1
by @sadiyanasir
RIKON SAKAINA
YA FARU A GASKE
NA
SADIYA NASIR DAN
Arewa Book
sadiya Nasir
SHAFI NA ƊAYA
Tunda na shigo layin gidan mu idona ya sauƙa kan motor d'aukar gawa dake tsaye kofar gidan mu. Lokaci guda na rasa nutsuwa zuciyata ta soma bugawa da karfin gaske. "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'um kar dai Abba nane?". Na ambata da karfi. "Kai aa sai dai ko daga kauye wani ya mutu a asibiti za'a sallace sa anan. Zuciyata ta raya min haka. K'ara saurin tafiyar nayi bana iya ganin gaba na. Maza ne cunkus a kofar gidan wasu na alola wasu na zaune, ko wanne idan kaga fuskarsa tashin hankali zaka gani k'arara.
Ɗan rufe fuskata nayi da mayafina na fara bin bango Ina neman hanyar shiga gidan. "Allah sarki Malam Saminu, wallahi na girgiza matuka da naji labarin Mutuwar sa, jiya haka fa muna tare a masallaci, rayuwa kenan Allah kasa mu dace". "Ameen fa, wannan rayuwa idan Bawa bai ji tsoron Allah ba me zaiji? Allah yaji k'an Malam Saminu". Ɗaukewar numfashi na samu na secons kalmar Allah yaji k'an Malam Saminu na yawo a kwakwalwa ta "Na shiga Uku". Na ambata da karfi na d'aura hanuna a kai na fad'a cikin gidan mu da gudu ban ko damu da dandazon Mazan dake kofar gidan ba". Ganin Matan dake zaune suna sharan kwallah yasa nayi palon Abba da sauri. Turus naja na tsaya sakamakon kafata da suka soma rawa ganin Gawar Abba kwance cikin makara ga shakikansa suna kewaye dashi. Runtse ido nayi na sake bud'ewa don gaskatar da abinda nake gani. "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'um " Na furta na durkushe a wajen na saki marayan kuka. "Abba naaa! Abba naaa". Kalmar da nake ta furtawa kenan hawaye na wanke min fuska. "Kiyi hakuri Khadija Ubangiji yafimu bukatarsa shiyasa ya d'auke kayan sa, a yanzu Addu'ar mu Malam yake bukata ba kuka ba don girman Allah kiyi shuru Khadija". Muryar kanwar Abba ta daki kunnena. kallonta nayi ba tare da nace da ita komaiba kuma ban daina kuka ba, zan iya cewa tunda nazo duniya ban tab'a jin tashin hankali irin ta yau ba, na rayu cikin maraici na rashin uwa, Abba kad'ai nake gani naji sanyi a zuciyata yau gashi shima ya tafi ya barni?. Da rarrafe na k'arasa jikin gawar Abba na rike na sake fashewa da kuka. "Ya Allah ga Abba na ka yafe masa kasa mutuwa ta zamo hutu a garesa, Allah yasa Kiran gaggawar daya amsa aljanna ce tayi kira, Ubangiji kaba zuciyata hakuri na rashin Abu mafi soyuwa a zuciyata".
Irin kukan da nake sosai yasa tausayina ya d'arsu a zuciyar mutanen ɗaki, wanda basu kuka ma take na karya musu zuciya suka shiga zubda kwallah.
Ina ji Ina gani bayan wani lokaci aka zo aka d'auki gawar Abba don aje a sallace sa, kuka nake har murya ta bata fitowa saboda tashin hankali. Sai da na tabbatar da tafiyar gawar Abba kafin na isa gun Ƙanwar mahaifina Goggo Kubra na tambayeta meye ya kashe Abba na bayan na tafi na barsa lafiya?. Sai da ta share kwallah yafi sau hudu kafin tace. "Khadija Ina gida nayi talge zan tuka tuwo aka kirani wai Yaya ya fad'i a kofar masallaci ko shurawa baiyi ba anan Allah ya d'auki rayuwar sa, idan akace ajali yayi kira to babu wanda ya isa ya kauce wa hakan, daga ni sai zani a kirji na iso a gidan nan, Hijab din ma a baibai na sakata, tabbas anyi mana mutuwa naji tsoron rayuwa tsoron Allah ta sake shiga jikina, ya Allah kasa tafiyar gaggawa da Yaya ya amsa Aljana ce tayi kira". Ameen na amsa murya ta a dishashe. "Kiyi hakuri kinji Khadija Mutuwar Yaya Saminu ba shine yake nufin kin rasa dukkan gata ba, matukar muna raye muna numfashi iyalan Yaya ba zasu tozarta ba, kuma baza suyi maraici ba". Kad'a mata kai nayi alamar to, ta shafa kaina ta fice cikin y'an uwanta.
