FEERYAL

5

by @rasheedasdirector

🌺🌺 FEERYAL 🌺🌺

NA

RASHEEDAT S DIRECTOR

( Book 1)

~Free page~

____________________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼

🇦SSOCIATION🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan👇🏻

***

____________________________________

Bismillahirrahmanurrahim

🅿️5

Wani zabgegen maciji tagani sakankanin kafafuwanta, a kanannad'e acure guri guda ya fasa kai.

takuma yin baya a muguwar razane,

da karfi ta furta "Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!."

cikin tsananin kad'uwa.

tana furta kalmar innalillahi da sauri macijin ya shiga ware jikinsa yana bi ta kan kafafun Feeryal da ke zaune tana wasa da shi, yanufi kofa yana isa dai-dai bakin kofa ta nime shi ko sama ko kasa ya b'ace mata bat bata kuma ganinsa ba,

bata kuma san ta in da ya bi ba dan kofar a rufe take.

Rasashi ke da wuya tasoma jin wani kara mai cike da amon sauti na dukar can cikin kunnuwanta.

da karfi ta rumtse ido tare da kai hannu cikin kunnenta da take ji kamar dodon kunnuwan nata zasu zazzago su fito waje.

ji tayi ana fad'in

"Ke kad'ai bazaki iya bata kariya ba dole sai da taimakon muuuu!."

kuma toshe kunnuwanta tayi da karfi tana juyi had'e da tangad'i har sai da ta zube kasa.

a dai-dai lokacin da taji kamar an fisge mata dodon kunne, nan da nan wani uban zufa ya shiga keto mata.

a hankali kuma taji yanayin ya d'auke cak cikin second 1 tadawo dai-dai.

Da sauri ta mike zaune tashi ja da baya tana bin Feeryal da kallon tsaro.

ita ko yarinyar baki ta b'are tana mika mata hanu alamun ta d'auke ta.

Cikin rawar murya Aunty tashiga fad'in

"Ban tab'a cutar da ke ba, ban d'auko ki dan na cutar da ke ba,

sai dan na taimake ki, ki dubi girman Allah kada ki cutar da ni,

zan mai da ke in da na d'auko ki,

nayi zaton ke d'in jinsin mu ne shiyasa na d'auko ki, ban d'auko ki dan na cutar da ke ba!."

Gaba d'aya Aunty ta birkice ta ko ta ina a jikinta b'ari yake, tsoro mai tsanani ya baibaye ta.

ta kasa iya mikewa kan jafafunta sai ja da baya take a zaune.

Jin karar bud'e kofa ta waigo da sauri a bala'in razane, dan tagama zaton macijin ne ya dawo.

ganin Daddy ne ya shigo da sauri ta mike a guje tayi gurin shi,

ta fad'a jikin shi ta kankameshi da karfi tana fad'in

"Daddy maciji na ganshi da ido na! dan Allah ka d'auke ta ka mai da ita in da muka d'auko ta,

wlh nahakura zanci cigaba da zama a haka gara na tabbata a matsayin juya, na hakura bana son d'a zanyi rayuwa ta ni kad'ai a haka!."

Da sauri yadad'a rukota sosai ganin yadda gaba d'aya ta fita hayyacin ta.

ya janyo ta suka karaso cikin parlour, ya zauna kan kujera tare da zaunar da ita a gefen sa.

"Fad'imatu."

ya kira sunan ta yana kallon fuskarta.

ido ta zuba masa sai kuma ta girgiza kanta kamar wacce ke son dawowa hayyacin ta.

ta yunkura zata mike da sauri ya ruko ta yakuma duban ta da kyau ya ce

"Ki dawo hayyacin ki."

wani nannauyan numfashi ta sauke da sauri ta waiga gefe da gefen ta sai kuma ta maida duban ta gareshi.

"Fad'imatu." yakuma kiran sunan ta

murya a raunace.

kai ta girgiza ta ce

"Daddy."

