NUUDARR

26

by @oumameer2671

NUUDARR 🥀🥀

(A 2025 NOVEL)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

AREWABOOKS@AMINATU IBRAHIM

WATTPAD @UMMU-AMIR

AMEENA IBRAHEEM

(OUM AMEER)

PAGE 26

Assalam Alaykum mutanen arziki mutanen kirki mutanena na jahar Zamfara da ma kewaye ina yi muku fatan alheri, Suna na REEDERT SKIN CARE wadda ke zaune a cikin jahar Zamfara Gusau Nigeria.... Ina mai farin cikin tallata muku kayana cikin aminci da kyakkyawar zuciya.......

Shin en uwa Kun dade kuna neman mayukan da zasu gyara muku jiki Baku samu ba???? 😳ina masu fama da sun burn?? ,knuckles?? ,glass?? ,Rashes?? ,spots?? Da sauran su? 😳ina masu qorafin suna shafa mayuka baya karbarsu,???😎ina wadda tayi bleaching ya bata mata fata tanaso fatarta takoma daidai ???🧚🏻‍♀️🧚🏻‍♀️shin kunada labarin REEDERT ORGANIC SKINCARE,dake jahar zamfara kuwa?? to idan baki taba amfani da products dintaba dan Allah ki jaraba kiga ikon Allah cikin qanqanin lokaci fatarki zatayi kyau ta murje tadinga sheqi kamar autar larabawa 👌❤️❤️ munada kaya kamar haka ➡️➡️

Amarya set

Mai jego set

Knuckles and dark spots removal set

Whitening and glow set

Lightening and glow set Etc........

Haka zalika munada supplements masu kyau da qayatarwa kamar haka ➡️➡️➡️

Weight gain supplements

Weight loss supplements

Anti-aging supplements

Whitening supplements

Breast enhancement and enlargement

Hips enlargement.

Reedert Organic skincare tana nan zaune a Gusau Motorgage Area behind masaqa

***,***

Delivery nationwide 🌍🌍🌍

Muna aikawa a duk inda kike cikin faɗin Nigeria da ma kewaye.

Familyn Aunty Zainab sun shiga tashin hankali iya tashin hankali musamman Aunty Zainab tunda ta farfaɗo ba ta uhm ba ta uh uhm! Sai dai bin mutane da ido hawayen ma sai can ba'a ra sa ba domin wa su mutanen kan ce zubar hawaye yana daga cikin samun sauƙin damuwa daga zuciya. Ita kam kukan ya ma kasa zuwa sai wani irin tuƙuƙi da zuciyar ta ke yi tamkar an ɗora ta akan tuƙubar tsirai. Umma ma duk ta gigice ta ruɗe ta shiga tashin hankalin da bata ta ɓa tsammani ba,daman can ga damuwar Asiya to sai wanga abu da yaxo mu su bagatatan.

Suna sannan a tsatstsaye sun yi cirko cirko aka turo Ruma akan gado zuwa in da suke tsaye za'a kai ta ɗakin ma su jinyar theater idan an gama.

'Bayan abin ya faru dai da ƙyar Firdausi ta lallaɓa ta kira Abba daga nan sai ga shi tare da Halifah, daga nan aka kira babanta Sufyan a ka ɗauke ta sai asibiti, cikin gaggawa akayi duk wani investigation aka shirya yi ma ta surgery na gaggawa domin ta samu damaged sosai a reproductive tract ɗinta wanda aka sanya su biyan maƙudan kudaɗe domin sun ce likitan da zai yi aikin ba ma anan ya ke ba dole sai an kira shi ya zo,bayan sun biya an shirya komai aka shiga da ita tun safe sai yanxu da yamma aka fito da ita'

Sufyan ma ko da 11am ta yi duk ya iso garin, kallo ɗaya idan kayi masa baka so ka sake marmarin kallon sa tsabar tausayi, ya sha kuka fuskar nan tayi mai suntum tamkar ba namiji ba, Yana ganin an fito da ita ya je ya durƙusa gaban gadon na ta jiki na ma sa ɓari ya fara sabbatu yana faɗin.

"Rumaisar Daddy! Waye ya miki haka? Dan Allah don girman Allah ki faɗamin waye wannan yayi miki haka?...."

Dukkan su kuka suka ɗaɗa tamkar waɗanda aka sanarwa saƙon mutuwar ta.

Abbah ya yi ƙarfin halin dafa kafaɗar sa ya ce.