Da kyar na iya mikewa na shiga ɗaki na rufe da sakata na kwanta a kafita na shiga duniyar tunani, rayuwata da Abba na shiya dawo min sabo, irin kulawa da shakuwa dake tsakanina dashi ya rinka dawo min. "Tabbas bango ya fad'i". Na ambata a zahirance na sake fashewa da kuka.
Tunda aka dawo daga makabarta na tabbatar da cewa Abba na ya tafi ba zamu sake had'uwa ba sai a darul salam maraici ya dawo min sabo, abinci sai anyi da gaske nake ci banda aiki sai kuka da tunani babu abinda nake. Ranar da Abba ya cika kwana Uku a ranar shakikan Abba suka yanke hukuncin yanda za suyi da iyalan sa. Baffa Kabiru shine Babba duk gidan su Abba, shi yace zai deb'emu duka babu anfanin raba mu. Sosai kowa yayi farin ciki da hakan, da dare bayan jama'a sun watse su Baffa Kabiru suka tara mu a palon Abba, nan suka sanar da Mama Asiya wato Matar Abba hukunci da suke yanke. Sosai ta shiga damuwa nan ta soma magiya akan a bar mata mu koba Malam a raye ita mai rikemu ne, Amma firr suka ce hakan ba zai yuyuba saboda za'ayi dasu a gari, alfarma d'aya kawai za suyi mata karamar gidan mu wato Auta muhibba zasu barta a wajenta har ta girma sai su karbe ta.
Mahaifina ya rasu ya bar yara Maza guda Uku sai mata guda biyu duka yaran Mama Asiya ce ni kad'ai Mahaifiyata ta haifa Allah ya karbi rayuwar ta.
Sosai na shiga tashin hankali jin wai a gidan Baffa Kabiru zamu koma rayuwa, gidan da idan ba dole ba sai na shekara ban jeba saboda isgili da rashin mutuncin da Matar sa take mana, musamman ni da ban san me nayi mata ba ta kafa min karar tsana, ba hali mu had'u sai ta zageni ta aibanta Mahaifiyata da bata a doron k'asa, tabbas yanzu ne zan yi maraici. Kwallah na cigaba da sharewa ina mai tausayin kaina, Ashe Abba yaji a jikin sa mutuwa zaiyi ko yaushe idan muka zauna sai yace yana tausayin mu idan yabar duniya bai san waye zai rikemu Amana ba? "Allah sarki Abba na". Na ambata a hankali na share kwallah.
Kafin kwana bakwai Goggo Kubra tasa mun had'a kaf kayan mu, da zaran anyi Addu'ar kwana bakwai ba zamu kwana a gidan ba saboda iyayen Mama Asiya suma zasu d'auki y'arsu. Allah sarki rayuwa, ranar da zamu tafi mutuwa ya dawo mana sabo, Mama Asiya da kyar ta iya raba jikinta da namu kace idan mun tafi gawar mu za'a dawo dashi. Haka Baffa Munir ya kwashe mu da kayan mu a motor sa muna kallon gidan mu har muka k'ule.
