11
by @surayyahms
NUR FIRDAUS...11
Arewabook@surayyahms
koda suka shigo cikin gidan layla na rike da hannunta sede tafiya kawai nur firdaus din take tanajin yadda gabanta yake faduwa dan in akwai abunda ta tsana a duniya baifi a zargeta da lefin da bata aikata ba, ga kuma abun magana da mahaifyarsun take yawan jawo musu akan siyasarta, barin ma da ake yawan alakanta komi da mijin mummyn nasu..
har suka karasa cikin babban gidan nasu da yadau wani irin shiru basuce ma junansu uffan ba suka wuce kawataccen dakin baccinsu, kai tsaye laylah ta fara rage kayan jikinta domin yin wanka, ita kuma nur firdaus ta zauna shiru abakin gado cikin rafka tagumi, tun da dama cikinsu acike yake da abincin da suka kwasa agidansu jadida basu damu da siyan komi yau a restaurant din bakin titi kamr yadda suka saba ba...
jim kadan layla ta gama cire uniform ta fito daure da guntun towel fari zata wuce bathrum sai kuma ta dawo jiki a sanyaye ta jikin gado ta tsaya tanata kallon yayarta nur firdaus data kafe ido akan wayarta tana daddanawa cikin yanayin damuwa...
layla ta dau minti biyu tana kallon nur fidaus cikin sanyin jiki dan alkalamina bazai iya fasalta irin wahala da raunataccen rayuwar da nur ta jima tana daukawa akanta ba..
she is just 17yrs old now,amma nitsuwarta da jajircewarta kusan yawuce name shekarunta nesa ba kusa ba sakamakon tasowa datay babu kulawar uwa dana uba ko wani a dangi,kuma ahaka itace ta zamo tmkr uwa da uba ma kanwarta layla, dan tun laylan tana yar karama sosai ake sakar mata komi, ta bata abinci, ta mata wanka ta shiryata, tay rainonta, cikin lafya da ciwo da duk wani kalubalen yaranta da balaga kusanma ince ita tafiyin hidima da ita akan mummyn nasu. sede duk haka bai saka mahaifyarsu talura da jarumtarta ba,saima ta kusheta.
mrs haseena sharif irin matan nan ne dat are self obsessed, ita din perfectionist ce. indai harkaga kuna shiri sosai da ita toh tabbas kana yin abun da yazo dede da ra'ayinta ne, ita sam bata yadda da kalman uzuri ko kuskure ba
babban yarta nur tana rayuwa ne me cike da wasu irin jarabawa wanda zan iya cewa acikinsu ta taso dan duk kkrinta uwar tasu bata gani iyakan kuskurenta kawai take iya hanga, sosai lamarin nur firdaus yake bawa laylan tausayi duk dama bai taba shafarta ba.
acikin sauke ajiyan zuciya me nauyi laylahn ta katse wayann tunanin aranta snn ta dafa kafadunta nur cikin sanyin murya tace big sis is everything alright? naga kim zauna shiru ko cire unirfom dinki bakiyi.
kusan agajiye nur din takalle layla tace "its fine" dama sakonnin Adnan kawai na tsaya ina amsawa, dan tunda kika kirani dazu mukaje kallon mumny a tv sai ban lura da ya turo sakonni ta wasap ba gashi ynxu inata kirarsa layinsa a kashe which is very unlike him..
cikin lumshe ido da budewa layla tace yaa nur just calm down ure just tense, kema kinsan baiya kashe wayarsa, if he does then he must be busy akan abunda yakaisa.
ajiyan zuciya ta sauke snn tace "hakane layla, dama yace min abubuwan sunyi masa yawa acan..toh kije wankan inkin fito zan shiga nima in watsa
babu yabo ba fallasa layla tace okay..snn ta wuce bathroom din domin yin wanka..
