03
by @nkds
_Sabon labari mai tafe da sabon salo, zallar soyayya game da yarda tare da ƙiyayya bita da ƙulli cin amana and so, so on!!!_
*💋UMMUL~JAANNAH✨*
BY: Nainarh KD ✍️
***.
03
“Alhaji wai kuwa kana cikin hankalinka kuwa? ‘Yarka Ummu Jaannah ce fa a gabanka.”
Mommy Reyhana ta faɗa tana ƙoƙarin saita nutsuwarta sai dai hakan ya gagara.
Shi kuwa Alhaji Mukthar kamar wanda shock yaja haka ya yi saurin yanje hannunsa saman fuskar Ummul, sai kuma ya fara bin Mommy Reyhana da kallon tuhuma wurin ya yi tsitt a ka rasa mai furta ƙala a cikinsu. Sai Ummul ce ta yi ƙarfin halin faɗin.
“Daddy kana lafiya?”
Ta faɗa ganin yadda ya ƙara riƙe kansa.
Bai ce komai ba fa ce kamo hannunta da ya yi sannan ya duba Mommy Reyhana da ta sha jinin jikinta ya gyaɗa kai kurum ba tare da ya furta komai ba still sannan ya ja Hannun Ummul zuwa Ɗakin da ta fito. Mommy Reyhana ji ta yi kamar ta yi hauka, dan kuwa ta tsargu da mugun kallon da Alhaji Mukthar ɗin yake watsa ma ta.
“to dai lamari dai bai yi daɗi ba sam, sai dai fatan gyaruwar lamarin, ni dai nayi gabas, ma'assalam.”
Cewar Hajiya Sara tana juyawa da sauri zata bar Palon Mommy Reyhana ta riƙo kyalenta tana faɗin.
“ina kuma zakije Aminiya ki tsaya mu tattauna a kan wannan wutar dake ƙoƙarin kamawa mana mu samo mafita kamar ko yaushe....”
“wai wa! Ba dai ni ba? Allah sitira ai in kin ganni a lahira to aradu kaini a ka yi, saboda haka kije can ki nemo wata Aminiyar ba dai Saratu ba naji ma da zawarcina.”
Hajiya Sara ta sake faɗa tare da kwace kyalenta ta yi gaba ko juyowa batayi ba, duk kuwa da irin kira da Mommy Reyhana take kwala ma ta daga ƙarshe sai Mommy Reyhana da ta ga da gaske Aminiyar nata juya ma ta baya ta yi sai ta fara kutuntumo ashar tana watsa ma ta sai dai a banza domin tuni Hajiya Sara ta fice daga gidan ma gaba ɗaya.
“Mommy ba wannan ne a gabanmu ba tashi zakiyi mu nemo mafita dan kuwa irin kallon da Daddy yake yi miki ya tabbatar min da ba zai kyaleki ba kuma alamu sun nuna ya dawo hayyacinsa sannan kin san menene zai biyo baya....”
“dallah rufemin baki shashasha duk ba kece silar komai ba da har kike da bakin magana”
Mommy Reyhana ta katse Rahina a tsawace tana miƙe wa tsaye da ƙyar sakamakon yanayin jikinta tana da ƙiba.
“ni dai dan Allah Mommy ku bar wannan abun, ku nemo mana mafita kawai, tun da ku ku ka tsara komai Dan Allah ya gani idan Daddy ya ce zai hukunta mu da irin azabtar war da muka yi wa Ummul da Mahafiyarta ni kam ina ga sai dai na mutu dan ba zan iya jura ba”
Rifaat ce ke wannan batu iya kar gaskiyarta, wata uwar harara Mommy Reyhana ta banka ma ta sannan bata sauraresu ba ta wuce sama fuu! Domin nema wa kanta da ƴaƴanta mafita a kan bala'in dake shirin tunkaro su.
JUJU POV.
Ta yi tsaye tana ƙare ma Bedroom da a ka sauketa ciki kallo kuma ya kasance wanda zata zauna ciki, mamaki take da bataji motsin kowa ba a gidan idan a ka cire Ƴan aiki da suma maza ne sai kuma shi kansa uban gayyan Jalal.
Doctor Waiba bata daɗe da tafiya ba bayan ta nuna mata wannan Bedroom a matsayin nata sannan suka ɗan yi fira da Jalal a palo lokacin Juju tana bedroom ɗin tana jin su sama-sama.
