25
by @surayyahms
NUR FIRDAUS...25
Arewabooks@SURAYYAHMS.
Huci me tsananin zafi Dr Simran othman take fetsarwa waje da mugun zafi ayayinda wutar tsananin kishin dake cinta arai ya sakata dunkule hannayenta waje guda batareda ta shiryawa hakan ba. kwayar idanuwanta dasuka zanca kala sukai jaa atake takafesu tarrrr akan hadadden xanen fuskar Nur firdaus batako kiftawa bare taja numfashi ahnkli kuma cikin wata irin zazzafar karsashi tace Wace ce wannan da har javeed zai zana fuskarta?
tun kan tay azaman catching breath dinta taji zuciyarta na wani irin ingizata da karfi dantaje ta gani.
acikin sauri da kasa iya danne me takeji ta matso kusa jikinta na rawa rawa tamiko yatsun hannunta dake dauke da wasu irin zukazukan expnsive transparents nails tana kokarin buɗe cikakken fuskar nur dake kan allon zanen cikin azama tana huci tamika hannunta kai harta kama farin kyallen da karfi zata jawoshi kasa tawatsar kwasam sai kuma tatsaya cakk tadena motsi sakamakon jin kakkarfan gyaran muryar Javeed mai razanarwa daya taho ata bayanta da wani irin karfin kwarjinin da yakatse ta atake..
ko iya sauke hannunta kasa batayi ba ta tsaya cak tana jiyo kasaitaccen takunsa ahnkli muryansa yake fitowa yana maganan kamar na wanda zaa karba masa...a nitse yace..
"Idan har kika kai hannunki kai, i will cut it off.
iyakar Dirar saukan kakkausar sautin muryansan yasaka taji wani abu me tsananin ciwo da zafi ya kuma daskarar da ita, duk saitaji takasa iya dauke idanuwanta daga kallon rabin fuskar nur firdaus din dake nunawa a allon zanen dake haskawa agabanta sosai wnda ko da bataga full face dintaba har cikin ranta takejin tsananin kishin yadda har javeed ya tsara kyauntan a zanen sosai.
alaka da yan mata wani baqon lamarine da bata taba sanin javeed dashi ba hasalima shi mutum ne kamar wani ghost ko aljani danme ganin sa a zahiri ma saiya shirya
kirjinta na tsananta bugawa tay tsayuwar cak awajen dan tama kasa juyowa takallesa tsaban yadda batajin kanta dede, duk wani kalubale data jima tana fuskanta awajen javeed zancen wata y'a mace bai taba shigowa cikin jerin matsalarsu ba atake sai taji kmr batama shiryawa hakan ba.
tana tsaye bata san lkcin da har ya karaso cikin dakin yazo ya tsaya daf da inda take ba, ahnkli taji jikinta yahau rawa ganin ko kallo dayabai mata ba barema yagane me take ciki dan yadda take daukar kanta kamar wata matarsa na sunna har gani take kamar hakan ne fa a zahiri.
ido ta zuba masa tanata kallonsa ayayinda murdadden hannunsa dakeda wani irin laushi da haske yamika gaban drwing board din yadada jawo farin rigartasa daya rufe zanen dashi data fara bude mishi cikin jan karamar tsaki kasar wuya yasake mayarwa mazauninsa yanamai kara rufe zanen dakyau kamr yadda yabarsa dazu.
fuskansa adan dore yadago kai har cikin ransa yaso ya tuhume simran yaji uban me ya kawota dakinsa da sassafen nan half naked amma kuma sai ya basar ya juya yay kmr zai fita dan bai fiyeson yin dogon magana da ita ba.
yana bata baya ranta amugun dagule tajuyo cikin shan qamshi tafara masa wani irin kallo me matsanancin zafi wanda iyaka mugun shakkarsa da tsoronsa datakeji aranta sune kawai suke dan danneta taciki daga irin guguwar haukar datake shirin tayarwa,
cikin kwakwalo makanta nitsuwar dole ahnkli tace "excuse me? ganin baiko juyo ba,tay rau da ido snn tace jayvee dakai nake magana"
dede nan...ya dan lumshe ido ahnkli snn yajuyo ya kalleta da gefen idonsa cikin wata salo medarsa fargaba yace "mene ne?..dan shiru tay ganin yadda ya hade rai kafincan ta sake kallon zanen daga bisani tadaga hannunta dake dan rawa rawa tanuna kan drawing board din dayar yatsarta da wani irin borin kishi a muryanta tace did u draw this??..
cikeda sanyin kasaita mai tafe da wata irin ko in kula ayanayinsa ya kalli board din kai tsaye cikin rashin kulawa yace "yes"..
