UMMUL~JAANNAH

07

by @nkds

*❤‍🔥UMMUL~JAANNAH❤‍🔥*

***

By: Nainarh KD.✍️

07

WAIWAYE....

WANENE ALHAJI MUKTHAR?.

Mukthar Abdallah shi ne cikakken sunansa haifaffen ƙaramar hukumar Dass ne dake jihar Bauchi ya taso su Biyar ne wurin Mahaifansa yayin da ya kasance shi ne na biyu cikin yaran Malam Abdallah, tun Mukthar yana ƙarami a ka kai shi jahar Kaduna karatun allo Saboda haka a can ya taso har girmansa sai dai lokaci-lokaci ya ke kai ma gida ziyara sai dai duk da kasancewar karatun allo ya yi amma yana da ilimin boko har matakin Degree sakamakon tallafawar Mutumin da ya riƙe shi tun yana yaro lokacin da a ka kaisa garin Kaduna ya fara aiki a gidan Mutumin shi ne da ya lura yana son karatu kuma yana da hazaƙa sai ya nema izni wurin Malaman Mukthar na makarantar allo da su bari ya saka shi a makarantar boko, da farko basu amince ba amma da Alhaji Saleh ya matsa shima kuma Mukthar ɗin ya dage a kan yana so, sai daga baya suka bari Alhaji Saleh ya saka shi a makarantar. Lokacin da ya kammala secondary school sunansa ya shiga cikin waɗan da gwamnati ta ɗauki nauyin karatunsu har zuwa kammala matakin Degree.

A lokacin da ya kammala degree ne kuma sai bai sama aiki ba, yayin da ta gefe guda kuma soyayya mai ƙarfi ce ta ƙullu tsakaninsa da Reyhana ɗiyar Marigayi Alhaji Saleh domin Shekaru biyar da suka gabata Allah ya yi masa rasuwa dalilin hatsarin mota.

Bala'in so Mukthar yake yima Reyhana kuma yanajin zai iya yin komai a kan ta yayin da ta gefen Reyhana ta kasance bata wani damu da shi ba duk da tana sonshi sai dai bai kai wanda yake yi ma ta ba dalili kuwa shi ne baya da gumbar susa ita kuma ta gama tsara yadda zata gudanar da rayuwarta na jin daɗi cikin gidan hutu da daula, sai dai an sama a ka sin lissafi sakamakon soyayyar wannan ɗan bafulatanin da ta yi ma ta kamun kazar kuku da ita kanta bata san lokacin da hakan ya kasance ba kuma ta yi iya yin ta don ganin ta yakice son shi daga zuciyarta sai dai abu ya cutura domin batajin ma idan ta rabu da shi zata sama mai kyau da nagartarsa ga nutsuwa ga kyawu duk da ita ba waɗan nan ne a gabanta abin da sani shi ne jin daɗi.

Tun suna ɓoye wa har a ka zo a ka fahimci irin alaƙar dake tsakaninsu a lokacin ne kuma a ka sha artabu da mahaifiyarsu Reyhana Mace mai son abin duniya, domin ta rantse ta maye ƴarta ba zata aura talaka kuma almajirin Mahaifinta ba, sai dai da yake Reyhana tana son Mukthar kuma tana ganin ba matsala ba ne tun da har ya gama karatunsa na Degree aiki mai sauƙi ne sai ma wanda ya zaɓa.

Hakan ya sa ita ma ta baɗama idonta toka ta rantse sai Mukthar idan kuma ba shi ba sai rijiya.

Sosai a ka kai ruwa rana kafin daga bisani Hajiya Rahama ta amince Reyhana ta auri Mukthar sai dai ta ce koma mene ne ya biyo baya babu ruwanta ciki tun da ita Reyhana ta ce taji ta gani sai Mukthar.

Wata ɗaya a ka saka bikin a lokacin kuma cikin amincewar Ubangiji lokaci ya yi a ka sha biki amarya ta tare a gidan angonta dake Anguwan nupawa cikin garin Kaduna da shima mahaifinta Alhaji Saleh ne ya mallaka wa Mukthar ɗin halak malak kafin rasuwarsa.