"Numfashi ya fesar sannan yakuma rukota da kyau ya ce

"A ina kika ga macijin Fad'imatu? akaf fad'in gidan nan da kewayen sa, ba macijiba ko kwaro in har mai cutar wa ne bai isa ya matso yankin gidan nan ba, ta ko wane kusurwa;

tazarar taku dubu ne ta ko wata kusurwa sakanin mu da duk wani nau'in kwaro mai cutar wa,

ko ta sama ko ta kasa,

sam maciji bazai iya shigowa gidan nan ba, a zagaye gidan nan yake da maganin su,

idan kuwa sukayi gigin shiga to kuwa zasu mutu tun kan su karaso,

koda ta cikin karkashin k'asa ne kuwa."

"Daddy na ganshi da ido na fa babba ne sosai agaban Feeryal tana wasa da shi, kuma naji ana magana da karfi kamar za'a fasa min kunne,

ni dai a maida ita kawai wlh na hakura."

shiru ya yi yana kallonta a kasan ransa yake fad'in

"Anya ba aljanu ne ke son shafarta ba?."

kwana biyu gaba d'aya yaga yanayin ta ya sauya, abin da bazai faruba tarika cewa ya faru.

kai ya jinjina sannan ya ce

"Gizo ne kawai."

da sauri ta ce "A'a Daddy wannan kam ba gizo bane nagani da ido na da gaske ne."

"D'azu bakya hayyacin ki Fad'imatu akwai abin da ke shirin faruwa da ke, yakamata a dakile faruwar hakan,

ina zuwa."

Yafad'a yana mikewa ya nufi bedroom yafito d'auke da Alkur'ani mai girma ya dawo in da take, ya bud'e ya mika mata.

ya ce "Kirika karantawa ina zuwa, bari naje na dawo, dan shi yafi komai kariya."

Ya isa ya d'auki Feeryal data fara kuka ya ajeta a gefenta.

yana cewa

"Ta gaji da zamane ko tana jin yunwa."

ido ta bita da shi harga Allah tsoro take bata yanzu.

Cikin hanzari yafita, Daddy yakai awa d'aya zuwa d'aya da rabi kafin ya dawo.

a bedroom ya same su dan ta sami kwarin gwuiwa da taimakon karanta Alkur'anin da tayi, har ta ji karfin zuciya ta d'auke ta ta je tamata wanka, tana gama shiryata kuwa tayi bacci.

Daddy ya mika mata kullin laidar daya shigo da shi.

ta karb'i laidar tana d'an jujjuyashi a hannunta sai kuma ta kunce laidar.

da mamaki take kallon kulli-kullin magunguna.

da fuskar tambaya ta dube shi,

sai kuma taga ya d'au abin saka kuraren wuta ya jona shi gijin wuta,

yana fad'in

"Hayaki ne da wanka na karb'o miki, zo maza kiyi hayakin anjima in zaki kwanta kiyi wankan maganin sai ki kara yin hayakin."

"Hayaki da wanka kuma? asabo da me ni fa lafiya ta kalau."

kai ya girgiza ganin ba tasowar zatayi ba ya janyo hanunta.

"Aljanu na son shafarki kice lafiyan ki lau, ina kuwa batun lafiya anan."

"Daddy kada ka rika yarda da wad'annan masu magungunan karyar fa."

"Zauna dan Allah."

ya yi maganar yana zaunar da ita.

da kansa ya bud'e yahakin ya saka yakuma rufeta da hijabinta kamar yadda aka ce masa.

sai da ya tabbatar hayakin ya ratsata sosai tana ta sauke tari da atishawa kafin ya bud'e ta.

yana fad'in

"Sai dai su kare a haka amma bazasu tab'a samin damar shigar jikin ki ba."

ita dai ido ta bisa da shi.

Da daddare kafin ta kwanta sai da ya tabbatar da tayi wankan maganin da hayaki.

duk da bataso ba.