"Sufyan ka yi haƙuri, Rumaisa ba za ta amsa ma ka ba a yanxu ka bari abi komai a sannu"

Ganin yanda aka turo ta tamkar gawa sai yanxu Aunty Zainab ta kalle ta ta fashe wani irin mugun kuka mai ciwo idon ta na ma ta gizaun yanda ta ganta a jiya...

"InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Rumaa... Rumaa.. ce.. Yanxu Ruma ce aka samu wanda ya yi mata haka Umma.."

Cewar firdausi ta na mai sa ke fashewa da kuka ita ma.

Su na nan a tare da ita su huɗu, Zainab, Sufyan, Umma, firdausi, domin Halifah su ka ce ya tsaya wurin Asiyah na ta mai sauƙi ne, shi ne Halifah ya tsaya tare da ita da kuma Hannatu.

Wuraren ƙarfe biyu na dare ta farko tana mai sakin wani irin ihu ta na faɗin.

"Mummy ki yi hak'uri! Mummy...."

Kalmar da ta fara fitowa daga bakin Aunty Zainba cikin karayar zuciya ta ce.

"Ruma waye la'anan nen da ya aikata miki haka?? Waye ne Ruma...."

Shiru tayi tana mai digesting maganganun Mummynta ta a ƙwaƙwalwar ta.

"Ruma ki faɗamin ko ƙuncin zuciyata zan sa mu ya ragu ya zama ko da zan mutu na samu wani rangwame da ga abinda ya ke ci ciyar zuciya ta"

"Mummy Hamid ne! Ya ce kuma zai kashe ki ya kashe Hidaya, Mummy shi ne ke ta mi ni tuntuni Mummy, ko da yaushe shi ne Mummy, kuɗin ki ma na Umma yana motar sa Mummy...."

Jin Kalaman Rumar ba ƙaramin haukata Zainab suka yi ba, jijjiga hannun ta ta shiga yi tamkar za ta ɓalla shi ta na mai sake fasgewa da kuka ta na faɗin.

"Babu abinda zai iya mana Ruma ƙarya ya ke yi yanxu ina so ki faɗamin mi ya faru, dan Allah ki faɗamin mi ya faru, wallahi zuciyata zata fashe umma.."

"InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un!"

Shi ne abinda su Umma ke ta maimaita wa jin abinda ya fi ƙarfin tunanin su.

Cikin ta ta dafe tana mai wani fisga ta na faɗin.

"Mummy wani abu ni ke ji a cikina.. Ciki na zafi sosai Mummy.. Mummy.. Wayyo Allah Mummy... Daddy..."

"Ga ni nan Ruma a tare da ke, ki yi hak'uri in sha Allahu zai dai na, ki yi hak'uri yarinyar daddy kin ji... InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Rumaa... Rummaaa! Wayyo Allah na wayyo kai na... Rumaaaaaa dan Allah kar ki mutu mana.. Rumaaaa"

"Matsa Sufyan, wallahi fa ba ta mutu ba,.... Likita? Nurse !"

Cewar Umma wadda ta ƙara gigicewa jin Sufyan na ambatar mutuwa ga shi kuma Ruma ɗif! Ba ta sa ke wani yunƙuri ba.

Cikin azama Nurse ɗin ta zo ta shiga bincikarta, tayi iya yin ta still ta sa ke kiran likita yazo suka bincika ta sai dai me? Lokacin Ruma ya riga da yazo.

Kallon Sufyan likitan ya yi ya ce.

"Alhaji sai dai haƙuri, Ruma Allah ya yi ma ta cikawa..."

Cikin wani irin ƙara ji ya damƙi kwalar likitan ya na faɗin.

"Wannan zancen banza ne ka ke yi likita, duba ta da kyau dai ƙarya ne Ruma ba za ta mutu a yanxu ba.."

"Kayi haƙuri Sufyan, Mutuwa ba ta da ƙarami ba ta da babba, pls take heart, we already done what we can, but Allah's plan is the best..."

Faɗuwa ya yi a ƙasa warwas ya shiga birgima tamkar wani ƙaramin yaro mai jin rigima yana ta ihu mai karya zuciya.

Kowa kuka ya ke babu wanda ke iya rarrashin wani sai dai wani abun al'ajabi shi ne, Aunty Zainab maimakon ta yi kuka, girgiza kai kawai ta ke tana mai yin murmushi dai kuma ta dawo ta girgiza kai tana sharar hawaye.

********

Abinda ya faru baya....

'Ruma dai bayan sun dawo daga makarantar boko, ta ɗora musu dahuwar spaghetti Kamar yanda Mummynta ta ba ta umarni, bayan abincin ya dahu ta sanya musu suka ci ita da Hidaya ta suka yi wanka su ka sanya uniform ɗin islamiyya har ta ɗauko jakar ta sai ta tuna da abincin da Mummy ta ce ta kwashe ta kai gidan su Maman Salima ka da a bar shi ya lalace tun da ba bu mai ci.