Da ɗan bugabugan da Mukthar ya samu yana yi ne suke samun na rufin asiri watanni uku da Auren ciki ya bayyana a jikin Reyhana, Mukthar ya yi murna sosai da samun wannan ciki yayin da Reyhana batayi murna da wannan cikin ba domin zuwa yanzu ta fara data sanin Auren Mukthar Mutun sai baƙin talauci a cewarta, ta manta Allah shike bayarwa da hanawa, yayin da gefe guda ƙawaye da ƴan uwanta masu baƙin cikin ta aura Mutum mai nagarta kamar Mukthar daɗi da ƙari yana matuƙar son ta sai suka shigo fagen, kowa da irin nasa zugar musamman ma masu yi ma ta baƙin ciki tun Reyhana bata ɗauka har ta fara ɗaukar karatun zugar ta tsana Mukthar da talaucinsa cikin ma ta yi duk inda zatayi domin ganin babu shi amma abu bai yiwu ba gashi kuma kullum ƙara dullmiya cikin baƙin talauci suke.

Da ƙyar ta yi haƙuri ta iya kai wa lokacin da ta haihu a gidan Mukthar domin yaƙi sakinta duk kuwa da irin rashin mutuncin da take zuba masa domin ta gaji da shi ta gaji da zama cikin talauci.

Namiji ta haifa saboda haka yaro yaci suna Ra'em a lokacin ne kuma Reyhana ta ƙara ɓalle masa da sabon rashin mutunci a kan sai ya sake ta. A taƙaice dai Ra'em yana da shekara ɗaya a Duniya Mukthar ya rabu da Reyhana, zo kuga farin ciki wurinta ita da Mahaifiyarta suna ganin sun yar da kwallon mangwaro sun huta da ƙuda.

Ba da jimawa ba kuwa Reyhana ta yi wani auren domin kuwa shi kansa Ra'em ɗin ba tausayi ta tsige shi daga mama ta kuma bar wa ubansa dole sai Mahafiyarsa ya kai ma ta ci gaba da kula da yaron.

Wani Alhaji Mai Dukiya Reyhana ta samu domin basuyi wata biyu da haɗu wa ba a ka ɗaura aure, lokacin ta gama idda da wata guda ke nan.

A yadda yake nuna ma ta ita da Mahafiyarta shi cikakke kuma hamshaƙin mai kuɗi ne hakan ya sa suka ruɗe ganin irin ruwan kuɗin da yake zuba musu gudun kar ya suɓuce musu ya sa sukai sunansa wurin boka domin a maƙalar musu da shi sai abin da suke so zai yi, ai kuwa hakan ce ta faru shi ya sa nan da nan a ka yi Auren sai dai me?

Aure da wata guda abubuwa suka fara sukurkuce ma Alhaji Idi Naira an yi ruwa an ɗauke gaskiya ya bayyana, domin shi ɗin mugun faƙiri ne ta wani ɓangaren ma gwara Mukthar da shi domin shi Alhaji Idi Naira koda gidan kansa bashi da shi ga bashi da ya yi masa ƙatutu kuɗin ma da yake musu facaka da su duk zallarsu bashi yake ci da kayan dayake sakawa har da mota hatta lefe na ji da gani da ya danƙarawa Reyhana duk arosu ya yi domin ko sati ba'ayi ba da Auren ya saka a ka biyo dare a ka kwashe ya mayar ma masu shi sai ya tsara abin ya kasance kamar ɓarayi ne suka sata. Reyhana ta yi kuka da baƙin sai dai ba yadda zata yi hakan nan ta haƙura, sai kuma ba'ayi wata da biki ba shima gidan da suke mutumin mai gidan yazo ya karɓe gidansa dama haya Idi ya karɓa kuma yaƙi ya bashi kuɗinsa. Duniya ta yi ma Reyhana zafi domin sai da lokaci ya ƙure ma ta ta lura da irin gagarumar kuskuren da ta tafka gashi lokacin har ciki gareta gashi duk irin rashin mutunci ta yi ma Idi dan yaji haushi ya saketa amma abu ya gagara wani lokacin ma sai dai ya ƙare da zane ta haka zata yita fama da ciwon jiki. Har wurin bokan da ya yi musu aiki suka koma wai dan a karya aikin amma boka ya ce an riga an yi, karya aiki ba zai yiwu ba sai dai su ɗauki na annabawa basu dandara ba suka sake komawa wurin wani shima ba riba haka suka haƙura.