Washegari da safe Aunty ta fito zata nufi kichin, tana bud'e kofar bedroom taga wani katon zomo fari soll,

idanunsa manya masu matukar razanarwa. yana zaune a dai-dai tsakiyar bakin kofa,

ya d'aga kunnuwansa sama yana juya idanun nasa da sam basuyi kama da idanun zomo ba.

wani irin juyi ta yi da farfe ta maida kofar ta rufe.

Tana waigowa kirjin ta ne yawani irin tsinkewa hango sa da tayi kan gadon Feeryal, wacce ke bacci yanzu kafin ta fita sai da ta gyara mata kwanci,

sai ga shi ta ganta zaune suna wasa da zomon da ta gani a bakin kofa,

yanzu-yanzu da ko second 1 baiyi ba

wani uban kara ta sake sakanakon had'a ido da shi da idanunsa masu matukar ban tsoro.

ta yanke jiki ta zube kasa.

Da sauri had'e da gudu Daddy dake cikin bathroom yafito, ya yi kanta cikin hanzari yana jijjigata da kiran sunan ta.

gani bata ko motsi da sauri yaje ya d'au gorar ruwa yazo ya yayyafa mata.

numfashi mai karfi ta sauke ta zabura zata mike, da sauri ya ruko ta.

"Fad'imatu mene ne ki natsu."

hannu ta shiga nunawa in da Feeryal ta ke

"Yana can yana can akwai wani abakin kofa."

ya waiga in da take nuna masa baiga komai ba, sai Feeryal da ke zaune.

ya ce

"Babu komai fa ni ban ga komai ba, bakiyi hayakin nan ba yau, muje maza kiyi."

ya d'agota suka karasa cikin d'akin.

Ranar haka Aunty ta wuni sukuku lamarin nason fin karfinta★★

Tekun Matip acan cikin fadar sarkin aljanu Matip,

dake karkashin teku cikin wani katon kasurgumin kogo mai matukar girma.

duniya ce guda a gurin.

matakan tsaro ne jiga-jigai masu matukar had'ari.

kifaffen masarautar da aka kifeshi tun tsawon shekaru d'ari biyu da hamsin da suka shud'e.

shine yakuma dawowa daram.

shugaba sarkin aljanu Matip yake cigaba da mulkarsa.

bayan tsawon shekarun da ya yi a tsare a kuma garkame sakamakon faruwar wani lamari.

Manya-manyan jiga-jigan dodanni aljanu majiya karfi masu tsuffar ban tsoro ne ke tsaron kofar masarautar, tasama da kasa.

Acikin fada sarki aljani Matip ne zaune a kan karagarsa na alfarma da aka yi sa da gundarin zinari.

ya yin da fadawa ke zagaye da shi.

Sarki aljani Matip ya dubi wazirinsa Kutub sannan ya yi gyaran murya, ya ce

"Akirawo Tarmuzu yanzun nan."

waziri Kutub ya dukar da kai ya ce

"Angama ya shugaba na."

wani kambu dake rike da shi ya murza cikin second 1 wani aljani ya bayyana a gaban sarki Matip. yazube gaban sa yana fad'in

"Na amsa kira ya shugaba na."

Sarki Matip ya dubesa sannan ya ce

"Tarmuzu Kudakata haka ku dai na bayyana ta ko wata tsuffa kuna razanin uwar gijiyarta,

zata rasa samin kula yadda ya kamata idan hakan ta faru kuma bazan yafe muku ba!."

"Tuba muke ya shugaba na a gafarce mu."

aljani Matip ya girgiza kai sannan ya d'aga masa hanu, nan take yab'ace..