Kallon Hidayah ta yi ta ce.

"Hidaya ki bari na je gidan Maman Salima na dawo sai mu tafi, naga ma ƙarfe biyu da rabi da minti takwas..."

Kwantawa Hidayah ta yi kan kujera ta ce.

"Kuma Aunty Ruma ai sai biyu da arba'in Malam ya ce ko"

Gyaɗa kanta ta yi ta ce.

"Eh, kafin na je na dawo ai na san ya cika, kar ki yarda ki yi bacci in xo in yi ta tashin ki ki rainamin hankali"

Daga haka ta shiga kitchen ta kwashe tuwon a kula ta juye miyar daban, hankalin ta a kwance ta fito gida, domin yanxu ta jima sosai da rashin ganin Hamid har ma tsoron sa ya fita daga kanta, domin ta daina ganin sa, ko da za ta ganshi to tana tare da Mummy domin duk in da za su yanxu a tare su ke tafiya, ko school ce ita ce ke kai su ta dawo da su, sai fa yanxu da wannan matsalar ta samu Asiyah.

Bayan ta shiga gidan ta fito lafiya ƙalau kwatsam sai ga mutum a gabanta yana wani murmushin mugunta ya ce.

"Baby Kwana biyu.. Ashe zamu sa ke haɗuwa cikin irin wannan kyakkyawar damar, ba kowa a layi tsit, ga gidanmu ma ba kowa"

Walwalar ta ce ta koma ciki, lokaci ɗaya ta haɗe fuska ta ce.

"Ka matsa min a hanya Malam..."

Zaro ido yayi cikin Mamaki ya ce.

"Iyyeh! Ni ki ke gayawa haka??"

Hannayenta ta sanya da dukkan ƙarfinta ta tura shi sai ga shi ya yi baya tangal-tangal saura kaɗan ya sha ƙasa.

Cikin ɓacin rai ya damƙi hannunta tare da sanya ɗayan hannu ya jimƙe mata baki da ƙarfin tsiya ya ja ta zuwa cikin gidan su.

Ɗakin sa da ke wajen gate ya kaɗa ta da ƙarfi ya sanya lock a ƙofa da ƙarfin tsiya ya raba ta da kayan jikinta, ihu ta ke, kuka ta ke amma bai saurara ba sai da ya dawo hankalin sa, ya jima jikin sa tamkar wanda aka zarewa laka sannan ya iya miƙewa daga baya yana mai jin tashin hankali ya ziyarce sa ganin yanda ta ke ta zubar jini babu ƙaƙƙautawa,goge mata yayi da wani bedsheet ɗin sa ya janye ta gefe amma still bai dai na zuba ba. Tashin hankali ya shiga iya tashin hankali, ƙarshe sai ya fito ya rufe ta da lock ɗin ya nufo bakin gate, ganin mai Gadin su a zaune yasa shi ruɗewa ya koma cikin gidan yana mai neman abinyi....

Can basira ta faɗo masa ya zo cikin dakiya ya ciro kuɗi 5k ya miƙa masa yana faɗin.

"Dan Allah malam Sanda ka je kasuwa ka siyomin zaren ɗinki na nema ko ina duk babu, kuma mai ɗin kin ya ce shima ya nema duk babu ni na siyo da kai na"

Cikin girmamawa ya amsa kuɗin ya ce.

"To wane kala za'a siyo?"

"Kawai a baka na duka ko wace kala a haɗo"

Yana nan tsaye sai da ya ga ya yi nisa sannan shima ya wuce shap shap ya je ya amso sanitary pad ya am so pain killer yaxo da sauri ya kawo ruwa ya ɓaɓɓala ya ba ta ya ce ta sha.

Ita dai babu abinda ta ke idan ba kuka ba, jikinta sai rawa ya ke ta kasa motsa ko ɗan yatsanta..

Sai da ya yi da gaske sannan ta karɓa ta sha daga nan ya facce ledar pad ɗin ya zaro da yawa ya tuttula mata ya mayar ma ta da pant ɗinta sannan dogon wandon islamiyya.

Bayan kamar mintuna ashirin ya taso ta zuwa gate, leƙawa yayi ya ga akwai mutane hakan yasa ya koma gida ya ɗauko mata bucket da wata kular mahaifiyarsa ya bata ya ce ta wuce gida gudun zargin mutane.