A taƙaice dai da ƙyar Reyhana ta samu wannan bawan Allah Idi ya saketa shima ɗin badan yaso ba sai dan Malamin da suka haɗa da shi ya yi aikin da a dole ya saketa zuwa lokacin kuma ta haihuwa Mace Yarinyar taci suna Rahina kuma a lokacin da Reyhana da Idi suka rabu Rahina tana da shekaru biyu a duniya.

A lokacin Reyhana bata sake Aure da wuri ba domin wasu har an fara tunanin zata koma gidan Mukthar ne kasancewar har zuwa lokacin bai ƙara Aure ba sai dai ita Reyhana babu wannan lissafin a kan ta duk da ta sha wahala gidan Idi amma bata saduda ba shekara guda da rabuwarta da Idi suka haɗu da wani Alhaji Mai mahaukatan kuɗi suka fara zuba soyayya inda ya tabbatar ma ta da ya taɓa aure sai dai matar tasa bata taɓa haihuwa ba har ta rasu, Reyhana bata fara sauraren Alhaji Zubair ba har sai da ita da mahaifiyarta suka bincike suka tabbatar da shin ɗin mai kuɗin ne da gaske sannan ta fara kulashi bada jimawa ba kuma a ka sha biki Amarya ta tare sai dai mene ne zai biyo baya?

Watanni uku da Aure Alhaji Zubair ya canza ma ta gaba ɗaya munanan halayensa suka fito har daga ƙarshe ta gane cewa ta kawo kanta mahallakarta ne domin Alhaji Zubair dai ɗan ƙungiyar asiri ne kuma duk matan da yake aura shi ne ajalinsu da dama zallarsu kwaɗayi ne ya saka su aurenshi.

Sai lokacin Reyhana ta gane Annabi ya faku domin ashe wahalar da ta sha a gidan Alhaji Idi nafila ce a kan ta gidan Alhaji Zubair, domin shi ga kuɗin da sai dai ba daman ci kuma ba kwanciyar hankali sai lokacin ta fahimta ta ƙara tabka babban kuskure na biyewa son zuciya har ta rabu da Mukthar mai ƙaunarta ta jefa kanta cikin halin ha'ula'i.

Jin daɗinta ɗaya shi ne da batayi ciki ba a gidansa sai dai murnarta ta koma ciki ne lokacin da shi Alhaji Zubair da kansa yake sanar da ita Akwai ciki a tare da ita kuma bada jimawa ba zai mallaka wa ƙungiya wannan ɗan tayin dake cikinta.

Duk da kasancewar bata ƙaunar haihuwa da shi amma ta shiga matuƙar tashin hankali da jin kalamansa nan ta fara ƙoƙarin ganin ta nemo hanyar rabuwa da shi sai dai abu yaƙi yiwuwa dan albishir ya yi ma ta da wannan gida shi ne gidanta na har ta mutu domin in an shiga ba'a fita.

Za'a iya cewa tsawon rai da kuma rabon kwana shi ne dalilin rabuwar Reyhana da Alhaji Zubair ta bar gidansa lokacin cikin jikinta yana tsoho a taƙaice dai a gida ta haihu shi ma ta haifa Mace ta saka ma ta suna Rabi'ah. Suna kiranta da Atuh.

