanci gaba kaci?”

Ganin firar ya koma na tsakanin su, Assistant John ya fi ce tare da ja musu ƙofar.

“abubuwan da suka faru a baya suna da yawan da manta su nan kusa zai yi matuƙar wuya a gareni”

Shiru Professor Zulfa ta yi na ƴan daƙiƙu sai kuma ta ce. “amma dai yau za'a sallame ka ba?”

“a'a”

“to sai yaushe?”

“nima ban sani ba tukunna”

Ya faɗa domin ji yake kamar kar ya bar asibitin bayan kuma yafi kowa ƙosawa da a sallame shi.

“ah,ah wannan mene ne?”

Professor ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaukar ATM ɗin da ya faɗi ba tare da Aliyu ya gani ba.

Da sauri ya ɗauka yana amsa ma ta da faɗin.

“Ba komai”

Kallonsa ta yi a nutse da kuma alamar tambaya sarai ya fahimta sai ya ɗa ge ƙafa yana ɗan murmushin da bai san ya fito ba ya ce.

“Huh, Mom! it's nothing serious fa”

Jinjina kai Professor ta yi tana miƙe wa tsaye tare kuma da kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta.

UMMUL POV.

Koda ta ƙari Police Station ɗin sai da ta yi musu bayanin komai bayan ta sanar da su dalilin da ya kaita na shigar da ƙarar ɓatan mahaifiyarta daga ƙarshe ta basu hoton Mahaifiyar nata sannan ta wuce gida zuwa lokacin an yi isha'i saboda haka a gajiye ta ƙari sa gidan.

Wani bugu mai ƙarfi zuciyarta ta yi lokacin da ta shiga gidan ta yi ido huɗu da motocin Dad da hakan ke nufin ya dawo.

Ajiyar zuciya ta sauke na rashin sanin abin da zai biyo baya ta sa ƙafa cikin Palon bakinta ɗauke da sallama.

*DELTA STATE, NIGERIA*

*JULIETH OSBORN JONAH (Juju) POV*

Tsai-tsaye suke kusan su uku cikin office ɗin da alama tattaunawa zasuyi mai muhimmanci kuma da wanda suke jiran ƙari sowarsa.

Kallon agogon hannunsa Anthony ya yi yana ɗan girgiza kai sai dai bai kai ga furta komai ba a ka turo Glass Door ɗin Office ɗin Kyakkyawar Matashiyar Budurwar da aƙalla zata kai Shekaru Ashirin ta bayyana sanye cikin Doguwar Riga ƙirar Kamfanin Prada sai shoe da bag ɗin ta kuma ƙirar Kamfaninsu daban kuma launin shigar nata Brown ne mai ɗan haske, ba komai a kanta sai ɗan mayafi da ta yafa sai dai kaso mafi yawa na dogon gashin kanta a waje yake, kyakkyawar fuskarta wadace da kwalliya sama-sama, ga ɗan lips ɗin ta launin ja, ƙari sa shiga Office ɗin ta yi lokacin da ta nema iznin shiga Anthony ya bata ta ƙari sa ciki tana zare Glasses dake fuskarta kyawawan manyan idanunta suka bayyana tar dasu, lumshe su take, cikin taku ɗaiɗai ta ƙari ta zauna sannan cikin daddaɗan muryarta mai sanyi bayan ta zauna ɗin ta furta.

“Apologies for keeping you waiting”

Anthony ya yi saurin faɗin.

“No, biggie”

Ta ɗan yi murmushi.

“Julieth... As Known As Juju, right?”

Ɗaya daga cikin sauran mazan dake Office ɗin ya faɗa yana ɗan jan sunan idanunsa ƙur a kanta yana kallon zallar kyau.

“Hey, it's me! Just call me Juju, okay? I'm so over Julieth”

“Okay, Mss Juju, pleasure to meet you”

Ya sake faɗa yana ƙoƙarin miƙa ma ta hannu duk da Akwai tazara daga inda yake tsaye zuwa inda take zaune.

“Me too”

Ta faɗa a taƙaice ba tare da niyyar miƙa masa Hannun ba.

Anthony da ya san za'ayi haka ya sa ya ɗan yi gyaran murya sannan ya furta.

“Mr Jethro wannan ita ce Juju wancan kuma Moses sune nake baka labari kuma zasuyi wannan aikin da kyau domin kwararru ne, musamman ma Juju”

Ya faɗa yanayi ma mutumin nuni da Juju da kuma ɗayan saurayin da bai ce komai ba.

“Okay, i see”

Cewar Mutumin da Anthony ya kira da Mr Jethro.

Anthony ya kalla Juju da saurayin da ya kira da Moses sannan ya ci gaba da.