..wani irin kafesa da wani irin ido tay snn tay shiru tana jiran karin bayani daga bakinsa saikuma ta tuna ba lallaine ta samuba dan "yes" is always a complete sentence a duniyar javeed mufasa.
wanni nade hannunta tay akan kirji dawani kalar big girl attitude cikin wata salo irinta kama kai da nuna abun be wani dameta din nan ba tay rau da ido tace ohh dats, very crafty. sai ta dan ja numfashi .."nd who is she kasan ta ne?..
tafara kallonsa kamr zatay kuka ahnkli takuma cewa javeed, nace wacece wann din ka zanata hala?dan shareta yay har saida yakaiga gaban wata soft chair snn yanemi waje yazauna akai calmy kafarsa daya akan daya ya kalleta da muryansa me tsananin taushi snn yace "ive started to think doctor"..tay rau da idanunta kamr zasu xubo tace" think abt what? kai tsaye yanamai darsa mata mayun idanunsa acikin nata data zuro masa yace.."macen da zan bawa zuciyata.
babu shiri gaban simran ya wani irin buga tawani juyo dakyau ta kara kafesa da jajayen idanuwanta ayayinda ranta yacika fammm da ɓacin rai zuciyarta na wani irin harbawa ta ciki tafi scnds uku tana kallon javeed amma bataga alaman wasa atattare dashi ba..
wani abu ta hadiye acikin makrownto dan da kyar ta iya daurewa cikin kame kanta snn tace "Me kake nufi da hakan? how, bangane wacce zaka bawa zucyarka ba, wani zuciyar??..kowani zuciyar kake dashi na daban wanda bansan dashi ba? ..tay minti biyu tana kallonshi amma bece mata uffan ba..ganin ba amsatan zaiy ba tawani ja numfashi me sauti sann tace "well, that is neva going to happen to us saidan inna mutu, bana duniyar, cos dis drawing girl will eva only exist in ur paintings nd not in our reality kanajina ko.
tana maganan ya katseta cikin wata iriyar sigar lumshe ido da budewa mai kashe jiki kusan akasale yace "ohhh,but she will exist..in my reality, and not yours doctor, kingane ko?
tana juyowa a fusace suka hade kwayar idanunsu waje guda yaga yadda take huci atake yasakar mata double smirk dats moreeee devilsh dan his words, ji tay kamar ta shakeshi amma bakaramin tsoronsa takeji ba cikin izza ta dan dauke kanta da wani irin fizga ta lumshe ido ahnkli taji muryansa yanacewa simi kikwantar da hanklinki "i will find her.. and duk sanda na sameta zuciyata nata ne. its a promise.
wani abu takaraji yarike mata magwaronta da karfin tsiya cikin kwaco numfashinta tay wata dakakkyar dariyar takaici muryanta yafara rawa, "jayvee enuf of ur dry jokes okay,..i am ryt here in front of you kadena min wann wasan, purnish me all you want, i will obey you, i will worship, i will do everything, sabida nasan baka kalleni bane shiyasa har kake iya tunanin wata kake hadani da wata zane, kaduba da kyau dai babu abunda na rasa ajikina javeed, my body is perfected just for you, ure mine and i am yurs,. ni bantaba yin tsammanin har zaka fara tunanin cin amanata ba...and who ever dis girl is i will surely find her and ...
idanuwansa masu cike da abun tsoro ya dago cikin katseta dashi sai kuma tay shiru cikin wani irin yanayin fixga ganin yamata kallon sama dakasa da wani irin kakkarfan izza a muryansa da alaman ba wasa yake da ita ba...
"is it me ure talking to in dis tone simran?
take taji kirjnta ya cika da takaici ta juyo zata amsashi cikin rauni, a dake ya nunata da yar yatsarsa.."bana wasa dake, meddle ur next word very carefully lady, karki sake ki furta abun da zai iya rabaki da nan gaba na taba miki wasa ne???
Wani matsanancin takaici taji ya rufeta tafara surutai kasa kasa tanacewa "Me nayi maka javeed pls what have i eva done wrong to you, me na rasa ajikina da zaka fara hadani da wata zane, are you making dis up to humiliate me??? u're just making me go nuts..this is very insulting haba mana!!!
ko kallonta baiy ba ya kyabe baki yana daga zaunen bai hankara ba tazo tawani zube agabansa tay lamoo tadan lumshe sexy idanunta tana kkrin daddana masa jakar nonowarta akan kafafunsa, ahnkli tafara nishi mai qarfi metafe da sheshekar numfashin karya tafara wani irin abu tana wani kankame mai jiki kamar wacce zata yagashi,
aranshi ya tabe baki yace dama dai kice iskanci ne kawai ya kawoki..
kallo daya yay mata kafin ya zame jikinsa da qarfi anata sannan yakureta da mayun mahaukatan idanunsa wanda suke tamkar bayajin komi in yana ganin tsaraicin mace agabansa yace simran "u need to leave. Tanata kallon bakinshi kamar mayya tasako wata murya ehm ehm ehm jayvee nide kawai gayamin matsayi na awajenka, dont u have any real feelings for me?? u won't even touch me.. har yaushe zan cigaba da jiranka jayvee kasan ina sonka sosai wallh da banasonka bazan dauki tsawon lkcina da rayuwata ina jiranka ba..lokaci yay da zaka dena min irin wnn wasar, we r not kids anymore. jayvee we need to get srious abt our future my love yakamata mu mufara maganan auren mu dis very month ko ya kace??..
tana gama rufe baki atakaice yadan balla mata harara calmy da wani irin kasaitacen nitsuwa ayanayinsa muryansa na fitowa kasa kasa yace "Aure?keda waye? simran are you okay...