Kimanin sati biyu kenan Aunty bata cikin walwalar ta, sai baya-baya take da Feeryal burin ta dai surabu lafiya.

kullum dai Daddy na karfafata da bata kwarin gwuiwa, yana ta so yaga ta cire kokonto kan Feeryal d'in, duk da shima yanzu lamarin yafara jefashi cikin nazari.

sun shefe tsawon sati gudannan bata kuma ganin wani abin tare da Feeryal ba.

sai dai wani lokacin idan ta barta ita kad'ai takanzo ta same ta tana ta wasa kamar tana yi da wani, haka nan zata d'auke ta, dan tayi alkawarin cigaba da kulawa da ita, amma cikin takasantsan burin ta dai surabu lafiya..★★

Haka rayuwa yaci gaba da tafiya Feeryal nata dad'a kara wayo, ya yin da suffarta dake saka kokonto cikin zukatan duk wanda ya ganta ke dad'a karuwa.

zuwa yanzu Aunty ta saki zuciyar ta da Feeryal.

har ta yarda abaya wancan lokacin da take gane-ganen Feeryal tana wasu abubuwan da gaske gizo ne, da kuma sharrin shed'anun aljanu da suke son shafarta kamar yadda Daddy ya fad'a mata.

sosai ta dawo kula da d'iyarta.

tuni Feeryal ta kai na yaye aka yaye ta..

Kamar wasa rayuwa mai tafiya da sauri shekarun Feeryal hud'u ke nan, amma a zahiri idan ka ganta zaka iya kira mata shekaru biyar har da d'ori.

Aunty bata barinta fita ko nan da can,

iyakacin ta cikin side d'in da farfajiyar sa zuwa garden d'in cikin side d'in.

bata zuwa side d'in kowa a gidan, kamar yadda kowa ma baya zuwa nasu side d'in.

in banda Hajiya Safiyyah da kuma 'yarta Meimei sa'ar Feeryal ce,

sai dai ta d'an girme mata ita shekarunta shida ke nan,

amma kusan tsawon su d'aya,

sosai Feeryal ta saba da Meimei, Hajiya Safiyyah tana kawota suyi wasa da ita.

Ganin bakinta ya bud'e sosai da magana,

Daddy yace za'a sata a makarantar su Ameerah.

Ranar wata juma'a Daddy na zaune a parlour'n sa yana waya.

Mommy ta shigo parlour'n ta taras da shi na waya, ta zauna gefe tana saurarar abin da yake fad'a

"Ashirya mata duk abin da ya dace zuwa ranar Monday nake so ta fara zuwa makarantar, a kawo mata uniform da sauran abubuwan bukata gida ranar Lahadi,

Monday kuma ta fara zuwa."

yana sauke wayar Mommy ta bishi da kallon tambaya

"Alhaji wa kuma za'a canzawa makaranta, kar dai ace Ameerah sarkin rigima ce ta kuma tada buren sai an sauya mata wani makarantar?."

ta karashe maganar tana washe baki da jin dad'in fitinar d'iyar tata.

Daddy ya ce

"Ai naga alama Ameerah yanzu tana son makarantar nan, tun da najita shiru bata kuma tada borin a canza mata wani ba,

Feeryal ce za a kaita makarantar tasu."

Da mamaki ta ce "Feeryal kuma wacce Feeryal d'in?."

dan ita tagama mancewa da wata Feeryal a gidan ma, dan tun lokutan baya da suka tab'a tafiya saceta sukaga abin da yafi karfin su.

tun da suka gudu basu sake gigin kuma zuwa ba, a sannu kuma suka mance da batuntu, tun da ba ganin ta suke ba, bugu da kari kuma gargad'in da Daddy ya yi musu, kan duk wanda ya fad'awa hajiya abakin auren ta.

Daddy ya ce "Feeryal y'ar wajen Fad'imatu mana."

wani uban ashar Mommy ta mulmulo tare da buga kirji ta gwalalo ido waje

"Kutumar ubancan Alhaji dama aljanar nan tana gidan nan!? muna shakar iskar numfashi d'aya da ita?

wato Fatima b'oye aljanar nan taye,

ta b'oye bakar gamasheka tayi ta raino harta hab'aka tazamo muguwar dafi,

to wlh bata isa ba

dolen ta tabar gidan nan, dan wlh bazamu rayu da aljana ba,

wai kuma har kake batun sakata a makarantar su Ameera, wlh bazai sab'u ba, bazai yuwu a had'a mana ya'ya da aljana ba, taje can ta karaci tsiyarta."