“kamar dai yadda na sanar daku ne cikin Garin Kaduna shi Guy da aikin naku ya kai kansa yake, wannan kuma shi ne Hotonsa; suna, Jalal Ubaidullah Tarauni, Shekaru Ashirin da Takwas sai...”

“Wait, what? Is he really a Muslim?”

Juju ta faɗa tana miƙe wa tsaye.

“Yeah, he's Muslim. Is there an issue?”

Anthony ya bata amsa shima yana miƙe wa tsayen da ɗan mamaki.

“I'm afraid I won't be able to take on this task. Would it be possible to assign it to someone else?”

“No! Please Juju kar muyi haka dake domin kece kika dacewa da wannan aikin ki faɗa min mene ne matsalar ko aiki da Musulmai ne bakyason yi?...”

“Yes!”

Ta yi saurin bashi amsa tana sauke ajiyar zuciya.

“amma mene ne dalilin?”

Anthony ya yi ma ta tambaya cikin kulawa.

Ajiyar zuciya nannauya ta kuma saukewa sai kuma ta kalleshi tana nazarin amsar da zata bashi domin ita kanta bata san dalilin ba a taƙaice ma dai bata da wani dalili kwakwkwara, kawai dai abin da ta sa ni shi ne; batason tarayya ko wata iri ce ta shiga tsakaninta da mutanen wata ƙila hakan na faruwa ne dalilin yawan jan kunne da Mahaifiyarta ke yi musu ita da sauran ƙanninta tun suna yara ne a kan mutanen, ta yiwu shi ne dalilin ta na farko, na biyu kuma ta yiwu saboda Musulmi ne ya kaɗe Mahaifinta da hakan ya yi silar Ajalinsa har lahira.

Ganin ta yi shiru ya sa Anthony ya ci gaba da faɗin.

“ki yarda dani a duk tsawon lokaci da muke irin wannan aikin ba'a taɓa samun matsala ba kuma ba za'a samu yanzu ba, ki daure ki karɓa aikin nan kinji Juju Please karki bani kunya”

Ya kai maganar yana ɗan marairaicewa duk dan ta yadda dan kuwa ya sa ni muddun ba itan ba, to fa ba za su sama mai kwarewan ta ba, baya da haka ita ta dace da wannan aikin.

Shiru ta yi na tsawon mintuna tana nazari dan bataso a sama matsala shi ya sa ko mene ne zatayi sai ta yi tunani a farko tukunna, yayin da Anthony ya matsu yaji amsar da zata bashi shi kuwa Mr Jethro yafi kowa ƙosawa sai dai har ya cire rai da zata amsa sai kuma yaji ta ce.

“Okay”

Murmushi duk suka yi shi da Anthony a tare sannan Anthony ya ƙara da faɗin.

“Thank you, Juju. And zan turo miki da sauran bayanan ta what'ssapp, sai ki duba sai dai wani abu guda shi ne yau ɗin nan ya kamata wannan mission ɗin ya fara saboda haka yau zaku tafi Kaduna tare da Moses dan kusan tare zakuyi aikin duk da dai nashi shi ne taimaka miki da wasu abubuwan da ba'a rasa ba”

Duk tattaunawar da suke yi cikin harshen turanci ne saboda haka wannan karon sai Juju ta furta.

“shi ke nan ba damuwa”

Cikin harshen Hausa.

Ci gaba da tattaunawa suka yi a kan yadda aikin nasu zai kasance zuwa bayan wasu awanni Juju ita da Moses sun isa Airport da za su hau jirgi zuwa Kaduna, kafin jirginsu ya tashi ne Anthony ya kirata yake sanar da ita idan sun sauka Akwai driver da zai ɗauke su ya kai su zuwa wurin wata daga nan ita ce zata kai su wurin Jalal U Tarauni ɗin. Sai da ya ƙarayi ma ta ƙarin bayani a kan wanene U Tarauni sannan ta kashe wayar, ba jimawa jirginsu ya tashi zuwa Kaduna

Awa guda da minti ashirin jirginsu ya yi landing a filin saukar jirage na garin Kaduna daga nan Drivern da Anthony ya tanadar musu ne ya ɗauke su da kayansu zuwa hotel a can ne Juju ta yi amfani da wannan damar da kuma basirarta a ɓangaren kwalliya ta yi ma fuskarta ɗan uban sun kwalliya irin na ƴan matan ƙauye sak! Ita kanta sai da ta yi murmushi lokacin da ta kalla fuskarta a madubi, riga da zani ta saka sai dai riga daban zani ma daban haka kallabi, sai dai fa an sha danbarwa kafin ta samu ta gama ɗaura zanin dan bata iya ba, lokacin da ta kammala shiryawa sai ta saka silifas sannan ta ɗauki ƙullin kayanta da ta ware da kuma ɗan yaƙunannen kyale ta saka ta fita harabar hotel ɗin inda driver da shi ma Moses da ya canza nasa kamannin sai dai ba shigar Hausawa ya yi ba, suke tsaye duk suka shiga mota domin ƙari sawa wurin Matar da Anthony ya faɗa wa Juju wato Doctor Waiba, a asibiti suka sameta kasancewar lokacin ƙarfe biyar ne na yamma, daga nan aikin drivern da ya kawo su ya ƙare saboda haka koda su ka ƙari sa asibitin wurinta; Juju a matsayin wacce tazo Aikatau daga ƙauye kamar yadda Doctor Waiba ɗin ta nema sai kuma Moses daga kudu a matsayin mai bawa flowers ruwa.