Mafarin Jarabawa ta
Da sallama muka shiga gidan ko wanne cikin mu da akwatin kayan sa, Baffa Munir na gaba muna biye dashi. A kofar Babban palon gidan mu kayi arba da Hajiya Indo cikin shirin zuwa office, shekeke ta tsaya tana kallon mu na ɗan wani lokaci kafin tace. "Munir ya dai daga ina?". Fuska babu annuri yace. "Ai sai ki gafara min a hanya idan mun Isa ciki kyaji dalilin zuwan mu". Ok ta ambata ta wuce gaba muna biye da ita, a k'asa muka zauna ko wanne cikin mu ya gaisheta, babu yabo ba fallasa ta amsa ta maida dubanta gun Baffa Munir. "Ina jinka kasan office zan tafi". Baice da ita komaiba ya kira number Baffa Kabiru, ringing biyu ya d'auka Baffa Munir ya shaida mishi yana palon k'asa. Rai b'ace Hajiya Indo ta dubi Baffa Munir "Amma dai akwai rashin mutunci cikin hidimar ka Munir, Kasan wajen Alhaji kazo shine zaka dakatar dani akan uzurina?". "Kika dakatar da kanki dai, yanzu ma lokaci bai kure ba zaki iya ficewa". Hajiya Indo na shirin bada amsa Baffa Kabiru ya shigo, da farin ciki ya k'araso palon. "Ikon Allah iyalan nawa har sun k'araso? Sannun ku da zuwa maraba sannu ko?". Murmushi mu kayi gaba d'aya muka gaisheshi cikin girmamawa. Fuska a sake yace. "Indo kin sake samun k'arin iyalai, duka yaran nan zan baki amanar su basu da gidan da zasu zauna daya wuce nan, Ina so kiyi kokari wajen ganin sun shaku da sauran y'an uwan su, Allah yaji kan Saminu Allah ya bani ikon rike Amana".
"Ban gane me kake nufi ba Alhaji? Yanzu tsaban mugunta ace kaf yaran nan kaine zaka rike su? Ina adalci anan kai da ba zaman gari kake ba? Asiya da kuruciyar ta ai zata iya kulawa dasu tunda ba jarirai bane, Amma sai a tattaro a kawo min su wato ga juji uwar shirgi".
"Ya isheki Indo ahir d'inki ko da wasa, gidan ki ko gida na? Na rantse da Allah basu da gidan zama sai nan, domin gidan uban sune kuma ya zama dole ki rike su matukar kina son zaman Auren ki, wannan ae shashanci ne da rashin tarbiya, oya Khalifa d'auko kayan ku mu raka Baffan ku na gwada muku inda za kuyi rayuwa, ke kuma Khadija zaki zauna a ɗakin su Aliya". Yana gama magana yasa kai ya fice su kuma suka rufa mishi baya. Hajiya Indo tana ganin k'ulewar sa taja dogon tsaki. "Na rantse da Allah Alhaji baka isa ba ko da Bura'uba sai an kwashe gayyar tsiyar nan a gidan nan, Ina dalili? Mtsww taja dogon tsaki ta d'auki Jakarta bata ko kalli inda nake fa ta fice.
Dogon numfashi naja na bita da kallo har ta fice a palon, Allah ya gani Ina tsoron kasancewa inuwa d'aya da Matar nan, tabbas akwai Kalubale. Na saki ajiyar zuciya mai karfi. Kallon palon nayi sosai yanda ya kawatu da kayan alatu, ga gida har gida. Ina tsaka da tunani wata Y'ar matashiyar Budurwa da ba zata haura shekara Sha shida ba ta shigo hanunta rike da mop, a ladabce ta gaisheni ganin na girme mata, aikin ta soma tana ɗan rera karatun Qur'ani, a haka har Baffa Kabiru ya shigo. "Khadija tu kina nan? Ya kamata ki isa ɗaki ki ɗan huta ko? Ke Sahura d'auki akwatin nan ki haura dashi ɗakin su Aliya". A ladabce ta amsa ta d'auki akwatin muka haura tare.
Mun jima muna knocking kafin Baby ta bud'e, jikinta a jike da Alama wanka ta fito. "Laaa Khadija kece?". Murmushi nayi nace. "Nice Baby". Mu shiga to, a gefen gado Sahura ta ajiye min akwati ta fice. Fuska a sake Baby tace. "Khadija ya gida ya kuma karin hakurin mu?". "Alhmdullah Baby ya school yau ba kije bane?". "Eh kin san dake mun kusa zana Waec d'in nan damuwa ake a school d'in Amma gobe zanje". Allah ya kaimu Ina Aunty Aliya?". "Sai yamma ki ganta suna daukar lokaci suna lectures, na ganki da akwati kin zo mata kwana biyu ne?". Ɗan murmushi nayi nace. "Na dawo gidan nan tare daku zan cigaba da rayuwa". Tsallen murna Baby tayi. "Kai kinji daɗi da naji Ina Mihibba?". Tana wajen Mama Asiya itama tana k'ara wayo zata dawo". Allah sarki ta ambata ta mike ta fara neman kaya ni kuma na dafa kumatu na cigaba da aikin tunani........