"Ke Halima ina ruwan ki, idan an sakata a makarantar su Ameerar ke zaki biya kud'in ko me? ki cire bakin ki a lamarin yarinyar nan tun ranki bai b'aci ba, idan aljanar ce sai me ni na shirya taimakon ta."

zumbur ta mike tsaye har tana kumfar baki

"Wlh ba a isa a sakata makaranta d'aya da ya'yan mu ba,

Alhaji kafa fitar da mayyar aljanar nan a gidan na, idan kuma ba haka ba to mu zamu kwashe ya'yan mu mubar mata gidan,

dan bazamu zauna da mayyar aljana ba,

Fatima ta gama asirce ka takawo mayya gida ka runguma wane d'iyar cikin ka,

sabo da haka ka hana Hajiya dawowa kasar ma baki d'aya, to wlh asirinsu sai ya tonu,

babu abun da zai hana ni sanarwa hajiya komai,

dan wlh ina ji ina gani kam bazan zauna da mayyar aljanar ruwa ba!."

Daddy ya gyara zaman sa tare da d'aukar gilashin sa ya saka, ya mai da dubansa kan TV sannan ya ce

"Sai dai kubar gidan nan badai Feeryal ba kam, je ki sanar wa Hajiya daga nan kinsan sauran."

Fuuu tayi waje tana cigaba da zazzage buhun masifa

ba'a isa a had'a musu ya'yan su da aljana a makaranta d'aya ba.

Har ta isa side d'in ta bata fasa masifar ba,

ta kirawo Umma Karima ta sanar mata da abin da ke faruwa.

a bujajan Umma Karima ta taho side d'in Mommy

tun daga bakin kofar parlour ta ke fad'in

"Kar ki gayamin wannan zance Hajiya Halima, ya akayi mukayi bacci ne bamu farka da wuri ba,

Eh lallai Fatima tasan me tayi, wato sai da tabi kowa ta toshe masa baki, tasaka kowa baccin ido biyu ta yadda babu wan da zai kuma batu kan aljanar nan,

hahahaa wlh karya kike Fatima bokanki ya yi kad'an."

tawani saki makirin dariya takaraso cikin parlour'n ta hakimce kan kujera.

Da sauri Mommy ta ce

"Meye mafita Hajiya Karima, idan fa bamuyi da gaske ba, Hajiya Fatima zataga bayanmu."

"Akwai mafita amma bazamu sami ganin Mali ba sai nan da karshen wata sabo da sun shiga mitin natsawon wata guda,

sai dai muyi hakuri zuwa lokacin."

kai Mommy ta girgiza tana ciza yatsa.

Farida da Sumayya dake zaune can gefe suna karatu a littafan makarantar su,

Farida ta rike had'a tana wani yamutsa muska cike da iyayi da manyance kamar uwar mata ta ce

"Yanzu dama har yanzu yarinyar nan tana gurin Aunty? sai da Hajiya ta ce wa Daddy su mai da ita

cikin ruwan da suka d'auko ta shine suka ki, ai Hajiyar zata dawo."

ta karasa maganar cike da zallar manyance da rashin kwab'a irin na iyaya.

idan manya suna magana

sai yaro ya tsoma baki, ba a hanashi ahaka duk

suka gina ya'yan su.

babu kwab'a ko kad'an.

"Ai rannan da naje side d'in Aunty na ganta tagirma kamar Ameerah, har ta ce zata bini Aunty

ta ce ta zauna, kun ga in da tayi kamar Miesho

nacikin Film d'in Tigezam, har idon su iri d'aya

da gashinsu."

cewar Sumayya tana waro ido.

Harara Mommy ta banka mata ta ce

"Ai ke kam albasa batayi halin ruwa ba, uban me ya kaiki side d'in nasu,

ai dole tayi kama da Miesho kin tab'a ganin mai

kama da ita ko a kasashen su ne bare a kasar nan mai tsuffar aljanu, idan na sake ganin ki a side d'in

sai na ci ubanki,

me za'ayi da Fatima gayyar tsiya."