..baki bude tayita kallonsa dan sun sha irin wann maganan amma kullum ahaka yake shashantarwa.
zatay magana ahnkli cikin katseta yace "simran, i dont have time to be repeating myself,..u make ur own choices, i will make mine, ni bance miki kijirani ba kinji ko?....
Tay saurin mikewa tsaye kamr zata kara matsowa kusa ya wani fixge jikinshi kamar wanda yake kyamarta snn ya daka mata tsimammen kallon da ya sata razana sosai dakanta taladabtar da kanta taja baya dashi.
fusknsa a murtuke yace "Ke, Nace kiyi waje ko sai Na saka an fitar min dake ne?
yatsun shi uku ta gani a iska yana reto, see
..3 secnds..is enuf for u, ki fita ryt dis minute kaina namin ciwo.
kallonshi taketay Duk jikinta sai yadau bari sabida wani irin zafin kai datasan javeed yakeji dashi sosai, ita kuma fa bakaramin ji dakanta takeyi ba. dangani take takai matsayin da tafi karfin walakancin daga wajen namiji koshi wayene.
lamarin javeed din ne kawai yake mugun daure mata kai despite kayan duniya da sukasha surgery a jikinta na nunawa a fili ba tay tsamnin namiji kamarsa me cikakken lafiya da kwarjini har zai tsaya agabanta ya mata tsawa batare da sha'awarsa ta motsa ba. she notice dat javeed kmr baisan ma metakyi akansa ba.
good 35yrs of her life, nan tafarajin kamar ta sulale kasa tafasa ihu mai cin rai,hawayen datake dannewa suka sauko kasa bisa kan kumatunta da sauri tareda jin rauni ta share tana dan jan ajiyan zuciya batace mai uffanba tafita daga ɗakin cikin fushi me tattare da borin kishinsa shikam baisan ma tanayi ba.
tafiya kawai take fuuu akan steps batama kallon gabanta, da takai kusada kan matattakalar sauka kasa ko ya akayi oho ta tazame timmmm
Ta faɗi ƙasa da ƙarfi tare da buge farcen ƙafarta ajikin karfen golden rail na step din daya tumbeke farcen kantin dakarfi. wani irin kara tafasa tazube kasa rike da kafartan dake tsidda jini dan saida kusan dukkan masu aikin gidan suka razana da ihunta suka yo tawajen agaggauce..
wani ihu simran takeyi
kamar karamar yarinya tanamai kwalawa javeed kira kamar kanta zai tsage tana wani irin narkewa yadda zaiji kamar wani mummun abune yafaru da ita. dan aranta ji take kamar tsawon lkcin nan data dauka tana nuna ma javeed mufasa dukkn soyayya he sumhow cares abt her kawaide bayason ya nuna mata ne a fili sabida yanayinsa na murdadden mutum.
Javeed na jinta yaja tsaki yay zamansa kamar baiji meke faruwa ata wajen ba sai dataci kamr minti shabiyar snn ya fito yatsaya daga bakin balconyn dake gefen dakinsa yana kallonta
duk tagama daukawa waizai sauko dakansa ne ya dauketa, sai ta dada narkewa. bata san shi ihun nata bane yake hatsala shi dan kwata kwata bayason jin karar muryanta dan jiya bai samu bacci isasshe ba kansa na mugun sarawa.
kallo daya ya mata kafin nan ya maida hanklinsa kan masu aikin gidan fuskansa a dore yace me kuke jira?? jikinsu na bari suka marmatso, dirin tsawarsa kawai kakeji ya karade gidan,.. yhall stupid kuɗauke ta zuwa ɗakinta mana Ku kira mata likita Bunch of nuisance!!...
gabaki daya masu aikin suka rufu akanta
..shikam yana furta hakan yajuya yakoma dakinsa kamar bashi yafito yay maganan ba
Simran dake kiciniya da masu aiki tabi bayan kofar da ido haka tadinga zubda hawayen takaici tanajin kamar mutuncintane gabaki daya yau ya zuba.
hajy mammy dake dakinta tanakan shiri tanajin muryan simran atsakar gidan suna drama da masu aiki, ko motsawa batayi ba cikin kyabe baki tace "yarinya kenan Bakiga komi ba, hmm aje yar uwarki tay tsafi ta aure min dana a matsayin qaddarar sa amma kekam wallh baki isa ba...
hakanan masu aiki suka rufu akanta aka kaita daki nan danan aka kira mata likitan gidan yazo yafara dubata dan tsaban sakalci baa wani jima da dubata ba tafara bacci dan dama baccin bai isheta ba.