shigarta bada jimawa ba nur firdaus ta sauke wata nannauyar ajiyan zuciya snn ta hau rage kayan jikinta ta tattara koina ta nade kayan layla data watsar akan gado ta kimtsa matasu, tahau fitowa wa layla duk wani abun self care, kama da ga mayukan jiki, turare, da kayan gyaran gashi nata datake bukata duk ta aje matasu akan gado kamar yadda ta sabayi mata tun suna yan kanana sosai...
dagata dayan bangaren wajajen 4:30pm mrs haseena sharif ta kammala cimma babban burin datake son cimmawa akan shirinta,wanda akalla ya jawo mata hanklin uwayen yara mata da maza da yawan gaske dake cikin matsatsin halin bukatar temako a ckin garin kano har da kewaye. kusan koina saida aka watsa labarin ummi, wann publicity datake bukata tay nasarar samunsa sosai da tun da aka fara shirin twitter da facebook da sauran kafafun social media ta dau zafi da muhawarori..
ganin samun nasara akan haka yasata daura himma dawowa Abuja cikin gaggawa, awa guda jirginsu ya dauka, sun iso Abuja ana neman 5:30 na yamma sede bata iya
tsayawa kai report ma uwargijiyarta ba ta kamo hanyar gidanta kai tsaye.
tun a hanyar gidan take neman wayan mijinta sadat, duk hanklinta ya mugun tashi dan badon komi yasaka bataso ta rasashi ba saidan wann sex din daya iya da kuma lokci isasshe daya ke bata tana harkokinta yadda taga dama, gashi kyakkwa da kwarjini sam bata son ace wani abu yazo ya rabasu, dan izuwa yanzu ta tura mai sakonni sunkai tara, fuskarta ba asake ba take tuka bakar landcruiser dinta na 2020, tana kusan daf da anguwar gwarimpa sai ga sakonsa ya shigo.
tana hango sunan sa akan screen na tsadadden wayarta kirar iphone 16 pro kusan agurguje tay parking agefen hanya kafin nan ta bude sakon taga adreshi kawai ya turo mata na marcoriano chiness restaurant dake victoria plaza tasan anan yake son zuwa domin cin abinci, babu bata lokci ta juya kan stiring ta doshi wajen, bata fi minti biyar ta isa wajen ba.
tana kammala parking ta bude safe din motarta ta fito da wata arniyar bakar spec ta toshe idanuwanta da shi snn ta sauko kasa cikin takunta me daukar hankalin duk wanda yay tozali da ita, ko kulawa da yawan mutanen da ke kallo batayi, kai tsaye ta
wuce regular spot dinsa wanda tunkan ta iso ta hangosa zaune yanata kallon cikin ruwa da yan mata karuwai ke shawagi aciki, wani abu me zafi taji ya doki kirjinta dan Allah ya daura mata sonsa dan haka tana mugun jin kishinsa duba da shi saurayi ne me jini ajika kyakkwa so tana da wann insecurityn din naji aranta cewa yan mata zasu iya saka masa kahon zuka
fuskarta ba a sake ba ta ja kujerar dake gabansa ahankli cikin yanayin jan aji tayi masa sallama sann ta zauna, ya amsa ta cikin shan qamshi...
cikin ruwan ta kalla snn ta kalleshi cikin kyabe baki "Daman abunda kake kallo kenan har da kashe min waya and why are u not picking my calls after the text message?? cikin tone dinta na manyan mata ta karashe magann tanamai kafesa da ruwan idanunta
wani irin rolling sexy idanunsa shima yay snn ya dago ya kalleta a takaice da sexy voice nashi yace kince kinason mu hadu toh gani.
cikin katseshi da hmmm tace toh muje gida mana, i am not comfortble here, tunda magana me muhimmnci xamuyi daya shafi yara na i think we shud go home and talk babyboy..
ransa a mugun harde muryansa kasa kasa yace na riga dana gaya maki abunda zan fada miki, babu inda zanje gaskiya, bcos i just cant allow myself to be emotionally blck mail by you and your evil god damn doters.
