NUUDARR

18

by @oumameer2671

NUUDARR 🥀🥀

(A 2025 NOVEL)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

AREWABOOKS@AMINATU IBRAHIM

WATTPAD @UMMU-AMIR

AMEENA IBRAHEEM

(OUM AMEER)

PAGE 18

Assalam Alaykum mutanen arziki mutanen kirki mutanena na jahar Zamfara da ma kewaye ina yi muku fatan alheri, Suna na REEDERT SKIN CARE wadda ke zaune a cikin jahar Zamfara Gusau Nigeria.... Ina mai farin cikin tallata muku kayana cikin aminci da kyakkyawar zuciya.......

Shin en uwa Kun dade kuna neman mayukan da zasu gyara muku jiki Baku samu ba???? 😳ina masu fama da sun burn?? ,knuckles?? ,glass?? ,Rashes?? ,spots?? Da sauran su? 😳ina masu qorafin suna shafa mayuka baya karbarsu,???😎ina wadda tayi bleaching ya bata mata fata tanaso fatarta takoma daidai ???🧚🏻‍♀️🧚🏻‍♀️shin kunada labarin REEDERT ORGANIC SKINCARE,dake jahar zamfara kuwa?? to idan baki taba amfani da products dintaba dan Allah ki jaraba kiga ikon Allah cikin qanqanin lokaci fatarki zatayi kyau ta murje tadinga sheqi kamar autar larabawa 👌❤️❤️ munada kaya kamar haka ➡️➡️

Amarya set

Mai jego set

Knuckles and dark spots removal set

Whitening and glow set

Lightening and glow set Etc........

Haka zalika munada supplements masu kyau da qayatarwa kamar haka ➡️➡️➡️

Weight gain supplements

Weight loss supplements

Anti-aging supplements

Whitening supplements

Breast enhancement and enlargement

Hips enlargement.

Reedert Organic skincare tana nan zaune a Gusau Motorgage Area behind masaqa

***,***

Delivery nationwide 🌍🌍🌍

Muna aikawa a duk inda kike cikin faɗin Nigeria da ma kewaye.

Meerah kuwa, bata san lokacin da ta faɗo daga kan gadon da ta ke kwance ba tsabar kaɗuwa da gigita, cikin tsantsar tashin hankali zuciyarta na wani bugawa da ƙarfi tamkar za ta fasa ƙirjinta ta fito ta ce.

"Kai Mahaukacin saurayi na! Ina ka ke tunanin zaka kai er mutane... Wait! Wai da waye ka ke iƙirarin zaka rabu? Ni? Ai wallahi kamar yanda na saba gaya maka ni dai kai Saif sai mutuwa, ka hawo mota yanxun nan ka zo ka kawo ta gun Mami na..."

"Meerah wannan ba abun wasa ba ne, duk yanda kike tunanin sa ya wuce nan, ke yarinya ce har yanxu, ba zaki fahimci komai ba, yanda kika fahimta daban fahimtar iyayenki kuma daban,sai an jima"

"Saif Alƙali... Saif..."

Haka taji ya tsinke wayar kai tsaye ba bu wani tunani.

Durƙushewa tayi akan ƙafafunta ta fashe da wani irin masifaffen kuka jiki na rawa ta sake gwada numbern tayi ta ringing ya ƙi ya ɗaga.

Dawowa ya yi in da nike zaune ya tsaya a kai na yana mai ƙare min kallo ya ce.

"Mi zaki ci kuma??"

Girgiza kai na nayi hawaye na bin kuncin na cikin magiya na ce.

"Yah Saif kayi min haƙuri, ko wannan ma da ƙyar na iya shanyewa. Pls ina jin fitsari"

Shiru yayi tare da juyamin baya tamkar bai ji mi nike cewa ba sai naga yana magana da wata mata a wurin, bayan sun gama ta ce na ta so mu tafi nayi fara tsarin.

Ina tafiya a raina ina cewa yah Saif kayi hakuri abinda yake kaina yafi gaban tsaya wa ko ruwa na kurɓa. Daman yana juya baya na juyewa almajirin da ke gefena Tea ɗin baki ɗaya na ce ya tafi.

Bayan na gama na fito ya ce naxo mu tafi. Wani irin tausayin sa ne ya kama ni, wato ni ya damu da naci abinci alhali shi ya ƙi ko ruwa ya ɗanɗana.

Wuri ya samu bakin bishiya ya zauna tare da saka hannayensa duka biyu ya dafe kansa.

Hawaye na ne suka shiga kwaranya waɗanda na san cewa na ƙulla da su kenan har abada ban san ranar dai na zubar su ba. Durƙushewa nayi akan ƙafafuna a gaban sa tare harɗe hannayena wuri ɗaya na ce.

"Yah Saif kayi haƙuri, duk laifina ne da na biyewa Emraan,haƙiƙa kuna iya ƙoƙarin ku wurin ganin tarbiyyar mu ta in ganta. Yah Saif na ɗauka babu abinda zai hana mu aure da Emraan, amma ashe a cikin al'amarin mu munyi gaggawa mun biyewa shaiɗan...ga shi na raboka da Mama da Yah Halifah, na raba da aikin ka, na raba ka da komai naka, pls kayi haƙuri... "

Ɗagowa yayi ya zuba min idanu kawai yana kallo na ba tare da ya furta min ko kalma ɗaya ba.