Hostel:
*****
sassanyar sautin kirar sallahn da ya hudo windown hostel dinne ya sa Nur firdaus bude idonta a hankali, lkcin da ta gani ne ya sa ta wara yan madaidaitan idanuntan takara duban karamin agogon dake kan bed side drawer taga har 5:30 da dan tsalleta sauko daga kan gadon gashinta mai tsayi da cika da ya barbaje tana bacci ta kama ta hade su in a messy bun sannan ta sauko cikin sauri ta hau tayar da kowa.
bayan kowa ya farka
hostel toilet tanufa ta kuskure bakinta da mouth wash tayi maza ta tube kayanta snnan ta kunna shower tana mai sake ma jikintan ruwan dumi can ta fito daga wankar bata tsaya yin wata wata ba ta maida kayan jikinta tsaf sukayi sallah bayan ta idar ta dauko ruwan sanyi ta sha kadan sai ta mayar da gorar shima ta ajiye..,
Wani nannauyan Ajiyan zuciya ne ya kufce mata mai alaman dawowa da Ita cikin hayyacinta daga tulin lissafin datakeyi nazuwa Gidan kawunsun anjima data kwana dashi aranta yau wanda taso ace ta tattauna hakan da yar uwarta layla amma inta tuna kalar murdadden kusancin dake tsakanon laylah da mahaifyarsun sai taga duk takasa furta mata komi. hakanan ta ayyana komi aranta
ita kadai danko jadidah datake aminiyarta bata gaya mata komi daga cikin shirinta ba. as usual by 7am na safyar suka gama shiryawa, yaune ranar fafatawa ta karshe yau din kusan kowa hanklinsa nakan nur firdaus ne da kuma yadda sakamakon gasar zai kasance gobe.
tun daga daki Nur ta gama shirinta da plain hijab me tsayi daya sha karin guga yana kyalli, snn ta jawo yar jakar baya brown color datake ratayawa tasaka wata black Kimono me kauri da veil dinsa aciki da goran ruwanta sai yar man baki snn ta zuge xip din jakar ta goya abayanta snn tazura niqab dinta da socks dinta suka fito wajen karyawa, duk wani cece kucen da akey awajen duk hanklinta baya wajen dan izuwa yanxu dalibai dayawa kwaxon nur firdaus na jiyan yahanasu samun bacci. cikin su harda yar uwarta laylah da ta saba da danne nata kishin aranta.
bayan sun kammala cin abinci su hudu ita da layla da aysha da jadida suka bi zugar dalibai aka wuce da su wajen gasa...
8.00am dot ya musu a kofar babban hall din nan na general hassan usman katsina, nan kowani dalibi ya nemi waje ya zauna hall din ya dau shiru dan abun ya matukar bawa mutane mamakin yadda dalibai mata suka kwaiwayi irin shigar nur firdaus kusan ince kowaccensu yau ta sako niqabi a fuskan ta wasu harda sock irin yadda nur takeyi, ya zamto badge din schl dinsu ne kawai yake bambamce su 8.30am na bugawa aka fara gudanar da gasar cikin aminci.
wajajen karfe 10am saura yauda farin ciki hajya mamy ta dauko hanya ganin tare suka fito da jikarta javeed, infact motocinsa ne suke famar biyo nata abaya, hankli kwance har suka isa wajen gasar saidai bata lura ba tun akan hanya jeep guda daya ya zame daga cikin convoy din yay hanyarsa daban.
bata tashi sanin javeed baya tare da su ba harsaida suka isa bakin hall, bata wani ji dadin haka ba amma hakanan ta dauke kai dan tasan tsabgogin javeed bare shi baya neman izini awajen kowa, nan ta shiga cikin hall aka kaita har wajen zamanta acan sama wajen manyan manyan baki ta zauna a spot dinsu na familyn mufasa
tanamai saurarar gasar wanda yauma kamar kullum an baza fasaha da basira na karatun alqur'ani. inda nur firdaus tay wani sabon ficce bawai dan tafi kowa zaqin murya ba saidan iya lura da kuskure da gujewa memeci da kuma sanyin nitsuwa.
an dauki lokaci me tsawo ana fafatawa babu wani hutu me yawa sabida yaune karatu na karshe, zaa tashi daliban by 5pm sabida a fara shirin rufe program din akan lkci musmmn ma da an gayyace manyan mutane....
tun farawarsu hajy mammy takasa gane zuciyarta dake rooting wa nur firdaus dan ko kirar sunan nur akayi a hall din sai kaga hjy mamy tasake zabura takasa kunne wajen sauraron muryanta dan haka kawai taji yarinyar ta mugun shiga mata ranta bana wasa ba. hanklinta gabaki daya ya zamto yanakan nur firdaus shikuma jikarta javeed acan Allah Allah yake ya kammala abunda yakeyi sabida yaxo wajen domin kar kakansan tay fushi dashi koda ma bazai jima ba dan aynxu ita kadaice a duniyarsa baiya iya bata mata ranta.
da yammacin ranar around 4:30pm jirginsa daya lula dashi fadar shugaban sojin kasar ethiopia ya saukeshi a kaduna yauko wani hutu bai dauka ba kai tsaye cikin gaggawa ya isa wurin gasar Qur’ani ana saura baifi minti goma a karkare ba, lkcin daga wani dalibi me tsananin kwaxo sai ita nur din dasuke kkrin yin final recitation
shida securities dinsa suka shiga daga baya batare da kowa ya lura da shigowarsu ba dan already Anriga an fara final recitation for the day...