Yanzun ma fitowarta ke nan daga bathroom ta fara neman inda ta saka ƙullin kayanta domin akwai wayarta a ciki, shiru ta yi tana nazari sai kuma can ta tuna inda ta watsar da ƙullin kayan, dafe kai ta yi tana ɗan cije lips ɗin ta sannan ta fito daga bedroom ɗin cikin sanɗa ta fara taku domin ƙari sawa Bedroom ɗin dake fuskantar wanda ta fito kuma take tunanin shi ne wanda ta shiga ɗazu har taga abin da ya firgita ta da hakan ya zama dalilin da ta watsar da ƙullin kayan ba tare da ta sa ni ba.
Ɗaura hannunta ta yi a kan handle ɗin ƙofar tana fatan ta kasance a buɗe kuma babu wancan mutumin a ciki wato Jalal.
Cikin Sa'a kuwa taji ƙofar a buɗe, murmushi ta yi ta zura kai ciki da niyyar shiga ke nan sautin muryarsa ta karaɗe wurin da faɗin.
“what do you want in my room?”
Ta firgita kasancewar ya yi maganar ne da amon sauti daɗi da ƙari kuma bata taɓa zato ko tsammani ba hakan ya sa ta juyo a firgice da yake babu takalmi a ƙafarta sai santsin tiles na wurin ya ɗibeta ta yi taga-taga zata faɗi, rumtse ido kawai ta yi tana sauke ajiyar zuciya yayin da Jalal ya yi saurin riƙo ƙugunta ta sai ya kasance shi ya ɗan rankwafa ita kuma tana karkace buɗe ido ta yi suka yi ido huɗu sai ta tsaya kallonsa na wasu ƴan sakanni da sauri kuma ta kyara tsayuwarta cikin rashin abin faɗa tana ɗan kama-kame tare da sosa wuya ta ce.
“dama-dama fa kayana nake nema”
“au wancan abin shi ne kayan?”
Ya faɗa yanayi ma ta nuni da ƙullin kayanta dake cikin dustbin.
Zaro ido ta yi ganin inda ya saka ma ta kayan sai kuma ta dubeshi ko'a jikinsa sai ma juya kai ya yi sannan ya koma ya zauna ajiyar zuciya na fusata ta sauke sannan ta ƙari sa ta ɗauki ƙullin kayan ta koma Ɗaki a fusace yayin da Jalal ya bita da kallo ta gefen ido yana nazari.
Sai dai bai kai ga tunanin komai ba, bayan wasu ƴan daƙiƙu ta dawo Palon a guje kamar wacce a ka korota fuskarta sharkar da ruwa har ga Allah ta ɗan bashi tsoro yanayin yadda ta fito a guje ɗin sai ya miƙe tsaye yana tambayar abin da ya faru.
Haki kawai take tana nuna masa cikin Bedroom ɗin sai da ƙyar ta samu ta furta.
“ba abin monon cikin banɗaki ba ne ya fesomin da ruwa a fuska daga na ɗan taɓa”😅
Jalal bai san lokacin da ya sa sauke ajiyar zuciya ba jin abin da ta faɗa dan shi ya ɗauka wani abin ta gani.
“Mtssw”
Ya ɗan ja tsaki cikin rashin abin faɗa.
“Yallaɓai bakace komai ba? ni tsoro nakeji kaje kawai ka kashe wancan monon in ba haka ba ni ƙauye zan koma abina na fasa aikin”
Ta faɗa murya a shagwaɓe kamar zata fashe masa da kuka.
Ji ya yi ya kasa kataɓus saboda yanayin yadda ta yi maganar ta kashe masa jiki a zuciyarsa ya furta.
‘Allah ya ƙara Jalal da shegen kauɗin ka na canje-canjen ƴan aiki gashi ka haɗu da gamonka Fisabilillah ji fa yadda take neman sakawa ka koma wani sususu cikin awa guda da zuwarta cikin Rayuwarka’
Ajiyar zuciya ya sauke sannan a fili ya furta.
“to yanzu me kikeso a yi?”
“ni kawai kaje ka kashe abin can tun kafin ya lalace kace saina biyaka a to”
Ta katseshi shi da faɗin hakan cikin zallar magana irin ta ƴan ƙauye har da ɗage hannu ta kuma ja baya kamar wacce ta yi gamo da abin tsoratarwa.
Ba musu Jalal ya shige gaba zuwa Ɗakin ita kuma tabi bayansa tana ɗan murmushi dan ba wai bata iya amfani da tap ɗin ba ne kawai wannan ɗin ma yana daga cikin aikin nata ne.
A bakin ƙofar bathroom ɗin ta tsaya yayin da Jalal ya shiga ciki ya kashe tap ɗin sannan yana tsaye a wurin ya dubeta tare da yi ma ta alama da ta ƙari sa ciki, kamar ba zata ba sai kuma a ɗan tsorace ta shiga ciki ya buɗe baki zai yi magana ta riga shi da faɗin.
