09
by @nkds
*❤🔥UMMUL~JAANNAH❤🔥*
Perfectly Pen's.
By: Nainarh KD✍️
09
“Sannu da ƙoƙari Baabaa Ladi aiki kike ta fama har yanzu ba hutu?”
Murmushi Baabaa Ladi ta yi tana faɗin.
“Yo ke kuwa ‘yar nan ai kwara nayi aikin tun da shi ya kawoni kuma banaso ya kasance ban ƙari sa ba Yallaɓai Jalaluddin ya dawo.
Taɓe baki Juju ta ɗan yi jin ta ambace shi, sai kuma ta furta.
“Au! Kice baya nan ke nan?.”
Ta faɗa tana kyatsine fuska.
Sarai Baabaa Ladi ta lura sai ta yi murmushi tare da bata amsa da faɗin. “E, ya tafi asibiti duba ɗan uwansa kuma Abokinsa ya yi hatsari ɗazu.”
“Ayya!”
Juju ta faɗa dan batasan da mai zata ƙara ba daga haka.
Baabaa Ladi ta ƙara faɗin.
“Kamar dai an sama rashin fahimta tsakaninki da Yallaɓai Jalaluddin ko?”
“Ba wani abu ne ba fa tsakaninmu.”
Juju ta faɗa a taƙaice.
Baabaa Ladi ta sake murmushi sannan ta ɗan yi shiru na sakanni sai kuma ta ce.
“Ko mene ne zakiga ya yi kiyi masa uzuri.”
Da mamaki Juju ta ce.
“kamar ya ya?”
Baabaa Ladi ta ci gaba da.
“saboda ya cancanci a yi masa uzurin a koma mene ne ya aika ta, tun yana da shekaru goma sha Biyar ya rasa iyayensa lokaci ɗaya dalilin hatsarin mota ya dawo bashi da kowa sai Ƙanwar sa da suke ciki ɗaya sai kuma yayyinsa da suke uba ɗaya wato Doctor Waiba da Professor Zulfa sai kuma wani attajiri yana zaune a Abuja, a hannun Professor Zulfa ya taso shi da Ƙanwar nasa da yake kansu ɗaya da yaron wurin Zulfa ɗin wato Aliyu sai kuma ɗan wurin Doctor Waiba wato Aamir duka su ukun sun taso ne kan su ɗaya kuma cikin shaƙuwa da ƙaunar juna sai dai daga bisani wani dalili ya yi sanadin rushewar amintar dake tsakaninsu da Aamir dalilin son zuciya da hassada na Aamir da sanadin hakan yanzu haka yana nan babu ƙafa ɗaya.”
Juju ta kama baki cike da al'ajabi jin Baabaa Ladi ta yi shiru yasa cikin sanyin jiki dana murya ta furta.
“to mene ne abin da shi Aamir ɗin ya aikata haka har ya raba alaƙar amintar dake tsakaninsu kuma ya ƙare babu ƙafa ɗaya, sannan dama ina son sanin dalilin da ya sa Jalal yake zaune shi ɗaya a gidan nan ina Ƙanwar tasa take? Sannan shima Aliyu'n yana ina kuma me ya sa duk da abin da ya faru amma Doctor Waiba take nuna kulawarta ga Jalal ɗin.”
Murmushi kurum Baabaa Ladi ta yi tana wanke hannunta a sink ta ce.
“Aliyu shi ne wanda ya yi hatsari shi ne dalilin fitar Jalal domin ya dubosa, ita kuma Doctor Waiba wannan karma ki saka ta a lissafin mutane masu yafiya duk da bana da tabbaci amma nasan bata haƙura ba da abin da ya faru kuma tana nan tana shirya hanyar ɗaukar ma ɗan ta fansa domin gamsheƙa ce ita akwai ta da sauya kala, yanzu Sallah zan yi lokaci ma ya ƙure amma nayi alƙawarin sanar dake abin da ya faru tsakanin Jalal, Aliyu, da kuma Aamir har da wani sirri ma daban.”
Baabaa Ladi ta kai maganar tana duban yanayin Juju.
“wani sirri ke nan?”
Juju ta faɗa hankali kwance tana ƙoƙarin kurɓan juice ɗin da Baabaa Ladi ta haɗa ma Jalal ta ɗiba a cup zata kai baki.
“labarin soyayyar Jalal mana ko baki so?”
Za'a iya cewa kusan kwarewa da juice ɗin Juju ta yi, da sauri ta a je shi gefe tana ɗan tari ta duba Baabaa Ladi ganin yadda ta zuba ma ta ido tana murmushi ya sa ta ce.
“uhm-ahm mai zai hana ai kuwa inason ji amma ina mamakin yadda yake a haka ba Aure ƙato dashi.”
Ta ƙari sa tana murmushin yaƙe.
Dariya Baabaa Ladi ta yi kurum sannan ta ce.
“ni dai yanzu Bara naje nayi Sallah tukunna.”
Shiru Juju ta yi a ƙasan ranta tana maimaita kalmar na 'Sallah' tanajin yadda zuciyarta ta kwaɗaitu da son sani. Duk da ba wannan karon ta saba ji Musulmai suke ambaton kalmar ba, ta kuma lura da yadda suke mugu-mugun bata lokacin ta.
Ajiyar zuciya ta sauke da ya yi daidai da jiniyar kwanin motocin Jalal da suka karaɗe gidan alamar ya dawo ke nan.
Ta ɗan taɓe baki tana faɗin.
“an cika mana kunne da ƙara har da wani jiniya.”
Ci gaba da zama a kitchen ɗin ta yi dan bataso su haɗu da shi sam sai ta fara aikin da tuni Baabaa Ladi ta gama.