seat guda biyune tsakaninsa da body gurds dinsa subiyar duk sun saka bakaken kaya, yana zama yadan lumshe idanuwansa yanamai saurarar muryan dalibin ayayinda yafara tuna yadda mahaifyrsa ta zamo malamar qur'aninsa ta farko a duniyan nan.
duk da yanayinsa na dakakken mutum da bazaka masa zaton akwai digon yaranta atattare da shi ba, but der is dis frail childish wish najin cewa hala da ya rayu da mum dinsa da shima yay wann gasar qur'anin kodan ya sakata taji dadi snn tay alfahari dashi.
har wann dalibin ya kammala karatunsa javeed bai dawo daga duniyar tunanin mamansa ba face saida wata strange Sautin karatu mai tsananin sanyin daɗi da sanyaya zuciya da ratsa gangan jiki yahau tasashi ayayinda nur firdaus tafara karanta ayoyin da aka ja mata cikin matsnancin nitsuwa da sanyin kulawa.
kwarjinin dake cikin muryan nata is serene enuf to summone the assembly of Angels...
sanyin rahama dake tattare da coolness din muryan nata daga tafara karatu sai kaga wasu suna hawaye wasu kuma tsigar jikinsu ne yake tashi sabida yadda take saka qira'arta a nitse yana kuma nuna lallai tasan ma'anar abubuwanda take karantawa acikin wata sanyin nitsuwa .
ji yay komi nasa ya tsaya cak dan Muryar nan...ya dada lumshe ido, jin sautin ta ya hanasa cigaba da zanta komi a brain dinsa, Wannan murya ce da ya riga yafarajin kamar ya saba da ita a cikin tunaninsa na kwanan nan.
suratul tawba in the most amazing way, sihitarccen ajiyan zuciya yay ya furta "Subhanallah."acikin kokon ransa jin yadda Muryar take ratsa shi kamar iska mai sanyi yanakuma jin yadda kalmomin nata suke ƙara nutsar da shi cikin wata irin duniyar tunani harma baisan ta gama ba saida yaji anyi kabbara me dan karfi, ahankli yabude lumsashen idonsa ahankli ya jefasu akan nur firdaus dake killace acikin niqab kirjinshi yaji ta sauya bugu saiyaga duk wanda suka saka niqab dinma bai musu kyau kamar yadda ya mata ba.
sumtin strange and alluring is all over her
acikin dakikanin secnds ya gama karkare mata kallo
altho he didnt get to catch her name in a wit, sabida bason wann yanayin saka idon yakeyi ya sabar masa ba amma babu karya yasan yarinyar national treasure ne.
Bayan an karkare kammalawa tun ba afara fita ba shi ya mike kai tsaye yafita, a gaban motocinsa ya tsaya tare da saurin kaucar da tunanin yarinyar aransa kwata kwata dan baiga amfaninsa ba, baiwani jima da fita ba Hajiya Mammy ta fito itama tana murmushin jin daɗi ganinsa aranta sosai, yau tunda suka kamo hanya hirarta kenan, ta kira masa sunan nur firdaus yafi sau ashirin cikin labaran nata datake bashi amma tsabar hanklinsa baya kai ko sau daya bai kama sunan a ransa ba saidai ya kalli kakarsan ya murmusa kadan, dan aransa yakanji kamar each time taje wajen gasar nan she misses his mum soo much kawai danne baqin cikin abun takeyi shiyasa take wann xumudin duk wani labaranta shide baiya cewa komai har suka koma gida.
ata bangaren nur firdaus kuwa ana kammala sallamarsu around 5;20am bayan sun dawo cin abinci a cantern layla da aysha already sunyi plan zasuy sneaking suje gidan antyn ayshan agari dan su kwana acan sabida amusu kwalliyar da zasuzo wajen final ceremonyn gasar gobe dashi, dan laylah tanaji ajikinta kamar Adnan zai iya zuwa a goben yay ma nur firdaus surprise tunda ya saba mata hakan, kuma tasan nur bata damu da make up ba ita kuma batason azo aganta ahaka, tana so tay kyau sosai koda adnan zai kalleta, shysa ta nace zata bi ayshan su kwana acan dan shigarsu yafi na kowa daukar hankali.
golden brown abaya me matukar kyau da akayishi duwatsun pearls da nur firdaus ta dinga ajiyewa akan zata saka agoben shi laylan ta dauke ta saka ajakarta aboye dan tasan ai nur bazata ce komi ba saidai tay hakuri ta saka wani..
yau jadida ita kadai ta koma hostel tana kkrin kimtsa musu kayansu dan goben duk zasu watse anata shirin hidiman goben kowa hanlkinsa baikan kowa
wann yanayin ne yabawa nur cikaken dama tazame tashiga washroom tacire hijabinta da niqab din ta maidasu jaka snn ta zaro black colour kimononta me kauri daga jakar ta saka takara wanke fuskarta da ruwa snn ta goga man baki dama itadin ba maabociyar son yin kwalliya bace, ta kofar bayan cantern din ta zille batare da kowa ya lura ba tadinga tafiya hartakai kofar fita after few mins ta samu me adedeta tace mai yakaita GRA Barnawa, dake bawani nisa suke da wajen ba within 14 minutes sai gasu nan a anguwa ta zaro dari biyar a jakarta ta bashi ya bata canji sann ta kama hanyar gidan kawun nata dake can karshen wata layi.