“aradu ba ruwana bani na lalata maka nomo ba au mono, kawai fa ɗan taɓa nayi kamar haka fa ka.....”
Ta faɗa tana kai hannu wai dan ta nuna masa irin taɓar da ta yi aikuwa ruwa ya sake fesowa.
Ihu ta kurma tare da ɗafewa jikinsa ta rufe fuskarta a saman chest ɗin sa tana sauke ajiyar zuciya.
Da dabara Jalal ya samu ya kashe tap ɗin sannan ya janyeta daga jikinsa yana faɗin.
“Are you mad? Baki da hankali ne zaki rungume wanda ba muharramin ki ba...?”
“muharrami? Wanene haka?”
Ta tambaya da iya gaskiyarta tana ɗan ya mutsa fuska.
Da kallon mamaki ya bita sai kuma furta.
“bakisan mene ne muharrami ba?”
Jinjina masa kai ta yi alamar E.
“What is your name?”
“huh?”
Ta faɗa da nuna alamar batasan me yake nufi ba.
Dafe kansa ya yi yana ɗan fitar da huci ya sake kallonta tare da furta.
“sorry i mean, mene ne sunanki?”
“au! sunana, Julieth a'a Juju, Juju ne sunana”
Ta sama kanta da kasa yi masa ƙarya wurin faɗar sunanta duk kuwa da hakan ya saɓa wa dokar aikin nata.
“oh you're not a Muslim?”
Ya sake faɗa yana nunata da ƴatsa.
Jin ya ambaci Muslim ya sa ta gyaɗa masa kai.
Shiru ya yi jikinsa a ɗan sanyaye, ‘au ashe ma ba musulma ba ce?' ya raya a ransa, sai kuma yaji ta bashi tausayi.
“Okay”
Kaɗai ya furta sannan ya fi ce daga bathroom ɗin sannan ya bar Bedroom ɗin gaba ɗaya maimakon ya koma inda yake zaune a Palon sai kawai ya haye sama cikin sassarfa.
Ita kuwa Juju jiki a ɗan sanyaye ta dawo ta zauna gefen gado ta ma rasa wani tunani zatayi abin da ta sani shi ne kawai ta yi ƙoƙari ta gama aikin nan cikin sauri ta yi gaba abin ta dama ba wai tazo ne dan zama ba.
‘wait Juju, me kike ci na baka ke zuba, kin manta yanzu a ka fara wasar, to kuma menene na sauri? Ki tsaya kawai ki nutsu ki kuma bi komai a hankali har ki kammala wannan aikin kiyi gaba abin ki dama ba zama ya kawoki ba.’
Zuciyarta ke yi ma ta wannan zance, shiru ta ɗan yi kuma ta ba kanta kwarin gwiwa ta hanyar faɗi a fili.
“dole na san yadda zan yi cikin wata guda Mutumin nan ya fara sona daga nan ni kuma zan yi abin da ya kawoni na ƙara gaba.”
Sai ta yi shiru sannan ta miƙe tare da ciro wayarta cikin ƙullin kayanta ta kunna Data ta shiga What'ssapp ɗin ta ta turawa Anthony saƙo.
Alhaji Mukthar da ya yi shiru tun bayan shigarsu Ɗakin shi da Ummul yana sauraren maganganun da su Mommy Reyhana ke yi ta waje har sai da yaji alamar gaba ɗaya sun yi sama sannan ya juya yana kallon Ummul da take bin sa da kallon mamaki ajiyar zuciya ya sauke tare da furta.
“wata ƙila a baya da bana cikin hayyacina ban kyautata miki keda Mahaifiyarki ba amma Dan Allah ki gabarceni ki kuma bani dama a karo na biyu na gyara kuskure na sannan ki sanar dani ina Mahaifiyarki take?”
Shiru Ummul ta yi kamar ba zata tanka ba sai kuma ta furta.
“ni da mahaifiyarta Bama buƙatarka cikin rayuwarmu saboda haka ka koma can wurin Ƴar lelen Matarka da ƴaƴanka abin so....”
Ta kai maganar tana fashewa da kukan da take ta ƙoƙarin ganin ta riƙe amma ya cutura.
Alhaji Mukthar ya yi kasaƙe yana dubanta ita kuwa cikin kuka ta ci gaba da faɗin.
# UmmuJaan
# Aliyu Haidar
# Juju Julieth
# Jalal
# Dr Waiba
# UMMUL~JAANNAH 🔥
# Nainarh KD ✍️
# ***