cikin katsetsa da hannu tace "hey, dont talk abt my doters dat way sadaat..waime kake nufi ne, meya faru???please tell me already.... kadena behaving kamar dan karamin yaro mana..
cikin idonta ya kalla yaja wata arniyar tsaki me sauti "malama wann tsawar dakike min da wa yayanki kikeyi da zaifi miki amfani, na yarda ni yaro ne agabanki amma aikinsan da tarbiyata kika auro ni bazakixo keda yaranki ku kasheni da baqin ciki tun lkcin mutuwata baiyi ba
ruwan idanunwanta ta zuba masa ganin yadau abun da zafi sosai atake sai ta sauke muryanta cikin lallami tace toh shkn please tell me exctly what happen..ina sauraranka.
wani hade rai yay dacan kamar bazai bude baki ba saiya tuna cewa haseena kamar iskace inhar ta bar nan wajen ba lallaine ya samu wani cikakken dama ba gashi bayason ya kara batawa hon farida bala ranta musmn akan wnn maganar.
nan ya fara hardahada mata labarin karya dana gaskiya ya fara gaggaya mata cewa wai har lekensa a bayin gida anayi, snn yauda safe ma anzo masa dakin naked ana seducing dinsa akan gado, yace akan gado ya tarda yarta daga ita sai breziya,kuma daga zarar zata wuce sai ta gogi jikinshi, kuma koda ya tambaya tace wai takarda ta kawo ayi mata signing zataje gasa and all the threath wanda duk baigaya mata asalin abunda ya faru ba...
amfani kawai yay da abunda layla ta masa ya yi makamashi ma sharrinsa snn ya dorasa akan nur firdaus, yy hakan ne badon komi saidan yanaso ya samu wani cikakken daman dealing da layla batare da anyi suspecting dinsa akai ba kamr dai yadda hon farida bala ta umarce sa daxu.
sosai hanklinta ya tashi sai kuma ta tuna cewa nur firdaus ce fa take nemanta akan maganan saka hannu akan takardar gasa..
ranta taji ya hargitsa ya baci amma duk da haka ta nitsu, she kept asking him to be clear with the narration, tanemi sanin wayace acikin yaranta take masa haka amma yaki sam ya furta mata kai tsaye saidai yay jam'i dan ya dada rikitata,
ta inda yake fita bata nan yake shiga ba, yace abun ya jima yana faruwa turane yakai bango, kodan yace ta haihu masa shine zata bullo masa da wann salon makarcin? ko kuma burinta na siyasa take so shima ta cimma dashi? babu irin zazzafar baqaqaen magana masu rikita xuciya da bai jefeta da su ba kuma sosai ya nuna mata yay fushi
karshe ma zatay magana cikin
katseta ya mike tsaye yana huci yana hura hanci yana cewa" look woman you have only two choices, ko ki magance wann abun ko kuma duk randa ya sake faruwa zaki nemi ni acikin rayuwarki ki rasa...i love you soo much haseena but i cant deal with bull shit i cant trust u anymore.
hakuri ta dinga bashi har kamar zata masa kuka amma ko ajikin sa saima cewa yay bazai dawo gidan ba sai ta gama magance matsalar yaranta akansa dan bazasu raina masa hankli ba
zuciyarta babu dadi suka rabu...
Bayan mintoci kadan da rabuwarsun ta iso gida cikin fushi ko amsa gaisuwar mlm liman batay ba Tana sauka daga motarta ta shige cikin gidan kai tsaye, anan ta sami Layla da Nur Firdaus a zaune a kan kujerar babban falon gidan,laylah ta saka wani plain blue dress daga cikin kayan nur firdaus,dukansu sunyi wanka sunyi kyau sun saka kananan kaya..
basu hankara da shigwoarta ba sukaji dakakkeiyar muryanta akansu..
"Nur Firdaus!"