manyan gidajen masu kudine awajen nagani na fada gashi yamma yarufa anguwan ya dada daukar shiru ahnkli cikin nitsuwa take tfiya kowani step sai taji kirjinta na kara bugawa, dan rabonta da nan wajen tun tana yar shekara biyar da sukazo ranar bikin sallah tare da mahaifinta alhj haroun ciroma. she rmbr clearly how fun it was, da yadda yan uwansa suke mugun sonsa, shidai baban nata bamai yawan son wasa bane amma yana da sanyin zuciya da tsananin haquri bata taba ganin abokin gabarsa ba.
duk sai tarasa yadda akay mumynsu take cewa yan uwansane suka cutar dashi musmn ma shi kawun nasu alhaj Abubakar ciroma wanda asaninta sunma fi shakuwa da mahaifin nata.
ahnkli take matsowa ayayinda early childhood memories dinta sukadinga dawowa mata kai har takai kofar wani tangamemen mansion me dauke da doguwar black burglar gate da kuma katoton katanga an rubuta A1091 ajiki.
saida tay tsayuwar minti biyu tanai karewa kofar gidan Kallo snn ta karaso jikin gate din ta fara buga bell din ahnkli, wani shiru kakeji with no answer harta gaji ta saduda tafara tunanin ko zata koma hostel kawai. idonta nakan mansion din ta kara gyara zaman jakarta dake rataye akafarda anitse ta juya kenan zata bar wajen sai caraf taji karar gate din na buduwa dakansa ahnkli batare da taga kowa dake budeshi ba. tsayuwar cak tay tana kallon ikon Allah, har gate din ya gama bude kansa cos it took her a minute kafin ta fahimce cewa is an automated gate hala daga security control room aka danna remote ya budu mata bayan sun gama tantace ta da cctv camerarsu ta ciki aikuwa tana daga kanta can sama ta hango cameran a manne akanta like a bird bazaka ma lura ba kyabe baki tay cikin sauke wata ajiyan zuciya tashiga cikin gidan da yar kwarin giwa atleast yanxu dai tasan ansan da zuwanta. she left here since wen she was 5yrs old aranta tanata lissafi da kokonton hala sun manta da ita komasaita sake musu bayanin kanta shiyasama tazo da hoton babanta ajakarta.
cikin gidan nada wani irin girman da bazan iya kayyade shi ba, wasu irin manya manyan sashe ne aciki masu kalar fenti irii daya wanda daga ganin tsarin gidan kai dakanka za kasan naira ya zauna.
dedekun masu aiki sanye da blue uniform dake shawagi anan tagani cikinsu babu wanda ya kulata itama hakanan batace musu uffan ba kanta na kallon kasa take tafiyarta har takai katoton kofar mai mansion din
batare da daga kai ba
Bayan ‘yan mintuna da tsayuwarta a bakin kofar wani security ya tabbatar da sunanta, snn ƙofar ta buɗu nan ta haɗu da wata me aikin gidan da ta jagorance ta har cikin babban falonsu da ya sha ado da manya manyan kujeru na zamani parlour ne mara tarkace amma yamugun haduwa yadda aka tsarashi wallpaper ne baqi mai zanen roseflower ja da baki zagaye da bangon daga tsakiya kuma akwai bakaken kujera masu L shape da throw pillows dinsu jajaye wanda suke manya manya saidan karamin round Table da ke gaban su da Wani sharbeben tvnsu dayakusa cinye rabin bangon...
Wani kamshi ne mai mugun dadi ke fitowa daga falon na turaren halut da sandal wood traditional incense hade da iskan Ac mai dadi da sanya nitsuwa.
nur firdaus tana shigowa mai aikin data bude musu kofa ta taho da Murmushi a fuskarta a ladabce tace "'Sannunki da zuwa hajiya Please come with me..
Nur tadan murmusa ta kalleta ayayinda tayi musu jagora suka karasa daga can ciki, Wani bene mai golden rail suka bi suka sauko daidai setin dinning area mai dauke da dogon dinning table shima dark colour with little touch of red Wanda Already an kawata kan dinning table din da manyan kwanuka na alfarma wajen ya karayin haske sabida crystal chandelier dake sama ta tsakiyar su yana fidda wani uban haske...