Ganin kallon da ya ke min yasa nayi saurin saukar da kai na ƙasa ina mai jin kunyar kai na.

Wayar hannun sa tayi ringing, cikin mamaki ya ƙurawa numbern da tayi appearing ido, daman ta through caller ne shiyasa sunan da ya gani ya yi matuƙar bashi mamaki. 'Na goma Maradun' sunan da ya gani kenan, wato Mahaifin Meerah.

Sai da tayi ringing 3times tana tsinkewa ba tare da yayi wani yunƙuri ba. 'Saifuddeen ka ɗaga wayar nan Na goma maradun ne.

Text ɗin da ya shigo kenan immediately bayan kiran na uku ya tsinke na en wasu daƙiƙu.

Yana tsaka ga kallon text ɗin sai ga kiran ya sa ke shigowa a karo na huɗu.

Ɗagawa yayi murya a darare ya ce.

"Assalam Alaika"

"Wa'alaikassalam. Saifuddeen Amira ta sanar da mu halin da kuke ci ki, Ina baka umurni a matsayina na uba wanda ya haifa ya kuma san da cewa ɗa na kowa ne , ka hawo mota tare da wannan yarinyar kazo da ita nan Kaduna ina jiran ku, kada kayi taurin kai ko don saboda wannan yarinyar"

Daga haka ya tsinke kiran. Sototo Saif ya yi yana bin wayar da kallo tamkar zai hango Mahaifin Meerar a ciki.

InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Lallai wannan Meerar ta haukace. Wannan wace iriyar kunya ce dan Allah!... Kiran Meerah da ya sake shigo masa shine ya katse masa hanzari, cikin karyewar zuciya ya ɗaga kiran kawai ba tare da ya ce komai ba.

"Saifuddeen na san ka da taurin kai, dan Allah ka bi umarnin Abbu ka zo da yarinyar nan, ita ma Mami na ta amince Saif, pls kar ka tsaurara abubuwa plsss..!"

Kashe wayar yayi baki ɗaya, sai kuma ya koma yana kallon Nuudaar tare da tunanuka masu yawa a ransa.

Kusan one hour muna zaune shiru tamkar zaman makoki daga ƙarshe ya miƙe ya fara tafiya, ganin ya tashi ya fara tafiya nima na bi bayan sa kawai ba tare da sanin ina muka nufa ba.

Abin hawa ya tare mana muka tafi tasha muka hau motar Zaria, daga can muka sa ke hawa ta Kaduna, wuraren Asr muka isa wani katafaren gida wanda ake kira gida.

Ko a ƙofar gidan ya fi minti goma kafin daga baya naga ya sauke ajiyar zuciya ya tura ƙaramar ƙofar.

Wata kyakkyawar budurwa ajin farko na ga ta taso daga kan kujerar da ke wurin shan iska ta nufo in da muke dosowa cikin sauri. Wannan da ganin ta zata yi sa'ar Aunty Nadee ko da bata kai ta ba kaɗan ne.

Maimakon tayiwa Yah Saif magana, ni ta rungume tana mai zubowa da Hawaye ta ce.

"Allah is with you kada ki damu kinji Nuudaa"

Ni dai sototo nayi ina kallon ikon Allah, a rai na ina faɗin ita kuma wannan wacece? Janyewa tayi tana mai riƙe hannuna da kyau cikin na ta tare da da share guntun hawayen ta tace.

"Sannu kin ji. Zo... shigo muje gida gun Mami"

Waigawa tayi sai a lokacin ta kalli Yah Saif, can cikin zuciyarta tana jin wata irin zazzafar ƙaunar sa na ƙara ninkuwa a ranta ta ce.

"Saif...! Allah ya saka maka da alheri, haƙiƙa kai yaya ne na gari, kuma hakan da kayi shi ya ƙara bani tabbatacin cewa babu wanda ya dace da rayuwata sama da kai, domin kai ne wanda zai iya kare ni ya kuma iya haƙuri dani a ko wane irin yanayi, wallahi ba kowa ne namiji ba ne zai iya abinda kayi, ka cancanci a kira ka da namiji, Allah ya ƙarawa rayuwarka albarka "

Daga haka ta ja hannu na muka shiga cikin gidan. Jiki na ne ya ɗauki mazari ganin mutane sun fi mutum bakwai a wurin. Dattijuwa ce zaune a kan 3seater sai en mata guda biyu zaune a gefen ta waɗanda zan ce za su iya yin sa'a ta ni da fauxa, sai wata ƙaramar budurwa kamar Hanna a zaune gefen kujerar da baban su ya ke zaune sai maza biyu kuma a 2seater suma ɗayan ya kai sa'an Nurudden ɗayan kuma da gani shine ƙarami baki ɗaya domin duk ya fisu ƙara ta.