Ta kira sunanta da karfi, tana tahowa kusa da ita daf a mugun fusace
suna hade ido tace "Menene wannan abin da nake ji akan ki? kifadi min,Me ya sa za ki bullomin da wani halin banza da zai jawo min abun kunya irin wnn? what the hell is wrong with you ehhhh.
Nur Firdaus ta mike tsaye gabanta na faduwa sosai ta girgiza kai da hanzari, hawaye suka cika idanuwanta amma be hanata yin magana cikin girmamawa ba
tace mummy har yanxu de ban fahimce me kike magana akai ba,dan ba zan taba yin wani abu makamancin abunda zai sakaki jin kunya ba kema kin sani sede in mijinki yayi wata magana da baki tantaceshi ba kuma kamata yay kigayamin dan insani..
Haseena ta kalli 'yar tata da fuskar mamaki da takaici.
"kikace bantantance ba? dont u play me for a fool...akan wane dalili zai sa ya zarge ki da wannan abu inde baki aikata ba? ko shin bakece kikai masa takardan signing na gasarki yau da safe ba, nur firdaus why are u dis disgustingly desperate
Nur Firdaus ta ja numfashi mai nauyi.
tace "mummy Bani nakai masa wata takarda ba. Amma ya kamata ki tambaye shi mena aikata masa na abun kunya daya gaya maki..
Layla, tana tsaye a gefe dede nan ta yi kokarin shiga mgnan mummy pls ki saurare big sis Ni ma na san ba ta da laifi. Sadat ne kawai yake neman...
rai abace mrs hasena tadaga ma layla hannu cikin daka tsawa tana cewa "stay out of this laylah, ke babu ruwanki da wann mganan, da wann munafukar sisternki nake magana datake neman banzatar da jikinta agaban mijina, nur yaushe kika balaga da harkinsan kiyi making moves da zai ja hanklin namiji akanki? who raise u dis way amma dai bani bako??
nur tafara jin maganan na mata nauyi hawaye suka fara sauka mata sosai
"look at you ure just seventeen, dont be a shameless pretender.
toh wallh inde asiri na kikeson tonawa a duniya toh naki ne zai tonu banawa ba. sede abun kunya ya kare akanki.. domin kuwa naji duk abunda kike ma sadaat agidan nan inbana nan kuma nasan bazai min karya ba. Nur Firdaus, idan gaskiya ne ba ki da laifi, zan binciki wannan maganar sosai. Amma idan na samu wata shaida da ke nuna akasin haka, kada ki yi tunanin zan dauki wannan abu a sauki. this is my last warning to you!!! cikin wani irin zafin rai ta furta mata haka
Nur Firdaus ta share hawayenta da suma zubo mata bazata tanata kallon mahaifiyarta cikin takaici, abubuwa dayawa na mata yawo akanta amma haka ta dannesu sabida ta karantu da ilimin qur'ani tasan cewa uwa duk yadda take tana da muhimmaci sosai dolene a girmamata
cikin danne fushinta da muryan girmamawa tace toh shikenan Ki bincika mummy ai za ki gane gaskiya idan kin yi binciken ko..
Haseena taja tsaki me yawa tajuya ba tare da wata kalma ba, zuciyarta cike da mamaki da fargabar abin dake faruwa da iyalinta wanda har yanxu kwakwalta bai gama daukawa ba
jin zancen bincike yashigo ciki layla ta mike tsaye ta dan ruko hannun nur fidaus da wani irin makrtaccen muryan kuka"Big sis dan Allah kibawa mummy hakuri kawai maganan nan ya kare anan wajen please lest not dig dis things up..
mummy fa yar siyasa ce bana son hakan ya shafi mutuncinta..
cikin katseta da mamaki nur firdaus tace Idan anbincinka akasan gaskiyan ai gaskiya bazai taba bata mata siyartaba saidai ma ya dada tsaftace shi.