Haka kawai atmospher gidan yayi ma nur firdaus dadi yakuma samata Wani sanyi a xuciyarta cos being around family wani abune da uwarsu ta riga ta datse musu shi aryuwrsu kwata kwata.
tana daga tsaye tunda bata motsa ba sukaji karar sautin tahowar mutum tana daga kai suka hade ido da kawun nata wanda mamakin ganinta yagama rufesa bakin sa bude yace "Nur firdaus mashaaaa Allah, Alhamdullhi!..Nur ta danyi murmushi ta saukar da kanta kasa. cikin sauri Alhaji Abubakar Ciroma ya karaso da wani irin murna ayanayinsa tana dan satar kallonsa dan shidin Dogon mutum ne mai cikakken girman jiki gashi fari sol da sumarsa baƙi sumul irinnna babanta kallo ɗaya zaka yi masa ka san arziki ya ratsa jininsa bana wasa ba cikin matsanancin mamaki da shaukin ganinfa ya karasa saukowa kasa da murmushi yana faɗin
"Nur Firdaus? wann ba nur firdaus din mu bace?? take kuma sai idonsa ya cika da ruwan hawaye masu zafi..
raunataccen murmushi ne ya suɓuce mata tare da gyara zaman gyalenta ta dan rusuna gabansa da ladabi tamasa sallama muryanta na rawa sann tace ni ce baba dan batayi tsammnin zai ganeta da wuri haka ba.
rikota yay ajikinshi da wani irin shaukin farinciki a muryansa yace yah Allah nagode maka, i knew dat one day u will find ur way and come my doter. wow wow look at you "Masha Allah! Nur Kin girma! dubeki Kin zama wata kyakykwar budurwa..
hawayensa dayaketa dannewa suka sauka
hannunta ya jawo jikinshi har na rawa tsabar murna Sai da suka zauna akan wata chair sannan ya fara share hawayen ya ɗaga wayarsa yahau kirar matarsa ta farko tana dagawa yace ke Hajiya Sa'adatu kifito marmaza kiga wani abu,.wacce ba jimawa ba tafito sanye da wata tsadadden riga da zani na blue shadda data sha aiki kanta a rufe da mayafi suna hade ido da nur firdaus tunkan yay magana ta taho ta gudu ta rungume Nur Firdaus din sosai tana faɗin "wayyo Allah, Masha Allah Nur firdaus??..kece yau agidan namu, A'a, kin girma sosai , masha Allah, Allah ya albarkace ki yar nan lale marhaba kai amma naji dadin ganinki. Bayan nan Nur bata kara samun wani hutu wajensu ba tsaban bada haquri da uban tambayoyi akan rayuwarta dana layla data sha. anan ne ma nur din takeji yadda mummynta tay ma yan uwan ubansun tijara snn takaisu kotu tace araba alaqarsu da ita. suna tsaka da hirar sai ga nan Hajiya Bilkisu, matarsa ta biyu da ta fito daga ɗaya ɓangaren cikin wata shigar abaya mai launin ruwan madara. itama tana zuwa ta hango tsabar kamnin nur firdaus din da na mahaifinta alhah haroun dan akwai hotonansa agidan, a ladabce suka gaisa dukkansu babu wanda bai yaba ma kokarinta na zuwa nemansu ba zuciyar nur cike yke da nuna godewa Allah da irin kyakkyawar tarbar da aka yi mata dan kusan kowa acikinsu zumudi yakeyi akanta.
musamn ma kawunta alhaj abubkar wanda duk dayana fama da baqin cikin tarkon da haseena ta kafa musu ta rabashi da yayan dan uwansa ganin nur firdaus ayaudin yasaka yadingaji kamar yasakata acikinsa dan tsabar farincikin dayaji..
oder na musamn aka kara bawa me aiki aka dada kara cikowa da abubuwan kwamulashe aka sake shirya musu dinning table din da kyau.
a tsakiya suka sakata da hirararrki kala kala har aka kira sallahb magrib alhaj abubakar din yabarsu ya fita masallaci, uwar gidan nasa hajiya saadatu ce ta jawo nur firdaus suka haura sama dakinta anan tay sallahn magrib har da isha bayan sun idar ta mammata nasiha akan rayuwa ta kuma tabbatar mata cewa su basu gujesu ba mahaifyartan ce tay duk wani abunda zatay dan ta nesanta su dasu kuma abune daya shafi siyasa, zubar da mutunci, da kuma doka me tsanani sabida haseena ta riga ta kirkiro wasu shedu masu nauyi akan yan uwan mijinta a kotu.
Nur dai batacewa komi amma already ta riga tasan halin mahaifyarta dan haka abun be wani dameta ba, kawai de yadda aka tarbetan ne cikin tsananin marmari da nuna soyayya yasataji wani iri aranta dan tasan da kawunta yana cikin rayuwarsu hala da bazatay kewar mahaifi a duniyarta sosai ba.
daga dayan ɓangaren gidan kuwa wani shantamemen dakine me matsanancin kyau wanda kallo daya zakamai kasan dakin yar gatace wanda iyayenta suke mugun ji da ita dan duk wani abuna kyale kyale akwaisa a dakin komi is Dark pink or peach hatta babban gadonta an lulluɓesane da bargo mai launin peach, wata yar matashiya ce wacce bazata wuce 24 yrs ba azaune agaban madubi wanda kallo daya zaka mata kasan takai makura wajen wayewa da kuma ilimin boko cos class and levels is screaming all over her.
zaune take agaban madubi akasaitance doguwace me wani faffadan hips gwanin shaawa, gashinta kuwa dogone har gadon baya, fatar ta is silky smooth laushi tamkar anwanketa a man zaitun.