Koda suka yi ma Doctor Waiba bayani dama an sanar da ita zuwan nasu sai ta ɗauke su a mota zuwa gidan da zasuyi aikin wato Gidan Jalal U Tarauni.

Tafiyar Minti goma sha biyar daga asibitin zuwa katafariyar Anguwan da yake zaune ya ɗauke su, koda suka ƙari sa Gidan ba Moses ba ita kanta Juju sai da ta yi santin Gidan duk da ta saba ganin ƙerarru kuma haɗaɗɗun gidaje ƴan ubansu a kudu sai dai wannan tsarinsa da komai ya mugun tafiya da ita kasancewar ba daɗewa Doctor zatayi ba, ya sa lokacin da suka wuce Gate na biyu suka isa zuwa harabar gidan da ya gaji da ƙayatuwa Doctor Waiba ta faka motar sannan ta fito ta nufa ciki Juju da ta rungume ƙullin kayanta a ƙirji ita da Moses suna take ma ta baya.

Lumshe ido Juju ta yi lokacin da ƙafafunta suka taka tattausan carpet ɗin dake baje a ƙaton palon yayin da wani ƙamshi mai sanyi ya baƙunci hancinta sai ta lumshe idon tare da sauke su a kan ginin benen da ya rabu kashi biyu ɗaya yabi right ɗayan kuma yabi left.

“Ku jurani anan ko? bari na shiga na kira Jalal ɗin”

Cewar Doctor Waiba, duk suka jinjina ma ta kai, sannan ta nufa benen da ya yi left.

Kalla-kalle kawai Moses yake yi cikin Palon bakinsa a sake dan shi kam wannan ne karonsa na farko a aiki irin wannan kuma bai saba ganin ƙerarru kuma haɗaɗɗun gidaje ba irin wannan sai dai kuwa a film, mamaki yake na irin haɗuwar gidan har yana tunanin wai dama a na samun irin waɗan nan tantsama-tantsaman gidajen a Nigeria kuma cikin garin Abuja?.

(😂😂 Ina ƴan uwana mutan KD ? ku an tayo mu bashi amsa Please!)

Ita kuwa Juju cikin nutsuwa take ƙare ma komai na palon kallo tana ƙiyasta adadin miliyoyin da a ka kashe ma palon kanshi. Wata kyakkyawar ƙofa ce taja hankalinta hakan ya sa bata san lokacin da ƙafafunta suka jata zuwa wurin ƙofar ba ta sa hannu tare da murɗa handle na wood door ɗin ga mamakinta sai ƙofar ta buɗu yayin da wani sassanyar ƙamshi na daban ya kuma bugun hancinta. Kusan suman tsaye ta yi lokacin da idanunta ya sauka a cikin Ɗakin.

“Aww... Woww Wowwww!!”

Ta furta a hankali kuma a fili tana zura ƙafarta ciki ta yi taku ɗaya biyu a na ukun ne kamar ance ta kalla bangon Ɗakin dake fuskantarta ai kuwa taga kamar bangon yana rabewa, ta ɗan zaro ido tana ƙure kallonta a wurin dan ganin mai zai bayyana ga mamakinta hanya ce sai ga ƙofa ta bayyana a wurin sai dai bata kai ga tunanin komai ba surar kyakkyawar halittar da ta sanya zuciyar Juju dakatawa da bugu na ƴan sakanni ya bayyana, ji ta yi ta kasa motsawa sai kawai ta fara ƙare masa kallo daga ƙasa zuwa sama, ai wani uban ihun da ya firgita Jalal ta kurma tare da ficewa da gudu daga Ɗakin tana sakin ƙullin kayanta, yayin da Jalal da a fari mamakin ganin Mace a Room ɗin ne ya kamasa, sai a lokacin da ta kurma ihu shima sai ya rikice ya rufe kunnensa da duka tafukansa yana rumtse ido sai da ta fita sannan ya fahimci dalilin ihun nata, ai da sauri ya ƙari sa cikin jikin wani bango a Ɗakin da sauri ya danna wasu madannai sai kuwa ƙofa ta bayyana yayin da wacce ya fito daga cikinta ta koma bangon ya haɗe tamkar ƙofa bata taɓa bayyana ba a wurin, cikin hanzari ya zura Gajeren wando da singlet sannan ya fito a fusace daga Ɗakin sai kuma ya tsaya yana kallon Doctor Waiba da ihun Juju ya sa ta sauko ƙasa a firgice tana tambayarta abin da ya faru yayin da Juju ta buɗe idanunta da ta rumtse sai kuwa su sauka a kan Jalal da ya ƙari so wurin saƙon kyakkyawar harara ya aika ma ta, ta yi saurin kawar da kanta yayin da taji gabanta ya faɗi.