kirjin layla na bugawa da guilt ta dubi mummynsu da hawaye taf a idonta cikin rawan murya tace mummy kima big sis uzuri kinji she is sorry pls mummy
mrs haseena ta kalle layla tace autata ban yarda da wani uzuri ba. nur firdaus ce sanadiyyar wnnan matsalar, ta yaya zan ci gaba da tsayawa cikin siyasa idan ta ci gaba da bata min suna?
sosai wann kalman ya hatsala Nur Firdaus
da karfi tace mummy meyena taba aikatawa dana bata miki suna?wallahi ba ni nakai masa lettar gasa ba! Sadat ya miki karya ne kawai saboda wani dalili da bazan iya fahimta ba, inda kuma kinason kiyi min adalci da zaki tambayeni meyafaru da zan iya fayyace miki komi, amma is alwys like dis baki taba saurarata ba..
"Saurararki? Me ya sa zan saurare ki? Ke da kullum kike kawo min matsala? Kece kullum kike bata tarbiyyar Layla da munanan halinki, ni be gayamin direct wacece acikin ku ba, amma ni nasan kece nur firdaus kece me taurin kan, shiyasa bazan ji wata banzan bayaninki ba, ko kin tabaji ance layla tana da samari? kece kika san wann dabiar toh wallhi karki sake ki kawomin wnn abun kunya cikin gidana kuma akan mijina nagaya miki kenan..
Nur Firdaus tagirgiza kanta cikin tsananin takaici hawayenta suna kwarara daga idanuwanta sosai..
zuciyarta na tafasa tace hakane dama i am alwys wrong a idanunki mummy amma bakince zaki bincika ki bincika..
daga nan sai bata sake cewa komi akan maganan ba, wajen ya dauka da shiru. saida ta tattara nitsuwarta tashare hawayenta snn tace abu na biyu, Layla tana fama da wasu matsaloli tun da dadewa, yanxu kuma ya fara shafar lmrin karatunta, Malamanta a makaranta sun sha neman ki amma baki responding, yau G/C unit sun kirani kan cewa laylah ta dena maida hankalinta a karatunta saboda abubuwan da ke faruwa da ita a gida, inde bazaki iya saurarar matsalata ba ai zaki saurare wann tunda ita layla kince babu ruwanta.
mrs Haseena ta katse tacikin tsawa ke yarinya Kada ki kuskura ki juya maganar nan ya dawo kan layla, dan Idan Layla na da matsala, duk kece sanadi sabida awajenki ce take koyi da dukkan wadannan halayen Ba ki taba zama misali na gari ba.
Nur Firdaus ta fusata
sosai cikin kuka tace mummy ya isa haka kamar ke kin taba zamowa wata abar misali agaremu, wai Yaushe ne ma kika taba tambayarmu halin da muke ciki? Ke kullum siyasa ce a ranki, bakisan me zan iya aikatawa da wanda bazan iya aikatawa ba shiyasa komi aka fada akaina kike amincewa, nauyin kulawa da layla akanki yake ba akaina ba, ko da yake bayau aka fara barin min nauyi ba tun da baba ya rasu nauyin kaina ma nina rike. kuma yanzu kina nufi ke kadai kike da gaskiya?
gabaki daya layla ta rude ganin yarda nur firdaus tay maganan da tsananin fusata da fushi. dan abune me tsananin cin rai ko daga yanayin yadda haseena take nuna bata amince da ita ba ko kadan. kuka take mai sanyi amma kallo daya kamata zakaji tabaka tausayi sosai.
mrs haseena ta mike tsaye kamar zata rafka mata mari cikin daka mata tsawa tace "Nur Firdaus! Kada ki kuskura ki yi magana da ni haka ni ba saar ki bace. Idan har kin cigaba da irin wannan dabi'ar, zakiji mugun mamakin abin da zai biyo baya, inna zauna muku ina kula daku uwar me zaku ci? shi ubankin daya mutu milliyan nawa ya barmin? gaskiya ce bakiso, amma kisani dik abin da na gina baki isa ki rushe min ba.