Da ƙyar ta ke iya taka wa har ta samu ta lallaɓa ta shiga gida tana mai jin wata azaba na ratsa ta wai duk cikin ma ya bata pain killer, ko da ta je Hidaya kwance ta ke ta na baccin ta hankali kwance.

Ɗakin su ta wuce direct ta kwanta akan gadon su ita da Hidaya, kuka ta ke yi ta tana nemawa kanta mafita,amma da ta tuna irin barazanar sa sai ta ji tashin hankalinta ya ninku, kafin wani lokaci gaba ɗaya jikinta ya gashe lilis wani mugun zazzaɓi ya saukar mata cikin ƙanƙanin lokaci.

Hamid kuwa, tunda ta tafi baya cikin nutsuwar sa, domin hankalin sa a tashe ya ke, sai da ya ga dare ya yi an kwana an wuni ba abinda ya faru shikenan sai ya waske ya ci gaba da lamarin gabansa.'

********

Washe gari ko da tara na safe ta buga har an gama shirya ta, gaban Aunty Zainab aka zo aka ajiye gawar domin ta yi mata addu'a da kuma yi mata ganin ƙarshe.

Kwantawa ta yi jikin gawar tana mai fashewa da matsanan cin kuka mai ban tausayi......

"Zainabu ki yi haƙuri... Dan Allah ki yi hak'uri, ki yi mata addu'a, kuka ba bu kyau kin sani annabin mu annabin rahama ya yi hani ga irin wannan kukan.."

Ɗagowa tayi ta kalli Umma da ke yi mata magana itama kukan ta ke ta ce.

"Umma! Shi kenan fa tafiya za'a yi da ita, shikenan har abada ba fa zan sa ke sanya ta a ido na ba, kai co na da irin wannan ƙarshe da kikayi Rumaisa! Da ma ace ban barku a wannan gidan ba, dama a ce na san hakan zata faru da ke da na zauna da ke na hana faruwar hakan a gare ki, babu wanda ya san gaibu sai Allah, ashe abin da ya ke ta damunki kenan tsawon lokacin nan ba tare da na sani ba... InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Yah Allah kai ne Allah! Yah Allah ka yi wa wannan baiwa ta ka sakayya akan wannan zaluncin da bawan ka Hamid ya yi mata... Rumaaisa! Na taɓa ki da alherin Allah, na yafe miki duniya da lahira, daman baki taɓa yi man komai ba wallahi wanda zai sa ace na riƙe ki a zuciyata, ke yarinya ce mai matuƙar biyayya da gudun zuciya, na yafe miki, na yafe miki, na yafe miki, Allah ya yafe miki ya kwantar da ke lafiya ya kuma amintar da ke,Allah ya bani hak'uri da juriyar rashin ki a tare da ni, duk da na san rayuwa za ta yi mini wahala sosai na rasa da nayi, Allah ya gafarta miki...."

Nan ta yi ta yi mata addu'a sannan daga ƙarshe Sufyan yaxo shima ya yi mata, tana ji tana gani a ɗauke gawar aka fice da ita.

Kowa sai kuka suna yi mata fatan alheri.

**********

Nuudaar

Sai da na kwana uku sannan a rana ta huɗu aka bani sallama daga asibiti bayan an tabbatar cewa ni da 'Abdallah' sabon jariri na muna cikin ƙoshin lafiya.

Tun ina asibitin Yah hadiza ta iso kamar yanda ta yi alƙawari amma daga ita sai Huda suka zo.

Bayan mun dawo gida ne na tarar da kayan akwati goma sha biyu wanda taxo da su daga Birnin Kebbi wai cewa na Yah Saif ne. Kaya ne abinda ake kira lefe, an darza kuɗi tamkar ba'a san zafin su ba, ni wani abin ma tunda ni ke a duniya ban taɓa ganin sa ba, ganin sai ƙauyanci muke yasa Hadiza ta ce muna wai babu abu ɗaya da ta siye shi a Nigeria, komai daga ƙasar waje ta siyo shi domin matar Yah Saif babbar mace ce.

Yah Halifah da kansa ya je wurin Baba da zancen zuwa Kaduna neman auren Yah Saif. Kai tsaye baba ya ce a shirya a je da sadaki da komai a ɗaura aure baki ɗaya kowa ya huta.

Amma Yah Halifah sai ya nemi alfarma akan a bar shi zuwa kwanaki tunda matar sa na gadon asibiti ba zai iya tafiya ya barta ba kuma ba, za'a yi wannan tafiya ba da shi ba.

Muna zaune a ɗaki ni na ma ɗan kwanta sai na ji sallamar Hajiyar Akki ita da su Sumayyah suka shigo.......

OUM AMEER