Ajeemal da yanzu shigowar sa ya b'ata fuska

"Mommy to ku ina ruwan ku da yarinyar nan, Daddy

shi yaji zai iya riketa imma aljanar ce meye matsalar ku, tun da Aunty ce ke rukon ta ba ku

ba."

"Dalla tafi can ka ba muta ne guri, me ka sani a rayuwar yau."

cewar Umma Karima.

Mommy ko ashar ta auna masa, ya girgiza kai yaja

kafarsa ya yi gaba.

Lanar Lahadi aka kawo wa Feeryal kayan makarantar

ta, ranar ba zama tun da aka gwada mata taki a cire har sai da Aunty ta lallab'a ta tayi bacci kafin a ka cire mata tana bacci bata sani ba.

Washegari ranar Monday da wuri Aunty tagama mata

shiri, tayi matukar kyau sosai cikin shigar uniform.

tagoya school bag d'in ta, sai tsalle take da murnar zata makaranta.

A can side d'in Mommy su Farida sun gama nasu shirin

suna zaune a dinning suna breakfast.

Mommy ta dube autarta Ameerah tashafa kanta tana fad'in

"Daddyn ku ya kafe sai da yasaka munafukar aljanar

nan a makarantar ku, nasan kuma karshe ajin ku

za'a kaita, kar ki kuskura kirika bari tana zama

kusa da ke, bare ta manna miki damuwa;

idan tamiki wargi kici uwarta da duka,

dan aljanu

tsoron duka ne da su, shegiyar yarinya mayyar aljana 'ya'yana sun fi karfin ki,

kuma kar wata ta raga mata acinku ba jinin ku bace

ita, babu abin da ya had'a ku da ita."

Farida da Sumayya suka girgiza kai alamun sunji gargad'in nata.

A b'angaren Umma karima kuwa

Harsu Bilkisu Saddika Rahama Nabila sun gama komai da komai suna shirin fita,

tun tashin su Umma Karima ke musu bitar tsiya har kawo yanzu da zasu fita,

ta dubi Nabila karamar su ta harare ta tana fad'in

"Ba an iya tab'aki ki bud'e baki haa ba, duk san da naji labarin aljanar can tayi miki kallon banza baki cire kwayar idanunta a hanun ki ba,

sai na ci kutumar uban ki da duka,

babu ragawa sakanin ku,

kurika yiwa shegiya dukar tsiya,

yar tsintuwa ce uban ku ba d'aya ba, ko ya mutu bata da gadon sa,

ita uwar kanzagin nata ma haka zata tashi a tutar babu, bata tab'a nishin haihuwa ba sai dai na kashi a shadda,

maza ku kama hanya bance ku ragarwa shegiya ba."

Aunty ta fito rike da Feeryal.

suna daf da fita bakin get d'in side d'in ta, ta ce

"Tsaya-tsaya y'anmatan Ammie, sa kafar ki ta dama kifara fita da shi, sannan kice tawakkaltu'alallah walahaula'wala kuwwata illa billah, sai ki fita da kafar da ma."

baki ta wace har da d'an tsallenta.

sannan ta ce

"To Ammie,tawalkaltu alallah walahaula wala kuwwata illa billaaaah."

murumushi Aunty tayi, batayi mamakin yadda ta iya addu'ar ba, dan ire-iren addu'o'in nan tana koya mata su sosai.

ta shafa kanta tana fad'in

"Yauwa y'anmata Ammie, to ban da kwad'ayi, ban da fad'a, ayi karatu sosai."

kai ta gyad'a tana murmushi itama, suka fito.