a zuciye cikin kuka Nur Firdaus tace Ba ni ce zan rushe ki ba Kin riga kin bar matsaloli sun girma a idon kowa saboda kin yi watsi da mu baki da yarda dani yar dakika haifa ba, mijinki da kika aura kwanan ma yafini matsayi a duniyarki.. watan ki nawa baki tare da mu amma lokaci guda yay miki karya akanmu har kin dawo gida...
tunda kina da wnn uban lokcin, ba zan cigaba da yin miki shiru ba..i am really tired of you frustating me...cikin kuka me tattare da bacin rai sosai tayi maganan
laylah ma tafara kuka sosai.. dan duk duniya babu wacce take saurin saka nur firdaus cikin baqin ciki kamr maman nasu.
Acikin sauri Nur Firdaus ta bar wajen takoma daki ta rufe kofa da karfi ta fashe da wani sabon kuka aranta tanajin inama da mahaifinta be rasu ba. tundaga nan kuma bata sake sanin meya faru agidan ba.
wajajen karfe takwas da rabi na dare har ta yi shirin barci amma zuciyarta na kuna, haka tafasa baccin ta nemi waje ta zauna a gefen gadonta tana jin zuciyarta na motsawa cikin tsananin bakin ciki da takaici furucin mahaifyrta akanta.
tuntuni abu daya ke yawo a brain dinta shin Me yasa mummy baza ta taba saurarata ba?" Ta tambayi kanta haka yafi sau dubu ta rasa meke mata dadi,
"Me yasa duk abin da ya faru sai tace lefinta ne, meyasa mummyn su ta fi damuwa da abin da duniya za ta ce Shin ba ta damu da ita bane? ko sonta ne kwata kwata batayi, ko nadamar haifan ta takeyi, izuwa yanxu tasan itada Layla duk ba su da wani muhimmanci a gare ta amma toh meyasa???
Hawaye suna kwarara daga idanunta yayin da take tunawa da kalaman mahaifiyar tan tana jin zuciyarta yana karaya sosai, harga Allah bataso tay fushi me yawa har yakai ga ta daga ma mahaifyatan murya dazu ba.
amma ta san cewa ba zata iya ci gaba da zama cikin wannan yanayin rauni ba. ga shi an mata sharri, gashi duk lefin ance nata ne, Duk da haka, tana jin rauni saboda tunaninta cewa ko da tabar gidan taje wajen kakansu DiDi a can yola hakan bazai iya gyara matsalolin da ke tsakaninsu ba saidai ma ya kara musu wasu matsaloli.
rayuwar layla take tunawa, ta gwammci ta amshi duk wni lefin da sadaat ya furta akanta da ace ma layla mummynsun take gayawa irin wann baqaqen kalaman sabida ita kadai tasan yawan ciwon da hakan yaji mata a zucyarta.
dagata dayan bangaren mrs.
Haseena tana zaune a kan kujera tana jin fushinta yana raguwa kadan kadan Amma zuciyarta ta cika da tunani me nauyi. Shin gaskiyane abin da Nur Firdaus ta fada game da matsalan Layla akan karatunta? Ko kuwa kawai wata dabara ce don ta guji zargin da aka yi mata akan mijinta sadaat datake kkrin tay seducing?
Tana cikin tunanin hakan amma aranta tana jin cewa ta riga ta yanke hukunci "Nur Firdaus ce batada gaskiya, kuma ba za ta taba zama abin dogaro ba," ta furta a hankali. Amma wata muryar zuciyarta tana yi mata tambayar toh "Idan kin yi kuskure fa?" ......SADLY REALITYN WASU KENAN, KANAYI AMMA BA AGANI, KANA DAUKAR NAUYIN DA BANAKA AMMA DUK ABNZA, I KNW ALOT OF PPL CAN RELATE TO THIS SO COMENT AND SHARE TO UR GROUPS NAGODE
SURAYYAHMS
***