Tana nan a kitchen ɗin bayan wasu ƴan mintina a tunanin ta ƙila zuwa yanzu ya shigo har ya haura sama, hakan ya sa ta juya domin ta bar kitchen ɗin ta koma Ɗakinta cak ta dakata ganinsa tsaye a bakin ƙofar kitchen ɗin ya harɗe hannu a ƙirji yana dubanta da fararen idanunsa masu launin gunmetal Blue da su.
Cak! Ta tsaya ba tare da ta iya ƙara taku ba.
“Hey come here.”
Ya yi maganar kamar da ƙaramin yaro yanayi ma ta alama da ta ƙari sa inda yake. Juju ta ɗan zaro ido tana nuna kanta sannan ta ce.
“Ni?”
Ya kuwa jinjina ma ta kai yana ɗan lumshe ido kamar mai jin bacci.
Ba musu ta fara taku domin ƙari sawa dan taga abin da yake shirin yi.
“Biyo ni.”
Sai ta tsaya tana maimaita kalmar 'Biyo ni' a ƙasan ranta tare da ƙoƙarin tattara ma'anar da kalmar ke nufi, sai dai bata kai ga tunanin komai tabi bayan nasa kamar yadda ya faɗa ganin ya yi gaba, stairs ya nufa ya fara taka wa a hankali, dan ta ƙure shi ta kuma ga abin da yake nufi da ita ya sa tabi bayansa har zuwa cikin palon dake sama daga nan ya ƙari sa wurin wata ƙofa ya buɗe sai ga wani palon wanda bai kai na sama da ƙasa girma ba amma duk ya fi su haɗu wa da tsaruwa tana ƙare ma palon kallo taga ya nufa Bedroom wannan karon dakatawa ta yi da tafiyar ta dubesa gabanta na bugawa tana ƙoƙarin hana zuciyarta tunani a kan abin da ya ke nufi, ta buɗe bakinta na ɗan rawa ta ce.
“i-ina kuma zaka kaini?”
Tambayar nata da kuma yanayin yadda ta yi maganar ta matuƙar basa dariya hakan ya sa ya ɗan murmusa tare da faɗin.
“ki shigo ki gani ai ba cinye ki zan yi ba.”
“nima ai ban ce cinyenin zakayi ba.”
Ta faɗa tana kawar da kai da kuma gunguni.
“me kike faɗi.”
Da sauri ta ce. “ni fa ban ce komai ba.”
“okay.”
Ta furta tare da nufar Ɗakin. Turo baki ta yi tare da bin sa ciki sai ta tsaya da mamaki ganin ashe ba bedroom ba ne, bathroom ne da ya gaji da haɗu wa sai ba komai ciki sai wani haɗaɗɗden sink da shower sai abin da ba'a rasa ba tun kafin ta gama tunanin dalilin kawota ciki da ya yi taji ya furta.
“Ƙari sa gaban sink ɗin ki buɗe bakin.”
Dariya ta ɗan yi cikin rashin fahimtar abin da yake nufi ta buɗe baki zatayi magana sai kuma taga abin da yake yi.
Sabon Brush ya ɗauko tare da matsar toothbrush ya nufa bakinta yana sake furta buɗe.
Da sauri Juju da mamaki ya cika ta ta ce.
“da..dakata please me kake nufi ne wai?”
Ta faɗa tana ɗan ja da baya.
“zaki gani yanzu.”
Ya faɗa yana kamota tare da ƙari sar da ita gaban sink ɗin a dole ya sa ta buɗe baki ya fara yi ma ta Brush kamar wata ƙaramar Yarinya. Juju tana ji tana gani ya ƙalƙale ma ta bakin tass har yaa jini dan mugunta a ganinta.
Miƙe wa ta yi bayan ya gama duk da taji daɗin bakin nata dan ta gaji dama amma sai ta cuno baki ta ce.
“Na gode.”
Bai ce komai ba ya fara ƙoƙarin cire hular da ta rufe kanta da shi. Dan ba halayyarta ba ne zama ba hula ko'a ina ne.
“ah ah yanzu kuma me kake shirin yi ne?”
Ta faɗa tana ɗan zaro ido tare da ja baya.
“dubawa zan yi ko shima kan yana buƙatar gyara.”
“to idan ma yana buƙata mai zakayi masa?”
“sai na aske shi kawai.”
Ya faɗa lokacin da ya sama nasarar buɗe kan nata ya cire hular ita kuma ta rumtse ido.
Sai ya tsaya cak! Da mamaki sai kuma ya cire ribbon ɗin kanta nan take gashin nata da ta faka ya warware ya sauka har gadon bayanta mai kyau da shi ga laushi sai ƙamshi yake fitarwa gashi an gyara shi in curly style.
Ganin yadda ya yi Shiru ya kuma dakata yana duban gashin nata yasa ta yi saurin karɓe hularta da ribbon ɗin cikin turo baki ta furta.
“kaje ka buɗe min gashi zaka ya mutsa min baka san tattalin shi da nake ba.”
Ta faɗa bayan ta mayar da hular duk da bai rufe gashin ba ta fito daga bathroom ɗin ta bar Jalal tsaye bai ma san tunanin mai yake ba.
Ƙasa ta sako da sauri ta shige Ɗakinta har da saka key ta jingina bayan ƙofar tana dafe daidai saitin zuciyarta tare da sauke ajiyar zuciya.
____
Wannan shi ne second to the last Free page's.
Idan kin shirya biyan kuɗin ɗari biyar, (500) sai ki tura ta nan.
8081129487. Sabi'u Khadija, MoniePoint Mfb.
Sai ku tura shaidar biya ta nan.
Chat via W
hatsApp.
***.
Telegram kuma.
***.
Sai najiku.
NainarhKD ❤️