Can ta hangi motar dake kaisu Ameerah school bakin get d'in dide d'in

Hajiya Nafisat ya d'auko Sahla ya karaso zai d'auki Mimi.

suna tsaye motar

ta karaso, direba yafito da sauri yad'an risina ya gaida Aunty kana ya bud'e marfin baya in da Meimei da Sahla suke zaune ciki.

baki Miemie ta washe da ganin Feeryal tana fad'in

"Zakije school inmu?."

Aunty ta maso jikin motar ta d'aga ta cak tasaka cikin motar gefen Miemie tana fad'in

"Ita ma ta zama y'ar school d'in ku yanzu."

aiko Meimei ta matsa ta gyara ta zauna tana ta murna.

Sahla ko fuska ta b'ata sai hararar Feeryal take, ga dukkan alamu itama ta sami hud'ubar tsiyai daga gurun uwar ta Hajiya Nafisat.

Aunty tayi musu Allah ya tsare, direba yaja motar zuwa bakin get d'in side in Umma Karima.

ya d'auki Nabila, su Bilkisu suka leko cikin motar suna hararar Feeryal, sai da motar d'aukar su suma tayi musu hon kafin suka bar jikin motar.

Direba ya ja motar zuwa side d'in Mommy.

su Farida suna tsaye agurin ga motar su ta iso yana ta musu hon,

amma suka ki shiga suna zaman jiran isowar motar da Feeryal take ciki.

direba ya sauka da sauri ya bud'ewa Amerrah ya ce

"Shigo da sauri kada mu makara."

ta leko cikin motar sai kuma ta yamusa fuska ta ce

"Ni dai bazan shiga a matse ni ba, ai a gurin zamata ta zauna sai dai ta fita na shiga."

ta nuna Feeryal da yatsa.

direba ya ce "Haba Ameerah dukkan ku yarane ai nan ya ishe ku, to zo ki zauna a gaba ke."

kafa tashiga bubbugawa kasa tana fad'in

"Ni bazan zauna a gaba ba, sai dai ta fita."

Farida ta ce

"Bazata zauna a gaba ba sai dai ita ta fita ta tado gaba, ko kuma tabi wata motar."

Bilkisu da Saddika suka leko daga motar su suna fad'in

"In bazata fita ba, ki fitar da ita da karfi Farida tun da ba motar ubanta bane."

Da sauri Isa direba ya ce

"A'a ku tsaya, fito ke ki dawo gaba."

ya janyo hanun Feeryal yafito da ita yasakata a gaba.

kana yakoma mazaunen sa yaja motar suka nufi babban get d'in fita daga gidan duka.

su Farida suka shige nasu motar suma bayan sun gama aika mata da mugun kallo.

Suna isa makarantar duk suka fito, Miemie ta rike hanun Feeryal Ameerah ta ce

"Sake ta ba 'yar'uwar ki bace."

Miemie ta make kafad'a ta ce

"Ai Ammah ta ce y'ar'uwa ta ce itama."

harran su tayi

"To kar kubi bayana kubi hanyar ku daban."

Ameerah tayi gaba tana hararar su.

duk wan da yazo wucewa in ys hango Feeryal sai ya tsaya ya kalleta, yara 'yan'uwan ta da kuma manya,

kowa sai fad'i ya ke

"La ga baturiya ta shigo school d'in mu."

ta dawo abin kallo har wad'an da ke cikin ajijjuwa leken ta suke.

Ajin su Ameerah kuwa a ka bata, tana shiga aji kuwa yara suka mike suna fad'in

"Laa ga baturiya laa ga baturiya."

Ameerah tayi musu tsawa

"Dalla ku zauna! waya ce muku baturiya ce to aljana ce, mayya bakuga idon ta ba."

hele yaran suka kuma suna leko fuskarta wasu suna fad'in

"Ga aljana ga aljana."

wasu ko daga cikin yaran basu yarda ba.

Miemie ta ruko hannunta ta ce

"Ku bari fa ba aljana bace 'yar'uwa ta ce."

jin hayaniyar su yasa malami shigowa ajin ya yi musu tsawa, nan kowa ya ni mi guri ya zauna.........!

Mommyn Twins ce