Rabi'ah tana da watanni uku a duniya dubun Alhaji Zubair ya cika asirinsa na duk munanan abubuwan da yake yi ya tonu ai kuwa mutane ba tare da jiran hukuncin hukuma ba suka banka ma gidan wuta lokacin yana ciki ya ƙone a ka rufe babinsa sai dai ƴarsa Rabi'ah da zata taso cikin maraici a lokacin wata yayarsa taso Reyhana ta bata Rabi'ah ta ci gaba da kulawa da ita amma fir Reyhana taƙi yarda haka ta haƙura.

Aka ce mai hali baya fasawa. Rahina tana da shekaru huɗu yayin da Atuh take da Shekara ɗaya da watanni Reyhana ta sama labarin Kuɗin da Mukthar ya yi domin tun bayan rabuwarsu ko labarinsa bata ƙaunar ji sai yanzu da ya fara zama hamshaƙin mai kuɗi kuma ta sama labarin ya yi Aure wai ya aura wata Balarabiya mai suna Asma'ul Husna da ita ce silar Dukiyar nasa. A cewar ƴan gulma.

Hankalin Reyhana dana Mahafiyarta ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin sagegeduwar da suka yi har Mukthar ya suɓuce musu gashi dabara ta ƙare ma ɗan kada.

Sai Reyhana da taci a yanzu kuma duk Duniya bata da wanda take so da ƙauna sama da Mukthar ta fito da tsifar yawan kiransa a waya shi kansa bai san inda ta sama lambarsa ba tun baya kulata har ta yi nasara a kan sa kuma duk silar aikin bokansu ne, sai dai duk da hakan Mukthar bai bari matarsa Asma'u ta sani ba domin ba ƙaramin so da ƙauna yake yi ma ta ba da Dukiyarta ne sila daɗi da ƙari kuma a kan sa ta bar kowa nata ta bishi suka gudo suka yi aure shi ya sa baya ƙaunar abin da zai sa taji babu daɗi domin batasan kowa ba sai shi.

Soyayya ta dawo sabuwa tsakanin Reyhana da Mukthar har a ka wayi gari an sake ɗaura musu aure a lokacin ne kuma Reyhana ta matsa sai da ya haɗa musu gida da Asma'u Baiwar Allah wacce duk da ƙarin Auren da mijinta nata Mukthar ya yi ba tare da ya sanar da ita ba abin ya yi ma ta zafi ga kuma wasu halaye waɗan da bata san shi da su ba da ya fito da su haka ta ci gaba da haƙurin zama da shi a lokacin da Reyhana ta shigo gidan sai zaman ya sauya salo kuma a lokacin Asma'u tana da ƙaramin ciki da sai da Reyhana ta tabbatar ta ɓarar da shi sannan hankalinta ya kwanta ba jimawa kuma ta sama ciki sai ta ƙara fito da sabon salo na rashin mutunci sai dai duka Asma'u tana ƙoƙari ta sanye kasancewarta mace mai haƙuri.

Har cikin Reyhana ya isa haihuwa ta haifa ɗiyarta mace ta ci suna Rifaat.

Rifaat tana da watanni a Duniya ciki ya sake bayyana a jikin Asma'u sai dai wannan karon duk yadda Reyhana taso ta ɓarar da shi abu bai yiwu ba har sai da ya fito Duniya Asma'u ta haifa Mace Yarinya taci suna UMMUL JAANNAH da Asma'u'n ce ta roƙi Mukthar a kan ya saka sunan.

Sai ya kasance tana kiranta da Ummul ko kuma Jaannah sai dai tafi kiranta da Ummul.