A hankali tabuɗe manyan idanuwanta masu sheƙi tana miƙa hannuwa zuwa ga kan dumb waiter daya kawo mata abunda tafi kauna a duniyarta wato coffe. kaf duniya inka cire bacci, coffe da shopping RAZIA ABU bata damu da komi ba. cos she alwys feel like she cant live witout these 3.
acikin mugun yanayi na daukaka da cikakken kwalisa take daukar kanta aynxn tana ajinta na karshe kenan a law school England, amma wann duk be darata ba dan babban burinta a duniya shine taga tazamo wata babba kuma shaharriyar jarumar film ko fashion super model a london koma dukansu biyu. shiwann karatun law din datakeyi kusan ince na dolene kawai takeyinsa badon son ranta ba saidan ta faranta ma mahaifinta ransa sabida yaki sam ya amince mata akan nata burin na zama yar film kuma model wanda har yau ji take bazata taba hakura dashi ba.
kusan rayuwarta gabaki daya a london takeyinshi, hutune yake kawota nigeria sama sama shidinma sai an takurata sabida she alwys think her parents are too traditonal sunfiyeson abubuwan gargajiya wanda already yayi hannun riga da yadda ta tsara nata rayuwar.
Dan duk wani abu dayashafi iya daukar wanka kyau, kwalisa, iya magana, kwarjini da sarauta awajen ya mace saidai shedan yaja baya ya bawa Razia kujerar zama.
despite being a top law student in england amma daga taje hutu london inda gidanta yake bata hutawa zakaga tana shiga lungu da sako wajen gogaggya da manyan world class beauty cougars and gays da barronesses just to update her feminine power and luxurious fashion sense.
tana zaune tafi minti talatin a Gaban babban mirrornta da ya ɗauki cikakkiyar surarta da baida maraba dana Dr simran othman waziri sede ita razia nata bountiful bodyn natural babu surgery ko kadan ajiki,everything abt them is almost perfect face jarkar nono dayaso ya dan musu yawa.
kullum razia tazauna agaban madubi ta kalle kanta sai ta tuna yadda jikintan yay matukar dacewa da irin dream din ta zabar makanta, dantana mugun mugun ji da kyaun fuska da kuma tsarin dirin da Allah ya mata bana wasa ba.
kwalliya tay me mugun daukar hankli kai bazakace bacci zataje maka ahaka ba slow and majestic ta mike tsaye tana cewa "Ohh my God! I’m hot!" Ta faɗa tanadada kallon hip dinta daya kara fitowa sosai.
bayan nan ta tashi tsaye ta shiga walk in closet dinta after few mins ta dawo sanye da wata designer pink doguwar rigar bacci wacce ta mannu da dirin jikinta sosai, komawa tay tazauna akan chair din mirron tanajin kasala ajikinta sosai dan batajin tana da bukatar sauka kasa ayau bare kuma taci abincii.
bayan ta gama shafe tsadadden turarenta original tom ford me shegen qamshi Ta kara juyawa gefe da gefe guda tana kallon yadda faffadan hips ɗinta ke motsawa a cikin madubi..
dan kadan ta rausaya tay wani irin run way cat walk in two steps snn ta juyo tay wani murmushi tace Nifa super star ce!! marilyn monroe of this era, haaaaa
,..Wallahi, ni dai bazan biye wa Baba wann karon ba, Ina son yin film kuma inson na zama babban supermodel, naga na taka manyan titunan fashion a duniya just like yasmine ghauri, gigi hadid, bella hadid, kendell nd the iconic naomi campbells.
dariya me sanyi tay kafin nan taɗauki wayarta ta duba wasu hotunanta data dauka tana turawa house of liberty fashion academy london da suke famar online auditioning tana murmushi,ta san dai duk yadda akayi wata rana zasu amsata kuma daga zarar an kirata tasan babu wani abunda zai iya dakatar da ita daga zuwa london domin achieving dreams dinta face mutuwarta.
tana aje wayar tahau kimtsa doguwar bakin gashinta da ribbon ta ɗaura shi a ƙeyarta wanda Daidai lokacin ne wata ‘yar aikinsu ta leƙo..a ladabce tace "ma'am, hajiya tace ki fito wai akwai baƙuwa yau a gidan.
ahnkli razia ta juyo ta kalle me aikin acikin tattalin kai tana daddana soson powder akan fuskarta lighty tace "Baƙuwa?"
mai aiki ta gyada kai
razia Tadan ja tsaki ta ajiye soson powder toh Wacece kuma da har sai ankirani naganta?"
kallo daya tama me aiki tace me sunan bakuwar?
mai aikin tace ranki shi drankiadi naji kamar ana ce mata Nur Firdaus.
Ta ɗaga gira sama da mamaki. "Nur Firdaus? its sound familiar amma dai duk tamanta Waye hakan
"ahnkli ta lumshe ido cikin kyaɓe baki tace Toh you can leave, kijje kice ina zuwa. Tana faɗin hakan ta ɗauki wata arniyar kimono mai taushi ta saka saman rigar baccinta sannan taɗora ɗan kwali dan daidai tafito tana takawa ahnkli kamar bazata taka kasa ba.....
#SURAYYAHMS
***
oya naaa, COMENTS, AND SHARE UR constructive VIEWS LETS KEEPWAKE THE HOUSE...❤️❤️❤️