Da ƙyar na iya buɗewa baki na tamkar mai koyon magana na durƙushe ƙasa akan ƙafafuna tare da sadda kai na ƙasa na ce.

" Ina wunin ku!"

Tasowa dattijuwar matar tayi wadda na lura da kallon da take min tun farkon shigowar mu taxo ta ɗagani tana mai ƙare min kallo sannan ta ce.

"Yaran yau ba ku da gudun zuciya, duk abinda Zakuyi ku zubarwa iyayen ku da kan ku ƙima da mutunci kun sani, miye ake da rayuwa irin wannan, Ina kike so mahaifiyar ki da ta saka ranta, a yanxu na san duk in da take tana can cikin tashin hankali da fargaba, to sabida Allah ina amfanin hakan uhm!... "

Girgiza kai Abbu yayi yace.

" Sun yi kuskure mai girma, amma kuma hukuncin da Alƙalin ya yanke bai yi kyau ba, Ina amfanin hakan?... " sai kuma ya kalli Yah Saif yace.

" Kayi abinda ya kamata Saifuddeen, naji daɗin hakan. Allah ya saka maka da alheri....yanxu kai Lukman (cewa da ɗayan saurayin) ka tashi ka kai shi wancan part ɗin idan ya huta sai muyi magana "

Cikin jin kunya ya Saif ya ce.

"Mungode so sai, Allah ya saka da alheri Allah kuma ya ƙara girma"

"Ameen yah Allah"

kallon ɗayar budurwar Mami tayi ta tace.

"Shukra ki kai Nuudaar ɗaki tayi wanka ki bata abinci, idan ta gama ta kwanta ta huta"

Miƙewa tayi tana faɗin.

"OK Mami"

Tashi nayi na bita bayan mun kai wajen wasu ɗakuma da ke jere kusan guda huɗu ga wasu ɗakunan kuma jere kamar su su na kallon su, duk cikin rufi ɗaya.

"Sis pls ɗan jira ni a nan na manta ban ɗauko key ba"

Gyaɗa mata kai na kawai nayi ba tare da nayi magana ba, Ina nan a tsaye har ta je ta dawo ta buɗe ɗakin ta shiga ta na mai umartata da na shigo nima.

Babban ɗaki ne mai ɗauke da set ɗin makeken gado da kayan tarkacen sa. Komai gyare ya ke tsab masha Allah.

"Sister a nan zaki zauna, ga toilet a can... Bari na sanya miki Ac ɗakin ya sanyaya naji da ɗan zafi zafi ko?"

Gyaɗa kai na sa ke yi ina mai gayyatar murmushi ta ƙarfi da yaji domin na bata haske akan ta fahimci na gode da abinda tayi min.

Bayan ta kunna Acn ta fice tana mai sakar min murmushi na faɗa kan gadon ina mai fashewa da wani marayan kuka...

Ni kai na na san ko ni aka ce nayi wa kaina hisabi ba zan taɓa yafewa kaina ba, Baba... Baaaba na! Ya iya yin sa a kai na da sauran en uwana, ana can ana auren Yah Halifah da Aunty Nadee cikin tsantsar baƙin ciki da tashin hankali kuma duk ni ce na janyo wannan, kuskure na ne! Wallahi kuskure na ne! Ya Allah, Ina ma mutuwa ta riske ni kowa ya huta da wannan baƙin cikin ni Nuudaar musamman Yah Saif da Mamana....

Na fi hour Ina Kuka daga ƙarshe na tashi na shige toilet ɗin da ta nuna min nayo wanka na ɗora alwala, ko da na fito na tarar an ajiye min tray mai ɗauke da kayan abinci iri iri.

Kauda kaina nayi gefe domin ko kallon abincin bana son ina yi jin wani ɗaci na bin maƙogwaro na zuwa baki na.

***********

Yah Saif kuwa, tunda ya shiga ɗakin ya kasa ƙwaƙwƙwaran motsi har yanzu ya kasa yarda da abinda Mahaifin su ya aikata.

Iyayen Meerah kuma, ya ma rasa da wane bakin zai yi iya amfani wurin gode mu su.

Yana nan zaune aka kawo masa abinci ya ɗan tsakura kaɗan daga baya ya miƙe ya fice daga gidan baki ɗaya.

Meerah na zuwa ta duba ko ina ba ta ga Saif ɗin ba cikin mamaki ta ɗaga waya ta kira shi kai tsaye ya ce yana hotel...cikin tsantsar mamaki ta ce.

"Hotel Saif?? Miye ya kai ka hotel?"

"Ba komai Meerah, kawai dai..."

"Pls just tell me where are you, gani nan yanxu zanxo, kada kaje ko ina pls"

Cikin mintuna talatin zuwa arba'in ta isa in da yake mamaki still bai barta ba ta ce.

"Saif what are you here for? Tell me the truth what's that in your mind?"

Kai tsaye ya kalli cikin idanuwanta ya ce.

"Meerah a misali, Ina nufin a misali Idan na ce miki zan auri Nuudaar shin still zaki iya aura ta???......."

OUM AMEER