Ummul tana da shekaru biyu a duniya Rayuwa ta fara yi ma Asma'u zafi domin ƙiri-ƙiri Mukthar da ya zama Alhaji ya juya ma ta baya sai fara zuba ma ta zallar rashin mutunci duk a kan kar ta bijiro da sai ya bata dukiyarta da sune kuma duk rufin asirin nasa domin ko ficika babu nasa a cikin domin sau da dama ya sha ya ware kaɗan daga ciki wai dan ya fara wani business da su a ƙarƙashin sunansa sai dai abin ya cutura dan watse wa yake ya rasa ta inda kuɗin ya bi tun yana yi har ya haƙura shi ya sa ya fara wulaƙanta Asma'u dan a tunaninsa inba hakan ya yi ba zata iya takurawa ya bata Dukiyarta ita kuma Reyhana da ta ga Asma'u'n ta koma da ita da babu duk ɗaya a wurin Mijin ya sa ta yi mai gaba ɗaya ta yi asirin da ta mallakeshi sai abin da take so yake saurara ita kuma ta ci gaba da mulkar gida kuma tun da ta haifa Rifaat bata sake haihuwa ba sai bayan wasu shekaru ta haifa ƴan biyu mace da namiji daga nan haihuwar ta tsaya, yayin da ita kuma Asma'u tun daga haihuwar Ummul bata ƙara ba sai baƙin ciki da take kwasa da kyara ita da ƴarta a wurin matar gida.

Abin har mamaki yake bata yadda Mukthar ya sauya ma ta ya nuna butulci ƙarara a gare ta.

Ita kuwa Reyhana Rayuwa sabo mai cike da jin daɗi takeyi ita da yaranta a gidan Mukthar domin Ra'em ma tun tuni ta karɓo shi a wurin mahaifiyar Mukthar, Atuh ce kawai take Hannun Mahafiyarta amma har Rahina tuni ta koma hannunta.

Azabtar wa kuwa babu kalar da batayi ma yar Asma'u wato Ummul.

Daga ƙarshe ma Ummul tana da shekaru goma a duniya Reyhana tasan yadda ta yi ta haukata Asma'u kuma hakan bai sa ta dena azabtar da Ummul ba a taƙaice dai faɗar irin wahala da azabtar war da Ummul ta sha a hannun Reyhana ba mai ƙare wa ba ne domin akwai lokacin da ba tare da Ummul ɗin ta yi ma ta komai ba ta saka ƙarfe a wuta ya yi zafi ta ɗoɗana ma ta a baya a lokacin Ummul tana da shekaru goma sha uku kuma ta sha wuya domin kamar ba zata rayu ba kuma duk tsawon waɗan nan shekarun cikin lalurar hauka Asma'u ta kasance har zuwa Ranar da Rahina ta buɗe ma ta ƙofa ta bar gida asirin dake jikin Mukthar kuma ya fita.

WANNAN KE NAN.

CI GABAN LABARI.

Mu tara next page....

___

Jama'a ku jiyemin wannan lamari dai wannan ai shi ne a dakeka a hanaka kuka, a ce an sama mace da mijinta amma a ke yi ma ta wannan bak'ar izayar.

Wallahi tallahi mata muji tsoron Allah mu kuma dena mu fa kiyaye Duniya ba mattabata ba ne, a bar kishi na hauka da ba zai amfane Mutum da komai ba sai Babbar asara da taɓe wa.

Kafin kaji mace ɗaya ta je gidan boka a kan wani abun daban zaka sama mata sama hamsin da suka je a kan namiji. Namiji! Namiji dai kuma zalla a kan kishi ne abin da ba zai amfane mu ba a lahira a Duniyar ma na ɗan lokaci ne.

Allah ya kyauta, masu hali kuma irin na Mommy Reyhana Allah ya sa su daina.

______

KUNA INA! NACE KUNA INA NE MUTANE NA??

KU MARMATSO KUSA KUJI WANI BATU!!!

Labarin Ummul Jaannah labari ne miƙaƙƙe ma'ana da ɗan tsayinsa ba laifi kuma Littafin na kuɗi ne a kan farashin Naira Ɗari biyar kacal, (500₦. Only) sannan free page's suna dab da ƙare wa saboda haka Indai kinaso wannan tafiyar ta kasance dake sai ki biya kuɗin ki kiyi karatu cikin sa'ada.

Ku tura kuɗaɗen ta wannan asusun:

8081129487. Sabi'u Khadija, MoniePoint Mfb.

Sai ku tura shaidar biya ta nan.

Chat via WhatsApp.

***.

Telegram

kuma.

***.

Sai najiku. Kada a manta saura kaɗan free page's su ƙare.