“Aunty!”

Jalal ya furta da mamaki yana kallon Doctor Waiba. Murmushi ta ɗan yi lokacin da ta mayar da dubanta gare shi ta furta.

“Au ashe ma kana ƙasa, ke nan kaine ka tsorata ta ko....?”

“who is she?”

Ya faɗa ba tare da ya kula zancen ta ba, murmushi ta sake sannan ta ce.

“Your new domestic staff”

“what?”

Ya faɗa a ɗan kyamace yana taɓe fuska da hakan ya mugun bawa Juju haushi sai ta kawar da kai tana gunguni.

Sarai ya lura da ita.

“Yes, is everything okay?”

“Yep”

Ya amsa ma Doctor yana zama saman luxury Sofa 1 sieter tare da mayar da dubansa kan Doctor Waiba.

“Dakata daga ina kike?”

Muryar nasa ya daki kunnen Ummul da ta zura ƙafarta da niyyar shiga Palon, da ace a baya ne waje zata koma da gudu saboda da gaske muryarsa ma kaɗai tsoro take bata.

Kallonsa ta yi tana ƙari sa shiga ciki ta furta.

“Daga neman Mahaifiyata da ƴar Matarka ta buɗe wa ƙofa ta fita”

“Mahaifiyarki!?”

Ya faɗa da ɗan alamar tambaya daga inda yake tsaye sanye cikin coat da wando.

“E Asma'u ba”

Ummul ta bashi amsa ganin sabon salon da ya ɓullo da shi dan ta lura so yake ya nuna bai gane wa take nufi ba.

Sai taga ya kama kansa da duk hannayensa kamar wanda ya tuna wani abu sai kuma ya dubeta ya sake dubanta da kyar ya furta.

“Okay, go to your Room”

Kamar zata tambaya abin da ya sameshi sai kuma ta share tuna cewa shi ɗin ma ai bai damu da ita da kuma Mahaifiyarta ba. Zata nufa ɗakinta dake ƙasan ta hango Mommy Reyhana da Aminiyarta Hajiya Sara suna saukowa batabi ta kansu ba ta shige ciki, sai dai taso ta tsargu da irin kallon da suke bin ta da shi.

“Alhaji Mukthar Abdallah M.A!”

Hajiya Sara ta furta cikin salo lokacin da suka ƙari sa saukowa ƙasa wurin da Alhaji Mukthar ke durƙushe ya riƙe kansa.

Kallon ta ya yi sannan ya mayar da dubansa kan Mommy Reyhana mamaki ne ya ɗan bayyana a kan fuskarsa, har ya buɗi baki kamar zai yi magana sai kuma ya fasa da sauri ya haye stairs zuwa sama yana faman kwala kira da faɗin.

“Husna! Ma'u!! Asma'u ”

Kallon juna Mommy Reyhana sukayi ita da Hajiya Sara kowacce tana zazzaro ido.

“wai fa kamar Asma'u naji Alhaji Mukthar yana faɗi?”

Mommy Reyhana ta faɗa fuskarta tana nuna tashin hankali ƙarara.

‘Tabbas kuwa yadda kikaji nima hakan naji lallai akwai ƙura, Reyhana taki ta ƙare’

Hajiya Sara ta raya hakan a ranta tana ƴar dariya sai dai kafin ta bawa Mommy Reyhana amsa Ummul ta fito tana ɗan zare ido daidai lokacin kuma Alhaji Mukthar ya dawo ƙasan bai dena kiran sunan Asma'u ba, hankali tashe suma Rifaat da Rahina dake ɗakunansu a saman suka biyo bayansa, ai kuwa yana hango Ummul ya yi ma za ya ƙari sa wurinta yana faɗin. “Asma'u kece shi ne kinaji ina ta kiranki baki amsa min ba?”

Da kallon mamaki Ummul ta bishi yayin da Rifaat da Rahina suka bishi da kallon zautacce ita kuwa Mommy Reyhana ɗaura hannu ta yi a ka cikin tashin hankali dan tasan yau kuma ƙaryarta ta ƙare.....

🔥🔥

_Alhaji M.A's house appears to be on fire! 🙂 There's an enormous amount of smoke!😂_

*UMMUL~JAANNAH🍂💋*

BY; Nainarh KD ✍️